Showing 24001 words to 27000 words out of 55823 words

Chapter 9 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

36

a hankali saboda ciwon ƙafata.Har na isa idanunsa na kaina,kusa da Ubaidah na yi tsaye ina ɗan jingina da bayanta na kuma riƙe ta gam na ɗora kaina kan kafaɗarta,a hankali na ce mata “na gaji”

“Aikin me kika yi ko cin abincin ya gajiyar da ke?” ta faɗa .Na turo baki tare da kai hannu na mitsike ta,tana dariya ta saki ƴar ƙara daidai nan Ya Ubaid ya gama wayar yana mai kallonmu.Ita ce ta soma yi masa magana,“Ya Ubaid me ka zo yi sukul ɗinmu?”

“Ya jikin nata? ” yayi tambayar yana kallona kuma madadin ya dubi wacce yake tambayar,na ɗan lumshe ido ina sauraren bugun zuciyata.

“Ga ta nan dai babu abin da ke yi mata ciwo sai dai yunwa kawai da take ji,dubi yadda ta rame“ Ubaidah ta faɗa tana ƙoƙarin janye ni daga jikinta,na takure wuri ɗaya na ƙi yarda.

“Mu je na kai ku restaurant ” ya furta tare da juyawa, Ubaidah ta ce “mu tafi ko?”

“Na fa ƙoshi iya ruwa nake son sha” na faɗa a sanyaye ba wai don kuma na ƙoshin ba,a'a ban so ina yin kusa da Ya Ubaid ɗin ne wata irin kunyarsa nake ji.

“To mu je ai can ma ana sayar da ruwan” ta faɗa tare da soma tafiya.
Na ce “ga kularki can fa na baro bakin ƙofar aji”

“Bai komai in Bahijja ta fito ta ɗauke mana” ta faɗa ,Bahijja a banci guda muke zaune ita ma ƙawarmu ce sai dai ba mu shaƙu sosai ba kamar yadda muke ni da Ubaidah.

Haka muka wuce,tuni ya shiga motarsa wannan farin gilashi ne da ita hakan yasa ina iya hango shi yanzu ma wata wayar ce yake yi.Muna isa Ubaidah ta buɗe gidan gaba ta ce “Suby shiga”
Na ce “zan zauna a baya ki shiga kawai”
“In muka dawo ke za ki shiga gaba yarinya” ta faɗa tare da shigewa,gabana ya faɗi jin wani zance haka na shiga baya ɗin ya figi motar .
Mun hau kan titi sosai ya ajiye wayar,madubin gabansa ya gyara da kyau hakan ya bamu dama kallon juna ni da shi.Wani irin amintaccen kallo ne yake yi mini,na sunne kai ina murmushi wanda sam ban yi tunanin shi ne mabuɗin alaƙar zuciyoyinmu ba.


Wani haɗaɗen gidan cin abinci ya kai mu,VIP PALACE can aka nufa da mu.Komai na ciki na ƴan gayu ne,Ubaidah ce ta zaɓa mana abin da za mu ci yayin da shi kuma ya ɗauki iya abin sha.

Da aka kawo mana abincin sai da na kasa ci na yi ta juya cokali,a hankali Ya Ubaid ya miƙe ya je can kusan window tare da yaye labulen wurin ya tsaya yana kallon abin da ke wakana a ƙasa.

Sai a lokacin kawai na soma ci,shi ma ban wani saki jiki ba.Ubaidah banda aukin murmushi babu abin da take yi sai kuma kallonmu,bai dawo mazauninsa ba har sai da na kammala ci ina shan lemu.

Zuwa aka yi aka kwashe komai da ke kan table ɗin,sai kuma ya soma yin magana.
“Ya jarabawar?”
“Ta yi daɗi sosai,su Suby tun da aka duƙe kai ba a ɗago ba an ga banza” ta faɗa tana mai kallona,harararta na yi na ce “ke ma ai banzar kika gani”


“Ya kamata dai tun yanzu ku ƙara ɗaura ɗamarar yaƙi,don da zarar kun ci exam za ku wuce jami'a a can karatun ya fi tsanani”

“Ni ai ɓangaren da zan karanta babu wani tsanani ,ka faɗawa dai likitoci” Ubaidah ta faɗa,ya zubo mini ido sai kuma bai ce komai ba ya miƙe.Bayan ya biya kuɗin muka fito yana mai tambayar in makaranta zai mayar da mu,“gidansu Suby za mu je” ta basa amsa.Bakin motarsa muka isa sai ta yi saurin shiga baya ina shirin shiga ni ma idanunmu suka sarƙe cikin na juna,ba don na so ba na zagaya ta can ɓangaren sai kuma na yi tsaye na kasa buɗewa sai shi ne da ya shiga ya buɗe mini ta ciki.Tsabar yadda jikina ke yi mini rawa na buge ƙafata mai ciwo,na rumtse ido ina mai daurewa na shiga na zauna.Sosai na yi ƙoƙarin mayar da hawayen da suka taru a idona,ita ce ta soma yi masa kwatance.Har muka isa ban ɗago ba, Ubaidah ta yi saurin fita yayin da shi kuma ya duƙo yana cewa “mu ga ƙafar” a hankali na ciro ta hawaye na zubo mini shaaa har suka ɗiga gefen kunnensa.Ya ɗago yana kallona,“ko in kai ki asibiti?”
Kai na girgiza,“zan sayo miki magani to” ya furta. Ban ce komai ba,ya kai hannu ya buɗe mini murfi,tare da zaro hankici ya miƙo mini na karɓa na goge fuskata sai na fita.Ina shiga cikin gida na ga Ubaidah a tsaye kamar an dasa shuka.

“Lafiya?” na tambaye ta,da hannu ta yi mini nuni da wata baƙar akuya mai gemu ta kuwa ƙuro mana idanunta jajaye.


“Wane ne?” daga can ɗaki muryar Mama Lantana ta faɗa kafin kuma ta fito.Tana ganinmu ta haɗe rai tana cewa “lafiya kuka wani tsaya nan? Ke don ubanki jiya ina kika kwana?”

Jikina na rawa na ce “gidansu Udah”

“Can ɗin gidan ubanki ne? Daga za ta auri ɗan uwanki shi ne kika kwashi jiki kika tafi can kika kwana saboda kalar dangi ,ki ci kaza ki sha lemun kwalba kin dai ji kunya.Ko da yake laifin gantalaliyar uwarki ce wacce ba ta san mutumcin kanta ba ballantana na ƴaƴanta...” sai da ta kawo nan kawai Ubaidah ta yi magana.

“A'a Mama in za ki yi mata faɗa ki tsaya iya ita amma kar ki taɓa Mamu don wallahi ba zan yi shiru ba.Ko ita Suby ɗin don kar a ce na yi rashin kunya ne da wallahi ba ki isa ki faɗa mata biyar ba ban faɗa miki goma masu muni ba” duk yadda nake son dakatar da Ubaidah amma ta ƙi yin shiru har sai da ta faɗi son ranta.

Mama Lantana sai ta kasa cewa komai,na yi matuƙar mamaki ashe Surajo ta gani ya shigo.Ba a ɗauki lokaci ba kuwa ya soma yi mata saukar kwandon rashin mutumci yana kamo sunanta yana ɗura mata zagi,sai tangaɗi yake alamun ya sha abar.
Ɗakinmu a rufe yake,ga shi kuma banda makulli dole muka fito muka samu adaidaita ya mayar da mu makaranta.A hanya Ubaidah sai masifa take yi har muka isa,motarta kawai ta ɗauko muka shiga na yi tunanin gidansu za mu wuce amma na ga ta kama hanyar gidan Uncle Suhail.


Roƙonta na fara yi amma ganin ɓata lokacina ne nake yi kawai sai na haƙura ,da zarar mun haɗa ido da ta wani kallo ne take yi mini mai kama da harara irin kana jin takaicin mutum.Yanzu da muka isa wata yarinya muka tarar yana yi wa ruƙiya cikin ƙira'arsa mai bala'in daɗi kamar sarewa,bayan an kammala mata ya ba mahaifiyar yarinya magunguna kafin su tafi .Sai kuma ya zubo mana na mujiya,Ubaidah ta yi gyaran murya tana cewa “yanzu muka je gidansu,sai muka tarar da baƙar akuya mai gemu a ɗaure da dukkan alamu kuma ta kishiyar Mamu ce kuma na faɗa maka ai ina zarginta ban yarda da ita ba”

“Akuya mai gemu dai alama ce ta sadaukarwar ruhin wani ga aljani,an fi amfani da ita wurin yin tsafin rarabuwar kai a tsakanin mutane” yana kawowa nan yayi shiru.

Ubaidah ta ce “Uncle Suhail don Allah ka yi wani abin”

Ya saki murmushi yana mai cewa “Ubaidah babu abin da zan iya yi akai dole sai wacce kike nema wa maganin ta yarda da kanta ba ta da lafiya”

Yana furta haka sai ta juyo ta dube ni,ta kamo hannuna tana mai cewa “Suby ki yarda don Allah ”

Bakina na ƴar rawa na ce “toh” faɗar haka ke da wuya sai Uncle Suhail ya miƙe ya ɗauko wani abu tare da zuwa ya riƙe kaina da kyau ya ɗiga mini shi cikin idanuna,bai da zafi sai wani irin sanyi mai kamar zai makantar da mutum don sai da na yi kamar kusan minti biyu ban ganin komai kafin kuma fitilun idanun nawa su dawo normal.

"Bayan fitarki a nan shekaran jiya faɗa mini abubuwan da kika gani wanda a can farko kafin na shaƙa miki magani ba ki iya ganinsu” ya furta cike da kulawa,nan take na soma jin ana yi mini motsi cikin kai kafin kuma tunanina ya fizgo mini wani baƙin sirri da ake mantar da ni.

Muryata na rawa na ce “Mama Lantana ta zo gidansu Ubaidah cikin siffar mage ,tabbas na ganta a madubi.Sai kuma ...sai kuma Hamida ” shiru na ɗan yi ,Ubaidah ta ƙara jimƙe hannuna ta ce “kar ki ji tsoro ki faɗa masa me Hamidar ta yi?”

Hawaye suka zubo mini sha kafin na ce “girkin da ta kawowa Ya Ubaid ta zuba magani a ciki wannan yasa na ga kayan cikin na motsi kuma tamkar ba a dafa su ba” a fuskar Ubaidah na karanci tsantsar mamaki haɗi da baƙin ciki,sai dai ta kasa cewa komai sai shi Uncle Suhail ɗin ne ya fara bayani.


“Ya tabbata Mama Lantana mayya ce,sannan tana daga cikin masu aikata shirka .Ita kuma Hamida tana yin wannan ne domin mallakar Ubaidullah.Zan baki wani hayaƙi ki turara shi a tsakar gida a duk lokacin da kika ga wani abu wanda bai dace ba,sai kuma nonon raƙumi da na yi wa karatu ki tabbatar kin bai wa duk wanda ya ci naman akuyar nan, ya sha kofi ɗaya da izinin Allah zai amayo shi”

Sai ya ƙara miƙewa ya je ya ɗauko mini duk abubuwan da ya kamata , wannan karon da ƙarfin gwiwata na karɓa har da yi masa godiya.

Bayan mun fito ne na jingina ga mota ina fashewa da matsanancin kuka,Ubaidah ta ce “me aka yi kuma?”

Cikin muryar da ba ta fita soyayya na ce “me na kashewa Mama Lantana Udah? Shin akwai inda na gaza ne wurin bata girmanta?”

Ubaidah ta taɓe baki ta ce “ai godiya za ki yi wa Allah tun da har ya toni asirinta”

Ban ce komai ba,haka muka shiga mota muka koma can gidanmu.A daidai wannan lokaci ne muka tarar ana yanka akuyar a tsakiyar gida,ita kuwa Mama Lantana ta riƙe ƙugu tana kallo.

Cikin ɗaga murya Ubaidah ta ce “tawakaltu alallahi laa haula wala ƙuwata illa billah! Hasbunallahu wani'imal wakil!” wanda ke yin yankan ne ya ɗago ya dube mu,idanunsa ya ranbaɗa musu kwalli ga wata ƙatuwar casbi a wuyansa.Hannunsa na kalla mai riƙe da wuƙa,sai na ga sam ba iya nasa ne ba kaɗai tamkar har da na wani ɓoyayyen ruhi wanda ba a iya ganin siffarsa sai dai inuwarsa.

Cikin ɗaki muka shiga ni da Ubaidah,duk yadda ta so Mama Lantana ta kula ta kuwa banza ta yi da ita.Muna kallo ƙiri-ƙiri Mama Lantana ke yin tsafi kafin a feɗe akuyar,na dai ga an saka masa naman a leda amma ban san wane ɓangare ne aka cira ba.

Jikina yayi wani irin sanyi,zubewa na yi kawai na kwanta ina jin zazzaɓi na rufe ni.Ubaidah kuwa sai addu'o'i take tofe ni da su.

★Hassana

Ta yi nasarar ganin Ubaidullah,sosai yayi mata kyau cikin shigar gizner ɗin.Sai da ta yi duk iya yinta kafin ta samu magana ta haɗa su da shi,gaishe shi ta yi ya amsa ba tare da ko ya kalle ta ba.Sam kasa sukuni ta yi tun bayan jin muryarsa,ciki ta koma tare da keɓe kanta ta dinga saƙa da warwara.Can kuma ta ji wani abu na luluɓe ta mai kamar inuwa ,wani irin canji take ji a jikinta tsikar jikinta na tashi ko ina yana yi mata yammm! Yammm! Wata irin ganga ce mai zaƙi take jin tana dokawa a kunnuwanta,a take kuma tunaninta ya canza zuwa na yadda halittar da ta gama shigar a yanzu ke burin ganin ta zama.Fitowa ta yi ta soma tafiyar ƙasa,duk nisan gidan malam Yawale haka ta je a ƙafa cikin rana.Layi ta kama tana zaune tana mai ci gaba da jin yanayin na ƙara mamaye ta,a haka har layi ya zo kanta.

Da ta shiga kallo ɗaya malam Yawale ya yi mata ya gane ta, Hassana ta zauna tare da gaishe shi sai kuma ta yi shiru.

Ya ce “ina jinki”

“Ina son ka yi mini aikin da zan mallaki wani saurayi da na gani ina so,aurensa nake son yi” ta faɗa tana jin tamkar ana matse zuciyarta.

Rubutu ya soma yi kan wani guntun madubi kafin ya ce “aikinki yana da farashi mai kauri,muna yin wannan aikin ne ta ɗayan biyu.Za ki duba a cikin almajiraina ki zaɓi mutum ɗaya wanda yayi miki,zan yi rubutu a jikin al'aurarsa sai ya yi mu'amala da ke domin cikar buƙatarki a rana ɗaya tak, sannan daga ƙarshe za ki biya miliyan ɗaya”


Normal group 300: posting biyar a sati
Vip 600: posting goma a sati
Via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
Kowacce ta zaɓi groupe ɗin da take da ra'ayi, wannan ba kalar sauran labaran da na saba yi ba ne sha ƙundum ne,ga soyayya ruwa-ruwa,ga kuma daru da tsantsar darasi
[10/06 16:19] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*

09

Hassana ta dube shi a ɗan firgice,ba wai yin mu'amalar ce damuwarta ba a'a hasalima da ya furta kalmar ji ta yi kamar ma a ce ta samu wani namijin ta yi masa fyaɗe.Damuwarta ɗaya, miliyan ɗaya da ya ambata.

“Miliyan ɗaya?” ta tambaya cikin wani yanayi,wanda yasa malam Yawale faɗa mata ɗayar hanyar.Ya ce “za ki iya yarda ni na mu'amulance ki amma ba za ki biya ko sisi ba”

Ko ida rufe bakinsa bai yi ba ta ce “na amince”

Malam Yawale na jin haka ya danna waya ƴar ƙarar rawa wacce ke nuni da ya tashi daga aiki sai kuma gobe,haka duk mutanen da ke zaune kan layi suka fara fita.
Can ya fito ya duba ya ga babu kowa sannan ya koma can ciki,a gabanta ya zumbule suturar jikinsa ya kuma yi rubutun shirka kamar yadda ya faɗa tun farko yadda tsarin yake.Bayan haka ya umarce ta da ta kwaɓe kayanta, babu kunya ballantana tsoron Allah malam Yawale ya mayar da Hassana cikakkiyar mace.Ta ci azaba fiye da ma kalmar,saboda ba iya ƙarfinsa na ɗan Adam ba ne a'a har da na maƙarabansa.Bayan komai kammala ya fita ya samo mata ruwan ɗumi ta yi wanka sannan suka ƙara dawowa ya soma rubuce-rubucensa tare da haɗa mata magani iri-iri wanda za ta saka masa a abinci da kuma wanda za ta yi hayaƙi da shi in zai zo.Karɓa ta yi ta fito tana tambayar kanta ita na za ta ga Ubaidullah da har za ta zuba masa magani? Amma a haka ta nufi gida.



★Hamida

Cike da takaicin abin da Ubaidullah yayi mata ta jawo motarta ta kai ta can gareji aka gyara mata tayarta da ta soma lalata wa da kanta.Daga nan gida ta wuce ,babu kowa sai ƴan aiki da suke ta faman bauta.Ɗakinta ta wuce,direct ta shiga toilet ko kaya ba ta cire ba ta sakarwa kanta shower hawayen takaici da baƙinci suna masu tsiyayo mata suna haɗe wa da ruwan pampo.Yadda ta ga Ubaid na rawar jikin kai Suby asibiti ya fi komai baƙanta mata rai fiye ma da ƙin cin abincin da yayi,don tana da sauran maganin za ta iya saka masa shi a gaba.
Kamar wata mage da ta sha kashin ruwa haka ta fito daga toilet ɗin ruwa na yi mata tsiyaya.Sai da ta je gaban madubi sannan ta warware sarin ya faɗi ƙasa,sai ta tsaya iya riga da wandon da ta sa a ƙasan sarin.

“Ko lukuta yake so ne? ” ta yi tambayar a fili kafin kuma ta girgiza kai ta ce “kai bai yi yiwa Ubaidullah ya so Suby wannan ƙaramar yarinyar da ko kama ruwa ba ta iya ba, sannan ba ta da wani ilimi” da wannan ta watsar da zancen Suby ta ida cire jiƙaƙun kayan ta sauya wasu na shan iska.
Cike da izzar da ta saba ta kira ƴar aikinsu ta gyara mata ɗaki,kan gado ta haye tana mai buɗe system ɗinta ta fara bincike akan asibitocin da ke buƙatar ma'aikatan kiyon lafiya cikin sa'a kuwa ta ga babbar asibitin da duk ƙasar Nijar babu kamar ta na neman ma'aikata.Wani ɗan ihun murna ta yi saboda ta yarda da kanta a fagen ilimi za ta iya cin jarabawa.Sam ba wai kuɗin da za a dinga biya na albashi ba ne damuwarta,a'a a kira ta matsayin ma'aikaciyar asibitin ma babbar nasara ce.

Haka ta yi wuninta cikin bincike babu sallah ko ɗaya da ta yi sai ta magrib kawai.Bayan sallar isha'i ta fito saboda ta ji motsi,Ummah ce ta dawo daga yawon bin malamai ta gaji duk ƙafafu sun yi mata fututu kamar mahaukaciya.
A yunwace take shan frut ɗin masu sanyi saboda uwar wuyar da ta sha.
Hamida ta ce “Ummah ina kika je yau? ” sai kuma ta nuna ƙafafunta ta ce “dubi yadda ƙafarki ta yi”

“Haba ke ta ƙafa kike,ni babban baƙin cikina shi ne ta yadda ban samo gidan Bokan da aka kwatanta mini ba.Tun safe muke shiƙa ni da ƙawata amma a banza ba mu ga gidan ba”

Hamida ta yi saurin zama gefenta tana mai cewa “Ummah mu da muke da malam Yawale har akwai wani malami da ya fi shi ne?”


“ Wannan fa boka aka ce miki ya fi ƙarfin malam Yawale,saboda a lamarinsa shi sam babu wani abu da ya danganci Allah ”

Hamida ta ce “yanzu ya za ki yi kenan?”
“Gobe za mu sake komawa,in kuma kina zuwa ki shirya mu tafi don kin san an ce zuwa da kai ya fi saƙo gara ki bi mu ki yi wa boka bayanin damuwarki tun da Ubaidullah ya cika taurin kai gara a kai shi ga bokan ”

“Ummah ai na yi tunanin saboda ni kike son ganin Bokan,amma to in haka ne ke wane aiki zai yi miki?”

Ƙwarewa Ummah ta yi ,da sauri Hamida ta miƙo mata ruwa ta karɓa ta sha.Sai kuma ta miƙe ta bar mata falon,Hamida ta bi bayanta da kallo tana mamakin Ummar sam ita ba ta yi tunanin akwai wata damuwar da ta shige mata ba da har take son ganin boka.
Tv ta kunna tana kallo,kafin ta sa ita ma a kawo mata fruit ɗin ta soma sha.

Abdul Hamid yayi sallama,ta amsa ba tare da ta dube shi ba idanunta na kan tv.Kusa da ita ya zauna yana mai ɗaukar ayaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login