Showing 9001 words to 12000 words out of 55823 words

Chapter 4 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

33

burgewa,ni kuwa ban damu ba na shiga can uwar ɗaka.Na samu Ubaidah zaune a bakin bed tana kallon ƙofa.Na yi mata hararar wasa ina mai cewa “dalla Malama ni faɗa mini shekaruna nawa ?”

Sai da ta yi wani murmushi kafin ta ce “goma sha bakwai da wata uku”

“To ban gode ba” na faɗa tare da fitowa,na ce masa “yawwa 17years da wata uku”

Murmushi yayi ya rubuta,ni kuma na koma wurina na zauna.Wayar Ya Ubaidullah ta hau ringing sai ya fita,doctor ɗin ya bi shi da kallo kafin ya juyo gare ni ya ce “lambar wayarki ” sam ban kawo komai a raina ba haka na basa ya rubuta,sai ya ce “zuwa gobe in na gama bincike zan sanar da ke result kin ji preety”

Na ɗan murmusa tare da sunne kai na lura yana son barkwanci.
Ya Ubaidullah ya shigo yana cewa “Abdul Hamid in ka gama ka same ni a mota ka ɗan yi sauri amma”

“Na ma gama mu je” ya furta tare da bin bayansa suka fice ni kuma na koma wajen Ubaidah na ce “na dawo ba su cinye ni ba sai ki taso ki mayar da ni gida”


★A can ɓangaren Ammy kuwa ko da ta koma ɗaki Mamu ta kira ta yi mata ta'aziyya tare da neman alfarma tana son Suwaiba ta kwana a nan saboda akwai aikin da za su yi mata.

Mamu ta ce “babu damuwa ni ina ma nan gidan makoki a nan zan kwana,ashe can ta tafi sam ba ta sanar da ni ba ma”

“Eh tana nan in sha zuwa goben za mu zo tun da ita ta san gidan ai shikenan ” ba su wani tsaya tsawaita hirar ba suka kashe.Ammy ta miƙe cike da damuwa tana tunanin maganar da yau wata bararoji ta faɗa mata.Allah ya gani ita mace ce mai riƙo da addini sam ba ta ma wani yarda da canfi ba,amma sai ga shi maganar wata ƙasƙantaciya ta yi tasiri a ranta.Ta ja ajiyar zuciya tana mai cewa “ni kam banda maƙiyi a duniyar nan ai ballantana na ce shi ne ke son ganin na tozarta ”

Sai kuma ta ƙara lulawa duniyar tunani nan ɗin ma ba ta samo maƙiyi ko ɗaya ba.Waya ta yi a can asibiti,wata nurse ta ɗauka Ammy ta ce “ki duba gado mai lamba uku har yanzu bararojin nan bacci take yi?”

“To madam” ta furta can kuma ta ce “eh ga ta nan har yanzu ba ta farka ba”

Ammy ta ce “yawwa kina jina kar a saki a bari ta fita,ki cewa doctor wanda ya hau gobe na ce kar a bata takardar sallama”

“To Madam ” ta sake faɗa,Ammy ta kashe kiran tana ɗan jin sanyi a ranta.


★A can gidan makoki kuwa tun da Sulaimanu ya shiga cikin gidan Mama Lantana ta soma cewa “to ga ma angon nan,ku dube shi ɗan albarka mai farar zuciya amma za a canfa aurensa ” yana jin haka ya fito ya bar su Mama Lantana na ƙara gishiri da magi a maganar.A haka har yamma ta yi,tsabar mugunta yasa ta fito waje cikin maza ta yi wa Abba magana ya taso ya zo inda take.

“Ka ga dai bai kamata a ce duk mun tafi an bar matar malam ita ɗaya ba,shi yasa na yanke shawara ni zan koma gida domin kula da yara.Ita kuma Zainaba ka ce ta zauna a nan ɗin don ɗebe kewa”

Abba wanda tun tuni ya zama mijin ta ce yayi na'am da zancenta.Har cikin gida ya samu Mamu ya bata umarnin kwana a nan yayin da ita kuma Mama Lantana ana gama kiran sallar isha'i ta tattara ita da ƴaƴanta suka koma gida zuciyarta fesss don ta yi alƙawarin yau sai ta tsorata Suwaiba fiye da jiya.

Suna isa ta tarar da gida a buɗe,duk a tunaninta Suwaibar ce ta buɗe shi kasancewar ita da Mamu kowa nada makulli.Direct ɗaki suka shige,dama sun ci abinci a gidan makoki.Waya Mama Lantana ta soma yi ita da Kaka kamar yadda suke kiran mahaifiyarsu ta tabbatar mata zuwa jibi take dawowa daga ƙauye.

Sun raba dare suna hira kafin Abba ya shigo,duk sai suka nufi ɗakinsu.Mama Lantana ta soma juya idanunta wanda hakan yasa Abba yayi saurin zama ƙasa kamar wani ɗanta ya ce “me kuma na yi yanzu?”

“Ba ka yi komai,dama so nake na ja ma kunne in ka kwanta kar ka fito sai sallar asubah da kaina ma zan tashe ka”

Cike da ladabi ya ce “to hajiyata”
Mama Lantana ta washe baki don tana mugun jin daɗi in ya kira ta da wannan sunan.Har uwar ɗaka ta yi masa rakiya sannan ta dawo falo ta kwanta bayan ta rufo ɗaki.Lamo ta yi kamar mai shirin yin bacci kafin ta rikiɗe ta zama mage,ta window ta fita tare da nufar ɗakin Mamu ta kuwa ci sa'a yana a buɗe sai dai tana shiga wayam babu Suwaiba.

Cike da takaici ta fito ta haye katangar maƙwabta ta soma koke-koke “minyau! Minyauuu!” amma babu wanda ya kula ta don in da sabo su makwabtakan ma tuni sun saba da wannan kukan saboda kusan ko wane dare suna jinsa.Mugunta kawai take son yi,wannan yasa ta bi gidaje sai dai yau ba a fito a sa'a ba.Har tana shirin komawa gida kuwa ta tuna cewa muddin Suwaiba ba ta gida to ba ta da wurin zuwa in ba gidansu Ubaidah ba.Kamar abin tsiya haka ta dinga ƙetara katangu tana wucewa har ta je gidan.



Duk yadda na so zuwa gida hakan ba ta faru ba saboda Ammy da kanta ta zo ta shaida mini yadda suka yi da Mamu.A dole na haƙura,na so kiran Mamun jin wai a can za ta kwana sai dai sam ban son jin wannan yanayin nata na damuwa.

Bayan sallar isha'i Ubaidah ta kawo mana abinci muka ci,sai kuma muka fiddo takardun makaranta muka shiga dubawa bayan nan muka yi shirin bacci.
Ni na soma kwanta ina mai lumshe ido,ta ce “gobe in Allah ya tashe mu tun da safe zan yi miki kitso irin mai taliyar nan”

Na saki murmushi na ce “a'a ni mai tuwo nake so” ita ma dariyar ta yi ta soma yi mini surutunta,tun ina saurarenta har ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.Sai dai bai yi nisa ba na soma jin kukan mage a can kusan window da ke rufe da madubi amma duk da hakan bai hana kukan nata ratsa dodon kunnena ba.A hankali na ɗan ware idona,ɗakin tarau yake da haske ba a kashe ƙwan lantarki ba hakan ya bani damar hango Mama Lantana cikin madubi tana a tsaye ta kafe ni da,juyawa na yi da sauri saitin window nan kuma mage na gani madadinta ina sake maido kallona cikin madubi sai kuma na ga Mama Lantana da kanta na mutane jikinta kuma na mage tuni ta ratso madubin window ɗin ta yi tsalle tana niyyar dirowa kan gado,ɗif numfashina ya tsaya cak .....
[05/06 09:03] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*
🚫Don Allah ko ba ki karanta ki yi sharing a wasu group domin mutane su amfana da darasin ciki.

04

Ubaidah wacce fitowarta kenan daga toilet ta hango mage kan gado tana son hayewa kan Suwaiba da ke kwance.Da wani mugun sauri ta ɗauki pilow tare da yin tsalle ta danne Mama Lantana da ke cikin siffar mage.
Zillo ta soma yi tana son fitowa amma ita kuma Ubaidar sai ƙara danne ta take yi,duk da idanunta ba su iya ganin cikakkiyar siffarta amma ta yi imani cewa ba normal mage ba ce muguwa ce.Wani irin kuka Mama Lantana ta soma yi irin na jarirai wai don ta tsorata Ubaidah ba ta san ta yi ga banza ba sam Ubaidah ba ta da tsoro.Cikin wata irin murya mai cike da ɓacin rai ta soma yin magana "wato kin zo ki cutar da masoyiyata duk damuwar da take ciki so kike ki ƙara mata wata akai to zan kashe ki ”

Mama Lantana na jin haka sai ta ɗauke numfashi ta yi kamar ta mutu, Ubaidah jin tsit sai ta ɗaga pilown wuf Mama Lantana ta yi tana mai yin tsalle ta haye window.Da wani irin gudun bala'i ita ma Ubaidah ta je ta ja madubin window sai ya dantse ƙafar magen ta baya,ta saki wata razananiya ƙara sai dai wannan karon ta muryarta ce dak.Da ƙarfi ta ja ƙafarta ta fito ta soma ƙetara katangu ta gudu ta bar gidan.


Ubaidah ta ja numfashi tana mai duban Suwaiba,sai a lokacin ta lura sam ba ta yin numfashi.Ruwan sanyi ta ɗauko ta zuba mata amma shiru ko yatsa ba ta motsa ba,da wani irin sauri ta fita tana kuka tana kiran Ammy.


Ubaidullah da ke nan babban falo yana kwance yana waya da Hamida yayi saurin ɗagowa ya dubi Ubaidar yana cewa “ke lafiyarki?”

Nuni ta yi masa da can saman ɗakinta,ya cewa Hamida “ ina zuwa” bai jira cewar ta ba kuma ya kashe kiran ya ƙara fuskantar ƙanwar tasa,kafin ya sake tambayarta ta ce “mayya ta shigo ta tsotse jinin Suby ga ta can a kwance babu rai”

Ƙirjin Ubaidullah ne yayi wata mummunar faɗuwa,jin ta ambaci mayya da kuma mutuwa.Idonsa na rufewa ya soma haurawa can saman,sam bai wani damu ba na ganinta sanye da kayan bacci.Taimako ya soma bata ta hanyar zuba mata ruwan sanyi jin ta ambaci har da mayya sai ya ƙara da tofi.Hannunta ya riƙe yana murza tafukanta da sauri yana mai ambaton sunan Allah da jero duk addu'ar da ta zo bakinsa,dandanan suka fara ɗaukar zafi sannu a hankali kuma bugun zuciyarta ya soma tafiya.


“Suwaah?” na ji amon muryar da ko cikin duhu ko magagin bacci ba za ta ɓace mini ba.Ina jinsa sarai yana mai ci gaba da tuntsire sunana na Suwaiba yana mayar da shi Suwaah ban sani ba ko tsayi yayi masa oho,abin da na sani shi ne kawai ba zan iya amsa ba saboda wani abu mai nauyi da ya danne mini kai.Duk yadda na yi yunƙurin buɗe idanuna kuma na kasa,kukan Ubaidah na soma ji a gefe yayin da muryar Ya Ubaidullah ke cewa “je ki tada mota Ubaidah ina ga sai mun wuce da ita asibiti”

Sautin kukanta ta ƙara ina ji,har lokacin da ta soma kiciniyar neman key ina jin motsi sai dai banda damar yi musu magana.

“Ki je key ɗin motata na kan kujera a falo” ya furta tare da sunguma ta.Ina jin duk lokacin da yake taka step yana sauka da ni ƙasa,har sa'ilin da iskan Ubangijin ya bugi gangar jikina.

“Zauna baya ki tallabe ta ni zan yi tuƙin” ya furta,ina jin lokacin da ya saka ni a motar sai kuma Ubaidah ta rungume kaina tsammm a ƙirjinta daidai nan na ja wata ajiyar zuciya tare da fashewa da kuka ina mai buɗe idanuna.

Ya Ubaidullah da ke ƙoƙarin yi wa mota key ya juyo da sauri cike da mamaki yana kuma yi wa Ubangiji hamdala.Har wata sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke wacce yake jin tamkar an dawo da ransa ne.

“Subyna?” Ubaidah ta faɗa tana bubuga bayana alamun rarrashi,ban amsa mata ba sai sautin kukan da na rage tare da tashi zaune.
Ya Ubaidullah ya fita tare da buɗe ƙofar ɓangarena,a hankali na ziro ƙafata wacce take sintir babu takalmi.Kamar wata baturiya haka na yi tsaye da kayan baccin waɗanda suka kasance wando ne iya gwiwa sai rigar marar hannu,gashin kaina wanda ya sha gyara sai tashi yake yi cikin iska.
Kamar yadda yake kallona haka ni ma na ɗan tsura masa nawa idanun da har yanzu ba su bar zubar da hawaye ba.

Hannuna ya kamo yana mai cewa “me kike ji? ”

Hannun nawa da ya riƙe na kai duba akai kafin na girgiza masa kai,ci gaba ya yi da kallona kafin kuma ya dubi inda Ubaidah take a tsaye jikin mota .Ni ma sai na kai dubana,sai na ga ta harɗe hannuwa ta tsura mana na mujiya.
A hankali na janye hannuna daga cikin nasa kafin na kama hanyar komawa cikin falo,ina tafe ina son tuna abin da ya faru da ni amma sam na kasa tunawa.Ko da na isa can ɗakin Ubaidah sai na yi zaune tare da zuba uban tagumi,Mamu ta faɗo mini a rai na ɗauko wayata zan kira ta sai kuma na fasa gudun kar na tayar mata da hankali.



A can kuwa ɓangarensu Ubaidullah,wani irin sanyi ne gwiwansa suka yi sam ba zai iya cewa ga dalilin da yasa ya damu da ita har haka ba.Ga shi kuma ƙanwarsa na yi musu wani kallo,ko don ta ga ya riƙe hannun ƙawarta ne oho.Ya cije leɓensa na ƙasa kafin ya cewa Ubaidah “ki shiga ciki sannan ki kula da ita,ƙila duk don ɗazu ta samu matsalar nan ne ta haɓo”

“To” ta furta tana mai goge fuska kafin ta wuce,ya bi bayanta da kallo har ta shige.Zagayen gidan ya soma yana tuna wasu hirarraki da suka yi da Hamida kaɗan daga ciki su ne “Ya Ubaidullah duk ranar da ka fara mugun sona to za ka ji iskan shaƙa na yi maka kaɗan,za ka fi son iskan waje kan na ac.Kuma za ka ce na faɗa ma duk ranar da ka tsunduma a kogin so to za ka kasa controling kanka ƙila ma ka yi abin da bai dace ba” ido ya rumtse kafin ya nufi can inda ke da flower dayawa ya soma shafa ta yana mai ɗaga kai yana kallon benen ɗakin Ubaidah.
Ya jima sosai yana kallon wurin kafin ya koma ɗaki,wayarsa ya ɗauka kafin ya ɗauki hanyar da za ta kai shi ga tabkeken benen part ɗinsa wanda shi ne ma ya kusan cinye rabin falon tsabar girmansa.

Yana shiga a falonsa ya zube kan kujera ,kiran Hamida ya shigo.Ya ja uban tsuki yana jin takaicinta,haka yayi ta kallon screen ɗin har call ɗin ya yanke.Sai a lokacin ya ga ta yi masa kira sama da ashirin,ya ja uban tsuki yana mai cewa “sai ka ce ita kaɗai ta fara sona a duniya kira kamar mayya, wannan da mayyar ce ƙila da tuni ta yi farfesuna ta cinye” sai ya saka wayar a silence kawai ya lumshe ido kamar mai shirin yin bacci.

Hirarsu da Dr Abdul Hamid ta faɗo masa wacce suka yi ɗazu bayan ya gama duba Suwaiba.Babu kunya Dr Abdul Hamid ɗin ya ce yana son Suwaiba ta yi masa ,har da yi mata wani suna wai shi pretty.A take ya ji ya tsani sunan da shi kansa wanda ya ƙirƙiro shi .Ganin baccin ba zai samu ba ya sa miƙewa ya wuce bedroom,wanka yayi ya zo yayi nafila tare da niyyar yin istikhara na dangane da abin da yake ji yana tunkaro shi in alkhairi ne Allah ya ƙara tsoma shi a ciki.Akan dadduma yayi bacci,bai farka ba sai da aka soma yin kiran sallah.Wanka ya sake yi sannan ya wuce masjid,bayan an idar da sallah ya dawo .Kamar ya je can ya dubo ta haka yake ji amma ganin gari ma bai gama yin haske ba ya haƙura ya koma ɗakinsa.



★Da ɗingishi Mama Lantana ta koma gida,tsinuwar da ta yi wa Ubaidah kafin ta isa gida ta fi shuren masaki.Ta yadda aka yi ta canza siffa daga mutum zuwa mage ta wannan hanyar ta sake bi.Tana gama ɗaukar siffarta ta bil'adama sai ta kai dubanta ga ƙafarta ta hagu yadda ta kumbura ta yi suntum tuni ma akaifar ƙaramin yatsa ta fice tana zubar da jini.

Miƙewa ta yi dakyar za ta fita daidai Hassana ta fito tana hamma,wani irin turus ta yi tare da maƙalewa jikin katanga tana kyarma tana mai ci gaba da kallon yadda idanun Mamarsu ke wani ƙyalli suna canza kala.
Mama Lantana a jikinta ta ji ana kallonta wanda kuma haka ne duk wani mugu ko ya aka ga ɓarrakar siffarsa yana ji cikin ruhinsa ne.Da wani irin sauri ta lumshe idanunta kafin ta waiga daidai inda Hassana ke tsaye ƙyam,“ke don ubanki tsayuwar me kike yi mini a falo?”

Hassana ta yi saurin jan ajiyar zuciya ganin idanun nata sun dawo daidai,ta ce “wallahi Mamarmu mugun mafarki na yi wai Hussaina ta mutu mayya ta damƙe mata kurwa,ina tashi kuma na ji mugun ƙishi shi ne fa na fito amma ba yawo nake yi ba”


Suman tsaye Mama Lantana ta yi jin an ambaci wai mayya ta kashe mata ƴa,a cikin zuciyarta ta ce ‘ Allah yasa ba gaskiya ne ba,don in dai mayya ta kame Hussaina ai asirina ya gama tonuwa a idon duniya’
A fili kuma sai cewa “kin kwanta babu addu'a ba dole ki yi mugun mafarki ba,je ki sha ruwan ki zubo mini a babbar roba ni ma zan saka ƙafata”


Hassana ta je ta buɗe ɗaki tana mai cewa “me ya samu ƙafar?” ƙin tanka ta Mama Lantana ta yi har ta fita,babu jimawa kuma ta dawo da ruwan kamar yadda ta ce ta ajiye mata a gabanta.
Mama Lantana aka samu wuri aka zauna sannan ta ƙara jawo robar,tana saka ƙafarta sai ta soma sauke ajiyar zuciya sanyin ruwan na ratsa ta.



★Sulaimanu
Tun da ya ji kawu ya rasu ya ji a ransa dole a bar maganar auren nasa zuwa wani lokaci.Garin ya ji duk ya fice masa wannan yasa ma ya dawo gida,tun dawowarsa daga gidan makoki bai tafi ko ina ba yana ɗaki.Iya Ubaidah kawai suka yi waya yana jin kamar ya janyo ta ya kawo ta kusa da shi.A cikin dare kasa yin bacci yayi saboda tunanin duniya,ga zuciyarsa na wani irin nauyi sam garin ya fita ransa .
Washegari ko da ya dawo daga sallar asubah sai yayi wanka ya jawo akwatinsa ya ƙara gyara shi.Lokacin da ya fito gari yayi haske,tuni su Mama Lantana ana waje a tsakar gida.Tana ganin Sulaimanu jaye da akwati ta saki wani makirin murmushi tana jin a ranta ba ƙaramar sa'a ta yi ba da ta samu Yawale matsayin malami ba.

“Ina kwana Mama” Sulaimanu ya faɗa cike da ladabi ,a gadarance ta amsa tana tsure shi da idanun da kullum su ne ke ƙara raunata ruhinsa yake jin tsoronta kamar rai da ajali.

“Sai tafiya?” ta jefo masa tambayar, Sulaimanu wanda ya sunne kai tun bayan da yayi ido huɗu da ita ya ce “eh Mama sai kuma in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login