Showing 51001 words to 54000 words out of 55823 words

Chapter 18 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

40

hanci ta buɗe tana kallon duniyar ƙasa,cike kuma da burge wa da ban sha'awa take ware idonta tana kallon gidajen da aka rufe babu bismillah.Kamar misalin tukunya ce babu murfi,haka idon Mayu ke gane gidajen da ba a ambaci sunan Allah ba a lokacin da ƙafa ta tsana za a kwanta.


Suna cikin shawagin suka yi ta haɗuwa da jiragen dare na Mayu, waɗanda suka kasance na tsafi ba wai zahiri ba.

“Duk ina za su je Dadda? Ya na ga mutane cikin gwangwanin kifi?” gimbiya A'ishah ta tambayi mahaifiyarta sai dai kafin ma ta bata amsa wani jirgin na tsintsiyar tsaye ya bi ta gabansu shuuu yana ɗauke da wata tsohuwa da kuma ƙaramin yaro.


Dadda ta yi murmushi tana mai cewa “A'ishah a duniyar ɓoye abubuwan da ba za su taɓa faruwa ba ne a duniyar zahiri suke gudana a nan ɗin.Muna amfani da duk wani abu da kika sani matsayin jirgin farauta,kamar irinsu turmi,jan zanen isimi,tsintsiyar tsaye da sauransu.Ke ma in kina sha'awa ai za ki iya hawa madadin ki yi yawo kamar leda”


“To mene ne banbancinsu Dadda?”

“Sauri! In kin hau jirgi kin fi saurin zuwa inda kike so,ko ba ki lura yadda mutane ke ta wuce mu ba?”

“Na gani,amma me yasa mu ba mu shiga ba?”

“Dama ina son fayyace miki komai ne,amma yanzu da zarar wata tawagar mayun za ta wuce zan tsayar da su don rage mana hanya”


Ai kuwa babu jimawa sai ga wata tsohuwa zaune kan baƙar akuya mai ƙahonni dogaye.Dadda ta tsayar da ita tare da neman alfarma,tsohuwar ta ƙara matsawa gaba gimbiya A'ishah ta fara hawa sannan Dadda daga ƙarshe.Kamar wani babur haka akuyar tsafin ke keta hazo da su.

Gimbiya A'ishah wacce duniyar ɓoye take sabuwa a wurinta sai cewa ta yi “ita ma akuya tana cikin jerin jiragen yawo?”


Wannan karon tsohuwar ce ta bata amsa bayan ta yi ƴar dariya mai fitar da zallar tsufanta,ta ce “ jikata ita akuyar nan protector ɗina ce,suna da banbanci da jirgin dare saboda ita tana numfashi sannan kuma tana kare ni daga dukkan sharri” gimbiya A'ishah ba ta kai ga cewa wani abu ba tsohuwar ta yi ƙasa da ƙahonnin akuyar sai ta yi shuuu ta fara yin ƙasa har ta sauka a wani babban gawo wanda ya cika tanƙam da Mayu da kuma matsafa.


Girki ake yi kan wata tunkunya wacce ke da zanen ƙwarangwal ta buɗe baki.Gimbiya A'ishah ta sauko daga kan akuyar tana wani riƙe Dadda ,ita kuwa sai cewa ta yi “ wannan ita ce TUKUNYAR MAYU ( ga mai son complete na Tukunyar Mayu yayi mini magana zan yi masa discount) duk dare muna haɗuwa a nan mu ci abin da wasu daga cikinmu suka yo farauta”


Sai kuma Dadda ta ja ta suka ƙarasa,hannu ta saka cikin tukunyar da ke ta faman tiriri ta tsamo wani abu mai kamar zare amma su a wurinsu nama ne,bakin gimbiya A'ishah ta kai ita kuwa ta buɗe ta saka mata sai ta soma ci tana jin wani irin yanayi na ratsa ta.
Dadda ta saki murmushi tana jin wani sanyi na luluɓe ta,a yanzu shirye take tsaf wurin tursasa ƴarta ta auri yarima Naslam ba don komai ba don ta san a cikin tabi'ar Mayu babu kara babu jin kunya,hatta uwar da ta kawo su duniya suna iya damƙewa ita kuma babban burinta shi ne ta bayar da yarima NASLAM a dafa shi kowa ci kamar yadda yasa aka yanke wa Ummarta hukunci kisa daga kawai asirinta ya tonu ta damƙe kurwar iyayen jakariya Ali.



Bayan sun gama cin naman sai idanun gimbiya A'ishah suka ƙara buɗewa ta soma gani tarau ,babu abin da ba ta iya gani da ke jikin mutum ko dabba.Rawa suka soma yi suna zagayen wuta,duk da mutane sosai hakan bai hana ta gane wasu fuskokin ba sosai kuma ta yi mamaki kamar yadda Dadda ta ce mata tun kafin zuwansu.


Alfijir na dab da ketowa suka koma gida,ta inda suka fita ta nan suka shigo.A gajiye duk suka zube suka ta yin rankon baccin da ba su yi ba.



A ɓangaren yarima Naslam kuwa tun bayan sallar asubah ya je ya samu sarki da maganar aurensa da gimbiya A'ishah.Ya yi haka ne duk don ya bar mafarkin Naomi,ba tare da ya san alƙaluman ƙaddara sam ba su rubuta masa auren wata mace ba bayan maƙiyiyarsa.


Gari na yin haske sosai sarki ya bada shelar baikon yarima zai kasance a yau bayan sallar asar in sha Allah.



Jakariya Ali ne ya dinga taimaka masa wurin shiryawa,yana daidaita masa hullar sarauta a kai ya ce “kana ganin kun dace kai da gimbiya A'ishah?”

“Me ya ja ra'ayinka wurin yin wannan tambayar?” cewar Yarima yana kallon mai tsaron lafiyarsa Ali .

Shi kuwa kai tsaye ya ce “na ga ba sonta kake yi ba”

“Haka kuma ban ƙinta“

“Duk da haka dai ya kamata a ce ka yi dogon nazari,na fi yi maka sha'awar auren soyayya gaskiya”

“Ita ma ina sonta tun da har na damu da ita” yarima ya faɗa yana mai zuwa bakin gado ya yi zaune,jakariya Ali ya duƙa ya soma saka masa takalmi yana mai cewa “in kana son mutum bai kai sai ka faɗa ba,ayyukanka ne za su bayyana hakan”


“Ko ma dai mene ne na yanke shawarar zan aure ta,kuma ta dace da ni tun da tana da addini sosai iya wannan ya wadatar” yarima ya faɗa yana tsayar da idonsa kan tantabarsa wacce ta yi wani saƙo kamar mai sauraren hirar da suke yi.


Jakariya Ali ya juya ya dubi inda yake kallo,sai ya saki ɗan murmushi kafin ya je ya ɗauko ta ya miƙawa yarima.Ya karɓa tare da soma shafar kanta,“zan je na duba na gani in sun gama shirya wurin taron” Ali ya faɗa tare da ficewa.


Yarima ya miƙe tsaye tare da zuwa bakin window yana kallon yadda ake ta kai komo cikin masarautar.Ko ina yayi kyau,hatta dawakai an yi musu ado na sarauta .Dokinsa wanda yake hawa a duk lokacin da zai fita yayi wani irin kuka,tantabarar hannunsa ta fizge tare da fita a guje tana kaɗawa yarima iskan fukafukinta da sauri ya lumshe ido kafin kuma ya ware su yana kallon yadda ta je ta hau kan dokin,duk wannan ɗin ma bai sa ya zargi wani abu ba kawai murmushi ya yi tare da fita.

Masjid ya fara zuwa,bayan an gama sallah ne duk aka dugunzuma zuwa wurin da aka ware domin gudanar da shagalin bikin baikon.

Zinare sarki ya ware masu yawa ya bayar matsayin kyautar mun gani muna so.Ayyub wanda ya kasance mahaifin gimbiya A'ishah da matuƙar farin ciki ya shaida wa dukkan taron jama'ar ya bai wa yarima damar auren ƴarsa,duk sai aka yi kabbara tare kuma da yin addu'o'i kafin a fita zuwa can inda za a yi wasar dawakai.




Ta madubin tsafi Dadda ke kallon komai,tun lokacin da aka yi shelar yin baikon ta shirya baƙin tsafi mai ƙarfi ta tura domin hallaka yarima.Ita dai gimbiya A'ishah cike take da farin ciki duk gajiyar nan ta jiya sai ta neme ta duk ta rasa,duk da cewa kuwa ta sha bacci sosai sai wuraren goma na safe ta farka.A bakin mahaifiyarta kuma ta ji abin da ke faruwa,sosai ta so a ce ta fita ta ga yadda komai ya wakana sai dai hakan haramun ne a masarautarsu zuwan mata a irin wannan taron.



Cikin rangaji ta ƙaraso ta zo ta yi tsaye ita ma tana kallon yadda ake wasar tseren .Wani irin murmushi ya suɓuce mata lokacin da ta ga yarima Naslam ya je kusa da dokinsa za su yi wasar tseren shi da wanda ya yi nasara akan dukkan dakarun da aka tsara wasar da su.Ita ma Dadda nata murmushin ta saki tana jin cewa saura ƙiris burinta ya fara cika don ta jefa kibiyar tsafi akan dokin yarima saboda in ya hau shi sai ya masakance.

Yarima ya hau kan doki yana mai ambaton sunan Allah tare da yin kabbara,Dadda ta ɓata fuska tana mai ɗan satar kallon gimbiya A'ishah wacce har yanzu murmushi ya ƙi barin fuskarta.


“Dadda dube shi ki ga yadda yake da ƙwarjini da cikar zati, wannan shi ne mijin A'ishah ”


“Haka ne ki yi fatan Allah yasa ya ci gasar kar ya kwabsa abin ya zama abin goranta miki” Dadda ta faɗa tana mai shafar madubin haɗi da yin wani surkulle daidai nan su yarima suka fara gudun.Ƙafar dokin ta ƙure da ido ta na shirin aika masa wata gubar tsafin kawai sai ganin bakin tsuntsuwa ta yi ya caki madubin ya tarwatse.

A tare suka ja ba,kafin su kalli juna.Da wani irin gudu kuma gimbiya A'ishah ta fita don jikinta ya bata babu lafiya,mayafinta ta ja ta rufe fuskarta lokacin da ta isa filin sukuwar.

Yarima NASLAM wanda ya lashe wasar tseren dokin ya juyo yana kallon inda take a tsaye,suka haɗa ido da sauri ta sunne kai tana wani murmushi kafin ta juya da sauri ta koma.Ya ja numfashi yana jin a ransa ya yi dacen mata.




An ɗauki tsawon lokaci kafin Ummilo ta farfaɗo wannan karon ma tana yin wasu kalamai a cikin Yaren da ban fahimci me take nufi.


“Alhamdulillahi lazhi ahayana ba'ada ma'amattana wa'ileyhi nushur” ta furta tare da ware idonta a kaina,na sakar mata murmushi na ce “sannu Ummilo” ba ta amsa ba sai martanin murmushin da ta maido mini tana mai shafar gefen fuskata kafin kuma ta miƙe ta fita.Haka na take mata baya sai na ga ta shiga banɗaki,can kuma ta fito ta soma wanke hannuwa da baki da fuska da hannuwanta hatta kai da kunne sai da ta shafa haɗi kuma da wanke ƙafafu.

Mayafinta ta gyara kafin ta zo ta fara yin wata irin bauta da ban san ta mece ce ba,ni dai ido kawai na tsura mata da na ga ba ta da niyyar idawa kawai na je gun baby Mila na ɗauke ta dama tun ɗazu ta tashi.Madara na soma bata tana sha tana kallona cikin ido, murmushi na saki ina jin sonta na ratsa ni.


Banah wanda tun bayan abin da ya faru ya koma can ƙofar gida yayi tsaye,sai yanzu ya shigo yana mai tambayata “mene ne can Ummilo ke yi?”

“Ina kifin har yanzu ba a gama dafawa ba?” na tambaye shi ,don sau tari in yayi mini tambayar da raina bai so ba nuna masa nake yi kamar ban ji ba sai na ɗauko masa wani zancen.

Fita ya yi ba tare da ya ce mini komai ba,can kuma sai ya dawo riƙe da kwano yana tiriri.Kamshin kifin ya daki hancina,nan take yawuna ya tsinke sai na shimfiɗe Mila na karɓa na soma ci shi kuma Banah yana aukin kallona.Ina gama ci na ji wata kasala ta rufe ni,sai na kwanta ni ma sai a lokacin kuma Ummilo ta shigo.

Banah ya ce “ga kifi nan da Naomi ta rage ki ci”

Da fara'a kuwa ta karɓa tare da gyara zama ta sa hannunta,sai dai fa ta gagara ci sai yamutsa fuska take haɗi da yunƙurin kai shi bakinta.Can dai ta haƙura tare da ajiye kwanon tana mai girgiza kai ta ce “in na ci wannan ai tamkar na cinye kaina ne,a'a sam maita ai ba hauka ba ce da zan ci jinsina ”


Banah ya ƙanƙance ido yana kallonta kafin kuma ya fice ya bar mu.Maƙoshina ne na ji yana wani irin zafi kamar ana hura wuta,murya kamar ta mai koyon magana na ce “Ummilo sanyi nake ji ki rufe ni” sai kuwa ta miƙe ta ɗauko bargo ta luluɓa mini.Daga wannan kwanciyar ban ƙara farkawa ba sai washegari da zakara ya fara cara,na buɗe idona da suka yi mini nauyi kafin na yunƙura zan tashi sai dai na kasa sakamakon bayana da na ji ya riƙe kafaɗata ta ƙara nauyi.


“Banah?” na kira sunansa kasancewar ni da shi ke kwana a ɗaki ɗaya,Ummilo kuwa cikin jerin ɗakunan da aka yi daga baya take kwana ita da Mila.

Shiru ban ji motsinsa ba,sai na ƙara yunƙurin tashi a wannan karon gangar jikina ta baro shimfiɗar sai dai na gagara tsayuwa kan ƙafafuna na faɗi kwacaaa.Jeren kwanukan da ke ɗakin duk ya baje,ƙarar ta jawo hankalin Ummilo ta shigo tana tambayar lafiya sai dai muna haɗa ido da ita ta ɗau haske.Da sauri ta zo ta taimaka mini na miƙe tsaye tare da riƙe ta gam,murya na ɗan rawa na ce “ki kai ni banɗaki na yi wanka” ita ce ta kai ni,sannan kuma ba ta fito ba sai da ta yi mini wanka.Bayan ta saka mini kaya sai ta miƙo mini wani icce ta ce na riƙe,na karɓa ina jin ƙusumbina da ya ƙara girma ya rinjaye ni na yi mini wani motsi.....


My book is only 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

Daga yau discount ya ida.
Last free page

10


Wata rusunawar dole ce ta zo mini saboda girman ƙusumbina ya wuce a yi kwatance sam tsayuwa ko tafiya babu sanda ba zai yiyu a gare ni ba.A haka na fito daga banɗakin ina jin wasu canje-canje na daɗa ƙaruwa a jikina,ban zame ko ina ba sai a ƙofar gida inda mutane birjit ke a wurin dukkansu kuma a ƙarƙashin ikona suke.Tamkar sun ga ubangijinsu haka duk suka tsaya da abin da suke yi suka zube ƙasa tare da yin kwanciya suna yi mini wani irin kirari da ba a taɓa yi mini shi ba.Idona na ƙanƙance ina kallon Banah da ke can ɗan nesa da ni yana wani irin murmushi da ban san mene ne ma'anarsa ba,don ko kaɗan ban zargi cewa a cikin kifin da ya bani na ci ba ne wannan girman ƙusumbin ya ƙaru.



“Sabbin dokoki sun sauka,don haka al'ummar gari ku kasance cikin shiri ga dukkan abin da shugaba za ta zartar” Banah ya faɗa yana mai takowa yana doso inda nake hannunsa riƙe da kwari da baka.
Sai da ya zo dab da ni sannan ya saita kibiyarsa a sama yana mai furta ɗalasiman tsafi,ji kake shuuu kafin wata wuta ta baje a sama.Babu kuma jimawa sauran jama'ar gari suka fara ɓullowa ta kowace kusurwa,tuni wurin ya ɗauki harama ya cika tanƙam.Sai kuma a lokacin ne na soma yin magana,“daga yau an zartar da yin hadaya duk ƙarshen mako,ruhikan ruwa su ne ke da alhakin zaɓar wanda suke so ko dai mu ɗauke shi mu bayar ko kuma su da kansu su kira mutum zuwa can domin ɗaukar ransa.Abu na gaba shi ne duk wani jinjiri da za a haifa sai an kai shi bakin kogo uwa gijiya ta saka masa albarka tare da ƙa'ide masa adadin shekaru ko watannin da zai yi a duniya”


Yanayin fuskokinsu duk sun nuna ba su ji daɗin wannan sabon tsarin ba,sai dai babu wani mai zarrar yi mini magana duba da irin ƙarfin ikon da ya ƙara hawa kaina ba tare da ni kaina na shirya masa ba.


A haka aka watse na koma ciki na tarar da Ummilo a zaune ta yi uban tagumi.Tana ganina ta miƙe tsaye tare da nufo ni,“na tuna wace ce ni ” shi ne abin da ta furta mini.Cike da jin daɗi na ce “kin tuna? Kai wannan babban abin farin ciki ne amma ya na ga ba ki murna?”


Idonta ya kawo ruwa tana mai cewa “na fito a yankin da aka haramta maita da kuma tsafi,ba tare da shuwagabannin sun yi la'akari cewa ba babu wani babban tarihi da magabatanmu suka shuɗe suka bari kamar Magic,ita Maitar ma ba ta fiya ƙarfi ba. Surukina kafin mutuwarsa ya yi matuƙar ƙoƙarin wurin ganin ya daƙile duk wata baƙar shirka,sai dai abin takaici Mayun ne suka haɗin gwiwa wurin kai shi barzahu.Wannan ya fusata mijina har ta kai shi da yin wani tsari shi ne kafa masarauta,yasa an gina babban wuri tare da yin shelar duk wanda ya shirya karɓar addinin gaskiya to ya shigo a cikin sabon ginin da aka yi.Ta wannan hanyar ce aka yi walƙiya aka gano mayu da matsafan cikinmu,sai ya soma yaƙarsu har ya yi nasara a kansu.Sai dai abin da bai sani ba ita maita bibiyar jini take yi,ga shi dai ya kashe tushenta amma bai cire inda ta yabanya ba.Sannu a hankali lokaci na tafiya mace-mace ya fara yawaita a daular,a bisa binciken wani mai bayar da magani ya gano cewa cutar maita ce sai kuma aka ƙara ƙarfafa tsaro.Tun ana yi wa mutum afuwa in an kama shi da cutar maita har aka zo zamanin yarona inda ya yanke ɗanyen hukuncin cewa duk wanda aka kama da laifin maita ko tsafi kisa ne kawai” tana kawowa nan ta yi shiru tare da kamo ni tana cewa “zo ki zauna hakan za ki gaji sosai,ya kamata ma Banah ya nemo miki sanda mai kyau”


Kan kujerar da aka sassaka da icce ta zaunar da ni kafin ta ci gaba da bani labarin.

“Mahaifin matar ƙanen mijina shi ne mutum na farko da ɗana ya fara cirewa da hannunsa saboda laifi mafi muni da ya aikata ya kashe mahaifan hadiminsa wanda ya ɗauka tamkar amininsa.Ƙarfin wannan raɗaɗin ya saka ita kuma matar ƙanen mijin nawa ta ɗauki tsanar duniya ni da ɗana ta ɗora mamu” nan ɗin ma shiru ta yi tana kallona tsakiyar ido da dukkan alamu akwai wani sirri mai nauyi da take son sanar da ni wanda baki ba zai iya furtawa ba.


Ta idonta kuwa ta shaida mini cewa “ni mayya ce! Ina ɗauke da kambun Maitar prophecy” sai kuma ta yi saurin janye idonta daga cikin nawa kafin ta je da sauri ta shige ɗakinta.Na lumshe idona tare da buɗe su kafin na yunƙura dakyar ina dogara sanda na take mata baya.


A zaune na tarar da kan shimfiɗarta,na ajiye sandar hannuna ni ma na zaune tare da kamo hannunta.Sai ta ɗago ta dube ni tana wani irin murmushi da ya fi kuka ciwo kafin ta ce “ban taɓa yin maita ba,ban taɓa cin ɗan wani ba kawai dai abin da na sani wani lokacin ina rikiɗa na zama kifi a irin haka ne har ita Dadda ta ganni cikin wannan siffa shi kenan ta je ta sanarwa sarki ai ni ma mayya ce.Ba tare da maganar ta fita waje ba aka titse ni sai na faɗi gaskiyar magana,in kuma na yi shiru na ƙi faɗa gobe gaban al'ummar gari za a yanke mini

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login