Showing 12001 words to 15000 words out of 55823 words

Chapter 5 - Romon Hakuri Compelet By Mrs Sadauki

13 Jun 2026

35

na sake dawowa”

“To ai ko ka tashin ba za ka sanar da ni ba sai dai na gan ka tun da yanzu ba a bakin komai nake ba” Mama Lantana ta faɗa cikin ɓacin rai wanda malam Yawale ne ya tabbatar muddin tana nuna masa haka to tabbas Sulaimanun zai ƙara tsoronta.

Jikinsa na wata kyarma kuwa ya zube gwiwansa a ƙasa yana bata haƙuri,amma saboda mugunta ta Mama Lantana sai ta juye kai tana wani yin ƙyaci a zuci tana cewa ‘ yadda saboda ƴar uwarka na ji ciwo kai ma sai na azabtar da kai’


“Mama don Allah ki yi haƙuri wallahi in kina fushi sai na dinga jin zuciyata na ƙunci kamar ana gasa ta a wuta” ya faɗa cike da rauni irin na wanda aka asirce.

Surajo wanda shigowarsa kenan ya ji kuma abin da Sulaimanun ke cewa,da mamaki ya dubi Mama Lantana yana mai cewa “wai ke mene ne haka ? Kullum cikin sabuwar masifa kike tsirowa ”

Jikin Mama Lantana ita ma yana ƴar rawa ta ce “Manu tashi ka tafi” bawan Allah sai ya miƙe,Surajo ya zo ya ɗauki akwatinsa yana mai hararen Mama wacce duk taƙadirancinta tsoron babban ɗan nata take ji Surajo don ba ƙaramin aikinsa ba ya ɗirka mata na jaki saboda ƙwaƙwalwarsa ba daidai take ba shaye-shaye ya rikita ta.

Suna fita Sulaimanu ya ja wata ajiyar zuciya,jininsa ya haɗu da Surajo sosai.“Ya kamata ka nutsu Surajo babu kyau yi wa iyaye irin haka,Mama uwa ce duk abin da ta yi daidai ne”

“Kai dai za ta yi wa,ni ta isa ma ta wani sa na zube ƙasa a gabanta? Dubi dalla yadda ta sa kayanka suka ɗau ƙura” ya faɗa yana wani juye baki irin ƴan daban nan.Shi dai Sulaimanu bai ce komai ba,a haka suka isa tashar mota dama ba su da wani nisa sosai.Sai da motarsu za ta tashi sannan Surajo yayi masa sallama da fatan sauka lafiya,Sulaimanu ya ciro kuɗi aljihunsa ya basa yana mai cewa “ga wannan amma don Allah iya abin amfani za ka saya da su”

Ya karɓa yana godiya kafin ya ɗaga masa hannu.Sulaimanu dai jingina yayi a jikin kujera yana jin ƙunzi,ko kaɗan kuma zuciyarsa ba ta wani tuna masa da Mamu ba kuma wannan yana ɗaya daga cikin makircin Mama Lantana ita ce ta asirce shi ta hana ƙwaƙwalwarsa tunanin daidai,duk wata daraja da ƙimar uwa ta maido ta a kanta madadin ya yi wa uwarsa Mamu.


Sun yi gudun awa uku kafin su isa,wani huci mai zafi ya furzar sa'ilin da ya fito ya shaƙin iskan garin wanda da ace yana da ikon canza ƙaddararsa da ko sunan garin ba zai ƙaunaci a furta ba ballantana yayi aiki cikinsa.Akwatinsa aka sauko masa,ya tari ɗan acaɓa ya kwatanta masa inda zai je kafin ya hau.
An yi gudun kamar min goma sannan suka isa wani gida ginin ƙasa.
Sauka yayi ya basa kuɗinsa ya ja akwatinsa,yana tura ƙofar ta buɗe .Kamar kullum yau ma gidan,matan banza sun cika shi sai ba'a suke da raha a tsakaninsu da kuma waɗanda suka kawo su.Kai ya kawar saboda kaf cikin matan babu wata mai suturar kirki,mai dama-dama a cikinsu ce ta yi ɗaurin ƙirji.


“Ah Sulaimanu har ka dawo?” Abbas ya tambaya yana mai ɗan ture wata mace da ke kwance a jikinsa.Ya ɗan murmusa ba tare da ya dube shi ba ya ce “eh wallahi yanzu na shigo” sai kawai ya nufi babban falon nasu wanda ke ɗauke da ɗakuna a jere sun fi biyar.Makulli yasa ya buɗe nasa ɗakin ya shiga,yana ƙoƙarin kwanciya Abbas ɗin ya shigo yana cewa “fatan dai lafiya na ga jiya-jiyan nan ka tafi?”

“Lafiya lau” ya basa amsa a takaice,sarai Abbas ya san suna cutar da abokin nasu wanda kaf cikin ƴan sandan da suka zo wannan yanki shi kawai ne bai harakar mata.


Zama yayi kan kujera tare da yin shiru yana kallon Sulaimanun wanda damuwa ta gama aurensa tasss.
“Ina su Mamu da kuma Auta?” ya faɗa don ya san a faɗin duniyar nan su ne kawai ke haska rayuwar Sulaimanun.

“Suna can na baro su gidan makoki kawu ya rasu maganar auren ma da na je yi shiru babu wani labari” ya faɗa kamar zai fasa kuka.
Abbas ya ji babu daɗi sosai a ransa nan ya shiga basa haƙuri,suna cikin haka ne ɗaya daga cikin baby's ɗin da suke kawowa ta shigo babu ko sallama,hannunta riƙe da plate sai wani yauƙi take ita ala dole ga macen da ta waye.

“Ga abinci ” ta faɗa tana miƙowa Sulaimanu plate ɗin,wani kallon tsanake yayi mata.Sanye take da ɗan ƙaramin sket iya gwiwa sai wata shegiyar riga wacce ba ta da marabi da bra,cibiyarta a waje ta saka mata wata wani ɗan kunne.Gabansa banda babu faɗuwa babu abin da yake yi,ba tun yau ba take gwada sa'arta wurin jan hankalinsa ya taɓa kama su suna hira ita da abokansa da kuma nata tana cewa “ni dai ina mugun ra'ayin Sulaiman,ku taimaka ku ce ya kula ni ko sau ɗaya tak”

Kansa ya kawar yana mai cewa “Abbas zan kwanta na huta saboda jiya ba wani baccin kirki na yi ba” yana faɗar haka ne tare da yin kwanciyarsa ya juya musu baya.

Abbas ya dube ta ya ce "mene ne haka? Don Allah fita.Sulaimanu ka yi haƙuri zan yi musu magana dukansue” sai kuma ya ja ta da ƙarfi suka fice suka bar Sulaimanu cikin wani yanayi da ya gwammaci ya mutu kan ya saɓa wa Ubangijinsa,hawaye ne masu zafi suka dinga ƴar rige-rigen fita daga idanunsa.Ya jawo wayarsa yana dubawa,sai a wannan lokacin ma ya tuna ko sallama bai yi wa Ubaidah ba.


★Washegari bayan mun yi sallar asuba ba mu koma bacci ba haka muka zauna ni da Ubaidah muna yi wa junanmu tambayoyi akan addini,hakan ba shi ne farko ba don ko a makaranta haka muke haɗuwa mu da sauran ɗalibai muna zancen addininmu.

“Faɗa mini surori nawa ne suka fara da Alif lamra? Sannan ki kawo mini su” Ubaidah ta tambaye ni.

Na ce “shidda ne,suratul Yunus, Hud,Yusuf,Ar-Ra'ad, Ibrahim da kuma Al-hijir”

“A wace sura ce aka taɓa faɗin sunan ɗaya daga cikin Sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama?”

“Suratul Ahzab”
“Wane sahabi ne?”
“Zaydu”
“Aya ta nawa ce?” ta ƙara jefo mini tambayar cikin salon ala dole sai ta ƙure ni,na ɗauki pilow na jefa mata na ce “wannan dai ya koma mugunta ”
Tana dariya ta ce “to ki faɗa mana aya ta nawa ce?”

“Ta talatin da bakwai ” Ya Ubaidullah ya faɗa daga can falo,sai muka kalli juna ni da Ubaidah kafin ita kuma ta fita da sauri tana ce “Ya Ubaidullah me yasa ka bata satar amsa?”

Daga nan inda nake ina jin yadda yake murmushi mai kamar dariya kafin ya ce “to ai duk ɗaya ne?”

“Kai da ita?” na ji ta jefa masa tambayar.
Shiru na yi ina jiran na ji amsar me zai bata sai kuma na ji tsit.Ƙamshinsa da na ji ya mamaye ɗakin yasa na yi saurin ɗagowa,ba tare da na shirya ba na ce “ina kwana Ya Ubaid?”

Yayi wani ɗan guntun murmushi iya leɓe,bai amsa gaisuwar ba sai ce mini yayi “ya jikin naki?”

“Da sauƙi sosai alhamdullah!” na basa amsa tare da sunne kai saboda yadda yake juya ƙwayar idonsa cikin nawa ba salon yadda ya saba ba ne.

Ganin yayi tsaye ƙiƙam bai tafi ba na ɗan ɗago zan saci kallonsa sai na ga ashe har yanzu idonsa na kaina.Gabana ne ya shiga faɗuwa,sai na soma tunanin ko wani laifin na yi masa.


Ubaidah ta shigo tana cewa “Suby sauko ƙasa mu ci abinci kafin mu shirya mu tafi ”

“Ina za ku je?”
“Wurin gaisuwa kawu ya rasu”
“Allah ya jiƙansa”

A tare muka amsa da Amin ,na miƙe muka fito ni da Ubaidah muka bar shi a can ɗaki.Har muka zauna muka soma yin kari bai fito ba,ni kuwa sai faman ɗaga kai nake yi ina kallon bene da na kasa haƙuri na ce "Udah ina jin tsoro kar dai a ce wani laifin na yi wa Ya Ubaid”

Tana shirin magana ya soma saukowa idanunsa a kanmu,kamar yadda mu ma muke kallonsa.“Ya Ubaidullah zo ka ji Subyna ta samo maka sunan ƴan gayu”

“Ƴan gayu kuma?” ya tambaya yana mai ƙarasowa,ta ce “ eh! Wai Ubaid”

Na ɗan harare ta na ce “yanzu don na ce Ya Ubaid shi ne wani abu?”

Ta ce “Eh ɗin me yasa ba ki ce Ubaidu ba”

Ban san lokacin da dariya ta kubce mini ba na ce “haba dai sai ka ce wani ɗan ga ruwa” shi kansa sai da ya dara kafin ya ja kujera yayi zaune,daidai nan aka ranga uwar sallama.Duk muka juya muna kallonta kafin Ubaidah ta yi ihu ta ce “laaa anty Hamida ” sai kuma ta je da sauri ta rungume ta har sari ɗin da ta naɗe jikinta yana warware wa .
Basket ɗin hannunta ta miƙawa Ubaidah,suna tafe tana ƙoƙarin gyara sarin har suka iso wurinmu.Ban sani ba ko ba ta lura da ni ne ba ko me,sai ta ja gemun Ubaidullah da ke yi mata wani kallo ƙila na mamakin ganinta.

“Ka ga ta warware mini sari,gyara mini?” ta faɗa a shagwaɓe tana wani karya dogon wuyanta,a tare Ya Ubaid da Ubaidah suka kalle ni sai dai kowannensu da manufar nasa kallon.....
[06/06 10:21] MRS SADAUKI{Laouali Rabo}: *ROMON HAƘURI* 🤍

MRS SADAUKI ✍️

FCWA ☀️

*Wannan labari ba ƙirƙira ba ce,labari ne da ya faru a gaske ina fatan za ku bibiye shi sau da ƙafa*
*__________________________________________________*

05

“Kin ga taso mu koma ɗaki muddin kina a gaban anty Hamida sai kin sha kunya,yanzu daga naɗin sari kin ji ta ce ya bata abinci a baki” cikin dariya da salon raha Ubaidah ta furta hakan.

Na ce “to” tare da miƙewa ba tare da na gama cin abincin ba,Ya Ubaid ya ce “zauna” tare da tsure ni da idanunsa masu matuƙar kaifi.Babu shiri na zauna ɗin sai na ga ita anty Hamidar na yamutsa fuska kafin ta gyara sarin da kanta sai kuma ta ja kujera ta kusa da shi ta zauna tana mai cewa “Ubaidah zuba masa girkin da na yi masa,yau dai na sha alwashi a gabana za ka ci abincin ka bani maki ” ta ƙarashe tana murmushi.

Ubaidah ta ciro kulolin daga cikin basket tare da ajiye su kan teburi sannan kuma ta buɗe su.Ƙamshin girkin ya garwaye ko ina,yau kuma waina ce da miyar kayan ciki.Anty Hamidar ce ta ɗauki plate ta zubawa Ya Ubaid kafin ta dubi Ubaidah ta ce “ku zuba naku ku ci ke ma ki faɗa mini in yayi daɗi sai ki bani maki”

Ubaidah ta yi dariya tana mai cewa “waina na ɗaya daga cikin abincin da muke so ni da Suby ” sai kuma ta ɗauko plate ta zuba wainar,tana soma zuba miyar hankalina ya tashi yadda na gani miyar ta rikiɗe zuwa jini ,su kuma kayan cikin ɗanyu ne ba a dafe ba.

Plate ɗin Ya Ubaid na duba wanda har yanzu bai ma kalli wainar gaban nasa ba ballantana ya ci.Motsi na ga kayan cikin na yi tamkar wasu masu rai,jikina ne ya ɗauki wata irin rawa kaina ya soma sara mini ita kuwa Ubaidah a gabana ta turo plate ɗin tana shirin zama ni na miƙe ina cewa "Udah ki kama ni kaina na yi mini ciwo” nan take kuma hancina ya soma zubar da jini,duk sai suka shiga ruɗu ita da Ya Ubaid ɗin.Wannan karon duk yadda ya so ya tsayar da haɓo ɗin abu ya cuttura dole muka fito zuwa asibiti.

Muna isa aka yi katari kuma Dr Abdul Hamid yana nan ,shi ne ya yi mini aiki wanda kusan ba a hayyacina yayi shi ba saboda yadda nake jin ana yi mini magana a ƙwaƙwalwa.
Ba a ɗauki wani lokaci ba jinin ya ɗauke,Udah ta zo ta zauna kan gadon na nake tare da kamo hannuna ba tare da ta ce komai ba.


“Tun yaushe kike shiga wannan yanayin?” Ya Ubaid ya tambaye ni.Kai na girgiza masa ba tare da na ce komai ba,wayar Ubaidah ta yi ringing sai ta fita ta bar ni da shi.A hankali ya soma takowa,wanda duk tako ɗaya har cikin zuciyata nake jinsa.Daidai kusan kaina ya tsaya tare da kama yi ɗan matse,na lumshe ido ina jin wani irin motsi na kai komo.

“Kina da jinnu?” tambayar da ta saka na ware idanuna cikin nasa kenan,na buɗe baki dakyar na ce “a'a banda”

“Ba ki da ko kuwa ba ki sani ba dai?” ya sake jefo mini wata tambayar.
Na yi ɗan shiru kafin na ce “ban sani ba”
Ya janye hannunsa tare da sauke ajiyar zuciya,Dr Abdul Hamid ya sake shigowa wannan karon tare da Ammy wacce tun da muka tashi ban saka ta a ido ba.

Kusan a tare muka gaishe ta ni da shi kafin ta tambayi jikina ya amsa da “sauƙi” kafin kuma ya ɗora da cewa “na je ɗakinki gaishe ki ban gan ki ba,wayarki kuma ba ta shiga ashe kina nan asibiti”

“Eh wallahi akwai abin da ya hana ni sukuni ne shi yasa na zo”

Hannunta ya kama suka fita waje,sai a lokacin Dr ɗin ya matso yana cewa “pretty ya jikin naki? Kin ga ki bar yawan damuwa shi ke jawo miki haɓo”

Kai na jinjina masa ina ɗan murmushi kafin na ce “na gode sosai” hira ya zauna yana yi mini wacce rabinta duk akan aikinsa ne,ya gabatar mini da kansa tun daga sunansa har manufar karɓar lambata a jiya da yayi.
Na dube shi na ce “wato wayo ka yi mini?”
“Ni na isa na yi miki wayo pretty? Kyawunki ne ya hana ni yin magana”

“Ni ai banda kyau” na furta ,ya ce “a'a bari faɗa don hakan babban zunubi ne,zo mu yi selfie” ya faɗa tare da ciro wayarsa ya ɗauke mu hoto,kafin kuma ya soma yin video yana cewa “yi murmushi mana prettyyy” ina shirin yin murmushin Ya Ubaid ya shigo sai na sunne kai ,murya a ɗan dake ya ce “ki sauko mu tafi”

“A'a da ka bar ta har zuwa an jima” Dr Abdul Hamid ɗin ya faɗa .

Ya ce “a'a yanzu za mu tafi” kallonsa na yi a raunace ,ni ma zan fi so na zauna a nan ɗin saboda na fara jin daɗin hirar Dr Abdul Hamid ko don ban taɓa yin saurayi ba ne oho.


“Sauko” Ya Ubaid ya furta tare da zuwa ya kamo hannuna,a dole na sauko na miƙe tsaye.Har muka fito farfajiyar asibitin bai saki hannuna ba,can na tsinkayo Ubaidah a tsaye tana waya.Hannuna na fizge tare da nufar a guje saura ƙiris na zame na faɗi,“ki bi a hankali” na ji muryarsa ya faɗa da ɗan ƙarfi amma ban juyowa ba na ƙarasa na rungume ta.

“ Hubby zan kira ka daga baya” ta furta tare da yanke kiran ta dube ni tana murmushi “ya jikin naki? Gida za mu wuce?”

Na ce “ni ma ban sani ba Ya Ubaid dai ya ce na fito ”
“Ok mu je” ta faɗa tana mai kamo hannuna,cikin tsokana na ce “wato sai ka ce wata ƙaramar yarinya har hannuna ake riƙewa”

“To mene ne banbancin? Ke ma baby ce dole a kula da ke” ta faɗa tana ƴar dariya,ban dai ce komai ba har muka isa kusa da motar Ya Ubaid ,Ammy muka tarar a zaune a gaba wannan yasa mu muka koma baya .

Sai da muka hau kan titi sosai sannan Ammy ta ce “da mun isa gida sai ki canza hijabinki Suby kawai mu wuce gidan makokin nan”

“Haba Ammy mene ne kuma na sai mun koma gida? A saya mata sabo kawai a hanya” Ya Ubaid ya faɗa.
Ammy ta ce “yanzu da safen ai ba kowa ya fito ba” bai ce komai ba sai gudu da ya ƙara,wani kantin kuwa ya tsaya da mu .Shi kaɗai ya shiga bai wani jima ba ya dawo mota tare da miƙo mini leda,na karɓa ina mai yi masa godiya sai na fiddo hijabin mai kyau kuwa launin green.A nan cikin motar na sauya shi,Udah ta ce “yayi matuƙar yi miki kyau kuwa” sai ta yi mini hoto Ni kuwa iya murmushi kawai nake zubawa ban ma san ta yi mini video ba saboda hankalina da ya ɗauku da idanun Ya Ubaid da ke kallona ta cikin madubi.Sunne kai na yi sai a lokacin kuma ya tambaye ni hanyar da za mu bi,dakyar na soma yi masa kwatance har muka iso gidan.Duk muka fito,a nan ƙofar gida suka yi wa Abba gaisuwa kafin mu shiga daga ciki.Mamu na a tsaye bakin murhu tana kaɗa kunu,duk cikin mutumci suka gaishe ta haɗi da yi mata gaisuwar,Ya Ubaid ya fita jin ana cewa a wuce can ƙurya matar malam na can.
Ni na kai su suka yi mata gaisuwa, sannan muka zauna.Muna nan irin kamar minti ashirin aka soma shigowa da kayan abinci .Mama Lantana wacce shigowarta kenan da dukkan alamu kuma ba ta lura da mu ba ta ce “wane ne wannan mai motar ? Manu dai bai da ita ballantana na ce shi ne ”

Hassana ta ce “bari na tafi wallahi sai na ga ko wane ne,maduban motar duk baƙaƙe ne zan bari sai ya fito”

Ni dai kallonsu kawai nake yi,ita Hassana ta fita yayin da ita kuma ta ida ƙarasowa tana ɗingishi.Kan tabarma ta sube tana cewa “matar malam ana zaman makokin shi ne kika runtuma wannan uban turare mai ƙanshi haka?”


“A'a Hajiya ce ta zo surukarmu” matar malam ta bata amsa,sai a lokacin kawai ta juyo inda muke.Da farko yanayin fuskarta duk a cije amma da yake ta iya munafurci sai ta washe baki tana cewa “ina kwananku Hajiya ashe kun ji labari,Manu ya sanar da ku ko? To ya za a yi kawun yara lokaci yayi babu rabon ganin bikin auren Manu”

Ammy ta amsa da “dama haka ne kowa bai wuce lokacinsa Allah bai nufa za a yi da shi ba”

“To Allah yasa dai a yi bikin wannan ɗage-ɗage ai ba na lafiya ne sai kace babu alkhairi tun ana ɗagawa yanzu an soma yin mutuwa.Wai amaryar ce nan? Ja'ira wato ba za ki gaishe ni ba ko kin yi tunanin kakar Manu ce kishi ya rufe miki ido?”

Ubaidah ta yi ɗan murmushi tana cewa “ina kwana Mama ya kuma haƙuri?”

Mama Lantana ji ta yi kamar ta je ta shaƙe mata wuya saboda ta sanadin bugun da ta yi mata ne yanzu take ɗingishi.
“An godewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login