Showing 39001 words to 42000 words out of 55823 words

Chapter 14 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

47

fita zuwa babban falo suka bar su iya su uku don duk inda yarima yake jakariyarsa Ali na tare da shi.Ɗan gefe kawai ya koma yana kallonsu,shi dai ko kaɗan bai ga dacewar yarima da ita gimbiyar ba duk da kuwa cewa ita ɗin kyakkyawa ce ta ajin ƙarshe.


“Amincin Allah ya tabbata ga shugaban gobe” ta furta tana mai takowa inda yake tana ɗagowa haɗi da yi masa wani kallo mai tsayawa a rai wanda a can da babu abin da ke matuƙar girgiza yarima irin kallon nan amma yanzu sai ya ji sam bai burge shi ba,hasali ma na Naomi ya tsinta a fuskarta.

Da sauri ya lumshe ido yana mai amsawa tare da cewa “shi ne ba ki zo kika duba ni ba tsawon kwana biyu ina a kwance”

Murya na ɗan rawa ta ce “subahanallahi! Meke damunka yarima? Ai ban san ba ka jin daɗin jikinka ba,saboda tun ranar da ka haɗa ni da matan nan nake koya musu karatu daidai da ɗaya rana ban taɓa leƙowa waje ba”


Wani numfashi ya furzar yana mai buɗe idonsa ya dube ta,iliminta yana ɗaya daga cikin abin da yake so a tattare da ita,“kar ki damu ai na samu lafiya”


Shiru ta yi tana mai ɗagowa ta dube shi,ita sai yanzu ne ma ta lura cewa kan kujera ne yake.Sai kuma ƙwaƙwalwarta ta tariyo mata lokacin shigowar su shi da jakariya Ali, kasancewar kwanyarta dama can ba kullum take tafiya daidai ba shi yasa ne ba ta fahimci hakan ba.
Rikicewa ta yi ta zube a gabansa tare da soma jero masa tambayoyi,wanda kuma in akwai abin da yarima ya tsana a tare da ita shi ne yawan tambayoyi da kuma wannan haukan da take yi a duk lokacin da wani abu na ƙi ya same shi.


Da wani irin sauri jakariya Ali ya matso yana mai dakatar da ita,yana cewa “don Allah ki yi shiru mana” sai ta ɗago kai tana yi masa kallon tsana saboda tun tuni ta san cewa Ali bai ƙaunarta.


Yana yi mata wani mugun kallo ya je ya kama kujerar da yarima ke zaune ya soma tura shi tare da mayar da shi ɗakinsa.Har Ali zai tafi sai kuma ya dakatar da shi yana mai cewa “kai ni wurin matar da aka kama ɗazu”

Jakariya Ali ya ce “tana da matuƙar hatsari yarima ,da bari ka yi zuwa gobe in sha Allah ka ga lokacin ka ƙara samun ƙarfin jikinka”

“Mu je dai ka kai ni ” ya sake faɗa ,ba don ya so ba ya tura shi zuwa kurkukun har suka isa ragar da aka killace ta.
Tana kwance a duƙunƙune cikin wani tsohon bargo,hatta kanta a rufe yake amma hakan bai hana ta ganin yariman ba.Cikin wata irin murya ta ce “barka da zuwa yariman musulmai,ka sani killace ni a nan ba shi ne maganin matsalarka ba.Hakan ma babban kuskure ne ka tabka,ko da yake ba ka san ko ni wace ce ba” ta ƙarashe faɗa tana yin wani nishi sai ga bargon da ta rufa a shi ya yi wani irin sama tare da buɗe ta.

Yarima da jakariya Ali suka kalli yadda bargon ya maƙale can sama cikin iska.Su duka biyun sun yi imani cewa tsafi ne ta yi,sai dai a yanayin da yarima yake a yanzu ba zai iya ɗaukar wani mataki ba a hannunsa sai kawai yasa jakariya Ali ya juya da shi.




A cikin abin da bai wuce kwana uku ba mulkina ya tsaga kowacce kusurwar yankinmu.Tuni na yi ƙaurin suna yayin da kuma gogaggin matsafa daga garuruwan ƙetare ke kawo mini tayin aure duba da yanayin shekaruna ina buƙatar abokin rayuwa musamman don gudanar da mulki yadda ya kamata sai dai ko kaɗan babu wanda ya kwanta mini a rai.

Muna zaune kan kututuren icce ni da Debora ,sai kuwa ga wata baƙar mujiya ta soma shawagi haɗi da yin wani kuka.
Debora ta furta kalaman tsafi tana mai buɗe tafin hannunta,sai mujiyar ta sauko tana mai sakar mata wata takarda ita kuwa jikinta har rawa yake yi wurin buɗewa.Rubutu ne reras da manyan baƙi,sai dai harufan na tsafi ne kuma ba su yi mini wuyar karantawa ba.A tare muka kalli juna,kafin na miƙe tsaye ina cewa “to a wane yanki ne aka kama ta?”

“Ba ta faɗa ba a cikin wasiƙar,amma ina zaton ɗaya daga cikin garuruwan da suka kawo miki tayin aure ne ba ki amince ba”

Shiru na yi ina tunani kafin kuma na karɓi takardar,ina furta tsafi rubutun ya goge sai na soma juya ido ina yin magana cikin raɗa rubutun ya soma rubuta kansa ina gamawa sai na umarci tsuntsuwar ta kai wa mahaifiyar Deborah .Ido na birkice suka koma farare tas ta haka ne nake iya hango gudun tsuntsuwar tana keta sararin samaniya tana wuce ƙauyuka tana shiga wasu garuruwa sai dai tana daf da ƙetara wata tutar wani yanki na ga wata kibiyar haske ta jefe ta ita kuma ta faɗi ƙasa ,duk kuma yadda na ƙware a tsafi ban ƙarashe ganin sauran abin da ke faruwa ba......
[12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

04



Hankalin Debora sosai ya tashi saboda ta lura da abin da ya faru.Ko kaɗan ban ga laifinta ba saboda na san yadda mutum ke ji in mahaifiyarsa ba ta tare da shi, wannan yasa na damƙo hannunta tare da yin wani irin kalar tsafi na gushe mata da damuwar tare da saka mata nutsuwa na danne ƙuncin zuciyarta.



Idonta da suka kaɗa suka yi ja na duba karin na ce “ki sani cewa babu wani sarki da zai gagare ni,ki sa a ranki ummarka tuni ta kuɓuta”

Muryarta na fitar da wani irin amo take cewa “ya ke shugabata in ba ki manta ba irin haka ne mahaifina ya tarar da wa'adinsa,silar zaƙulo bincike domin rubuta tarihi ya haɗu da wasu mabiya addini mabanbanta suka kashe shi a ƙarshe sai mahaifiyata ce ta maye gurbinsa domin ci gaba da rubuta littafin kudin binciken duniyar ruhaniya” tana kawowa nan da zancenta sai ta ɗan yi shiru kafin ta ci gaba da cewa “ina jin tsoron kar a ce ita ma Umma nata ajalin ne ya zo”


Kai na girgiza mata ina mai cewa “muddin ina raye hakan ba zai faru ba”

Rungume ni ta yi tana sauke wata irin ajiyar zuciya,yayin da ni kuma na shiga tunanin hanyar da zan bi na ƙwato Umma ɗin saboda a duniyar nan a halin yanzu banda wani masoyi da na fi so da ƙauna sama da Debora.Cikin hikima na mayar da ita cikin gida gabanin ni kuma na fita zuwa can cikin baƙin jejin garinmu mai cike da aljanai da fatalwa.


Cikin tafiyar rauni ta masu larurar ƙusumbi nake tafiya ana take mini baya,ko kaɗan ban san su wane ne ke take sawuna ba kuma ban jin tsoro ko fargaba wani abu.A haka na isa bakin wata iraciyar kuka mai zubin halittar mutum don da baki da hanci gare ta.Ina gama daidaita tsayuwata sai kuwa bisashin ganye suka fara zubowa a kaina kamar ana ruwa kafin ɗanye ƙwaya ɗaya ya faɗo a gabana.Ɗaukarsa na yi tare da tofa yawuna a kai,sai na soma juya ido babu jimawa yawun suka rikiɗa zuwa rubutu.Sai a lokacin na miƙawa itaciyar ganyen mai ɗauke da bayanin abin da ya kawo ni nan ɗin.Tafin hannuna na ji ya cika da wasu duwatsu,ina dubawa sai na ga suna sheƙi akan kowanne dutse an rubuta karlis .Ban yi jinkiri ba na nufi ɗaya daga cikin magudanar ruwa na je na yi tsaye ina kallon yadda ruwan ke a kwance sun nutsu ko motsi ba su yi.Dutse ɗaya na cilla ina sauraren yadda ƙararsa ya ratsa ruwan tare da soma yin gudu har zuwa inda nake son ya isa.


Ba a ɗauki wani lokaci ba wata iska mai sanyi ta soma kaɗawa tana fitar da wani ƙanshi irin na gawa.Can sai ga Maa ta ratso ruwa ta fito,fuskarta ta yi wani fari fat kana ganinta ka ga matatta ga kuma fararen kaya a jikinta.


Cike da soyayya na je da gudu na rungume ta,sai dai kamar na jimƙi iskan gas haka na ji babu wata alamar gangar jiki.Da sauri na ja da baya ina kallonta tana wani fitar da murmushi,wani irin tausayin kaina na ji wanda ko ranar mutuwarta ban ji shi ba.


“Me kike buƙata Nao?” don haka take kirana a duk lokacin da take shauƙi ko kuma take son isar mini ƙaunar da zuciyarta ke ƙumshe da ita.


“Maa shi kenan ba zan ƙara jin taushin gangar jikinki ba?” ita ce tambayar da na yi mata madadin na sanar da ita matsalar da ta kawo ni.


Ta ce “Naomi a zangon da nake na fita daga sawun duniyar bil'adama na koma cikin duniyar matattu,ki kira ni da ruhi kai tsaye”

Kallonta na yi,tabbas ita ɗin ruhi ce kamar yadda ta faɗa ɗin.Na kai hannu na shafi kumatuna da nake jin wani damshi,wanda na yi imanin cewa ruwan hawaye ne .Murya na ɗan rawa na ce “mahaifiyar Deborah ta faɗa hannun mugaye shi ne nake son sanin ta ya zan ceto ta?”


“Babu buƙatar yin haka,saboda ita ɗin ba kanwar lasa ba ce.Za ta iya fitar da kanta kar ki wani damu kanki” Maa ta faɗa .


Na ce “amma kuma ita ce da kanta ta aiko da takarda domin sanar da mu”


“Ta yi haka ne domin ku ci gaba da rubuta littafin bayanai ba wai don kawo mata agaji ba.Ki sanar da Deborah cewa lokaci ya yi da ita ma za ta ɗauki muƙaminta na rubuta tarihi kamar yadda mahaifinta ya karɓa gun mahaifinsa,ita kuma mahaifiyarta ta karɓa daga mahaifinta,yanzu kuma ƙaddarar littafin tarihi ta dawo hannunta” Maa na gama furta haka sai ta soma nitsewa cikin ruwa haskenta na tarwatse wa haɗi da disashewa.A gaban idona ta ɓata,na lumshe idona ina mai furta kalaman tsafi tare da buɗe su kuma a nan na tsinci kaina a ɗakina.


Deborah na kwance amma ba bacci take yi na.Kallonta na yi kafin a takaice na sanar da ita abin da Maa ta shaida mini,da wani irin sauri ta miƙe ta zauna tana kallona can kuma ta soma furzo da wani irin furuci sai na ji tsafin da take yi ba irin nawa ba ne yana da banbanci kamar yadda Hausar wani gari ba ɗaya take da ta wani garin ba.
Babu jimawa sai muka soma jiyo kukan jemage yana wani tsala shi kamar zai fasa gidan,a tare muka fita nan muka yi gamdakatar da wani baƙin jemage baƙi ƙirin da shi ga kuma wani irin girma na ban mamaki.

Kan ƙafafunsa ya sauka bayan ya cillo wani tsohon littafi ya dira a tafukan hannun Deborah.
Kallo ɗaya na yi masa na fahimci cewa shi ne wanda aka wakilta domin tsare littafin ya basa kariya.A hankali ya soma yin tsalle har ya isa gun Deborah,babban farcenta na ƙafar hagu ya kama ya fasa shi tare da soma shan jininta irin sosai ɗin nan don har sai da ta soma yin wani irin haske irin na rashin jini amma ko kaɗan ban yi yunƙurin tsayar da shi ba har sai da ya gama sha sannan ya tashi sama,sai dai bai yi wani nisa ba ya ɓace ɓat.
Sai a lokacin na je na kama ta na ja ta zuwa ciki na zaunar da ita,magani na ɗauko na soma rufe mata yatsan da shi wanda har yanzu yake ɗigar da jini.


“Ki kwanta ki huta na san kin gaji” na furta.

“Ki soma karanta littafin kafin ni na karanta miki ” ta furta tare da miƙo mini,kamar ba zan karɓa ba sai kuma na kai hannu na karɓi littafin na ajiye a gefe.Ido ta lumshe ta soma yin bacci mai kama da mutuwa,wanda na yi imani cewa a cikinsa ne za a miƙa mata wasu asirai da kuma power kariyar kai da kuma ta abin da aka damƙa mata amanarsa.


A cikin wannan daren ne na soma karanta littafin tarihi wanda ya ƙunshi rayuwar jarumai da kuma irin gwagwarmayar da suka yi fama a kai.Na samu sirrika dayawa,na yaƙi da kuma yadda ake sarrafa maita ta sigogi daban-daban.
Wannan littafin ya ƙara saka mawa zuciyata cewa duk inda babu magic to lalle babu rayuwa mai inganci, Magic shi ne komai na duniya a cikinsa ne za ka samu ƴanci da kuma gata.Rufe shi na yi tare da raɓawa gefen Debora na kwanta,ina lumshe idona na soma jin wani irin motsi a cikin kunnena tamkar ƙwaro na tafiya.Ƙara nutsuwa na yi sai na soma jin tamkar ana yi mini magana ne,amma ta ina? Ban sani ba.Ji na yi ana danne ni ana saukar mini nauyi,na furzar da huci mai zafi jin wasu kalmomi daga wata murya da ban san mamallakinta ba.


“ A duk inda kike a faɗin duniyar nan sai na nemo ki,ni ne nan zan kashe ki da hannuna ƙaramar matsafiya muguwa mai idanun maciji” muryar namiji ce amma ban san wane ne ba, sannan ban fahimci abin da yake nufi ba har ya ƙara yin wani furucin “ina ma ace annabi sulaiman bai yi wafati ba,da na roƙi alfarmarsa ya tura rundunar aljanu su gana miki azabar da ta fi ƙarfin tsafinki ”

Saurin buɗe idona na yi,ina mai tambayar kaina “wane ne kuma Annabi Sulaiman?” sai dai banda amsar wannan tambayar,in akwai wanda zai faɗa mini ita to bai wuce Deborah ba wannan yasa na kasa haƙuri na kai hannu na shafi fuskarta.Ta buɗe idonta tarau a kaina,sai dai babu ɗigon baƙi a cikinsu da alamu har yanzu ba ta dawo daga balaguron ruhi ba.

“Wane ne Annabi Sulaiman?” na tambaye ta,idanunta ne suka dawo normal nan take ta tashi zaune sannan ta bani amsa da cewa “ ya kasance ɗa ga Annabi Dawuda shi ma kuma annabin Ubangijin Ka'aba ne.Yana da matuƙar power don a tarihin annabawa shi ne kaɗai ya mulki mutane da kuma aljanai,sannan kuma yana iya yin magana da dabbobi da kuma jarirai waɗanda bakinsu bai buɗe ba.Ya yi mulki cikin hikima da adalci ga al'ummarsa”


Zuciyata ce na ji tana wani irin bugawa na jin bayanin da Deborah ta yi mini.Kamar mai tsoron sake jin wata buwayar na ce “amma me Annabin ke nufi?”


“Mutum mai isar da wahayi daga Ubangijin Ka'aba zuwa ga al'umma ” ta bani amsa kai tsaye.Ban ce mata komai ba sai tashi da na yi na fito waje ina kallon taurari ina kuma juya kalamanta.
Ƙofar gidan na ji ana bugawa,na je na buɗe sai na ga gungun matsafan garin ne da alamu sun fito maitar dare ne suka biyo.


“Ranki shi daɗe mun samu baƙuwar fuska a yankin nan,wani mutum ne maharbi mun tsince shi a wata gona yana bacci.Mun ɗaure shi da duk wata igiyar tsafi amma ta ƙi yin tasiri a kansa saboda girman tsafinsa wannan dalilin ne yasa muka zo zuwa gare ki” ɗaya daga cikinsu ya faɗa .

Raina a mugun ɓace na ce “me yasa ba ku kashe shi ba?”

Kallon juna suka yi kafin wani kuma daga cikinsu ya ce “ kamar dai yadda ya faɗa miki ɗin ne,tsafinsa nada matuƙar ƙarfi da dukkan alamu mutum ne na daban ko a duniyar ruhaniya”

Ban ce komai ba na yi gaba a fusace yayin da su kuma suka take mini baya.Tun kafin na isa gonar nake jiyo numfashin baƙin tsafinsa,ina isa ya yi saurin tashi tsaye muna fuskantar juna.Ɗan saurayi ne da ba zai haura shekara ashirin da takwas ba,sanye yake cikin kayan maharba ya rine gefen fuskarsa da baƙin abu yayin da kuma ƙirjinsa aka zana wata baƙar kunama.

Ban tsaya tambayar wane ne shi ba na kai masa farmaki,ya tare kafin kuma mu shiga masayar kalaman tsafi muna haɗawa kuma da yaƙin gangar jiki.Kamar yadda suka faɗa ɗin tabbas shi ɗin na daban ne,ban ida fahimtar haka ba sai da ya kai ni ƙasa ya saita kibiyar tsafinsa daidai idona.

Yana jan wani numfashi ya furta “kafin a farmaki baƙo a fara tambayarsa da wace aniya ya zo,duk waɗannan matakan tsaron na ruhikan ruwa da kika saka ba su iya tare ni na shigo yankin nan ba sai ke ce kike tunanin za ki hana ni yin abin da na zo yi?” shi abin da ya furta,amma duk da haka ban saurare shi ba na fito da wuƙar mahaifina na daɓa masa ita a ƙirji daidai kunamarsa yayi wata irin kururuwa da ta saka dajin amsa wa kafin ƙyafta ido sai ganin kunamu muka yi suna zubowa kamar ana ruwa.....
[12/06 12:37] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *TIF DA TAYA*🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐🪐
"""""""""""""""""""""""
LoVe aNd HoRrOr StOry☠️

```MRS SADAUKI```💫✍️

FCWA☀️
____________________________________________

05


Yadda baƙaƙen kunamun suka dabaibaye jikina shi ya fi komai ɗaga mini hankali,ga shi kuma masarafin tsafina ya ƙi aiki.Idona ƙurrr kan mutumin da na cakawa wuƙa yana tsaye ƙyam kan ƙafafunsa,yayin da kuma kunamun suka buɗe hannuwansu da alamu umarninsa suke jira su shiga harbata.
Tafin hannunsa ya buɗe ya soma yin furuci cikin Yaren tsafi wanda ya sha banban da nawa,a hankali duk kunamun suka yi ɓata dabo sai a lokacin na yunƙura na tashi zaune ina kallonsa cike da mamakin me yasa bai kashe ni ba kamar yadda na yi yunƙuri.


“Wane ne kai?” na tambaye shi.Bai bani amsa ba sai nuni da yayi mini da wuƙata wacce har zuwa yanzu tana nitse a cikin ƙirjinsa.A hankali na miƙe tare da zuwa na ciro wuƙar,abin mamaki sam babu ko da ɗigon jini da ya zuba illa kawai alamun an huda ƙirjin.


“Banah!” ya bani amsa,na maimaita sunan a bayyane kafin na ce “me ya kawo ka YANKIN MUTUWA?”

“Ke!” ya bani amsa kai tsaye,kallon ban gane ba na yi masa kafin na ce “ni kuma?”

Kai ya jinjina mini kafin ya ciro wata sarƙa da ke a wuyansa mai tambarin gumki ya miƙo mini,na karɓa tare da juya ta sannan na ɗago na dube shi.


“Ba ki ga komai ba?” ya tambaye ni.

“Me kake son nuna mini?”

“Duba da kyau dai” ya sake faɗa ,sai na nutsu da kyau nan ne na ga gumkin jikin sarƙar zanen mace ne da ƙusumbi a bayanta.


Na shafi ƙusumbin da ɗan yatsana,nan take ya kawo wani haske kamar an kunna ƙwan lantarki.Banah ya matso kusa da ni shi ma ya ɗora nasa yatsan kan nawa sai hasken ya ƙaru a hankali kuma muka fara yin sama ƙafafuwanmu suka bar ƙasa muka lula can cikin iska.


Mutanen gari ne suka fara fitowa,sai kuma suka shiga yin kiɗa da bushe-bushe yayin da wasu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login