Showing 6001 words to 9000 words out of 55823 words

Chapter 3 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

32

bai zauna lafiya ba,kullum cikin jajensa yake yi ga shi kuma ya zama ajalinsa”


“Haba! Haba matar malam ya za ki ce haka? Ta ina auren Sulaimanu ya zama ajalinsa sai ka ce dai shi ne mutum na farko da ya taɓa mutuwa a hatsarin mota? Ku fa musulmai ne ,ƙaddara mai kyau ko akasinta yana ɗaya daga cikin ginshiƙan imani.Kar ku bari sheɗan yayi tasiri a zukatanku mana ”


Mama Lantana ta karɓe da cewa “laaa to ai ni sai yanzu na fahimci me suke nufi,ta ina dama mutuwar kawun yara ke da alaƙa da auren Manu ? Wannan sam ba adalci ba ne matar malam ko kowa ya faɗa ke ai bai kamata ki ce ba mene Manu ɗin bai yi muku? Hatta da abincinku na wata in ya kai gidanmu haka yake kawo wa nan gidan”


Mamu wacce ita sam ba ma ta da labarin haka ta ce “abincin wata ?”
Mama Lantana ta ce “i,ai duk wata sai ya kawo musu abinci ga kuma matar malam ɗin nan ki tambaye ta in ƙarya nake yi”

Mutane dai da ba su san halin Mama Lantana ba sai kallonta suke,don ta zama tamkar sawun keke ba a san gaba ba ballantana baya.

Ƴan biyu ma suka shiga nasu tsiyar gumin suna kare Yayansu,hakan da suka yi sai ya sanyaya zuciyar Mamu take ganin iya Lantana da ƴaƴanta ma kaɗai sun isa su tare mata ba sai ta saka baki ba.


★UBAIDULLAH

Shi ne babba a kaf gidansu Ubaidah,shekarsa talatin da shida.Captain ne na sojoji,bai da yawan fara'a yana da tsanani sosai a wurin da ya kamata ya nuna tsananin.Yana son ƴan uwansa musamman ma Ubaidah kasancewar ita kaɗai ce mace kaf gidansu kuma autarsu.Amma ƙauna da gatan da yake yi mata ba su hana yi mata hukunci ba in ta yi laifi,sau ɗaya tak ya taɓa yi mata mugun duka ita da ƙawarta a ranar da ya kama su suna rawa a wani shagalin biki da aka shirya tsakanin ɗalibai.Yadda ake cuɗanya maza da mata shi ya hassala shi tun a can wurin taron ya naɗa musu na jaki sannan ya sako su a mota ya kawo gida.

Tun bayan wannan lokacin bai ƙara saka Suwaiba da idonsa ba sai yau da ya ganta a cikin yanayin da ya kasa barin tunaninsa.Har ji yake a ransa da ya san zai same ta a haka da ya haƙura da key ɗin motar tun farko,saboda ko bayan ya fita ya koma sashensa kasa sukuni yayi haka yayi ta ganinta tsaye da towel tana hawaye.
Yanzu ma abin da ta yi sosai yayi mamakin yadda ya ga tsoronsa ya rufe mata idanu,hakan yasa ya bi bayanta da kallo yana jin wani sanyi a duniya yana son mace mai matuƙar jin tsoronsa da ganin girmansa.Bai ma damu da kayansa da ta ɓata ba haka ya je ya sauyo ya fito,yana karanta saƙon Hamida wacce ke tambayarsa in girkin da ta aiko masa yayi daɗi sosai .Yamutsa fuska yayi yana shirin maida mata ya soma jin sautin takun Suwaiba ,a dole ya ɗago ya dube ta yana kallon yadda kayan da shi ne ya sayawa Ubaidah suka ɗame mata jiki.
Fasa mayar mata da saƙon ya yi kawai ya fice,ɗaya daga cikin motocinsa ya ɗauka yayi mata key.


Direct gidansu Hamidar ya wuce,tarba mai kyau ya samu daga ahalin gidan wanda suka kasance ƴan uwansa ne.Duk kowa ya bar falon sai kuma a lokacin Hamida ta fito cikin shigarta ta kullum wato sari,kasancewarta marar ƙiba yasa ta zaɓi sari matsayin sutura.
Tun da ta fito ya kafe ta da ido,yadda take tafiya tamkar iska zai ɗauke ta sama tsabar sirranta.Ita kuwa tana ganin haka ta ci gaba da lanƙwasa ƙafafu tana tafiya cikin salon jan hankali.Tana zuwa ta zauna tana mai cewa “ya dai? Kallon fa? Ko na canza? Na yi kyau sosai?”

Kamar zanar bunu bakinsa ya furta “eh amma ba ki kai ta ba!”

Hamida ta gimtse fuska ta ce “wace ce?”

Ubaidullah ya ɗan lumshe ido yana sauraren bugun zuciyarsa da ya canza gudun tun bayan da ya ga Suwaiba.Murya a ɗan dake ya ce “Jeedah mana”

A nan take wani murmushi ya suɓuce mata tana mai cewa “in kuma ta ɗauko kamannina madadin naka?”

Ya ware idonsa ya kalle ta kafin ya ce “jinina ya fi naki ƙarfi,ina ji Jeedana da ni za ta yi kama”

“To na ji! Yanzu dai faɗa mini ya ka ji girkin yayi daɗi kuwa?”

“Sosai ma sai dai ban wani ci sosai ba”

Ta ɗan ɓata rai ta ce “saboda me?”
Ya yamutsa fuska kafin ya ce “kin san Ubaidah da shirme yau ƙawarta ta zo gidan”

Hamida ta ja tsuki tana cewa “ƴar talakawa za ka ce wacce ta sauya mata ra'ayi ta ƙaƙaba mata Yayanta ”

Ubaidullah ya ce “Hamida me yasa kike da riƙo a rayuwarki? Allah ne bai nufa Abdul Hamid ya aure ta ba shi ne kawai,sannan ki bar zaginta ban so”

“To“ shi kaɗai ta furta tare da yin shiru,a duniya in akwai wacce ta tsana to bayan Suwaiba take ba don komai ba sai don ta yi yaƙinin cewa tsabar tsagwaron ƙaunar da Ubaidah ke yi mata ce har ta kamu da son Yayanta Sulaimanu.

“Zan wuce!” ya furta tare da miƙewa tsaye,Hamida ba ta ce komai ba har sai da ta ga ya juya sannan ta miƙe da sauri ta rungume shi ta baya.Ya ɗan rumtse ido,a lokutan baya yana matuƙar jin farin ciki in Hamida ta yi masa haka amma yau a karon farko da ya ji tsanar haka.
“I love you !” ta furta tana wani murmushi mai sauti,tana jiran ya juyo da ita su fuskanci juna kamar yadda ya saba yi mata sai yayi mata kiss a goshi amma shiru kake ji sai ita ce ta zagayo da kanta ta yi tsaye tana kallonsa.

“Wai fushi kake yi don na zagi wacce ta yi silar raba ɗan uwana da farin cikinsa?” ta furta idanunta na ƙanƙancewa.

“Zan tafi sai in mun yi waya” ya sake furtawa.

Ta ɗan ja da baya saboda ta fi kowa sanin halin Ubaidullah in yayi haka to fa babu wanda ya isa ya sauya masa ra'ayi.“To babu damuwa ka kula da kanka sosai”

Wani murmushin ne ya suɓuce masa bai shirya ba wanda kusan kullum in ta furta masa ya kula da kansa sai ya ga kamar ma ta raina shi ne ko tana yi masa ɗaukar yaro.Ya ce “kina bani mamaki Hamida sai ki ce wai na kula da kaina,sai ka ce wanda bai da cikakken hankali dai”

Ta yi ɗan murmushi tana mai cewa “Ubaidullah a kullum in kana faɗar irin haka sai na ga kamar ba ka fara sona ba har yanzu,saboda zuciyar da ta kamu da so ne kawai ke fahimtar kalaman so da bege da kuma tattali.In na ce ka kula da kanka ai don na damu da kaina ban so wani abu ya same ka”

“To na ji na gode” ya furta tare da ficewa ita kuwa ta bi shi da ido har ya ɓace mata.Da wani irin sauri ta nufi sashen mahaifiyarta tana ƙwala kiranta “Ummah? Ummah?”

“Lafiya ?” Ummah da ke zaune kan gado tana jera sarƙoƙin da take yi wa Hamida tariya a cikin akwati.
“Ba lau ba Ummah, Ubaidullah ya sauya mini fuska ya kamata ki kira malam Yawale ” jikin Ummah ya ɗauki wata rawa ta ce “me kuma ya faru? Cewa ya yi bai son ki? Halan maganar auren kika yi masa? Kin san da sarai malam Yawale ya ce kar ki furta masa kalmar aure ki bari da kansa zai faɗa ko?”

Hamida kallon Ummah ta dinga yi,in Ummah na yin wani abin sai ta ga kamar ma ta fi ta damuwa akan ta auri Ubaidullah ɗin.Ba ta ce komai ba dai ,sai Ummah ta kira shi a waya suka yi magana ta kashe kafin ta dube ta tana mai cewa “ki ɗauko ƙwan da ya baki ki juya shi cikin ruwa har sau bakwai kina ambaton sunan Ubaidullah sannan ki je ki yi wanka”
Hamida ta ce “to” kafin ta fita zuwa ɗakinta,ruwa ta zuba a bokiti ta ɗauko wani ƙwan kaza da aka yi wa rubutu a jiki ta shiga juya shi tana kiran sunan Ubaidullah sannan ta yi wanka da ruwan.Kamar kullum yau ma wani mugun sonsa ne ta ji ya ƙara luluɓe ta,daman hakan ce ke faruwa da ita muddin ta yi wankan....
[03/06 17:48] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*

03

Sai wuraren sallar magrib Ubaidah ta maido ni gida,sai dai a rufe muka tarar da gidan alamun har yanzu su Mamu ba su dawo daga gidan makoki ba.

“Gidan naku a rufe kin ga dole yanzu mu koma dama ban gaji da ganinki ba ki ka wani matsa ala dole sai kin dawo sai kace wacce ta bar yaron da take shayarwa ” Ubaidah ta faɗa tana buga sitiyarin motarta.

Na ce “a'a zan fita na jira su”

“Yau ga Ubaidar mahauka ba,sai na bar ki a nan ke ɗaya”

“Gidansu Fiddo zan shiga sai na jira har su dawo”

Ta haɗe rai tana cewa “wai meke haɗinki da Fiddon nan ? Magana ɗaya biyu sai kin kawo mini zancenta”

Na yi ƴar dariya na ce “Yaya Surajo ke sonta fa”

Ta ja dogon tsuki ta ce “wace marar aji ce za ta so Surajo? Ga muni ga ƙanzanta ga kuma shaye-shaye taɓ”

Duk da abin da ta faɗa gaskiya ne amma sai ban ji daɗi ba kasancewar shi ɗin ɗan uwana ne,ubanmu guda shi ne babban yaron Mama Lantana.Wata harara ta banko mini ƙila na ganin na canza fuska ne kafin ta ci gaba da cewa “ke ai dama duk waɗanda ba su ƙaunarki kin fi manne musu to je ki ga Surajo ɗin,ina ce dai uwarsa ce ta saka ki kwana asibiti”

“Uwarsa kuma?” na tambaya cike da mamaki,ta yi ɗan shiru kafin ta ce “to eh mana,kika ce saboda ita Abba ya ƙi fitowa”

Na ja doguwar ajiyar zuciya ina mai cewa “haka ne”

Key ta yi wa motar muka koma gidansu,sam ban yi mata gardama ba don wani sanin sa'in Udata akwai rigima da mayar da ƙaramin abu babba.
Tana yin parking duk muka fito amma ban ɗauko ledar kayana da ta raba ta bani ba.Ciki muka shiga sai muka tarar da Ammy ta dawo daga aiki, Kasancewa ita ɗin babbar likitar mata ce tana yin aiki a asibitinta da ma sauran asibitoci na gwamnati da na kuɗi.

“Oyoyo da Suby,yau an tuno da mu” shi ne abin da ta faɗa tana murmushi,ba tare da wata kunya ba na gaishe ta tare da zuwa na rungume ta ina cewa “ai tun ɗazu na zo mun fita ne”

“Ubaidah me yasa ba ki kira ni ba? Tun ɗazu na sauka kawai na tsaya cikin office ne ina duba saƙonnin wayata.Ina Mamarki fatan duk kuna lafiya?”


“Lafiya lau tana can gidan rasuwa,kawunmu ya rasu” na bata amsa.

Ta ce “innalillahi yaushe? Amma kuma ba ta kira ni ba Allah ya jiƙansa”

“Amin !” Ubaidah ta yi saurin amsawa tare da zuwa ta janye ni daga jikin Ammy tana cewa “ya isa haka to malama,Ammy ni yaushe rabon da ki saka ni jikinki saboda Allah?”

Sallamarsa ita ta katse mana ɗan nishaɗin da muke yi,ni dai sunne kai na yi ban sake ɗagowa ba ina jin su dai suna magana Ubaidah na shaida masa ta ga key ɗin motarsa.


Ammy ta ce “ku wuce can sama in kun yi sallah ku sauko akwai aikin da zan saka ku” kamar ta luntsuma ni aljanna haka na ji,wannan yasa har tuntuɓe nake yi wurin nufar sashenta sai dai ban ma kai ga fara hawa step ba Ubaidah ta yarfa ni.

“Ita fa can tsoron Ya Ubaidullah take yi shi yasa ki ga tana wancan saurin” shi ne abin da ta faɗa tana dariya,na juyo zan yi mata masifa karaf idanuna suka sauka cikin nasa a dole na fasa kawai sai na sa kai.

Cikin fushi na shiga toilet ɗin, wannan karon ma kamar jiya a asibiti haka na ji ana yi mini magana cikin ƙwaƙwalwa sai dai wannan karon ban iya tantance me ake faɗa ɗin don ji nake kamar muryoyi dayawa ne ke magana lokaci guda.A nan take kaina yayi wani mugun sarawa,a dadafe na ɗauro alwala na fito.
Jiri na soma gani kafin na ji wani abu mai ɗumi ya biyo hancina,na kai hannu na laƙato na duba sai na ga baƙin jini baƙi ƙirin mai duhu.A nan take casbin hankalina ya tarwatse,daidai nan kuma Ubaidah ta shigo.Da idanuna da nake jin tamkar an sauya mini su na dubo ta a raunace,ta zo da wani irin sauri ba tare da wani tunani ba ta saka hijabinta ta fara goge mini jinin wanda kamar ma sake tunkuɗo shi ake yi.


“Me ya faru? Don Allah yi haƙuri ban san ranki zai ɓace” tana furucin ne idanunta na cikowa da hawaye.

“Udah kaina! Ciwo yake yi mini” na furta dakyar ina mai kama kan,yayin da ita kuma ke ci gaba da goge mini jinin da zarar ya ƙara zubowa.

“Kin ga zo mu sauka ƙasa” ta faɗa tana wani jana da ƙarfi,haka na take mata sawu.Step ma bibiyu muke taka shi .
Ko da muka sauka tuni jini ya gama wanke mini gaban rigata don tun zan shiga alwala na cire hijabina.


“Ammy? Ammy ?” haka take ƙwala kiran Ammy sai dai ba ta fito ba sai Yaya Ubaidullah ne ya fito sanye cikin farar jallabiya,ɗan madaidaicin gemunsa na ɗigar da ruwa da alamu alwala yayi.


“Subahanallah ! Me ya same ta?” ya tambaya.

“Ni ma ban sani ba kawai na same ta jini na ɓulɓulo mata ta hanci” Ubaidah ta basa amsa.

Ya ce “shi ne kuma kika bar ta a tsaye madadin ki zaunar da ita“ yayi furucin a ɗan ruɗe kafin ya kama hannuna ya zaunar da ni kan kujera sai ya ɗaga kaina sama tare da soma bubuga goshina yana yin addu'a “As'alullahul Azima Rabbal Arshil Azimi an yashfiki” ya karanta wannan addu'ar har sau bakwai kafin kuma ya ja “lahaula wala ƙuwata illa billah!” ita kuwa ban ma san adadi ba,sannu a hankali duk na ji abin da ya taso mini ya ɗauke ɗif sai ajiyar zuciya da na shiga saukewa.

Ya ja da baya yana kallona,na ɗan sunne kai murya na rawa na ce “na gode” bai ce komai ba ya fice .Ubaidah kuwa kusan ƙafafuna ta zauna ta saka ni a gaba tare da zuba uban tagumi,na fi kowa sanin ta yanzun nan sai ta shiga damuwa saboda hakan.Ta ƙasan ido duk nake ƙare mata kallo kafin na ɗago na ce “ tashi mu je mu yi sallah Udah” tana jin na ambaci wannan sunan sai ta ja numfashi saboda muddin ina fushi da ita ban kiranta da shi,sau tari kuma ina ambatonsa don nuna mata ƙaunarta a raina dashe ne daga Rabbi.

A tare muka koma can sama, wannan karon da zan shiga banɗaki sai da na yi addu'a.Rigar na cire na yi wanka haɗi da alwala na fito na gabatar da sallah,ita ma kusa da ni ta zo ta yi.Muna zaune dukkanmu muna lazimi Ammy ta shigo ita da ɗaya daga cikin ƴan aikin gidansu ita kuma hannunta riƙe da kayan gugar tiles.Duk inda jinin ya ɓata ta goge,Ammy ta zo tana tambayata jikin kafin kuma ta ce “doctor na kan hanya zai zo ya duba ki”


“Ammy ai na warke kin ga jinin ya tsaya” na faɗa .
Ta ce “ba ni ce na kira shi ba Yayanku ne“

Ban ƙara cewa komai ba sai Ubaidah ce ke cewa Ammy “don Allah ki kira a gidansu ki ce a bar ta nan ta kwana har zuwa da safe sai ta koma”

Ammy ta ce “kin ga na ma manta ina cewa in kira ta na yi mata ta'aziyya kafin mu je”

Sai kuma ta fita,sai a lokacin kuma na harari Ubaidah ina mai cewa “yarinya ni gidanmu zan je”

Ta ce “daɗin abin dai ni ma gidanmu ne kuma na fi ki iko da shi saboda wata rana dole ki fita cikinsa zuwa gidanki”

“Tun da ni na ce miki zan yi aure...” sai kuma na yi shiru jin sallamar Ya Ubaidullah daga can falo.

Da sauri ta fita kafin ta dawo tana yamutsa fuska,na ce “ya dai?”

“Ki fita ga likitan nan” ta bani amsa .

“Kamar ya na fita? Ke kuma fa?”

Kafin ta bani amsa daga can falo Ya Ubaidullah ya kira ni “Su...by” yanayin yadda ya kira sunan yasa muka saki murmushi tare ni da ita.

Na amsa da “na'am” kafin na miƙe na kamo hannun Ubaidah don mu fita tare amma ganin ta tirje yasa dole na fita zuwa falon.Suna a tsaye shi da wani farin matashi siriri,gaishe su na yi a ladabce shi kaɗai ya amsa yana mai cewa “ita ce patient ɗin?”

“Eh ka duba ta” ya basa amsa.

“Zauna” doctor ɗin ya faɗa tare da nuna mini kujera,na zauna yayin da shi kuma ya buɗe ɗan akwatinsa na likitoci ya saka safar hannu tare da ɗauko fitila da kuma wani abu dogo siriri.Nan take tsoro ya kama ni,murya na ɗan rawa na ce “ban so”

Da mamaki ya ce “me?”

Na nuna masa abin ina cewa “ban so ka sa mini shi a hanci”

“Babu wani zafi” ya furta tare sunkuyo wa zai kama kaina da wani irin sauri na kauce.

“Ya Ubaidullah ina ga sai ka riƙe mini ita” doctor ɗin ya faɗa .Ina jin haka na soma yin hawaye muryata na ɗan rawa na ce “Udah?” ita ce kawai za ta zo na samu sukuni sai kuma ta ƙi fitowa.

Ban ga tahowarsa ba sai ganinsa na yi a gabana,kan nawa ya ɗaga tare da sa ɗaya hannun ya rufe mini idanu.Kokowa kawai na soma yi da numfashina ina jin doctor ɗin na taɓa hancina,ba a wani ɗauki lokaci ba Ya Ubaidullah ya matsa sai na buɗe ido ina kallon doctor ɗin da yake yi mini dariya.

Wani ɗan ƙaramin book ya fiddo yana mai cewa “me sunanki?”

“Suwaiba Abdullahi ” na basa amsa sai ya rubuta tare da ƙara yin wata tambayar “shekarunki fa?”

Shiru na yi ina tunani kafin na ce “na manta amma Udah ta bani shekara uku da ko wata nawa ma ne.... Na manta amma bari na tambayo ta”

Ido ya tsura mini yana yi mini kallon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login