Showing 21001 words to 24000 words out of 55823 words

Chapter 8 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

37

Suby ido,duk da tana bacci amma farin sanin da ta yi mata yasa tana iya hango zallar damuwar da ke ƙunshe a ruhinta.Ta lumshe ido tana jin ya zama dole gobe su tafi wurin Uncle Suhail,domin kuwa tsugunne ba ta ƙare musu ba.Cike da tunani iri-iri ta samu bacci ya ɗauke ta mai cike da mafarkai iri-iri kamar yadda ta saba.


Suwaiba
A hankali na soma ware idanuna da nake jin sun yi mini nauyi .Sanyin ac haɗi da ƙamshin da ya ziyarci hancina su suka tabbatar mini a inda nake kafin kuma ƙwaƙwalwata ta tariyo mini abin da ya faru.Da sauti na yunƙura na tashi zaune,sai na ga ƙafata naɗe da bandeji ga kuma Ubaidah a kwance tana bacci wato gadina ta tsaya yi.Na saki ɗan murmushi tare da furta kalmar da ko kaɗan ban taɓa tunanin za ta sauya ƙaddarar ƙawar tawa ba.

“Allah ya kula da lamurranki fiye da yadda kike kula da ni,ya so ki ya ƙaunace ki,ya wanke miki duk wata damuwa da ƙunci,kamar yadda kike ƙoƙarin yi mini” sai kuma na miƙe a hankali ina ɗingishi na buɗe frigine sai dai babu komai a ciki sai mangoro da madara,ni kuma ƙishi nake ji.Wannan yasa na fita na sauka ƙasa tare da nufar kitchen,falon yayi tsit babu motsin komai an kashe fitilu sai hasken da ya keto maduban ƙofa ya shigo.

Na san komai na gidan wannan yasa ina shiga kitchen ɗin na kai hannu ga maɓallin wuta zan kunnawa amma sai na ji wani hannun a kai.Wani uban ihu na buɗe baki da niyyar ƙwalawa na ji an toshe mini baki,tsoro da firgicina sai suka ƙaru dandanan numfashina ya fara bazaranar ficewa.

“Ni ne” na ji muryar Ya Ubaid ya furta a slow yana mai janye hannunsa da ya toshe bakina da shi.A take na yi ajiyar zuciya ba tare da na ce komai ba na sake yunƙurin ƙara kai hannu na kunna wutar nan ma ya tare ni yana cewa “kar ki kunna” kallonsa na soma yi ta cikin duhun wanda yake sharara ba mai ƙuna ba.A hakan na iya gane babu riga a jikinsa,ƙila kuma shi ne dalilin da yasa bai so na kunna haske.

Kamar wata yarinya mai koyon magana bakina ya soma rawar furta “ruwa..so..in sha” shi ya buɗe frigine ɗin ya ɗauko ya bani gora ɗaya,na buɗe ina ƙoƙarin kai bakina suka zubar mini a jiki wani sanyi ya ratsa ni na ja wata irin doguwar ajiyar zuciya kafin na soma shan ruwan.Kamar zan mutu idan na sauke gorar haka nake ji, wannan yasa ban cire ta daga bakina ba sai da na shanye su tasss shi kuma yana tsaye yana kallona.Gorar na miƙa masa ya karɓa,na ce “na gode” sai kuma na juya na barsa nan.

Na hau step ina takawa a hankali,jikina ya bani ana kallona na dubi ɓangaren kitchen inda yake sai dai ban iya ganinsa a yanzu.A haka har na ƙarasa ɗaki na zo na kwanta kusa da Ubaidah don ban saba kwanciya kan kujera ba.Ko kaɗan bacci ya kasa ɗaukata,sai tunanin Ya Ubaid nake yi da dalilin da yasa ya fito a wannan yanayin .Sai kuma na tuna shi ne ya kawo ni nan gidan,ga shi kuma na yi bacci cikin motarsa.Na waro ido wani tunani na shigo mini,na miƙe da sauri tare da tayar da Ubaidah ta ware ido tana kallona.

Da sauri cikin rawar murya na ce “ wa ya kawo ni nan ɗakin?”
“Ya Ubaid” ta bani amsa tana mai mayar da ido ta rufe,na ƙara jijigata ta tashi ta ce “me?”

“Gaske shi ya ɗauko ni ya kawo nan?”

“Eh! Me aka yi?” cike da takaici na ce “oh ba a ma yi komai ba kenan?”

“Suby bacci nake ji don Allah ki bar ni” ta furta tana mai juya mini baya.Tashi na yi na wuce bedroom ɗinta,wayata na ɗauka da na duba sai na ga baƙuwar lamba a ciki kuma ya gabatar mini da kansa.Mayar masa na yi da saƙon babu jimawa shi ma ya maido nan muka shiga yin chating, kasancewar shi ɗin mai barkwanci ne babu wuya na ji na saki jiki da shi .Ya tabbatar mini yana asibiti a can zai kwana,wasa-wasa sai ga shi har an soma kiran sallar asubah muka yi sallama na je na yi wanka haɗi da alwala na fito.

Na buɗe drower Ubaidah ina mitar yadda duk kayanta sun matse ni ta shigo,cikin nata haukan ta ce “wa ya ce ki zama ƴar lukuta ai ga irinta nan”

Na ce “ai dai irinmu ake yayi”

Ta ce “oho dai je ki ga yayin,in kika yi aure babu wata soyayyar turawa yo wane ɗan banza ne zai iya ɗaukar ki lukuta da ke”

Cike da jin haushi na buga mata doguwar rigar hannuna da na ɗauko ina cewa “shi ne kuma Ya Ubaid ya iya ɗauka ta?”

Tana dariya haɗi da nufar toilet a guje ta ce “shi ai soja ne,ko kuma sai in shi za ki aura”

Cak na tsaya da ƙoƙarin binta na dake ta ina juya kalmar sai in shi zan aura.Ta shige toilet ta bar ni da abin duniya,dakyar na iya watsar da tunanin na saka rigar na zo na yi sallah.Bayan na gama kan bed na haye tare da yin shiru ina mai ci gaba da tunanin maganar Ubaidar,ta zo ta hau gefen gadon tana cewa “kar ki koma bacci Malama don wallahi na samu labarin yau za a yi mana jarabawar bazata kin ga tashi mu ƙara duba takardunmu ”

“Wane malami?” na tambaye ta a sanyaye.
Ta ce “malamin lissafi mana ai kin san halinsa” ban ƙara cewa komai ba na miƙe muka shiga dubawa ɗin.Ƙarfe bakwai saura muka ƙara yin wanka ta bani uniform ɗinta ɗaya na saka,sannan muka sauko ƙasa.

Ammy muka ga ta shigo da dukkan alamu fita ta yi,a tare muka gaishe ta kafin ta ce “bari na je na kira Ubaidullah ya fara kai mu wurin addu'ar uku kafin ku wuce makaranta.

A ta ɓangaren Ubaidullah kuwa ,sam bai samu baccin kirki ba ga shi kuma bawan Allahn ya ƙi yarda kan cewa ya kamu da son Suby.Wannan rikici na tsakanin zuciyarsa da tunaninsa su suka haifar masa da ciwon kai,duk da ya yi wanka abin ba sauƙi.Wuraren ƙarfe huɗu na dare ya fito kitchen don ɗauko ƙanƙara saboda frigine ɗin ɗakinsa iya sanyi kawai take saka ruwa.Bai daɗe da shiga ba ya ji bugun zuciyarsa ya sauya,a hankali ya ɗan leƙo kuma sai ya hango Suby na ɗingishi .Ba zai iya fita ba don hasken falo ya fi na nan ɗin yawa wannan yasa ya tsaya har ta zo,kamar ya san kuwa za ta kunna ƙwan lantarki in ta shigo shi yasa duk ya ɗauki wani mataki.Ba ƙaramin jin daɗi yayi ba da Allah yasa ba ta gansa a wannan yanayin ba,ƙanƙarar ya ɗauka ya tafi bayan ya tabbatar ta gama shigewa.Cikin wani towel mai taushi ya saka ƙanƙarara ya dinga ɗorawa a kansa,a sannu a hankali ya soma jin dama har bacci ya ɗauke shi.Kiran sallar asuba ya tashe shi,bayan ya dawo daga masjid ya shiga ɗakin motsa jiki sama da awa ɗaya kafin ya fito ya je yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya amma bai saka hulla ba.Yana fesa turare Ammy ta soma danna ƙarar rawar neman izinin shiga.Wayoyinsa ya ɗauka da kuma agogonsa ya zo ya buɗe,cike da girmamawa ya gaishe ta kafin su juyo su yo ƙasa.


Ubaidah ta ce “ma sha Allah tubarkallah yau ka fito sak ango ”

Kaina na ɗaga ina dubansa cikin wata fitinaniyar farar gizner da ƙyallinta da zubin ɗinkin da aka bazama mata suka haɗu suka fitar da kukan kuɗi.Agogon hannunsa yake gyarawa kafin a hankali ya ɗago idanunsa ya sauke su cikin nawa,zuciyata ta soma rawa nan take babu shiri na sauke idanun ƙasa.

“Ya Ubaid ko ɗaurin aure za ka je?” Ubaidah ta sake faɗa.

“Ba ki iya gaisuwa ba sai shegen surutu” ya furta yana dungure mata kai kafin ya ja kujera ya zauna.Ina jin idonsa a kaina amma na ƙi ɗagowa,ga shi ina son gaishe shi amma ina tsoron ya ce don na ji ya yi wa Ubaidah ƙorafi ne.

“Ya jikin?” ya furta cike da nutsuwa,sai a lokacin na ɗago a hankali na dube shi tare da buɗe baki dakyar cikin sauti can ƙasan maƙoshi wanda na tabbatar bai ji ba sai dai in yanayin motsin laɓana ya duba.
“Da sauƙi”

“Ubaidah ya na ga kin bar ta za ta je makaranta?” ya furta yana mai soma cin abincin da Ammy ta zuba masa,ita na kalla ina jiran amsar da za ta basa.

“Muna da jarabawa ne ” ta basa amsa kafin ta zuba mana abincin mu ma,sai dai wani abin mamaki kasa ci na yi a gaban Ya Ubaid wai kunyarsa nake ji.
Juyin duniya ko ruwa na kasa sha,sai wata ƙaramar kula da Ubaidah ta saka ƴar aiki zuba mini nawa a ciki.
Duk fitowa muka yi, Ammy ta shiga motar Ubaidullah ni kuma ta Ubaidah.Kamar yadda ta ce za mu je can gidan makokin haka muka yi,muna fitowa da Hassana idanuna suka fara yin tozali tana tsaye sai raba ido take yi kamar mayya.Yadda ta yi wani murmushi tana mai fitowa waje gaba ɗaya shi yasa na juya domin ganin abin da take kallo har ya saka ta farin ciki haka,Ya Ubaid na gani wanda ke gaisawa da Abbanmu.

“Mu je mana ko ba ki iyawa na ɗauke ki?” Ubaidah ta faɗa ,na ɗan harare ta kafin mu wuce ciki Ammy na take mana baya.Yau ma cikin ɗaki muka shiga,har ina shirin zama na tuna na shanya pant ɗina a can uwar ɗaka sai na je na ɗauko shi .Ganinsa na yi a yage,cike da takaici har zan jefar sai kuma na riƙe shi a hannu.
Mamu ta zo muka gaisa kafin ni da Ubaidah mu fito don lokacin shiga aji ya kusa.Muna isa bakin mota sai ganin mutum na yi a gabanmu,ya dube ni ya kai kallonsa ga ƙafata wacce na saka silifas kafin ya dubi Ubaidah ya ce “ki kula dai da ita in kin ga wata matsala ki kira ni”

“To in sha Allah ” sai kuma ya buɗe mini ɗaya ɓangaren,cike da mamakin abin da yayi ɗin na dube shi ,laɓansa na gani sun motsa amma ban ji sautin ba.

“Ki kula da kanki sosai” shi ne abin da suka bayyana mini.
Ya rufo mini ƙofar kafin ita kuma ta soma tuƙin ,tana mai cewa “Subyna wani abu nake gani a idanun Ya Ubaid da zai tabbata haka tabbas da na fi kowa farin ciki”

Yi na yi kamar ban ji ta ba duk da kuwa na fahimci me take nufin,pant ɗin na buɗe ina cewa “kin ga pant ɗin da kika sayo mini an samu wani ɗan baƙin ciki ya yage shi”

Wani irin ƙuuuu! Ta soma yi tana ƙoƙarin jan birki har sai da na ji tsoro,pant ɗin ta wani fizge tana cewa “innalillahi!” sai kuma ta figi mota ta canza hanya,na dube ta na ce “lafiya? Ina kuma za mu?”

“Wurin Uncle Suhail,Suby ke ban san meke damun ƙwaƙwalwarki ba da ba ta kawo wuta.An ciri pant ɗinki amma hankalinki kwance,wato duk abin da za a yi ke ko oho”

"Don Allah kar ki kai ni wurinsa ban so! ” na furta cike da tashin hankali ba tare da ni kaina na san dalili ba,sam ba ta saurare ni ba sai ma gudu da ta ƙara.Yau ba mu tsaya ko ina ba sai wani wurin da yake kama da wurin kiyon dabbobi,ta ko ina shanu ne da sauran dabbobi.
Daga inda nake zaune nake hango shi yana a duƙe yana tatsar madarar shanu,miƙewa yayi ya je ya tara wani ƙaton bokiti a ƙarƙashin wani raƙumi da ke takaka fitsari sannan ya nufo motarmu.Jikina ne ya ɗauki wata kyarma ganin ya zo ta ɓangarena ya buɗe tare da furta “fito” kamar wacce ya tsafe haka kuwa na fito ɗin sai a lokacin ita ma Ubaidah ta fito .Shi yayi mana jagora zuwa cikin wata ƙatuwar buka wacce muna shiga ƙafata ta sandare na kasa motsi ballantana tako ɗaya.




Normal group 300: posting biyar a sati
Vip 600: posting goma a sati
Via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
Kowacce ta zaɓi groupe ɗin da take da ra'ayi, wannan ba kalar sauran labaran da na saba yi ba ne sha ƙundum ne,ga soyayya ruwa-ruwa,ga kuma daru da tsantsar darasi
[09/06 17:28] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*

08

Tamkar na shiga wuta haka nake jin wannan bukar,ga shi kuma na kasa yin motsi kamar bishiyar da aka dasa.
Ubaidah ta yi tsaye tana kallona yayin da shi kuma Uncle Suhail ɗin ya ɗauko wani turare mai wani irin ƙamshin wanda kana ji ka san ba dai wa al'ummar bil'adama ba sai dai jinnu.A hankali na ji jiyoyina sun fara ci gaba da aiki kafin na soma tafiya,wata tabarmar kaba ya nuna mini a can na zauna Ubaidah ma ta zo kusa da ni ta yi zaune.
Ruwa ya ɗebo cikin wata randa ɗaya da wata ƴar ƙaramar moɗa ya miƙo mini, Ubaidah ta kai hannu za ta karɓa ya ce “a'a barta da kanta ta karɓa”

Kamar mai ciwon hannu haka na kasa miƙa sa ballantana na karɓa,sai ya zo da kansa ya matse kaina tare da soma yi mini karatu nan take na ji wata halitta a cikin jikina tana kuka ta bakina amma sarai na san da ba ni ce ke yinsa ba.
Ruwan ya soma ɗura mini waɗanda nake jin tamkar saukar dalma a cikin hanjina,yana gama yi mini ɗuren ya koma gefe nan na soma kakarin amai ina wani gurnani.

Ya dubi Ubaidah yana mai cewa “akwai daɗaɗen sihiri jikinta,irin wanda ake yi wa mutum tun yana ƙarami ga kuma motsin jinnu nan a kanta”

Ubaidah ta ce “yanzu ya za a yi kenan?“

Ya ce “ke da ita akwai banbanci,kamar yadda na faɗa miki ke jinnunku na ahalinmu ne wanda kusan kowa yana da su,sannan kuma ba su cutar da ke sai ma dai don baki kariya.Saɓanin ita da nata suke na ture ga kuma sihiri,dole da buƙatar a yi mata ruƙiya don gaskiya magani ba zai isa ba”

Ubaidah ta miƙa masa pant ɗin tana cewa “ka ga kuma yau ɗin nan ta samu an ciri wani sashe na ɗan kamfanta ”

Uncle Suhail ya karɓa tare da dubawa yana kallona,zuwa wannan lokacin na dawo hayyacina.Kallon tausayi yake yi mini kafin ya ce “ke kam laifin me kika yi wa mutane da har suke bibiyarki da sharri haka? ”

Wasu hawaye suka zubo mini masu ɗumi,ya maida hankalinsa ga Ubaidah kafin ya ce “da dukkan alamu wanda ke bibiyarta da sharrin nan babban maƙiyinta ne, wannan aikin na ɗan kamfai ana yinsa ne domin saka mace yawon banza.Amma tun da har Allah yasa an yi saurin fahimta zan bata magani wanda za ta dinga amfani da shi da auduga sannan abu mafi muhimmanci shi ne addu'a da yaƙini.Ya kamata ki dage da addu'a,ki tsare zikirorin safe da yamma,ki kuma kiyaye haƙoƙin Allah,ki guji sauraren kiɗa”

Ubaidah ta kamo hannuna ta jimƙe cikin nata don ƙarfafa mini gwiwa,sai dai tamkar saƙaƙo haka na zama jin wai an yi mini sihiri ne don na dinga yin yawon banza.

Jan muski,da muski A'isha ya haɗe wuri guda ya soma yin karatu a ciki muna zaune sama da minti talatin kafin ya rufe kwalbar ya miƙawa Ubaidah ta karɓa sai kuma ta sunne kai.

“Mene ne kuma?” Uncle Suhail ya tambaye ta.

Ta ɗago fuskarta shaɓe-shaɓe da hawaye kafin ta ce “ Uncle Suhail ina cikin damuwa,jiya Sul ya kira ni ya ce sam babu sauƙi game da rayuwarsa ta can.Kwanaki in ba ka manta ba na yi maka magana kan matar da ke bibiyarsa,to har yanzu ba ta bari jiya ma ta so jan ra'ayinsa”

Uncle Suhail yayi murmushi ya ce “duk sun yi su gama,ki ce masa ya ƙara yin haƙuri da izinin Allah komai zai wuce”
Ta goge hawayenta ta ce “yau na yi mafarkin an yi auren amma wai kafin ma a kai ni ya mutu”
“Sharrin sheɗanu ne,bari na baki jibda duk dare in za ki kwanta ki tabbatar kin shafe jikinki da ita musamman bayan kunnenki”

Sai ya ɗauko wata ƴar ƙaramar kwalba ya bata,ta miƙe tsaye ni ma da sauri na tashi muka fito ba tare da na ga ta basa ko ƙwandala ba .Muna shiga mota na ja numfashi ina mai cewa “wai wane ne wannan mutumin?”

“Uncle Suhail ne,ƙanen Ammy ne ya mutu a wani hatsarin mota da suka yi a hanyar Maiduguri,bayan wasu shekaru kuma sai ya dawo amma ahalinsa suka ƙi karɓarsa suka ce fatalwa ne”

Baki da hanci na saki ina kallonta,na haɗiye wasu yawun tsoro na ce “kina nufin wurin fatalwar ne kika kai ni har ya bani magani?”

Ta yi wani ɗan murmushi mai sauti kafin ta ce “ba fatalwa ba ne,mutum ne wallahi sai da abubuwan da ya fuskanta a rayuwar da yayi bayan mutuwar bogin yasa duk ya canza za ki ga yana abu kamar aljani ”

Wani irin tsoro ne na ji ya mamaye ni jin ta ambaci aljani,don ni duk duniya na tsani abin da ya shafe su.Har muka isa makaranta a takure nake ga Ubaidah sai sake zaƙulo wasu ababen tsoron take yi.Ko da muka isa bakin aji tuni malami ya shiga,amma bai hana mu ba muna shiga muka ɗauki takarda muka soma zana jarabawar.Duk da mun zo a latti amma sai da muka rige wasu idawa,fitowa muka yi sai kuma a lokacin ne ta bani abincina na yi zaune kan step ɗin ƙofar ajinmu na soma ci hankali kwance ita kuma tana daga tsaye tana yi mini hira.Na ɗauki kamar minti biyar haka sai na ji jikina na ɗaukar rawa,da sauri na rufe kular tare da cewa “Ya Ubaid ya shigo makarantar nan Udah” sai na soma waige-waige.

“Wane Ubai...” shirun da na ji ta yi shi ya tabbatar mini da ita ta gansa,na juya saitin inda take kallo sai na hango shi a tsaye kunnensa maƙale da waya amma idanunsa suna kaina sai na ji duk jikina ya ƙara yin sanyi,wato yana ta kallona ina buga loma ban sani ba.Da wani irin sauri Ubaidah ta nufe shi ,babu shiri ni ma na miƙe na soma tafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login