Showing 33001 words to 36000 words out of 55823 words

Chapter 12 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

44

don fallasa wa duniya ita karuwa ce”

Wani sanyi ya ratsa zuciyar Mama Lantana,tana zuwa gida kuwa tun a waje ta watsar da nonon duk ya faltsa ko ina,da ta shiga gida kuma ta cilla ɗaya abin a masai suka haɗe da tun wancan na farko.

★Bayan sallar juma'a,duban jama'a suka shaida auren Sulaimanu Abdullahi tare da amaryarsa Ubaidah Yusuf.Ɗaurin aure ne da hatta Abba bai sani ba,ya dai ga wani ɗan uwansa da ke can Katsina ya ziyarce shi sannan kuma shi ya bada shawarar su je masjid ɗin.Duk da wani ɓangare yayi murna amma hakan bai hana shi yin masifa ba.


★Suwaiba
Tun da aka tafi jama'a hankalina ya ƙi kwanciya,wanka na shiga domin yau na ɗauki alwashi sai na tafi gidansu Ubaidah tun da banda waya a hannuna.Ina fitowa da Ya Ubaid na soma cin karo yana tsaye a tsakar gidan,Allah yayi sa'a ina sanye da hijabi.
Gaishe shi na yi ya amsa yana mai ɗan kawar da kai,da sauri na wuce ciki a gaggauce nake shirin sai a lokacin kuma Mamu ta gama sallah tare da fita tana amsa sallamar da ni dai lokacin da ina wanka ban ma ji ba.Har ɗaki ta yi masa iso,a lokacin kuma tuni na shimfiɗa dadduma sai na soma yin sallah amma a hakan ina jin yadda yake yi mata barka da kuma fatan alkhairi a ƙarshe kuma ya ce ya zo ya tafi da ni ne Ubaidah ke son haka.Ina gama sallah ya fita bayan yayi mini wani kallo,turare na fesa sai kuma na yi zaune.

“Ki je yana jiranki” cewar Mamu, har zan tafi sai kuma ta miƙo mini wayarta ta ce na kira mata Sulaimanu.Yadda na ga tana farin ciki sai na ji wani sanyi a raina,ina jin ya ɗauki kiran na fita.Zaune ciki mota na same shi,ya buɗe mini gidan gaba na shiga na zauna tare da gaishe shi,bai amsa ba sai ce mini da yayi “na yi kewarki ” wani irin dummm na ji kunnuwana sun yi sai na ji kamar dai ni ce ban ji daidai ba,amma abin da ya ci gaba da cewa yasa na yarda eh hakan ne ya furta.

“Har lambarki na karɓa gun Ubaidah sai dai ba ta shiga”
Ina shirin yin magana sai ganin Abba na yi ya shigo layin,idonsa kuwa na kan motar.

“Suwaah?” ya kira sunan da shi ne ya ƙirƙiro shi,na amsa da “umhum?” ba tare da na juyo ba,key ya yi wa motar muka bar wurin daidai lokacin kuma shi Abba ya isa a ƙofar gidan.Na ja wani dogon numfashi saboda ko ba komai bai zubar mini da mutumci ba a gaban Ya Ubaid.

Sai da na ga mun hau titi da kyau amma Abba bai biyo mu ba sannan kawai na saki jikina.Na ɗan waigo na dube shi sai na ga ni ɗin yake kallo,na saki ɗan murmushi tare da sunne kai.Bai ce komai ba har muka isa can gidan nasu wanda ya cika da jama'a saɓanin namu da babu wanda Mamu ta sanarwa.Cikin zumuɗin son ganin Udah na ɓalle murfi na fita,ina shiga kuma direct a can ɗakinta na yi tsinke.Ba ta yi shiri ba,tana dai zaune danginta duk sun kewaye ta.

Guɗa na yi tare da zuwa na faɗa jikinta,a tare muka saki kuka muna rungume juna gam.Tsawon lokaci muna a haka kafin na janye daga jikinta,na ja hancinta ina mai ce “my Udah ta zama amarya”
Ta turo baki gaba,na ce “ki je ki yi wanka ki yi shiri ”

“Na ƙi! Sai yanzu za ki zo?” ta faɗa tare da kama hannuna zuwa can bedroom,“ki zaɓar mini kayan da zan saka zan shiga wanka na fito” ta faɗa tana nuna mini tulin kayan amare da ke kan gadon,haka na shiga duba su ko da take fitowa tuni na fitar da waɗanda za ta saka ɗin.Ni na taimaka mata ta shirya,sannan ta miƙo mini wanda zan saka su ɗin size ɗina.Na ga jikina na cire na saka sabbin,hatta sarƙa da ɗan kunne duk nata na saka.

Muna fitowa aka soma yi mata hotuna kafin mu sauka ƙasa,inda mai hoton da aka kira ya yi mana iri-iri.Har da Ya Ubaid ya shigo a hoton ,inda na gode wa Allah da har aka gama shagalin bikin anty Hamida ba ta zo ba.Sai ana dab magarib na baro gidan,cikin adaidaita na koma.

Ina shiga gidanmu Abba ya ce “daga gidan uban wa kike? Wato ni za ki nunawa ke kin isa kin tunbatsa a gabana ƙato ya zo ya ɗauke ki?” tsaye na yi jikina na rawa .
Mamu ta fito tana kallona,yayin da Mama Lantana ke cewa “ƙarshen raini ya kai a ɗaura auren ɗanka amma ba ka da labari? Amma ai gara dai auren kan yawon ta zubar da take yi ,ni kamar ma ciki ne da ita ya kamata dai ka kai ta asibiti a duba mana ita kar ta kwaso mana abin kunya”

Tamkar ta zuga Abba kuwa haka ya soma yin masifa yana zagina ni da Mamu,a ƙarshe ya ce wa Mama Lantana ta duba ni tun da dama ta saba yin ungozumanci.

“Ban gane ta duba ta ba?” Mamu ta tambaya cikin wani irin yanayi.
“In kika ƙara yin magana Zainaba akan aurenki,ke Lantana ja ta ki duba mini ita” Abba ya faɗa,Mama Lantana ta karɓi fitilar hannun Abba tana mai kallona.Daidai nan free page ya ida,mai son ci gaba group biyu ne.

Normal group 300:Posting biyar a sati
Vip group 600: posting goma a sati.
Via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822

NB: Daga lokacin da ya zama complete 1k ne farashinsa.
[12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCRW☀️
____________________________________________

01

Cikin duhun dusar ƙanƙara wata mata mai ƙusumbi ke ta ɗangala sanda cikin sauri har ta isa wani ƙaton kogo mai cike da hayaƙi kamar an yi gobara.Tana shiga kogon ya fara rawa yana fitar da wani sauti,baƙin bargon da ta luluɓe kanta da shi ta sauke kan kafaɗunta hakan ya bayyanar da shafafar fuskarta wacce babu ido,babu tsinin hanci sai iya baki kawai.Bakinta ta buɗe tana yin wani gurnani mai fitar da magana cikin wani yare na ƙarnin baya “ uleja naho kajulu ramhakaya fyayal!” cak kogon ya tsaya da rawar da yake tare da ɗaukar wani irin shiru kamar mutuwa ta ratsa,babu jimawa kuwa wasu fararen halittu suka fara shawagi ko ta ina.

Da sauri ta zube kan gwiwanta tana mai buga gundulalun tafukan hannunta a ƙasa tana mai daɗa furzo wasu kalaman.

“Za ki iya gabatar da abin da ke tafe da ke” wata murya ta ratso iska ta bata umarni.

“Naomi!” ta furta cikin rawar murya.

“Alƙaluman doka sun riga da sun ƙafe babu wani canji da za mu iya yi miki” aka bata amsa.

“Ita ɗin yarinya ce ƙarama ƙwaƙwalwarta ba za ta iya ɗaukar wannan hatsabibin tashin hankali ba” tana gama rufe bakinta wata tukunyar ƙasa ta faɗo a gabanta ,“ki bata waɗannan ruwan ta sha daga nan komai zai tafi kan tsari”

Tukunyar ta ɗauka kafin ta gyara luluɓinta sai kuma ta fito,bai wuce tako uku da ta yi ba sai ta furta wani furuci wanda ya haifar da wata hatsabibiyar guguwa tashi ta zo ta zagaye ta tana fitar da wani iska,sannu a hankali guguwar ke daɗa yin sama da ita a haka ta ɓace ɓat kamar walƙiya ba ta bayyana ko ina ba sai a ƙofar gidanta.


Ina zaune ina ƙulla garin magunguna na ji motsi,da sauri na ɗago kai sai na hangi Maa na daidaita rufin ƙyauren gidanmu.Murmushi ne ya wanzu a fuskata ba tare da na ce mata komai ba na ci gaba da kallonta har ta ƙaraso ta zauna kusa da ni tana mai miƙo mini tukunyar hannunta.Na karɓa,sanyin haɗi da wani shock suka ratsa ni yayin da na ji kwaɗayin shan ruwan ciki.Baki na kafa na soma shan abin da ya kasance a ciki don sai bakina ne kawai ya iya tantance mini kallon kitse na yi wa rogo don kuwa ba zallar ruwa ne ba. Ina ajiye tukunyar sai na ji tamkar wacce aka yi wa wankin ƙwaƙwalwa,wasu abubuwa da suka keɓancin mahaifiyata nake son sani.

“Maa me yasa ake kiranki da mayya?”
“Saboda ababen bauta sun mallaka mini baiwar da ta keɓanta da ta sauran mutane”
“Kina nufin makantar ido?”
“Eh! ”
“Amma ai kina gani duk da babu gurbin ido a fuskarki ”

“Naomi??” muryar ƙawata ta katse zaren tambayoyin da nake yi wa mahaifiyata wacce ta kasance jigona,bango abin jiginata.

Miƙewa na yi da sauri ina ƙara gyara zaman fatar dabba wacce ta suturta tsaraicina ina mai duben Debora wacce ke sanye da wani tsohon bargo duk ta yane jikinta da shi.Murmushi ta sakar mini kafin ta yi mini alama da hannu,Maa na duba ina mai cewa “zan yi wa Debora rakiya ne”

“To kar ki jima saboda lokacin zuwa farauta ya kusa” Maa ta bani amsa,ba tare da na ce komai ba na kama hannun Debora muka fito ƙofar gidanmu wanda ya kasance na kara.


“Ya meke labari?” na tambaye ta .
Kamar munafuka ta yi ƙasa da murya ta ce “zo mu je na nuna miki wani abu” sai kuma ta fara ɗan gudu-gudu tana nufar bayan gari yayin da ni kuma nake take mata baya har muka isa bakin Teku .Da wani irin kallo na bi ta da shi ina mai cewa "me kuma za mu yi a nan?”

Da hannu ta yi mini nuni da can tsakiyar ruwa,sai dai sam ban ga abin da take son nuna mini ɗin ba.Lura da hakan yasa ta ce “yi kamar za ki rufe idonki” hakan na yi na lumshe manyan idona kafin na ɗan buɗe su a hankali sai a lokacin na ga wani abin mamaki wanda tunani da hankali ba za su ɗauka ba.Dogon tsani ne a cikin ruwan tare da shata wata doguwar hanya da alamu za ta ɓulle a wani wurin.Umarnin zuciyata ƙafafuwana suka bi ba tare da na shirya hakan ba na ji sanyin ruwa ya ratsa ni.A hankali nake tafiya har na isa kan tsanin na fara taka matakalansa sai dai ban fi tako uku ba na ji kamar an tunkuɗo ni sai ganina na yi a wani wajen na daban ko kuma na ce wata duniyar wacce ta sha banban da wacce na taso na tsinci kaina a cikinta.


Wasu halittu ne masu irin siffata sai dai yanayin launin fatarsu da kuma shigarsu ya sha banban da irin ta duniyarmu.A karon farko da na ji tsoro,don ban taɓa ganin irinsu ba .Ƙafata ta hagu na ɗan mayar a baya ina kallon yadda wani mutum ke musayar wuta shi da maƙarabansa,ina daf da na koma cikin ruwa muka yi ido huɗu da shi hakan ya haifar mini da matsanancin faɗuwar gaba tare kuma da rikicewar tunani.Mun shagala da kallon juna ,ƙarar wani abu da ban san me ake kiransa ba ya dawo da ni hayyacina.Sai da na yi dogon nazari sannan na fahimci cewa ta cikin ƙirjinsa ne aka halba masa abar kashe mutane.Faɗuwa yayi ƙasa,wanda hakan ya jawo hankalin tawagarsa kusan su duka na ji sun ce “yalaɓaiii?” kafin su yo kansa,ɗaya daga cikinsu ne ya zube ƙasa tare da ɗora kansa kan cinyarsa yana mai cewa “Naslam?” cikin tashin hankali yake kamar yadda fuskokin sauran suka bayyana.


Abokan adawarsu ne suka fara yi musu sarƙa suna gargaɗarsu da su miƙa musu wannan mutumin kawai suke buƙata in kuma sun ƙi za su kashe su duka su tafi da shi.


“Rayukanmu fansa ne akan shugabanmu babu gudu babu ja da baya don haka dakaru ku juya ku fuskance su” shi ne abin da ya faɗa yana mai shimfiɗe Naslam ɗin.

A wannan gaɓar ce na ga wani al'amari mai shige da irin rayuwarmu ta can duniyar,yadda su mutanen da ke neman ran Naslam duk suka wani zazzalo harshe waje suna sarrafa shi,kafin ƙyaftawar ido sai gawarwaki nake gani suna faɗuwa.

Idona na ji suna yi mini ƙaiƙayi ,babu jimawa suka furzo da wani hatsabibin haske wanda ya tarwatsa taron Mayun duk suka faɗi babu rai sai ɗaiɗaiku ne suka gudu.

“Naomiiii?” na ji muryar Debora tana kirana daga ta can ɓangare,kamar kifi haka na faɗa ruwa na koma duniyarmu.Ko da na fito daga cikin ruwa jama'ar gari na tarar duk sun cika wurin suna jiran fitowata.Ko kaɗan babu wani damshi ruwa a jikina a bushe nake ƙamas,sai dai a akwai banbanci tsakanin lokacin da na shiga da kuma yanzu da na fito.Kaf illahirin jikina ya rine yayi baƙi yayin da kuma wani abu da nake tunanin ƙusumbi ne ya bayyana a bayana.Fuskokin wasu cike da mamaki yayin da wasu kuma na hango tsoro da hassada a tattare a ciki.



“Naomi me kike yi ƙasan ruwa kusan kwana biyu ba ki fito ba?” ƙawata Debora ce ta zo gare ni tare da tambayata.


“Kwana biyu ?” na maimaita yayin da kuma cike da mamaki,ɗaya daga cikin tsofin garin ta matso tana mai nuna ni da yatsa tana mai cewa “dama tun ranar da aka haife ki na hango ajalin mahaifiyarki a tattare da ke saboda kin tabbata butulu ki rasa wacce za ki kashe sai wacce ta kawo ki duniya” sai kuma ta juya ta fuskanci mutanen gari tana mai cewa “kuna ta tambayar wa ya kashe Maa to ƴarta ce”

Normal mutane ne kawai suka tsorata da furucinta yayin da su kuma dangina masu ido uku suka rufo kaina suna mai cewa “ita ma a kashe ta” sai dai ko kusa da ni ban bari sun ƙaraso ba na yi wani furuci duk suka ƙame ƙyam a wuri guda kamar wasu bishiyoyi.

Magana na soma yi sai dai abin mamaki ba muryata ba ce ke fita,ta mahaifiyata ce.Gargaɗi ne mai ban tsoro haɗi da bushara ga waɗanda suka yarda suka miƙa wuya a bisa sabuwar dokar da na shimfiɗa musu.Kamar yadda ake rusunawa sarki haka duk suka zube suna jinjina mini haɗi da gaishe ni,ƙawata Debora ce kawai a tsaye tana wani mayen murmushi mai fitar da tsantsar farin ciki.
Hannunta na kama na ratsa ɗimbin jama'ar muka wuce,har muka isa gidanmu ni da ita babu wanda ya cewa wani kanzil.A ɗaki na tarar da gawar Maa a kwance tuni ta fara ruɓewa tsutsotsi na shige da fice ta bakinta.A lokacin ne na ji wata murya daga can cikin ruhina tana bani mafita da shawari,yayin da ni kuma na yi tako ɗaya na aiwatar da abin da na ji.Hannuna na ɗora a goshin Maa na soma yin wani furuci wanda ban koya ba,kawai zuwar mini yayi.Babu jimawa ta soma bajewa tana komawa hayaƙi a haka har ta baje gaba ɗaya sai sautin muryarta da ya soma yi mini bushara “ ina tare da ke a duk inda za ki kasance ƴata Naomi kar ki yi baƙin cikin rabuwarmu wannan shi ne matakin nasararki,hidimar da za ki yi kuma na san mahaifinki zai yi alfahari da ke.Zan tafi na koma asalina,a duk lokacin da kika yi kewata ki je magudanar ruwa ki cilla dutsen karlis zan jiyo sautin kiranki” tana gama faɗar haka aka kece da ruwa mai bala'in ƙarfi wanda rufin ɗakinmu bai iya tare shi ba.Na yi saurin lumshe idona ina jin sabuwar halittata na yi mini wani irin motsi haɗi da ƙara girma wanda silar haka na ji kafaɗata ta ƙara nauyi hakan ya haifar mini da ɗan rusunawa kamar dai yadda mai ƙusumbi ke yi.

An ɗauki lokaci kafin ruwan ya tsaya cak ,sai a lokacin kuma na tsinci muryar Debora na cewa “haƙiƙa kin kasance mai babban rabo ƙawata,ina mai sanar da ke cewa nan ba da jimawa ba amon mulkinki zai ƙetare duniyarmu ta ruwa ya tsallaka duniyar turɓaya ”


Sai da na haɗiye wasu yawu masu ɗaci kafin na ce “a yau na ga wata duniya ,wasu mutane na gani a siffar tawaga biyu,ɗayar tawagar ta kasance ta Mayu ce yayin da ɗayar kuma ban san ta mece ce ba abin da kawai na iya gani shi ne fuskokinsu na fitar da wani irin haske mai natsuwa haka ma hannuwansu.A goshin shugabansu na ga abin da ya kusan dakatar da numfashina,wani baƙin tabo ne wanda ya ƙawata goshin nasa ya kuma fitar da tsantsar hasken fuskar tasa”


“A yadda kika siffanta su sak sun fito a al'ummar nan da ke bautar wani Ubangijin Ka'aba,sam ba su nuna tausayinsu ga matsafa da kuma waɗanda suka saɓa dokar Ubangijinsu”

Zuciyata ce na ji tana wata irin tafasa hakan yasa na juyo a fusace ina kallon Debora wacce ita ɗin ta kasance ƴa ga babban malamin ilimin tarihin duniya.Tun da na ji ta ambaci haka tabbas kuma na san gaskiya ta faɗa ,“dama har akwai masu tsanar Magic a duniya? Shin ba su san tasirin tsafi ba ne ko kuwa sun jahilci lamarin ne?”


“Ko ɗaya! Su ɗin sun yi imani a kaf duniya babu wanda ke tafarkin gaskiya sai wanda ya kasance ɗaya daga cikinsu.Wannan dalilin ne ma yasa suke shirya yaƙi duk shekara suna shiga ƙasashen matsafa.Kin ga mu bar maganar nan ma saboda ba ta shafe mu ba”

“Ta ya za ki ce ba ta shafe mu ba alhalin kin san duniyarmu ba mu yarda da wani addini ba? In fa suka farmake mu?” ban san me yasa na ji tsoro da shakku dangane da mabiya addinin ba, musamman in na tuna fuskar mutumin nan Naslam.


Debora ta riƙo hannuna tana mai cewa “masana tarihi sun tabbatar mana cewa yankinmu zagaye yake da ƙoramai ta yadda babu wata halitta da ta isa ta ƙetaro izuwa nan sai da izinin esprit ɗin ruwa,kina tunanin uwayen gijinmu za su lamunta a kawo mana hari ?” wani irin numfashi na sauke ko ba komai kalaman ƙawata sun ɗan rage mini fargaba amma duk da haka ban yi ƙasa da gwiwa ba na yi shela ina son ganin dukkanin matsafan garin domin zuwa kowacce kusurwar ruwa su kai saƙo zuwa ga aljanai da ruhikan ruwa.......
[12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

02

Ƙananun shekaruna ba su hana ni jagorantar tsoffi da kuma dattizai zuwa bakin kowacce kusurwar ruwa ba.A tsaye nake ƙiƙam ina kallon yadda ake masayar kalamai tsakanin aljanun ruwa da kuma matsafa,kamar yadda na faɗa musu tun farko ina son a bai wa garinmu kariya haka su ma suka faɗa sai dai aljanun sun ƙi lamincewa da ƙudirinmu kai tsaye sai da suka kawo nasu sharuɗan.Daga ciki akwai bayar da jinin baƙaƙen dabbobi duk ranar laraba, sannan a kowacce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login