Showing 18001 words to 21000 words out of 55823 words
da tozo da kuma ƙafafunsu,bakunansu kuwa an saka almakashi an datse su ko kuka ba su iyawa.
Dukkaninsu idanunsu sun rufe haka suka saka zakarun da ransu,Hassana ta furta wannan wanda ta gani a yau shi take so Yayan Ubaidah tana mai zuba ƙasa ta rufe zakaran.Da yake ba kunya ta ishe su ba sai suka alwala kuma suka yi sallah tare da roƙon Allah yasa aikin ya ci.
★Sulaimanu
Wayar da ya samu yayi da Ubaidah ita ta kawar masa da duk wata damuwa,ya ji sanyi a ransa tare kuma da dawo masa yaƙinin cewa sannu a hankali wata rana komai zai wuce kamar ba a yi ba.Tunani ya soma yi yana murmushi shi ɗaya a haka bacci ya ɗauke shi, lokacin da ya farka kuwa tuni gidan kowa ya watse.Wanka yayi sannan ya ɗora indomie ya ci sannan yayi alwala ya wuce masjid,bayan ya dawo ne kuma ya kimtsa cikin kakinsa na ƴan sanda.Mashin ɗinsa ya fiddo roba-rina,wurin aikinsu ya tafi duk da kuwa cewa ya ɗauki hutun kwana biyar amma babu amfanin zaman nasa shi ɗaya . Waɗanda suka san da zancen tafiyar tasa sai tambaya suke yi lafiya amma bai faɗa musu ba,saboda ba a yi ciki don cin abinci kawai ba .Aiki yayi tuƙuru har dare,nan ya ci abinci kafin ya wuce gida.Yanzu kuma moɗi ya tarar suna yi suna shan shayi sai dai iya su kaɗai ne banda mata, wannan yasa baya sun gaisa shi ma ya ja kujera ya zauna aka soma shan shayin da shi suna moɗi shi kuma yana chating da Ubaidah sai murmushi yake yi shi ɗaya kafin kuma ya miƙe ya je ya cika bokiti yayi wanka,bayan ya fito ya shige ɗaki ya kunna fanka sannan ya kira ta.
Tana ɗauka ya ji ransa ya daɗa yin haske kafin su soma hirar masoya ,ƙarara yake faɗawa Ubaidah rashin haƙurinsa akan rashinta da kuma yadda yake muradin samunta a kusa da shi.Ita kuma kwantar masa da hankali take yi, musamman abin da ya faru na dangane da mutuwar kawu.
Cikin wani irin yanayi yake cewa “Ubaidah ko dai ba alkhairi ba ne auren nan? Kin san a baya kusan kullum Mama sai ta faɗa mini haka tare da bani sharawa...” sai kuma yayi shiru,zuciyar Ubaidah kamar za ta kama da wuta haka take ji .Ta sani sarai wa yake nufi da Mama, wannan yasa ta ce “shawarar me take baka?”
Kamar ba zai sanar da ita ba sai kuma ya ce “wai na janye maganar auren”
“Dalili?”
“Gani take yi kamar kin wuce ajina duba da cewa ke ƴar masu hali ce,ni kuma talaka”
Ta ce “arziki ai na Allah ne,da a ce don kuɗi ake aure ai da na auri Ya Hamid amma na zaɓe ka Sannan ba tun yau ba na sha faɗa maka ba duk abin da Mama ta ce ne gaskiya ba,kawai in ta faɗa maka abu ka saurare ta sannan ka yi watsi da shi”
Ya ja numfashi ya ce “to Udar Suby ” ya ƙarashe yana wani murmushi mai sauti,Ubaidah ta turo baki ta ce “ai na yi fushi ma da ita,wallahi Sul ban san me yasa Allah ya jarabce ni da ƙaunarku ba kai da Suby kuma kullum ku ne ke wahalar da ni kuna ɓata mini rai .Dubi fa tun da ka zo ba mu ga juna ba,ka kwashi jiki ka koma.Ita kuma yau ta zaɓi zama gidan makoki kan ta zo tare da ni ”
“Yi haƙuri mana Matar Sul kar ki yi kuka” ya faɗa cikin sigar rarrashi, Ubaidah ta soma yi masa kukan shagwaɓa wanda hakan ya dagula masa lissafi da sauri ta nutsu jin yadda ya canza yanayin magana,wani irin tausayinsa take ji.Shi ma gudun kar abin ya tsananta daga ƙarshe ya cutu sai kawai yayi mata sallama,magani ya sha saboda kansa da ya soma sara masa kafin ya kwanta.Babu jimawa bacci ya ɗauke shi,sai dai bai yi wani nisa ba bala'in da kunuwansa suka soma jiyo masa ya tashi da wani ƙarfi yana dafe saitin zuciyarsa.Jikinsa har rawa yake yi wurin jawo jallabiya ya saka,duka gidan ba ka jin komai sai sautin abokansa da matan banza suna masha'a wa'iyazubillah.
Idonsa na wata irin rufewa saboda takaici da baƙin cikin shiga haƙinsa da suka yi, babban abin haushin ma wasu a falo ma suke ba a ɗakinsu ba .
Gidan ya buɗe ya soma tafiya cikin duhun daren kamar wani mahaukaci,yayi tafiya mai ɗan nisa kafin ya zauna yana kallon sama.A zuci ya soma yin magana ‘ Ya Allah in kana yin haka ne don jarraba imanina Allah na tuba ka yafe mini,iya abin da kunnena ke jiye mini kusan kowanne dare yayi mini yawa ga shi yau kuma na soma gani da idona har ana yi mini tayin zina.Allah ka tsare ni kamar yadda ka tsare Annabinka Yusuf da ƙangin zina’ sai wasu hawaye masu zafi suka zubo masa,ya maido kansa ƙasa yana danna waya domin kiran Ubaidah.
★Suwaiba
Sannu a hankali ƙafata ta soma borarrai alamun wutar ta fito har ta yi ruwa .Banda hawaye babu abin da nake yi,sai kuma a wannan lokacin ne na tuna wayata na can ɗakin Ubaidah.Mamu kuwa sai sannu take jero mini,inda na samu sassauci shi ne ɗan bacci da na samu shi ma bai yi wani nisa ba na ji wani azababen zafi a ƙafata ina buɗe ido na yi tozali da Mama Lantana ce ashe ta latsa wutar da ƙarfi duk suka fashe.Hawayen azaba ne suka soma zubo mini ina shirin janye ƙafar kuma ta soma barbaɗa mini magani tana cewa “shegen rawar kanki uwata duk shi ya kai ki ga haka,Zainaba ga wannan shi kuma ta sha in za ta kwanta yanzu na sayo shi bayan na karɓo mata maganin ƙunar”
Mamu ta shiga yin godiya kafin ta karɓi maganin,yayin da ita kuma Mama Lantana ta ci gaba da yin iya yinta na kalar dangi mutane kuwa sai yaba mata suke yi.
Sallolin ranar nan duk a zaune na yi su,ga shi kuma na kasa cin komai har dare.Bayan sallar isha'i Mamu ta ɓallo maganin ta bani ƙwaya biyu,na karɓa na saka bakina tare da kora shi da ruwa.Bai wani ɗauki lokaci ba na amayar da shi,cike da masifa Mama Lantana ta karɓa tare da ɓallo mini wasu biyun haka na karɓa na sha ina soma yin kakarin amai ta kama bakina ta dantse da hannu,tun ina yunƙurin har maganin ya zauna don dole.Wata irin zufa ce ta soma karyo mini,ba a kuma jima ba na soma jin jikina na yin wani irin mutuwa.Na miƙe dakyar,Mama Lantana ta ce “ina za ki je?”
“Banɗaki na yi wanka”na bata amsa kafin na je na cika bokiti ina ɗingishi,wanka na yi tare da yin ɗaurin ƙirji na fito.Can uwar ɗaka na shiga na cire zanena tare da shanya pant ɗina da na wanke sannan na mayar da kayana na kwanta,sai dai mugun sanyin da ya soma rufe ni yasa na je na ɗauko ƙaton hijabin da Ubaid ya saya mini na saka .
Ina shirin kwanciya sai kuma na soma jin wani ƙunci na luluɓe ni ,babu abin da nake da buƙata sai kaɗaice wannan yasa na fito ina ɗingi ban zame ko ina ba sai ƙofar gida .Kan dakali na zauna ina yin hawaye , ƙwaƙwalwata kuwa kamar ana meeting ɗin majalisar ɗinkin Duniya haka nake jin ana yin magana barkatai a cikinta.Wani haske ne ya soma sauka a gare ni,na kai hannu na rufe fuskata sai na ga mai motar na gangarawo inda nake kafin ya kashe fitilun ya kuma fito,duk da ƙofar gidan babu ƙwan fitila hakan bai hana ni gane shi ba.Da wani irin sauri na tashi tsaye ina mai cewa “Ya Ubaid?”
“Me kike yi a ƙofar gida?” ya tambaye ni,kamar mai jira haka na fashe da matsanancin kuka ina mai faɗar wani sirri da ya fito daga can cikin ruhina.
“Ƙunci nake ji,na tsani komai ban son mutane ji nake yi kamar na ta yin ihu” na furta ina shafar ido,ina jin idanunsa masu kaifi suna kallona a cikin duhun daren.
“Shiga mota” ya faɗa cikin salon bayar da umarni sai kuma ya buɗe mini gidan gaba,saura ƙiris na faɗi wurin shiga saboda yadda idanuna suka soma kumshe wa,shi ne ya taro ni tare da rufe ƙofar sannan ya zagayo ya zauna tare da yi wa motar key.
Muna tafe ina ɗan gwale idona ina son hana baccin ɗaukata,cikin magagin bacci na ce “ina za mu je?”
“Wurin Ubaidah zan kai ki” ya bani amsa,ban ƙara cewa komai ba na jingina kaina ga madubin mota daga nan ban sake sanin abin da ke faruwa ba.
Ubaidullah
A natse yake kallon Suby wacce yanzu yake jin tamkar rayuwarta ta fi tasa muhimmanci.Tun da ya tafi wurin aiki ya kasa sukuni,daidai da sakan ɗaya ƙwaƙwalwarsa ba ta gushe ba akan tunaninta.Haka kawai yake jin kamar tana cikin damuwa ne wannan dalilin yasa ya je can gidan makokin,sai kuma zatonsa ya zama gaskiya yana shigo layin ya hango ta kamar aljana ita ɗaya a zaune cikin hijabin da shi ne ya saya mata shi.Gefen hanya ya parker ganin yadda kanta ke ɗan buguwa ga madubin in ya hau tudu,a hankali ya jawo ta ya gyara mata zama ya maƙala mata belt sannan yayi ɗan baya da kujerar .Goshinta da ke tsatsafo da gumi ya kai hannu a kai sai ya ji shi gau kamar gatau,iya gumin kawai ya goge mata kafin ya ci gaba da tuƙi.Tun akan hanya ya kira Ubaidah sai dai tana busy wannan yasa ko da isarsa bai ɓata lokaci ba ya kewaya can ɓangaren ya ɗauki Suwaibar ya nufi ciki da ita.
A falo ya so ajiye ta sai kuma ya fasa ya nufi benen Ubaidah,yana shiga ya soma ƙwala kiranta yana mai shimfiɗe Suwaibar kan doguwar kujerar falon.Ubaidah wacce take a rikice jin Sulaimanu ya sake kiranta yana yi mata kuka kamar ƙaramin yaro,yanzun ma a ɗan firgice ta fito jin muryar Ya Ubaid ɗin don sarai ta ga kiransa na shigo mata ne sai dai babu halin ɗauka ne.
Tana fitowa ta yi tozali da Suby,ƙafarta na fitar da jini.Da sauri ta ce “innalillahi wa'inna ileyhi raji'un na shiga uku ni Ubaidah ” sai kuma ta zo da sauri ta kama ƙafar,shi Ubaid sai yanzu ma ne ya lura da ko takalmi babu a ƙafarta ga kuma ciwo.Har wani hayaƙi ya ji zuciyarsa na yi kamar an ɗiga masa dalma,tambayarsa Ubaidah ke yi amma ya kasa cewa komai.Sai sauka da yayi ya kira Ammy kasancewar ita likita ce tana gani ta fahimci ƙunar wuta ce sannan ta sha maganin bacci ne,akwatinta na asibiti ta ɗauko ta wanƙe ƙafar sannan ta saka mata magani ta naɗe ta da bandeji.
“Cire mata hijabin ta sha iska” Ammy ta faɗa tana kallon Ubaidah da ke yin kuka,dakyar ta motsa ta cire hijabin.Suby ta ja wani numfashi,Ya Ubaid ya dubi kwantancen gashin gaban goshinta yadda ya wani lafe yana tsatsafo da gumi.Sanyin ac ya ƙara kafin ya fice ya nufi sashensa.
★A can gidan makoki kuwa Mama Lantana tuni bacci ya ɗauke saboda nutsuwar ruhi da ta samu za ta yi aiki a tsakar dare na tuɓe ɗan kamfan Suwaiba.Wannan yasa ba ta ma san lokacin da Hassana ta dawo ba,ita kuma ta zo nan ne da tunanin gobe ƙila Ubaid zai dawo.Lokacin da ta zo kusan kowa yayi bacci,bokiti ta cika da ruwa ta je ta yi wanka sannan ta shiga ɗaki.Matar malam ta gani a rakuɓe tana kukan kewan mijinta,ba ta ce mata komai ba ta shanya pant ɗinta sai kuma ta ga wani mai bala'in kyawu.Sam ba ta kawo na Suwaiba ba ne sai ta ɗauka ta saka sai dai yayi mata yawa Kasancewarta siririya a dole ta fidda shi ta ajiye.Nata ɗin ta mayar tana tunanin kar yadda ta so sace na wata ita ma a ɗauke nata,can waje ta fita ta kwanta.Cikin tsakiyar dare Mama Lantana ta farka,kamar munafuka haka take tafiya har ta shiga can uwar ɗaka inda take da tabbacin Suwaiba na nan amma wayam.
“Wa kike nema?” matar malam ta tambaya wacce ta dawo daga banɗaki.
“Ina Suwaiba?”
“Ta yi wanka ta fita ai har yanzu ba ta dawo ba” ta bata amsa tana mai zuwa ta yi kwanciyarta.Cikin sa'a idanun Mama Lantana ya kai ga ɗan kamfan,a yadda ta gansa tsadede ta fahimci iya mai kuɗi zai sayensa wato Ubaidah ta bai wa Suwaiba shi.Ɗan kamfan ta ɗauka sannan ta fita,can banɗaki ta shiga ta kira malam Yawale wanda kamar Aljani take da wuya ka kira ba ka same shi ba,yana ɗagawa ta ce “na samu ɗan kamfan amma ƴar baƙin cikin ta wanke shi”
Ya ce “babu matsala ki yage daidai tsakiya ki kawo mini” cike da farin ciki ta kashe kiran,tsabar mugunta da baki ta yi amfani ta ciri tsakiyar pant ɗin kafin ta fito ta mayar da shi inda yake,sauran kuma ta ƙulle ga haɓar zane.......
Normal group 300: posting biyar a sati
Vip 600: posting goma a sati
Via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
Kowacce ta zaɓi groupe ɗin da take da ra'ayi, wannan ba kalar sauran labaran da na saba yi ba ne sha ƙundum ne,ga soyayya ruwa-ruwa,ga kuma daru da tsantsar darasi
[08/06 12:46] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍
MRS SADAUKI ✍️
FCWA ☀️
*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*
07
Washegari tun asubar farin aka soma hada-hadar sadakar uku.Duk wani dangi na nesa da na kusa da abokan arziki sun zo.Hidimar nan ta mantar da Mamu wata Suwaiba ballantana ma har ta neme ta, wannan kuma ba yau ne farko ba sau tari tana jin wani duhu ya gilma mata ta mance ma tana da wasu ƴaƴa musamman ma Sulaimanu.Wannan yasa hankali kwance duk ta tsaya kai da fata komai ya tafi kan tsari,a ɓangaren Hassana kuwa ta kasa ta tsare tana tsaye a bakin ƙofa tana baza ido cikin taron dandazon mazan da ke wurin.Ita kuwa Mama Lantana kamar fitar tusa haka ta fice ta bar gidan zuwa na malam Yawale ,yau kam ta yi sa'a babu kowa sai wata mata da suka yi ban hannun makafi ita tana fita ita kuma tana shiga.
Kan tabarma ta zauna tare da kwanto wani sashe na pant ɗin Suwaiba ta miƙawa malam Yawale shi kuma ya karɓa tare da saka shi cikin wata baƙar rariya sannan ya ɗora kan wata ƙwayar da ke cike da kiyashi.Magani ya barbaɗa kan ɗan kamfan yana mai furta wasu surkulle na shirka,sannan ya ɗauko wani jan ƙyalle ya saka guntun pant ɗin a ciki ya ɗaure ya miƙawa Mama Lantana ya ce “ki jefa shi a cikin masai/salanga ”
Ta karɓa tana mai washe baki tana cewa “ka tabbata zai yi?”
Malam Yawale ya nuna mata rariyar da ke kan ƙwarya ya ce "yadda kiyashin nan duk suka baro ƙwarya suka yaɓe rariya haka mazan banza za su dinga tururuwar bin layin lalata da ita”
Zuciyar Mama Lantana fesss ta ce “ita ma na uwar nasu da buƙatar a sabunta aikin,na ga take-takenta ta soma yunƙurin nuna mini cewa ƴaƴanta ne tana da iko da su.Kamar yadda ka saba yi,ka saka mata ganin laifi da baƙin Abdullahi mijinmu sannan ka nuna mata ni ce babbar masoyiyyarta sannan duk wani sirri nata kar ta ɓoye mini in ta yi yunƙurin yin haka kuwa ka saka Aljanu su yi ta birkita mata lissafi suna yi mata magana cikin kwanya har sai ta kasa jurewa ta zo ta sanar da ni ”
Malam Yawale ya ɗauko wani baƙin kundi nasa ya rubuta jawaban Mama Lantana kafin ya ɗago ya ce “wannan aiki dole yana da buƙatar yanka,za ki nemo baƙar akuya mai gemu ki sa a yankata nan tsakiyar gida ,akwai wani magani da zan baki sai ki cilla shi cikin ramen da jinin akuyar ya zuba kafin ki rufe.Zuciyar akuyar kuma ni za ki kawowa ita akwai aikin da zan yi da ita ,sai dai wani sharaɗin lokacin yankan ba mu buƙatar ambaton sunan Allah domin wa aljanin da zai yi miki gadin Zainabar za a yi yankan”
Ba tare da wani shakku ba ta ce “wannan duk babu damuwa,kenan sai ka aiko da ɗaya daga cikin almajiranka ya zo yayi mini yankan ,ka ga ba zan kirawo wani bare ba in faɗa masa sirrina”
Malam Yawale ya ce “babu damuwa,kuɗin aiki kuma sai komai ya tafi yadda ake so zan sanar da ke” nan ta yi masa godiya kafin ta fito.Tana tafe tana magana ita ɗaya “wato har wani tunƙaho kike yi ɗanki zai auri ƴar masu kuɗi zai zama ɗan gata shi ma a mallaka masa dukiya,ita kuma munafukar ƴarki ta ɗauki girman kai ta ɗorawa kanta ita ma jiran mai kuɗin take yi.Hasken fatar da ta ɗan fito da shi shikenan ta mayar da shi jari,to in kin zama karuwar gida sai na ga ta jiran mai kuɗi”
Sai da ta zo bakin hanya ta samu abin hawa,sam ba ta koma gidan makoki ba gidanta ta wuce ta je ta aiwatar da baƙin nufinta ta cilla abin a masai sannan kawai hankalinta ya kwanta.
Lambar Iroro ta kira wanda shi ne ke kula mata da sayen duk wata dabba da malam Yawale ya buƙata.Bayan ya ɗauka ta faɗa masa irin akuyar da take so har da masa alƙawarin tukuici mai tsoka.Shi ma da jin haka ya bazama nema,hankalinsa bai kwanta ba har sai da ya samo mata ita.Ta biya kuɗin akuyar da kuma na alƙawarin da ta yi masa, sannan ta ɗaure ta ga turmi.
★A can gidan Ammy kuwa cikin wani irin yanayi Ubaidah ta ƙara kai wayarta a kunne ganin har yanzu bai kashe kiran ba.Ta ja wani dogon numfashi ta ce “ka yi haƙuri”
"Me ya samu Suwaibar?”
“Ƙafarta ce ta samu ƙuna,amma da sauƙi Ammy ta yi mata aiki ga shi tana ta bacci ma.Ya naka jikin?”
“Babu sauƙi Udah ji nake kamar na yi hauka,ke kawai nake da buƙata a kusa da ni don Allah ki nemo mafitar da za a bikinmu nan kusa domin ki tare”
Jikinta duk yayi sanyi ta ce “in sha Allah zan yi ƙoƙari Sul kar ka damu” nan ta ci gaba da kwantar masa da hankali har suka yi sallama.
Pilow ta ɗauko da blanket ta yi shimfiɗa kan capet ta kwanta tare da tsurawa fuskar