Showing 54001 words to 55823 words out of 55823 words
hukuncin kisa bayan an tabbatar shi ne kawai na yanke shawarar bin dare na gudu.Amma duk da haka bai ishi Dadda ba sai da ta jefe ni da baƙin tsafi ta haukata ni”
Na ce “don me yasa kika gudo kika bar ahalinki? Me yasa ba ki zauna ba ki sanar da su babu wata baiwa a duniyar nan da ta wuce maita? In ma ba ki son a sani ai sai ki ɓoye kayarki ”
Kai ta girgiza mini tana mai cewa “akwai wani garin magani da ake shaƙawa mutum a hanci muddin yana da ɗigon maita a jininsa to zai bayyana cikin ɓoyayyar siffarsa ne ya dinga tonawa kansa asiri”
Na ja dogon numfashi kafin na ce “shi kuma yaronki fa,kin yi tunanin halin da zai shiga bayan tafiyarki? Me yasa ba ki taho da shi ba?”
Wani murmushi ne wannan karon ya suɓuce mata bai bayyanar da tsantsar farin ciki da dukkan alamu tana mugun son ɗan nata.Ta ce “Ba fa yaro ne ƙarami ba,ko a lokacin da na bar masarauta ya haura talatin da ɗaya kawai dai a idona ne nake ganinsa ƙanƙane”
“Me sunansa?”
Kai ta girgiza cike da kunya tana mai cewa “a al'adarmu ba mu faɗar sunan ɗan fari, wannan yasa na yi masa laƙabi da Noor”
Samun kaina na yi ni ma da yin murmushin kafin na ce “me Noor ɗin ke nufi?”
“Haske!” ta bani amsa.
Na ce “zan so na gansa kuwa,da na ji daɗi sosai ni ma zan yi babban yaya” ina faɗar haka sai ta ɗan ƙara matsawa ta jawo kaina ta ɗora kan cinyarta,sai ta cire luluɓin kaina ta soma warware manyan kitson kaina tana mai cewa “wata rana za ki gansa ai ”
“Yaushe kenan?”
“Ranar da lokacin komawa ta can ya yi,ai zan tafi da ke ne ki ga yayanki in ya so sai Banah ya tsare miki daularki ”
Shiru duk muka yi,bayan ta gama warware kitson sai kuma ta ɗebo ruwa ta zuba yaɗo ta wanke mini dogon gashina sannan ta ƙara yi mini wani kitson mai kyau duk da ƙwaya biyu ne kacal amma ya yi kyau.Wunin ranar ne muka ƙara yin wata shaƙuwa ta musamman ni da Ummilo ta dinga bani labarin Yaya Noor lokacin da yana ƙarami da kuma abubuwan da yake so da waɗanda ke saurin saka shi fushi.
“Wane abinci ya fi so?” na samu bakina da tambaya.
“Gurasa da zuma,yana matuƙar son cin gurasa yana dangwala ta a cikin zuma” ta bani amsa tana murmushi.
Na ce “ni ma ina son zuma,kullum in na je farauta sai na je na nemo ta na sha”
“Wato yayanki kika ɗauko wajen son zaƙi.Bani labarinki,ina iyayenki suke?” Ummilo ta faɗa .
Wani iri na ji duk babu daɗi kafin na ce “dukkansu sun mutu,shi Abbana ban san shi ba ita kuwa Maa a ranar da na karɓi prophecy ɗina ta yi gushewa.Ina sonta sosai,ina jin kewarta a kodayaushe samunki ne ya maye mini gurbinta nake jinki tamkar ke ce ita” na ƙarashe faɗa hawaye na silalo mini masu zafi.Na ƙanƙame ƙafar Ummilo ita kuwa ta shiga shafar kaina haɗi da rarrashina kafin ta ce “ina matsafiyar tarihi sai yaushe za ta zo?”
“Ta ce na yi miki sannu da jiki ma tun jiya ”
“Ina amsawa,ina ne gidansu?”
“Ita ma ba ta da iyaye mahaifinta ya rasu,mahaifiyarta kuma an damƙe ta”
“Ayya ki ce ta dawo nan wurina sai mu zauna tare” Ummilo ta faɗa ,sam ban ji zan iya yi mata muso ba hakan yasa ba tare da na shawarci Banah ba na ƙara aika saƙon wasiƙar tsafi zuwa ga Deborah ba ta kuma ɓata lokaci ba ta zo har da ƙullin kayanta.A ɗakin Ummilo na yi mata masauki ,a ɗan wunin da muka yi a tare sai kuma muka ƙara ɗinkewa ni da ita muka manta mun taɓa samun saɓani.
Da dare muna zaune bayan mun gama cin abincin,Ummilo na ririga Mila da ke yin rigima ta ƙi yin bacci sai ta soma rera waƙa wacce ta saka mu duk nutsuwa.Ba da Yaren da muke magana ba ne,haka kuma ba Yaren tsafi ba ne wani yare ne can daban da ita kaɗai ta san ma'anarsa amma sosai na ji daɗin baitin.Babu jimawa Mila ta yi bacci sai ta shimfiɗe ta tana murmushi tare da cewa “a duk lokacin da Noor ya fitine ni da kuka wannan waƙar nake rera masa ko kuma in ina son saka shi bacci”
"Amma Ummilo da wane yare ne wannan?” na tambaya,Deborah da ke rubutu cikin littafin tarihi ta yi karaf ta bani amsa da “Yaran serena ne,yare ne da halittun ruwa ke yi ita kuma waƙar suna yinta ne domin janyo wani ruhi zuwa gare su domin aiwatar da abin da suke buri”
Ido na tsura mata ina kallonta ta hasken farin wata,kafin na ce “ ta ya aka yi kika sani?”
“Ta ya ba za ta sani ba,matsafiyar tarihi ce fa” Ummilo ta faɗa .
Deborah ta yi murmushi tana mai cewa “tun jiya da na yi tozali da Ummilo na cika da mamakin me ya kawo Siren a nan”
Na ce “ai na lura da yanayin yadda kike kallonta,to sai da safenku zan je na kwanta” na faɗa tare da lalubo sandata na miƙe na shiga ciki.
Kan gadona na kwanta tare da yin shiru ina nazari,can sai ga Banah ya ratso rufin ɗaki ya shigo.Sam hakan bai kuma bani mamaki ba,illa kawai na mujiya da na zuba masa ina kallon yadda jikinsa ya ƙara rinewa kamar wanda ya fito daga cikin rijiyar kunama.
Gefen gadon ya zauna tare da miƙo mini wata ƴar kwalba ya ce “shafa mini” ba tare da na miƙe daga kwancen da nake yi ba na karɓa na soma shafa masa sannu a hankali tiririn dafin jikinsa ya soma disashe ganina.
★
Da dare bayan gama bikin baiko sai aka zauna kan teburin cin abinci.Yarima NASLAM ne da dakarunsa masu taya shi yaƙi,suna cin abinci suna raha yayin da shi kuma yayi shiru yana ta juya gurasar da aka ajiye a gabansa ya kasa ci.Jakariya Ali da ke gefensa ya ce “bari na nemo maka zuma in ba za ka iya ci da markaɗaɗen yaji ba”
Ya ɗago ya dube shi tare da yin murmushi kawai, Jakariya Ali ya fita zuwa madafa bai wani sha wahala ba don ya tarar da masu aikin kula da abinci ita ta miƙo masa zumar ya karɓa kafin ya zo ya kawowa yarima.
Cikin ƙarfin hali yarima Naslam ya karɓi zumar ya soma dangwala gurasar a ciki ya kai bakinsa,sai dai ko kaɗan bai ji wani ɗanɗano ba.Gudun kar ya ɓata wa kansa lokaci sai ya ture abincin, Jakariya Ali ya dube shi cike da mamaki yana shirin yin magana yariman ya miƙe ya nufi ƙofa sai a lokacin ne kuma Ali ya hango baƙin tambarin maita ya fito yau a bayan wuyan yarima Naslam.Cikin bugawar zuciya shi ma ya miƙe ya fita,bai zame ko ina ba sai gidan Barham.Kamar zai ɓalla ƙofa haka yake bugunta,Barham ya buɗe yana mai kallonsa da mamaki yake cewa “lafiya dai ko?”
Sai da ya shige ciki tare da rufe ƙofar sannan ya basa amsa da “ina fa lafiya yau baƙin tabon maita ya fito a wuyan yarima sam ya kasa cin abinci”
Barham ya saki kofin hannunsa yana mai kallon jakariya Ali cike da tashin hankali,kafin ya ce “tabo? Wane iri? Baƙi ko ja?”
“Na faɗa maka baƙi ne”
“Hakan na nufin bayan kambun baka yarima na ɗauke da ɗigon baƙar maita ?” Barham ya faɗa tare da zuwa ya ɗauko wani littafi sai dai duk bincikensa ya kasa samo gamsashiyar amsa ,tsabar firgici goshinsa har ɗigar da gumi yake.Ya ɗago ya dubi Jakariya Ali cike da rauni yana cewa “babu abin da na samu a binciken da na yi”
Ali ya ce “ya zama dole mu nemo mafita tun yau kafin gari ya waye ,saboda muddin aka kwana to Maitar za ta rinjaye shi ya fara sarrafa ta ”
Idon Barham suka kaɗa suka yi ja,ya rasa meke yi masa daɗi kafin can ya ce “yawwa ina matsafiyar tarihi da aka damƙe?”
“Tana can a kulle” ya basa amsa.
“Mu je ka kai ni can ita ce kawai za ta bamu mafita” Barham ya faɗa tare da ɗaukar wata takarda.Haka suka dugunzuma zuwa can inda ake ɓoye masu laifi,ko kaɗan babu wanda yayi gigin hana su shiga saboda duk wani dakare a ƙarƙashin ikon jakariya Ali yake shi ne shugaban dakaru gaba ɗaya.
Suna zuwa suka tarar da ita a zaune tana yin rubutu a ƙasa,ba tare da ta ɗago ba ta ce “me kuka zo yi? Kun zo tafiya da ni ne a kashe ni ?”
Sai suka kalli juna kafin Barham ya yi shahadar cewa “wane laƙani ne ake yin amfani da shi domin daƙile bujurowar baƙar maita tsafi wacce ke bibiyar jini?”
Ta ɗago da sauri ta dube su kafin ta ce,“ba zan taɓa faɗa ba ,kamar yadda yake son tozarta al'ummar Mayu da matsafa shi ma sai na bari ya tozarta a idon duniya kowa ya san wane ne shi”
Barham ya furta surkullen tsafi sai ga shi tsundum cikin ragar da take ciki,har ƙasa ya zube alamun roƙo kafin ya ce “kar ki dubi wannan ɓangaren,ki dubi matsayinki na babbar matsafiyar tarihi ki sanar da ni laƙanin”
Ta kawar da kai tana mai cewa “babu wani laƙani da zai daƙile maitar yariman masarauta ,sai dai a basa magani domin ɓoye ta.Daƙile ta duka kuma dole sai sarauniyar matsafa ce da kanta za ta iya yin haka”
“Bani na ɓoyewar” Barham ya faɗa ,ta juya masa baya tana mai cewa “yana can a kusa da duniyar ruwa,fure ne na floris mai matuƙar muhimmanci da zarar ka kai gare shi za ka ji ƙamshinsa na sanar da kai shi ne abin da ka zo nema“
Barham ya miƙe yana yi mata godiya,yana shirin tafiya ta ce “ban ƙare jawabi ba,masu tsaron furen nan fararen fatale ne da ba su aminta da irin tsafinka ba” Barham ya juyo cike da tsoro kafin kuma ya dubi Jakariya Ali ya ce “na gode”
Yana fitowa sai kuma suka fara shawarar ta yadda za a yi su fita daga cikin masarauta ba tare da kowa ya gani ba.Jakariya Ali ne ya je inda ake ajiye dokin yarima,kamar yana magana da mutum haka yayi masa bayanin komai kafin ya jawo shi ya fito.
Barham ne ya fara hawa don shi ne ya san hanya sannan shi Ali ɗin daga ƙarshe.Cikin amincin Allah suka fita daga masarautar zuwa inda aka shaida musu za su samu maganin,ana kawowa wurin kuwa ƙamshi ya buge musu hanci kafin su yi wani yunƙuri kuma fatale duk sun zagaye su shi kuwa Barham ganin mutuwa a maƙoshi tsautsayi yasa ya furta baƙin tsafi,sai kuwa aka damƙe su aka jefa ɓoyayyar duniya.
A can masarauta kuwa yarima Naslam ne kwance a ɗakinsa,har aka yi sallar asuba bai farka ba sai da hasken rana ya hudo ya daki tabon maita na wuyansa,wani irin kuka yayi da ya girgiza masarautar.Daidai nan free page ya ida,duk mai son shiga paid group zai biya kuɗin karatunsa 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank
DM +22795045822
*Daga yau discount yake idawa 13.April*
*NB:* Da zarar book ya kammala kuɗinsa 1k ne.
MRS SADAUKI