Showing 27001 words to 30000 words out of 55823 words

Chapter 10 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

49

ya kai bakinsa ya ce “ƙanwar na fa samu mata aure”

Da wani irin sauri Hamida ta juyo ta dube shi tana washe baki,cike da tsantsar farin ciki ta ce “a ina? Wane aiki take yi? Ƴar wane family ce?”

Ido ya zuba mata kafin ya ce “ke ban son shirme ni ina ruwana da family ɗinta,kawai ni dai ina son ta”

Hamida ta taɓe baki tana cewa “tun da ka faɗi haka ya tabbata kuwa ƴar talakawa ce,to Allah yasa dai tana da kyau don in ka ɗauko mummuna abin zai yi yawa wai shege da hauka ”

Kallon mamakin da yake yi mata yasa ta ci gaba da cewa “eh mana yadda kake babban Dr ai ka san dole ka tsaya ka ɗauko matar shiga tsara wacce ba za ka ji kunyar nunawa ba akan kowanne irin taro”

Kai ya girgiza yana mai cewa “na ma fasa nuna miki hotonta”
Ta ce “ai gara dai ka nuna mini in ba ta yi ba na sanar da kai,saboda ina son matar da za ka aure a ce ta fi Ubaidah kyawu ta hakan ne za ka nuna mata ka yi mata zarra”


Abdul Hamid ya ce "wallahi ta fi Ubaidah kyawu kawai dai don iyayenta ba masu kuɗi ba ne amma ina mai tabbatar miki in ta ji gata sosai za ta fito da irin ƴaƴan Daddy”

Hamida ta yi shewa tare da cewa “to kai ka sa ta zama ƴar gidan Daddyn,bari ma na tashi na ɗauko takarda na yi maka liste na abubuwan da za ka saya mata,cikin wata ɗaya kacal za ta dawo ƴar gayu” ba tare da ta jira cewarsa ba ta miƙe ta je ta ɗauko takarda kuwa ta zauna ta soma rubuta masa shi dai yana daga gefe yana kallo sai bayan ta gama ya karɓa ya soma karantawa.


★Sulaimanu.

Bayan sun gama waya shi da Ubaidah sai ya ƙara ɗaukar tazarar lokaci kafin ya koma gida.Ya ci sa'a kuwa duk sun kammala masha'arsu yana jin wasu suna hirar batsa yayin da wasu kuma ke baccin gajiya.Ɗakinsa ya shiga,ya kunna fanka sannan ya kwanta yana tunanin ko mene ne ya samu Suwaibar amma bai ji hankalinsa ya wani tashi sosai ba saboda ya san Ubaidah sai ta fi kowa kulawa da ita.Cikin hukuncin Ubangiji ya samu bacci mai daɗi ya ɗauke shi har da tsarabar mafarkin Ubaidah,da ya farka sallar asubah sosai ya ji daɗin mafarkin don ya samu ya rage dattin da ke damunsa.Tsabtace jikinsa yayi ya fito ya wuce masjid,yadda Abbas ya wani shige sawun gaba sai ya bai wa Sulaimanu takaici.A zuci ya ce ‘ ko kunya bai ji,jiyan nan ya gama yin laifi mafi muni amma ga shi a sawun gaba,ko da wane irin ƙarfin zuciya ne ya zo ganawa da Ubangijinsa?’ sai kuma ya basar,ko da aka gama sallah bai koma gida ba nan ya zauna yayi ta zikirori da jinjina haɗi da godiya ga Ubangijinsa da yake tsare shi daga dukkan tarkon matan banza.Sai da rana ta hudo sannan ya fito daga masjid ɗin,yana shiga gida ya tarar matan suna ƴar rige-rigen shiga banɗaki yin wanka.Kai kawai ya kawar yana istigfari kafin ya shige can ciki,wayarsa ya ɗauko ya turawa Ubaidah saƙo sai kuma ya hau facebook hana chating hakan ya ɗauke masa da hankali sam bai ba kwanyarsa damar ma tsayawa jin abin da suke cewa ba.Kafin wani lokaci gidan ya ɗauki wani shiru,sai a wannan lokacin ya fito sai ya ga Abbas na wankin toilet.Suna haɗa ido ya ɗan sunne kai,shi kuwa Sulaimanu baki ya taɓe yana mai cewa “kunyar Ubangijinka ya kamata ka ji ba tawa ba,ni mene ne nawa a ciki? Lada gare ni ko zunubi? Iya abin da zan ce ma shi ne ka ji tsoron ka guji saɓon da ke rushe aikin lada a nan take”


Abbas wanda can farko mutumin kirki ne,zama da mutanen banza ne ya ja ra'ayinsa.Ɗan numfasawa kawai yayi yana sauraren abokin nasa kafin ya ce “ka shiga ka yi wankan,na gama wanke toilet ɗin”


Sulaimanu ya saki baki cike da mamaki yana kallon Abbas ɗin kafin kuma ya shige banɗakin ya yo wanka ya fito.A gaggauce ya shirya cikin uniform ɗin ƴan sanda kafin ya fiddo babur ɗinsa ya wuce.


★Ubaidullah

Bayan ya ajiye su Suby direct gidan gonarsa ya wuce,yau jinsa yake wani iri na daban tamkar sabon jariri sabuwar haihuwa wanda ya shigo zangon wata sabuwar rayuwa da bai san da ita ba.Murmushin da Suby ta yi masa har ƙahon zuciyarsa haka ya ji shauƙi ya cake shi,yana driving yana tunaninta har ya isa aka buɗe masa babban get ɗin.

Ya jima sosai zaune cikin mota kafin ya fito,ma'aikata masu kula da wurin duk suka zo suka gaishe shi.Zagaye ya soma yi kafin ya nufi wani keɓaɓen wuri da aka tana domin hutawarsa shi ɗaya.Wayarsa ya fiddo yana jin ina ma yana da lambarta da ya kira ta ko ya tura mata saƙo don jin ya take,saboda haka kawai yake jin kamar ba ta cikin walwala.Tun yana jurewa har ya kasa ya kira Ubaidah,bayan sun gaisa sai kuma ya yi shiru ya rasa ta ina zai fara.

“ Hello!” Ubaidah ta faɗa .
Ya ja numfashi kafin ya ce “tana ina? Ya jikin nata?”

“Ta nan a kwance zazzaɓi ya rufe ta kuma ta ƙi shan magani,sai addu'o'i dai da nake yi mata a ruwa tana sha” ta basa amsa ,shi kuwa ido ya rumtse yana cewa “zan turo likita ya duba ta”

“A'a Ya Ubaid ban so don Allah...” ya ji amon murya Suby daga can cikin shashekar kuka.Hankalinsa sai ya ida tashi,kiran ya katse ya kira Abraham cikin ɗan taƙaitaccen lokaci yayi masa bayani kasancewar shi Abraham likita ne a cikin sojan.

“In kuma an ce ka faɗa soyayya ka ƙaryata mutane ” Abraham ya faɗa yana ƴar dariya.
Ubaid ya ce “don Allah duk mu yi wannan daga baya amma ka je ka duba ta,ni na yi nisa da gari kafin na iso za ta galabaita”

Abraham ya ce “ ok turo mini location ɗin gidan”

“Zan turo maka lambar Ubaidah sai ka kira ta ” a haka suka tsayar da zancen,yana kashewa ya tura masa lambar shi ma sai ya tashi ya fito ya shiga motarsa domin komawa cikin gari.



Ban taɓa sanin tashin hankali na haifar da zazzaɓi ba sai yanzu,zuciyata wani irin ƙuna take yi mini ga shi kuma babu wata mafita don na san ko na sanar da Mamu ba za ta yarda ba,uwa uba daɗa Abbanmu wanda ba wai mu da muke gida ɗaya ba hatta maƙwabta sun san da an shanye shi.
Kaina na kan cinyar Ubaidah sai addu'o'i take yi mini a ruwa ina sha tana kuma shafa mini ruwan a fuskata da take daɗa yin zafi fiye da ko ina na jikina.Ina jin lokacin da take waya da Ya Ubaid saboda hand free/main libre ta sa saka.Cikin ƙwatowar numfashi na roƙe kar ya turo likita,jin ya datse kiran na yi tunanin ya bar zancen har sai da na ji Ubaidah na yin wata wayar tana yi masa kwatancen gidanmu.Ba a ɗauki lokaci ba kuwa ya zo,ita ce ta fita ta shigo da shi.Ina jin maganar Mama Lantana na cewa “abin kuma har ya kai da shigo mana da ƙattai cikin gida?”

“Mama ni likita ne na zo duba marar lafiya ne” na ji muryar wani namiji na yi mata bayani.

Ta ce “a'a ba sai ka yi ƙarya ba ɗan nan wuce ai kowa da sana'ar da ta karɓe shi” cikin tsantsar farin ciki take faɗar haka.
Sosai kuma na yi mamakin ta yadda aka yi Ubaidah ba ta tanka ta ba har suka shigo ita da likitan.Wani ƙarfi ne ya zo mini na tashi zaune ina ce masa “don Allah kar ka yi mini allura ka bani magani”

“Ina ga wannan sai kin riƙe mini ita” ya faɗa,Ubaidah ta matso za ta riƙe ni na ce “wallahi in kika taɓa ni cizon ki zan yi”

Ta yi wata dariya tare da zuwa ta yi mini kyakkyawan riƙo,wasu hawaye ne suka soma zubo mini kafin kuma na soma yin ihun azaba.Bayan ya yi mini allurar ya warware bandejin ya zuba magani sannan ya sake mini wani.

“ A yi shiru Madam an gama” ya faɗa cikin raha,sai kuma ya kira Ubaidullah a gabanmu yana mai cewa “aboki kana fa da jan aiki a wurin nan,dakyar na samu na yi mata allura abu sai ka ce ana yaƙin duniya” ban ji abin da Ubaid ɗin ya ce ba, Dr dai yayi ƴar dariya kafin Ubaidah ta yi masa rakiya ta dawo.Babu jimawa kuwa Mamu ta dawo, Ubaidah ce ta yi mata bayanin banda lafiya ne wani abin mamaki ko kaɗan Mamu ba ta nuna damuwarta ba a kai ballantana na yi tsammanin samun kulawa.


Kiran Ubaid ya sake shigowa wayar Udah,amma sai ba ta ɗaga ba saboda yadda damuwa ta sauko mata sai wani satar kallon Mamu take yi.Horne muka ji a ƙofa,ta miƙe tana cewa “ina ga Ya Ubaid ne”sai ta fita babu jimawa ta dawo ta ce mini “shi ne.Ki ƙoƙarta ki taso mu tafi”


“Tsoron fita nake yi Udah,ban son ganin jini” na furta.
“An rufe ramen fa,ki taso mu je” ta faɗa .Sai da na wanke fuskata kafin na miƙe na canza hijabi,hannunsa cikin na Ubaidah muka fita.Yana zube cikin motarsa ,yana ganinmu ya fito.Ƙatuwar leda ya miƙawa Ubaidah sai kawai ta tafi ta bar ni a nan tsaye,nan take jikina ya fara yin rawa dole na jingina jikin motarsa.


“Ya jikin naki ? Ya kukan kin gama?” ya tambaye ni.
Na ɗan sunne kai murmushi jin wai har da kuka ya tambaya.
Ya ce “ko a sake kiran Dr Abraham?” kai na girgiza masa cike da tsoro,sai na ji yana murmushi mai sauti na ɗauke a hankali na dube shi idonmu ya sarƙe cikin na juna ,na ɗan kawar da kai na dubi ƙofa na ce “har yanzu ba ta dawo ba”

“Kin matsu ta dawo ta tafi da ke don kar na tsere da ke ko?”
Kunya furicinsa ya bani sai na rufe fuskata,yanzu ma dai murmushi mai sauti yayi yana cewa “wuce ki koma gida”
“To” na furta tare da saurin tafiya,tako biyu kawai na yi na ji amon muryarsa na cewa “ki kula da kanki” ban juyo ba sai dai sosai kalmar ta dake ni har na kasa motsi na wani ƴan sakanni kafin na wuce ciki.

A tsakar gida na tarar da Mamu ita da Mama Lantana suna yankan naman akuyar tsafi,ban ce musu kanzil ba na wuce ɗaki.Ubaidah na ganina ta soma yin dariya,"su Suby an shiga kogin soyayya ”

“Wace soyayya kuma?” na tambaye ta,sai ta yi mini kallon kar ki raina mini hankali kafin ta nuna mini abin da Ya Ubaid ɗin kawo.Fruit ne da jus sai kuma magunguna,iya lemun kawai muka sha kafin Ubaidah ta yi mini sallama ta tafi ta bar ni nan ni ɗaya.

Sai da aka kira sallar la'asar kawai na fita na ɗauro alwala,ina ƙoƙarin komawa na ga Mama Lantana ta ciro zuciyar dabba wacce nake kyautata zaton ta akuyar nan ce,an rubutu a jikin zuciyar sannan an tsire ta da wani tsinke.Kan garwashi na ga tana juya ta tana gasa ta,fuskarta ɗauke da murmushi.Daidai nan Mamu ta fito daga banɗaki ,kan wani dutse ta zauna tana dafe ƙirji haɗi da watsa ruwa jikinta.
Ƙafafuwana suka ɗauki wata irin rawa,dakyar na isa ɗaki na zube kamar wasu kayan wanki.So nake na sanar da Ubaidah sai dai kuma ina ganin lokaci yayi da zan ɗauki dakon damuwata ni ɗaya na bar Udah ta huta haka nan,dakyar na gabatar da Sallah.Ina nan zaune kan dadduma Mamu ta shigo,ita ma a zaune ta yi sallar tana idawa ta kwanta tana mai cewa “bani ƙanƙara a frigine ”

Na tashi dakyar na buɗe na ɗauko na miƙa mata,cikin riga ta saka shi daidai zuciyarta sai ta soma jan numfashi kamar mai shirin mutuwa.Gefe na koma na zabga uban tagumi,kafin kuma tunanin kiran Sulaimanu ya faɗo raina.Cikin kuka na shaida masa Mamu ba ta da lafiya,sai dai amsar da ya bani ita ta ƙara saka ni wani tashin hankalin.


“Mama Lantana ta sani? Ni yanzu ba zan iya barin nan ba kin san halinta sarai in na je faɗa za ta yi mini,kuma na san ko na tambayi izininta ba barina za ta yi na zo ba” ya faɗa cikin wata murya.

“Wa kenan zai baka izini?” na tambaya don dai tabbatar wa.
“Mama” ya bani amsa,sai kawai na kashe kiran.Haka na ci gaba da kallon Mamu na murƙususu,tun ina hawaye har ta kai da na yi ƙarfin halin tashi na fito.Mama Lantanar dai na gani a inda take tana gasa zuciya sai wani baƙin abu take ɗiga wa mai wari.Idona sun rufe , wannan yasa kawai ba tare da wani tunani ba na tunkare ta tare da zuwa na ƙwace tsinken hannunta na zaro zuciyar.Ta wani miƙe da sauri za ta karɓa kawai na tsira mata tsinken a hunnunta har sai da ya hudo ta bayansa,ta saki ihu yayin da ni kuma na je na ɗauko ruwa mai sanyi na zubawa zuciyar tare da ina mai nufar ɗaki a guje sai na samu Mamu tana wani jan numfashin sassauci....

Normal group 300
Vip group 600
Via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[11/06 17:41] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*
10


Nan take na ga bacci ya ɗauke Mamu ,tausayinta na ji kawai sai na shiga yin kuka ga ni kuma da gasassar zuciya a hannuna wacce dukkan alamu suka nuna an yi aikin ne domin cutar mini da mahaifiya.A can tsakar gida na soma jin maganar Abbanmu,yadda muryarsa ke rawar tsoro na fahimci tuni ya samu labarin aika-aikar da na yi wa Mama Lantana amma dai ban fita ba sai ma zaune na yi ina tunanin yadda zan yi da zuciyar.Uncle Suhail ya faɗo mini da rai sai dai banda lambarsa dole dangin naƙi na kira Ubaidah,tana ɗagawa na fashe mata da kuka.

“Mene ne kuma? ” ta tambaya.

“Ki zo gida ina cikin tashin hankali Udah ,Mamu na shirin mutuwa saboda aikin da Mama ta yi da zuciyar akuyar nan” na faɗa ita kuma ba ta ce komai ba ta kashe,ina nan cikin halin da ya aure ni ta zo.Miƙa mata zuciyar na yi,kafin ta ce “tashi mu tafi” dama da hijabi a jikina haka na miƙe muka fito. Tsakar gidan babu kowa ,muna fita waje muka shiga motarta sai gidan Uncle Suhail ɗin.Yanzun ma Ubaidah ce ta yi masa bayani,ya karɓi zuciyar,yana karatu yana bubuɗe ta nan ne fa asalin tashin hankalin yake yadda can cikin zuciyar yayi ta ciro jariran allurai ƙananu sosai duk in ya cire ɗaya sai wani baƙin ruwa mai wari ya ɗiga a haka har ya kammala ya ɗebo ruwan randar nan ya wanke zuciyar ya ce zai fita ya rufe dukkan abin nan.Bayan ya dawo ya ce “ya kamata ku fallasa matar nan in ba haka ba ta'asar da sheɗancin da za ta yi a gaba sai ya fi wannan”

Ubaidah ta dube ni na ce “ko na faɗa babu wanda zai yarda,Abbanmu ya zama mijin ta ce sai abin da ta shimfiɗa masa ta hau akai ne kawai yake yi.Yayana ma da Mamun ta haifa shi ma ya zama ɗan Mama Lantanar na kira shi a yau ina sanar da shi mahaifiyarmu ba ta da lafiya amma ya ce sai ya tambayi izinin Mamar kawai zai iya zuwa.Faɗa mini to,wane ne zan sanar da shi don tona mata asirin ? Babu ”

Uncle Suhail ya furzar da huci kafin ya ce “to ki dage da addu'a domin ita kaɗai ke canza ƙaddara” da wannan muka fito daga gidansa.


A ɓangaren Mama Lantana kuwa,cikin raɗaɗin azabar nan ta je ta shiga ɗakinta ta kira Abban yara ta sanar da shi.Babu jimawa ya zo kuwa,yadda ya ga tsinke a hannun Mama Lantana sai hankalinsa ya tashi ya soma tambayarta amma babu amsa sai asibiti da take cewa ya kai ta.Cikin adaidaita suka je, asibitin kuɗi ce wannan yasa dandanan aka yi mata aiki aka cire tsinken tare da yi mata allura aka kuma naɗe hannun da bandeji.A bisa hanyar dawowa gida Mama Lantana ke cewa “daga na ce don me za ta jawo mana ƙato har cikin gida inda ka ga mugun kallon da ta yi ta ma kama hannun saurayin suka shige ɗaki,abubuwan da kunnuwana suka jiye mini marasa daɗi yasa na je na leƙa saboda kar a ce don tana ƴar kishiyata ce,wallahi malam turmi da taɓarya na tarar da su .Haka na dawo jikina na yi mini rawa inda nake gasa nama,da yaƙe ƴar nan tantira ce shi ne a gaban idona ta zo ta cika bokiti za ta yi wanka,saurayin ne da ya fito na tare masa hanya na ce ba zai fita ba nan muka hau kokowa shi ne fa ta tsira mini tsinken nan a hannu amma da niyyarta idona da ya gansu ta so makantarwa” tun da ta fara magana zuciyar Abba ke tafasa yana jin kamar zai ƙone,wani abu da ya tokare masa zuciya shi ya hana shi yin magana sai mai ɗan sahun da ya ɗauko ne ya ce “ai Hajiya yaran yanzu sai addu'a haka ƴar maƙaucina ke yin wannan iskanci,yadda kika san ana layin waina haka za ki ga samari masu mota na zuwa wurinta,kuma a cikin motar fa take shiga ana yin hirar”

“Ana dai yin iskanci,ita wannan ganin uwarta ba ta gidan ne shi ne dalili kawai ni kuma ba a bakin komai nake ba”

Yadda Mama Lantana ke cacabkewa ita da mai adaidaita ita tana muzanta Suwaiba shi kuma ƴar maƙaucinsa saura ƙiris jinin Abba ya hau amma Allah ya tsare .




Sai wuraren magrib sannan muka iso gida,Ubaidah ta sauke ni tare da wucewa.Ina shirin shiga gida adaidaita ta tsaya a ƙofar gidanmu,Mama Lantana ta fito tana cewa “Abbansu ina ce ka gani da idanunka ? Dubi an sauke ta daga mota”


“Daga gidan uban wa kike?” Abba ya fito yana mai tambayata,kasa cewa komai na yi saboda ƙarya ba tabi'ata ba ce kuma ba zan iya ce masa gidan Uncle Suhail ba.

"Wane ne wancan da ya ajiye ki a mota?” ya sake tambayata,hankali tashe na ce “Abba Ubaid...”

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login