Showing 3001 words to 6000 words out of 55823 words

Chapter 2 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

31

naƙarƙasata,ban san inda nake jefa ƙafa ba kawai tafiya nake bayan na fito daga gidan mutuwar.Na yi tafiya mai nisa kafin na samu wata bishiya na zauna kan wata ƙatuwar tayar mota,ajiyar zuciya na yi ta saukewa kafin na kira Ubaidah.Tana ɗauka na fashe mata da kuka,duk sai ta rikice ta soma tambayata lafiya amma ban ce mata komai ba har sai da na ji ta ce “gani nan zuwa”

“Ba ni gida”

“Kina ina to?” ta tambaye ni,sai a lokacin na duduba wurin da nake sannan bata amsa da “wajen makarantar makafi ” kashe kiran ta yi,ba fi minti ashirin ba sai ga ta cikin mota.Ta buɗe murfin da ta fito tare da zuwa da sauri ta miƙar da ni tsaye,jikinta na shige na ci gaba da yin kukan ban yi shiru ba sai da na ji Ubaidah ta kama mini ita ma tana kukan.
Na yi ɗan baya tare da jingina jikin motarta murya na ɗan rawa na ce “wai kuka kike yi?”
“Me kike so na yi Suby? ”sai kuma ta kama hannuna tare da buɗe mini gaban mota ta zaunar da ni,sannan ta zagaya ta zauna ita ma tare da yi wa motar key.Gudu take yi sosai har sai da na ji tsoro,“ina za mu je?” na tambaye ta.

“Nigeria” ta bani amsa.

Wa waro ido na ce “Nigeria kuma? Wurin me?”
“Sayar da ke zan yi na huta da tashin hankalin da kike saka ni a kullum”

Ban san lokacin da murmushi ya kubce mini ba,sai na jinginar da kaina a kafaɗarta ina mai cewa “ke ce farin cikina my Udah ”

Gefen titi ta samu ta parker motar tana mai cewa “tun kafin dai yayanki ya more ni duk kin bi kin ɗale mini jiki”

Na janye daga gare ta ina mai yi mata hararar wasa na ce “jikin naki ma da bai da komai sai shegen tauri ”

Ta yi wata mahaukaciyar dariya kamar ba gobe kafin ta daki bayana sai kuma ta yi shiru tana wani murmushi.Inda ta ƙurawa ido na duba sai na hango wani mutum yana tahowa da dukkan alamu kuma wurinmu zai zo.

“Wane ne kuma wannan mutumin Ubaidah?” na tambaye ta saboda tsikar jikina da ta soma tashi sakamakon iya ganin zubin halittarsa da nake iya gani a yanzu da yake daf mu.Fari ne sosai,sai dai wani abu duk ya ɓata masa fuska kamar ƙuraje kamar kuma cutar kuturta.A kallon farko kawai da mutum zai yi masa zai iya ajiye shi cikin ƙabilar Fulani duba da ƙaramin jikinsa.

Gilashin motar ya ƙwanƙwasa ta yi ƙasa da shi,ya miƙo mata wata gora mai cike da madarar shanu yana mai sauke idanunsa a kaina.

“Wane ne wannan mai cike da ƙuncin rayuwa?” ya tambaya cikin hausarsu ta Fulani.

“Ƙanwar Sulaiman ce“ ta basa amsa tana mai jan wani dogon numfashi.
Bai ce komai ba sai idanunsa da ya tsura mini masu matuƙar kaifi,ni ma kamar wacce aka yi wa dole haka na ƙi sauke nawa.....
[03/06 09:10] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*

02

Tamkar yana lalubo ruhina haka nake jin idanunsa masu matuƙar kaifi na kashe duk illahirin jikina.Ajiyar zuciya na soma saukewa akai-akai kafin kuma na lumshe idanuna na shige can jikin kujerar da nake zaune sosai.

“Zai iya ƙara masa ruwa ko kuwa haka zai sha shi zalla?” na ji muryar Ubaidah na tambayawa.

Cikin muryar nan tasa ta Fulanin da ba su jin Hausa sosai ya ce “zai ƙara ruwan zam-zam ko kuma ruwan hadari,sannan ki kula sosai da kanki kamar yadda na faɗa miki da sauran lokaci har yanzu kar ki wani tashi hankalinki da sannu duk katangu sharrin za su rushe dama duk abin alkhairi kafin a same shi sai an sha daga”


Cikin wata irin murya mai cike da takaici na ji Ubaidah na cewa “uncle Suhail ka fi kowa sanin yadda nake kula da kaina wannan dalilin ne yasa mugaye ma ba su fiya son zuwa inda nake ba ,babbar damuwata shi ne yadda ake cutar da na kusa da ni saboda an san zan ji zafi”


“Jira ina zuwa bari na kawowa ƙawarki wani magani” jin furcin da ya furta ya saka ni saurin buɗe idanuna,sai na ga tuni ma ya juya baya yana tafiya.Tamkar wanda ake tunkuɗawa gaba haka tafiyar tasa take kai ka ce cikin iska yake.Bai wani jima ba ya dawo hannunsa riƙe da wani ɗan ƙullin magani cikin tsumma.

Jikina ne ya soma rawa jin yana cewa “ta shaƙa wannan cikin hanci zai sassauta mata yawan firgicin da take shiga”


Tsabar mugunta irin ta Ubaidah sai cewa ta yi “Uncle Suhail ka shaƙa mata da kanka mana” ta yi furucin ne tana mai sauke gilashin ɓangaren da nake zaune .

Bakina ya soma rawa,cikin rarrabe wa murya na ce “ban..ban. so” sai dai tuni ma ya zagayo inda nake.Babu shawara ballantana neman izini kawai kama kaina tare da yin sama da shi,ido na rumtse jin hannunsa da wani bala'in sanyi kamar wanda ya fito daga mutuware can inda ake ajiyar gawa.A daidai lokacin da ya shaƙa mini maganin kuwa ji na yi kamar an ɗora ƙwaƙwalwata ne kan kan tanda ana yi mata juyin waina.Da wani bala'in sauri na ware idanuna ina jin su ma suna yi mini yaji,atishawa na soma yi ba ƙaƙautawa.Yayi ɗan baya yana kallona kafin ya ce “akwai damuwa sosai a rayuwarta sai dai ƙofofin taurarinta sun ƙi buɗewa ballantana a san ta ina za a soma”

A wannan karon muryar tasa sai na ji ta tamkar ba ma ta mutane ba,da wani irin sauri na damƙo hannun Ubaidah ina mai kallonta da jajayen idanuna so nake na ce mata mu tafi amma na kasa furta ko da harafin A.

Sauran maganin ya ɗaure tare da cillo mini shi kan ƙafafuwana ya ce “a duk lokacin da kike cikin tsoro ki shaƙa wannan ” ko kallon inda yake ban yi ba,cikin wata murya kamar ta mai yi mini faɗa ya ce “ko ba ki ji ba? Ki riƙe maganin a hannunki” jiki na rawa kuwa na ɗauke shi na jimƙe.


“Allah ya tsare” ya furta , Ubaidah ta amsa da “amin!” kafin ta mayar da maduban motar ta kuma yi mata key.Duk sanyin Ac da ke tashi bai hana zufa tsatsafo wa a goshina ba,atishawar ta tsaya sai dai ajiyar zuciya da nake saukewa akai-akai ina jin kuma zuciyata na rage nauyin abin da nake jin ya danne ta.

Har muka isa gidansu babu wanda ya cewa kowa komai.Ta yi horne mai gadin gidansu ya tura ƙofar da sauri ta wuce,cikin jerin manyan motocin da kusan kullum sai ka ga sabbi ta ajiye tata.Sai a lokacin ta dube ni “ya jikin naki?” ban ce mata komai ba sai muguwar harara da na yi mata.Ta sakar mini murmushi kafin ta buɗe murfi ta fita ta zagayo ta buɗe mini ni ma,a hankali na ziro ƙafata ta dama na fito sai dai fa tamkar wacce aka yi wa duka haka na ji duk jikina na yi mini ciwo ga kuma ƙafata ta hagu da ta ƙage.Hannuna ta kama muka nufi hanyar da za ta sada mu da lafiyayyen falonsu mai cike da kayan more rayuwa,kujeru na zama kusan kala uku ne ma a ciki sai babban teburin cin abinci wanda shi kansa abin kallo ne.

Tsit falon yake babu kowa sai ƙatuwar tv wacce ta kusa cinye bangon ɗakin tsabar girmanta,iya hotuna kawai take nunowa babu magana.Can ɗakinta muka haura ba tare da ta damu da kashe tvn ba,muna shiga ta je ta ɗauki remote ta saita sanyin Ac kafin ta ce “bari na haɗa miki ruwan wanka” sai ta wuce can bedroom ni kuma kan kujera na zube ina maida numfashi tare da tunanin mutumen nan da ta kira uncle Suhail.

Ina nan ta fito,ta zo ta kama hannuna tana cewa “taso ki je ki yi wankan,ko na yi miki?”

Duk da ban jin jikina sai da na yi dariya tare da kai mata duka na ce “ki jira in kin auri Ya Sulaimanu can ki yi masa amma ni jikina ya fi ƙarfinki”

Wani kallo ta yi mini na tara saura kwabo kafin ta ce “farar fatar ce ta fi ƙarfina ko me? Daɗin abin dai launina ya fi tsada”

“Matsalata da ke hauka,ana gabas kina yamma yanzu ke sai ki yi mini wanka?”

“Me yake yi to? Ai bisa larura ne”

“Mu je to ki yi mini” na faɗa ,banza ta yi da ni tare da haye kujera ta soma latsa waya.Na yi murmushi tare da tafiya na shiga bedroom na wuce can toilet ɗinta wacce ta ko ina ta haɗu.Komai na cikinsa pink ne kamar yadda falonta yake,cikin bahon wankan na shiga na kwanta bayan na cire kayana.In ba a gidansu Ubaidah ba ban taɓa yin wanka ko da pampon sama ba ne ballantana shiga bahon wanka,saboda ni ko toilet ɗin ɗaki ba mu da shi iya ta waje ce kawai ita ma babu pampo a ciki.

Ido na lumshe ɗumin ruwan na ratsa ni,ina jin kamar yanzu ne muryar Uncle Suhail ke cewa akwai damuwa a cikin rayuwata.Hawaye masu ɗumi suka silalo mini tuna abin da ya fito da ni daga gidan makoki.Ture tunanin na yi na yi wanka soso da sabulu har zan fito sai kuma na warware dunƙulin gashina na wanke shi fes yayi taushi da sheƙi.Gaban shower na je na ƙara wanke jikina sannan na ɗaura towel da kuma ɗaukar ɗaya ina tsane jikina.Inda take ajiye abin busar da gashi na duba sai dai ban gansa ba,cikin ɗaga murya na ce “in kin gama soyayyar zo ki bani abin busar da gashi” amma shiru ba ta ce komai ba,na nufin falon ina mai cewa “wallahi Udah zan yi miki rashin mutum...” sauran maganar ce ta maƙale mini a maƙoshi sakamakon ganin Ya Ubaidullah da ke tsaye ƙiƙam yayi tsayuwarsu ta sojawa kunnensa maƙale da bluetooth ɗaya yayin da kuma ɗayan ke a hannunsa.Yadda ya zubo mini ido yana kallo ni ma haka nake kallonsa da nawa cike da tsoro,muryata na ɗan rawa na soma i'ina.

“Ban san..ban san ka shigo ba ,Udah ce...” hawayen da suka zubo mini shaaa su suka katse mini maganar.Daidai nan kuma Ubaidah ta shigo a shagwaɓe tana cewa “ni dai don Allah ka yi haƙuri har zuwa gobe wallahi ban gansa ba”

Sai a lokacin kawai Ya Ubaidullah ya maida dubansa ga Ubaidah wacce ni ma ita nake kallo idanuna na ci gaba da zubar da hawaye.Muna yin ido huɗu da ita ta ce “Ya Ubaidullah me yasa za ka hukunta Suby madadina? “ sai ta zo da sauri ta rungume ni yayin da shi kuma ya fita.
Wata ajiyar zuciya na sauke ,a duk lokacin da Ubaidah ke tare da ni a yanayin damuwa ina jin wani sassauci sai nake jin ita ɗin tamkar garkuwa ce a gare ni.


“Yi haƙuri kin san halinsa in allurar sojojin ta motsa masa bai da mutumci,rabon a yi ne yasa na ɗauki motarsa jiya na tafi shopping to ban san ina na jefa key ɗin ba shi ne fa kawai.Faɗa mini me yayi miki Allah sa dai ba marinki yayi ba?” sai ta ɗago tana duban fuskata.


Na ce “bai yi mini komai ba fa,kin san ni dama tsoronsa nake yi tun bayan dukanmu da ya taɓa yi”

Ubaidah ta ja wani uban tsuki tana mai cewa “aikin banza! Shi ne kike hawaye? Wai ke sai yaushe za ki girma ke komai kuka,shan magani ma kuka kike yi masa”

“Ke dalla bani abin busar da gashi” na faɗa tare da yin gaba,sai da na je gaban madubi ne na tuna cewa ashe towel ne ɗaure a ƙuguna,firgicin ganin Ya Ubaidullah duk ya mantar da ni.Wata irin kunyar kaina ce ta kama ni, Ubaidah ta zo tana busar mini da gashi bayan ta gama sai ta shafa mini mayuka ta kuma ɗaure shi.

Kayanta ta ɗauko ta bani na saka sai dai sun kama ni saboda na fi ta ƙiba da kaɗan.Hotuna ta shiga yi mini kamar kullum saboda ita ciwon hoto ce,har sai da na gaji na je na kwanta bakin bed.Na lumshe ido ina mai cewa “ba ki tambaye ni dalilin kukana da ɗazu ba”

“Malama taso mu ci abinci,ƙarfe biyu ta kusa”

Ni sai yanzu ma da ta ambaci abinci na tuna da yunwa ce ta tashe ni daga bacci a ɗazu.Saukowa na yi ba tare da na ce komai ba muka fito,har yanzu babu kowa falon.Dianing muka je,ta soma buɗe kwanukan da ke kan teburin tana mai cewa "me za a zuba miki? ”

Na dubi ɗaya kular da ba ta buɗe ba na ce “ita wannan mene ne a ciki?”

Buɗewa ta yi,ƙamshi ya bugi hancina wanda ya zaburar da yunwar da nake ji.A duniya ina mugun son farfesun kifi,tana murmushi ta ɗauko plate ta saka mini ƙaton kifi guda ɗaya tare da sakwarar doya. Hannu na saka na soma ci hankali kwance ita ma ta zuba nata kalar abincin muka shiga yin hirar makaranta.

Ƙamshinsa ne ya fara yi mana sallama kafin shi ya ƙaraso,kamar an yi ruwa an ɗauke haka na yi shiru.Jikina ya yi sanyi liƙis ganin ya ja kujera ya zauna wato shi ma abincin zai ci,Ubaidah ta ajiye cokalin hannunta ta miƙe ta zuba masa farfesun kifin tana mai kawo wata tasar ruwa wacce kusan kullum tana kan dianing ɗin ban taɓa sanin amfaninta ba sai yanzu da na ga ya wanke hannunsa ya soma cin abinci.

Ɗan satar kallonsa na yi ,sai na ga ya kalli plate ɗin gabana.Wani irin dammm ƙirjina ya bada wato abin da na fahimta iya shi ɗaya aka girkawa abincin amma rashin mutumcin Ubaidah yasa ta zuba mini ni ma.
Ji na yi duk na tsargu kawai sai na miƙe da sauri,ya ɗago ya dube ni.Idanunsa har sun fi na Uncle Suhail kaifi da shiga jiki,wannan yasa saura ƙiris na faɗa kansa amma duk yadda na yi ƙoƙarin haka sai da hannuna mai kumfan abinci ya kai jikinsa.Zuwa wannan lokacin tuni fitilun idanuna sun disashe don tsoro,murya na rawa na ce “yi..yi haƙuri” sai kuma na nufi hanyar kitchen duk da ina jin idanunsa a kaina ban tsaya ba.


Saura ƙiris na kai wa bango karo Allah yayi sa'a ƴar aikinsu ta fito ita ce ta riƙe mini hannu kafin ita Ubaidar ta iso.Har kitchen ɗin ta yi mini rakiya na wanke hannuna,ta buɗe frigine ta ɗauko mini gorar ruwa mai sanyi ta bani na sha.Babu laifi na ji ƴar nutsuwata ta dawo,sai a lokacin na harari Ubaidah ta ƙyalƙyace da dariya tana mai cewa “to me kuma na yi yanzu?”

Cikin jin haushi na ce “a'a ki dai kashe ni sai ki huta kawai,kin san iya shi aka yi wa girkin amma kika zuba mini”

“To me yake yi? Shi fa bai da matsala kawai raini ne bai so da rashin jin magana” ta faɗa .

“Yanzun ma ai raini ne tun da kin san ba zai ji daɗi ba” na faɗa tare da zuwa na leƙa sai na ga tuni ma ya bar falon.
Ta matso kusa da ni tana mai cewa “mu je ki ƙarasa cin abincinki”

“Na ƙi ɗin” na faɗa tare da fitowa,ina ƙoƙarin hawa step ta biyu shi kuma yana saukowa daga benen ɗakinsa ya canza kaya sai ƙamshi yake bazawa yana kallon wayarsa yana yamutsa fuska.Ina ganin zai ɗago na yi saurin tafiya a guje ina haɗawa da gudu-gudu hakan ya fitar da sautin takalmin ƙafata.


“In dai kika faɗi babu wanda zai hana ni yin dariya” Ubaidah ta faɗa tana take mini baya.Ina shiga direct toilet na shiga na yi alwala na zo na gabatar da Sallah,ita ma haka.Bayan mun gama ne nake bata labarin mafarkin da na yi ina cewa “ina tashi kuma daga baccin na ga Mamu wake da shinkafa ta dafa,kuma kamar a mafarkin dai haka aka kwashe shi aka kai gidan makoki.Babban tashin hankalina shi ne yadda wannan karon ma aka sake...” sai kuma na yi shiru jin kuka zai zo mini , Ubaidah ce ta ƙarashe zancen tana cewa “aka ɗaga bikinmu ko? Hum! Na sani dama ai kin ji yanzu ma uncle Suhail ya ce da saura”

Da ɗan mamaki na dube ta na ce “ya aka yi kika san abin da nake son sanar da ke?”

“Saboda ni ma na yi mafarkin” ta bani amsa.

“Wai wane ne Uncle Suhail ɗin nan?”

“Oho! Ni ma ban sani ba“

Baki da hanci na saki ina kallonta kafin na ce “kuma kika je wurinsa?”

“Eh magani yake bani”

“Ya kuke da shi?”
“Ni ma fa ban sani ba,kin ga zo na nuna miki kayan da na sayo mana jiya ”

Sai ta miƙe ta buɗe drower ta ciro manyan ledoji ta zube abin da ke ciki kan capet,saukowa na yi muka shiga duba kayan a ciki muka ga key ɗin motar da ta yi ta nema.Ta ɗauke shi ta ɗora kan ɗan ƙaramin teburin madubi tana mai cewa “na huta da uƙubar Ya Ubaidullah,ko da yake ma ai kin sa ya canza kayan”


“Wai har yanzu yana nan da aƙidarsa ta in ya sa kaya sai ya dubi motar da za ta hau da su?” na tambaye ta ina dariya.Ta ce “to Ya Ubaidullah fa aka ce miki,wai nan duk cikin gayu ne don a burge anty Hamida ”

“Budurwarsa?”

“Eh cousin ɗinmu wacce nake faɗa miki ta maƙale masa ta rantse in ba shi ba to ba za ta yi aure ba”

“Tana tare da wahala kuwa,ni ko don ban taɓa soyayya ba amma gaskiya ina jin ba zan maƙalewa namiji guda ba na ce dole sai shi”

“Ke wa yake biye ta taki? Macen da ko kwalli ba ta sakawa ido to wane banzan namiji ne ma zai kula ki da ido kamar na macen ɓera”

“Eh na ji dai,kawai sai na saka abin da zai hana ni sukuni ”
“Kawai dai don kin sakawa ranki ne amma daga shafa kwalli sai ido ya hau ƙaiƙayi?”

“Ba za ki gane ba ne” na faɗa cike da damuwa.


★A can gidan makoki kuwa haka Mama Lantana ta saka shakku a zukanta duk wani na kusa da ita ana sukar auren Sulaimanu ana alaƙanta shi da hatsarin da Kawunsu yayi.Tun Mamu na jurewa har ta kasa musamman da ta ji matar shi kawun tana cewa “ai tun da aka fara zancen ƙaddararren auren nan malam

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login