Showing 45001 words to 48000 words out of 55823 words

Chapter 16 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

39

kan kumatunta ba tare da ta goge su ba ta ce “na san kin karanta littafin tarihi,kin gani da kanki muddin shugaban tawagar Mayu ta fito a mace babu ƙaddarar aure a rayuwarta,in kuma ta yi shi to ki sani akwai ranar da mulkin sai suɓuce mata.Sannan yadda tarihi ya nuna ke dai babu aure a tarihinki da ya zo da wanda ma zai zo gaba, sannan na faɗa miki sharaɗi in ma kin yi auren to ki sani ba a wannan duniyar ta ruwa ba”




Cike da tsana da takaici nake sauraren jawabinta.Da a ce za a tambaye ni babban maƙiyina a duniyar nan a yanzu to babu makawa zan ce Deborah ce,saboda duk wanda ke da ja da lamarin aurena to ban ɗauke shi masoyi ba.


Baya na juya mata a karo na biyu kafin na ce “ina shawartar ki da ki bar gidan nan kafin na yanke miki ɗanyen hukunci”


Ba tare da ta ce komai ba ta tafi,babu jimawa kuma shi Banah ya shigo hannunsa riƙe da ƙwallon kwakwa ƙwaya ɗaya.Tsakiyar ido ya dube ni kafin ya ce “muddin kina gama baki da matsafin tarihi to mulkinki ba zai taɓa ci gaba ba saboda a kullum so suke su canza maka ra'ayi akan abin da kake buri”


“Me za ka yi da kwakwa?” na tambaye shi ba tare da na bai wa abin da ya gama faɗa muhimmanci ba.


“Jirgin dare ne na Mayu ,a cikinsa za mu tafi” ya bani amsa.Kallon mahaukaci na yi masa don sam ban san komai ba game da maita saboda ban taɓa gwada yi ba.Sai da dare ya zo tsakiya ne na ga abin al'ajabi yadda Banah ya mayar da kwallon kwakwa jirgi,kuma ma ni ce farkon shiga bayan shi sai kuma ya soma zagayawa da mu yana ɗibar jama'ar gari waɗanda ke ɗauke da kambu maita ko tsafi.
A wani gari jirgin namu ya yi dirar angulu,tsit garin yake kowa na yin bacci .Haka muka zagaye shi kafin mu soma sarrafa mugunta muna fito da su daga gidajensu muna cillawa cikin jirgi,duk wanda ya yi gardama a nan take muke aika ransa ga ruhikan ruwa.Cikin ƙanƙanen lokaci garin ya hargitse da ihuce-ihuce da kukan mata da ƙananun yara,gefe ɗaya kuma wuta ce ke tashi.
Har mun shiga jirgi za mu koma sai idona ya sauka kan wani gida,shi kaɗai ne ba mu rogaza ba.Kukan jinjiri na soma ji,cikin azama na dire tare da zuwa na ratsa bango na wuce saboda yadda duk ƙwayoyin tsafi suka game jinina.

Wata mata ce na tarar a ciki,gefenta jinjiri ne sabon zuwa duniya don ko cibi ba a yanke masa ba.A hankali na duƙa na ɗauki yaron,sai a lokacin kuma na ji muryar matar na cewa “kar ku kashe mini yaro ” yadda na ga soyayyar uwa da ɗa a cikin ƙwayar idonta shi ya tuna mini tawa mahaifiyar.
Ban kai ga cewa komai ba Banah ya shigo,kafin ƙyaftawar ido ya soma jan ragamar ruhinta.Cikin gargardar murya na ji tana cewa “ Ash-hadu an la'ilaha illallah! Wa'ash-hadu anna Muhammadu Rasulullah!” wata irin walƙiya ce haɗi da zubar ruwa suka zo a nan take,yayin da kuma ni da Banah muka zabura muka yi baya saboda ɗacin amon sautin abin da ta furta yayin da shi kuma yaron da ke rungume a hannuna ya ci gaba da canyara kuka.


“Mu bar wurin nan yi sauri kafin alƙawari ya karye” Banah ya furta cikin wani irin tsoro wanda ban san dalilinsa na yin haka ba.Ina ɗaga kafaɗa haɗi da sake rungume jaririn a ƙirjina na fito,ina shiga cikin jirgin Banah ya jefo mini wani mugun kallo yana kallon jaririn.Na ƙankance ido ina mai ce masa “kar ma ka fara,ka tuƙa jirgi mu tafi”

Ba don ransa ya so ba ya ja ragamar jirgin namu na matsafa har muka isa yankinmu,a ƙofar gidanmu aka zube dukkan mutanen da muka kwaso kafin ni na shiga can ciki na bai wa sauran umarnin su tsaya su tsare mutanen.


Kan gado na shimfiɗe jaririn,ina shirin kwanciya na ji wata murya a cikin ƙwaƙwalwata tana shaida mini an samu baƙon haure a yankina.
Ba tare da na fita ba na yi surkulle na aika Banah can gaɓar ruwan,bai dawo ba sai da gari ya yi haske sai ga shi saɓe da wata mata.


Kan tabarma ya shimfiɗe ta,kallo ɗaya na yi mata tal na ji ƙaunarta ba don komai ba sai don na hango tabon ruhaniya a jininta.

Fuskarta na shafa nan take ta buɗe idonta,sai kuma ta tashi zaune tana mai kallona da kuma inda take.

“Su wane ne ku? ” ta yi tambayar tana ajiye idonta kan gado inda na shimfiɗe jariri.Da sauri kuma na ga ta miƙe tana cewa “me yasa har yanzu ba a yanke cibi ba?”

“Ban san ya ake yi ba” na bata amsa.

“Bani wani abu mai kaifi” ta furta,na zaro wuƙata na miƙa mata,da ita ta yi amfani ta yanke cibin kafin kuma ta ciri suturar jikinta ta kulle daidai wurin da ta yanke ɗin.

“Gefen cikin jaririn duk yayi baƙi saboda mahaifa ta taɓa shi,a kawo ruwa na yi masa wanka” ta sake faɗa .

Banah ya ɓata rai yana shirin magana amma na dakatar da shi,na je na kawo mata ruwan.Sai dai tana saka hannunta ciki ta ce “waɗannan ai masu sanyi ne,masu ɗumi nake so” idona kawai na juya ruwan suka soma tafasa suna fitar da tiriri.Sai ta yi ƙuri tana kallona kafin ta ce “wannan tsafi ne kika yi kuma sarki ya haramta haka”

Sai muka kalli juna ni da Banah tare da haɗin baki wurin tambayar “wane sarki?”

Kai ta girgiza sai kuma ta soma yi wa jaririn wanka,ta saki murmushi ta ce “mace ce ashe” sai ta fito da ita daga cikin ruwan,ta cire uban kallabin da ta yane kanta da shi ta saka jaririyar a ciki.

“Wace ce ke?” na tambaye ta.

“Ni kaina ban sani ba,amma sai nake jin tamkar an aiko ni nan ne saboda isar da wani saƙo” ta bani amsa tana mai ɗago kai ta dube ni.Idona ya sauka kan goshinta nan na ga irin tabon nan da ke a goshin NASLAM ita ma yana fitar da haske sai dai bai cutar da ni ba,hakan kuma sai ya yi mini daɗi na ji a raina cewa ko da a ce ita ma wannan Ubangijin Ka'aba take bauta ma zan iya zama da ita.





Wuraren ƙarfe tara na safe daular abu NASLAM ta samu wani rikitacen labari.Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya yarima ya miƙe kan ƙafafunsa bayan ya yi wanka da magani ya kuma sha a cikin shayi.
Cikin tafiyar jarumta ya soma ratsa dakarun har ya isa inda Sarki ke tsaye yana jawabin yadda komai zai kasance,kamar kuma yadda Sarkin ya tsara jakariya Ali ne zai jagoranci tafiyar.


“Zan tafi ni ma don haka a shirya dokina” ya faɗa yana mai kallon mahaifinsa cikin ido.Sarki ya kawar da kai,don ya san ko da a ce ya yi yunƙurin hana shi ba zai ji ba.
Haka duk suka fito kowanne ya hau doki,da yarima zai hawa kan nasa sai da jakariya Ali ya taimaka masa amma a haka suka tafi.

Tun a bakin ƙofar shigar garin suka fara cin karo da kayan tashin hankali,babu shiri yarima ya diro yayin da kuma jakariya Ali ya soma take masa sawu.
Gawarwakin mutanen da aka kashe,Ali ya kalla sai ya ga duk kusan kalar mutuwar iri ɗaya ce.Ya kai hannu ya damtsi ƙasa sannan ya kai kusan hancinsa ya sunsuna,yarima ya dube shi tare da cewa “me ka fahimta?”

“Farmakin Mayu ne” ya basa amsa,ran yarima ya ƙara ɓacewa amma a haka suka ci gaba da duba ko ina har suka shiga gidan da matar nan ta haihu.

Cak jakariya Ali ya tsaya yana kallon ustaza Jamila,wacce ta bayar da dukkan lokacinta domin yin hidima ga addininta.Yarima ya ƙarasa yana mai cire rigarsa ta sarauta ya luluɓe ta,tare kuma da baiwa dakaru umarnin a ɗauke ta a kai ta can masarauta tun yanzu ba sai an jima ba......
[12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

07


Ustaza Jamila ƙanwa ce ta jini ga jakariya Ali,mijinta ma ya mutu ne a wajen yaƙin haɓaka musulunci sai ga shi ita ma ta mutu wurin da'awar jawo hankulan waɗanda ba musulmi ba.Kamar yadda tsarin masarautar yake,suna aika maza da mata garuruwa don koyar da mutane karatu.


Yarima NASLAM ya dafa kafaɗar jakariya Ali yana mai cewa “ dukkan rai zai ɗanɗani mutuwa,ka sa a ranka lokacinta ne ya yi.Mu ma muddin namu yayi babu makawa a duk inda muke mutuwa za ta riske mu”


Idon Ali sun kaɗa sun yi ja sosai,muryarsa ma cikin wata irin sarƙaƙiya take fita.“Na yi imani ga Ubangijin Ka'aba,dukkan wata ƙaddara mai kyau da akasinta daga gare shi take.Sai dai babbar damuwata ɗaya ce ,cikin jikinta sam babu shi a yanzu hakan yana nufin kenan ta haihu in kuma ya tabbata haka ina jinjirin yake?”


Shiru yarima Naslam yayi na wani ɗan lokaci kafin ya ce “a duk inda yake Ubangijin Ka'aba ne zai tsare shi,ka dai kawai ka sa kyakkyawan yaƙini ga ubangijinka ” kalamansa suka yi tasiri a zuciuar jakariya Ali, wannan ya basu damar ci gaba da binciken ko ina.


Bayan sun gama haka suka haƙa rame aka rufe sauran kafin su juyo su dawo masarauta inda Sarki Haroon da sauran al'umma ke dakon jiransu.

Suna shigowa sarki ya je ya tarbi yarima tare da soma tambayarsa abin da ke faruwa.

“Farmakin Mayu ne,duk sun kashe mutanen gari da alamu kuma sun tafi da wasu.Babban baƙin cikin shi ne ba su bar wani sawu ba da zai sa mu gane ta ina suka fito ”

Barham da duk ya ji abin da yarima ya faɗa sai ƙara matsawo yayi yana mai cewa “a yadda ka yi bayanin ya tabbata cewa wannan rundunar Mayun ta samu jagoranci Banah maharbi”

Sarki da yarima Naslam sai duk suka maido dubansu ga Barham ɗin,shi kuwa kai ya jinjina kafin ya ci gaba da cewa “tarihin da ya fara zuwa na wannan ƙarnin ya bada labarinsa,Banah maharbi ne kuma babban matsafi wanda ya fito daga tsatson aljanar ruwa.Mahaifinsa ya kasance masinci ne,ya iya ruwa sosai a irin alƙawarin da mutane ke ƙullawa da ruhikan ruwa mahaifin Banah ya yi gamo da wata aljanar ruwa har yayi tarayya da ita suka same shi.Tun da aka haife shi a cikin jeji ya tashi tare da fatale da aljanu,kafin mahaifinsa ya mutu ya koya masa farauta da kuma baƙin tsafi na ƙarnin baya sannan kuma ya ɗora shi kan turbar yi wa aljana ZAƘUMA bauta” Barham na kawo nan da zancensa masarautar ta ɗauki wani salo,guɗa ce kamar an kawo amarya ta karaɗe ko ina kafin kuma iska ya soma tashi babu jimawa kuma aka soma yin wasu yayyafin jini.

Hankali a matuƙar tashe Barham ya ce “Attakbirrrr!”

Dukkan mutanen da ke wurin suka amsa da “Allahu Akbar!” nan take yayyafin jinin ya tsaya cak wanda duk ya ɓata fuskokin mutane.Sai kuma sararin samaniya ya soma ɗaukar launin ja yana nuno inuwar wata halitta marar kyawun gani can ita ma ta ɓace komai ya dawo normal.



Ran sarki da na yarima ya ɓace,saboda ba tun yau suka saba ganin ire-iren waɗannan surkullen ba.
Barham ya ce “ Aljana ZAƘUMA ce,wato uwar gijiyar Banah da ita yake tsafi.A kullum yana shayar da ita jinin mutane,ita kuma tana basa ƙarfin iko ”


“Ina zan samu shi Banah ɗin?” yarima ya tambaya.

Barham ya ce “Ubangijin Ka'aba ne kawai ya san daidai ina yake a yanzu,saboda tamkar guguwa haka Banah yake bai zama wuri ɗaya yawo yake yi gari-gari yana shanye jinin al'ummar yankin”

Yarima zai buɗa baki ya sake yin magana amma sarki Haroon ya dakatar da shi ta hanyar cewa “yanzu abin da ya fi muhimmanci shi ne yi wa ustaza Jamila sutura,don haka a kira gimbiya A'ishah ta yi mata wanka”

Sai a lokacin ne kawai Ayyub ƙanen sarki Haroon kawai ya saka bakinsa,“ gimbiya A'ishah tana kwance babu lafiya tun jiya,na so na sanar da kai sai kuma wannan al'amari ya danne niyyata ”

Hankali a tashe yarima ya ce “meke damunta?”

“Ciwon ido ne mai tsanani ,idanunta sun zama kamar gauta ” Ayyub mahaifi ga gimbiya A'ishah ya faɗa .

Yarima bai ƙara cewa komai ba ya shiga can ciki,direct kuma sashensu gimbiyar ya wuce.


A kwance ya tarar da ita don tun lokacin da Dadda ta fice ta bar ta take nishin azaba idonta sai ƙara ciwo suke yi saboda ta ga abin da bai kamata a ce ta gani ba.

Tana jin muryar yarima ta yi ƙarfin halin buɗe idon nata sai dai tamkar mai ɗauke da sabuwar makanta haka take ji dole ta ja su ta rufe.


“A'ishahhh?” ya kira sunanta cike da tausayinta.Murya na ƴar rawa ta amsa da “na'am yarima”

“Mene ne ya shiga idonki?” ya sake jefo mata tambaya,sai dai ba ta kai ga amsawa ba jakariya Ali da Barham suka shigo.


Barham ya matsa kusa da kanta yana ajiye jakar kayan aikinsa,bai ɓata lokaci ba ya soma zuba magani yana wanke mata idanunta duk da yana haɗawa da Magic babu wanda ya sani in ba ita gimbiya A'ishar ɗin ba.

Cike da aminci ta buɗe idonta da suka dawo normal tana kallon Barham da yake yi mata ta idanu.

“In yau na wanke miki ido kin samu lafiya ki sani gobe ba zan yi ba,zan bar ki da mugun halinki ”

“Ban taɓa ganin inda maye yake gorantawa ɗan uwansa ba sai kai Barham” ita ma ta basa amsa ta ido.

Ya ce “ni ba maye ba ne,ban taɓa yin maita ba hasali ma ina adawa akan duk masu yinta.Ke ma kin san cewa iya Magic kawai nake yi shi ma ba don komai ba sai don ci gaban masarauta”


“Me yasa dole sai ni kake son na bayyana kaina? Don me shi yarima ba ka damu da tasa maitar ba?” ta tambaye shi,sai dai shi Barham ɗin bai bata amsa ba ya juye kansa ya mayar da dubansa ga yarima Naslam yana mai cewa “ba wani babban abu ba ne ya same ta,kawai wani ɗan tsautsayi ne”


Yarima NASLAM ya dube ta yana mai cewa “ki kwanta ki huta” sai kuma ya fice jakariya Ali na take masa baya.



Wasu mata aka samu suka yi wa ustaza Jamila wanka.Sai da aka ma fito da gawar ne sannan gimbiya A'ishah ta san abin da ke faruwa,sosai ta ji zafin mutuwar har da zubar da hawaye.Ana yi mata sallah aka kai ta gidan gaskiya,sai kuma a wannan lokacin ne jakariya Ali ya nuna rauninsa ya soma yin hawaye waɗanda zubar da su ba ƙaramin sanyaya masa zuciya suke yi ba.


Sai da aka yi kwana uku ana jimamin mutuwar ustaza Jamila kafin kuma lamurra su ci gaba da tafiya.

A yau ne yarima yasa aka fito da matsafiyar nan da ta raira waƙa tsafi.Gaban sarki aka gurfanar da ita,tare da umartar ta da ta faɗi laifinta.


Amma ta yi shiru ta ƙi cewa komai sai yariman ne ya shaidawa sarki yana mai ƙara wa da “a yanke mata hukunci nan take ban son ajiyar mayya a cikin masarautata ”

Sarki Haroon ya kafe ta da ido yana kallo kafin ya ce “ki amsa laifinki sannan ki tuba ki rungumi addinin Musulunci domin tsira da ranki”


“Babu wani addini da zan shiga,na fi son zama babu alƙibla.Sannan kuma ni ba mayya ba ce duk da ina da ilimin sarrafa maitar,maganar ƙarshe kuma ita ce zan koma gida”

Rai ɓace yarima Naslam ya zaro takobinsa da niyyar sauke mata kai amma jakariya Ali yayi saurin riƙe shi yana cewa “ka nutsu yarima kar ka yi saurin yanke mata hukunci jira na kira Barham”


Zuciyarsa na ƙuna ya ce “ba ka ji yadda take magana ba sam babu ɗa'a?” bai ma kai ga cewa wani abu ba Barham ɗin ya shigo.


Kallo ɗaya ya yi wa matar ya gane wace ce ita,hakan yasa ya ƙarasa gun sarki yana mai yin ƙasa da murya ya ce “kar ku kashe ta,za ta yi mana amfani a nan gaba” sosai sarki yake ɗaukar shawarar Barham saboda shi ɗin aminin mahaifinsa ne sannan kuma dattijon arziki na masarautar.


“Ku mayar da ita” sarki ya faɗa wanda hakan sam bai yi wa yarima daɗi ba sai kawai yayi zuciya ya fita daga wurin.

Jakariya Ali ya bi bayansa yana mai cewa “ gaggawa aikin sheɗan ne,matar can tana ɗauke da wani ɓoyayyen sirri wanda nake jin cewa ita ce makullin da za mu yi amfani da shi wurin buɗe duk wata ƙofa da ta yi mana wuyar shiga”


Ba tare da yarima ya ce masa wani abu ba ya soma cire kayansa na sarauta yana ajiye wa.Toilet ya shiga ya soma yin wanka ko zai ji sassauci,har ya fito jakariya Ali na nan.Shi ne ma ya taimaka masa wurin tsane jikinsa ya saka kayan zaman gida,daga nan sai suka wuce can inda tantabarunsa suke.


Yana son tsuntsaye, wannan yasa ko ƙunci yake sai ya ziyarce su yake jin daɗi.Jakariya Ali ya buɗe su,da gudu kuwa duk suka shiga fitowa suna nufo shi,ɗaya ta sauka kan kafaɗarsa ya kai hannu ya damƙo ta yana shafar jikinta yana murmushi.

Sai ya ji kamar ana kallonsa,ido ya baza cikin tantabarun nan idonsa ya sauka kan baƙuwar tantabara idonta ƙurrr kansa.Kasancewar bai yarda da canfi ba sam bai kawo komai a ransa ba,haka ya ratsa ya je ya ɗauko ta wani irin shock ya ratsa shi nan ɗin ma bai sa a ransa wai lamari ne da ya shafi sprituality ba.


Jakariya Ali ne kawai ya farga da abin da ke faruwa,amma kuma sai ya ja bakinsa yayi shiru.Duk yadda yarima ya so tantabarar ta saki jikinta amma abu ya cuttura kawai sai ya wuce da ita can ɗakinsa yana mai cewa “ban san daga ina ita wannan ta zo ba,da alamu ta ƙi sabawa da sauran ne”

Jakariya Ali ya ce “ dama ai kullum cikin samun baƙi tantabaru ake yi,ita ma za ta saba”

Cikin ɗakinsa ya sake ta,ai kuwa sai ta shiga yin walwalar.


A can ɓangaren gimbiya A'ishah kuwa abubuwa ne duk suka dagule mata,ga rashin ƙawarta Jamila ,ga ɓatan Dadda kusan kwana uku har yanzu ba ta dawo ba,ga kuma yanayin jikinta da take jin ya sauya.Zaune ta yi cikin halin ƙaƙanikayi tana wasiƙar jaki,sai ta ji ana magana ƙus-ƙus ba ta jin abin da ake cewa, da ta nutsu sosai sai ta gane a cikin drower kayanta.A hankali ta je ta buɗe,ɓerayen

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login