Showing 45001 words to 48000 words out of 53964 words

Chapter 16 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

754

mana baki, ko mu ?arasa ki" Ya yi mata tsawa.
Sai dai ba ma ta fahimtar abin da yake faWa, wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, jikinta ya din ga karkarwa. Gaba Waya hankalin Waliban ya tashi wasu suka fara kuka.
Dukansu suka fara yi, da kan bindigogi su na taka su da ?afa, tare da yi musu barazanar harbi, hakan ya tilasta musu jan bakinsu su yi shiru.
Jin Rahama ba ta da niyyar yin shiru, ya sanya Wayan sanya bakin bindiga ya buga mata a kanta, hakan ya sanya ta sulalewa a gurin.

*****
Ta na daga kwance a kan gadon Asibiti, duk ta rame ta yi zuru-zuru, cikin damuwa Ummi ta ri?o hannunta ta numfasa ta ce "Ru?ayya, haryanzu jikin naki? Yakamata a sallame mu zuwa gida"

"Tsoro nake ji ne" Ta yi maganar cikin rauni, tana fashewa da kuka.

"You are safe dear, gida zamu koma babu wanda zai biyo ki gida ya cutar da ke, in sha Allah. Ki nutsu ki kwantar da hankalinki ki yi ta addu'a.

"Ummi an tafi da Rahama fa. Kuma harbi suka harbe securitynmu" Ta yi maganar tsoro na bayyana a muryarta.

Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah za ta dawo cikin aminci." Ta yi maganar tana shafa kanta da sigar rarrashi.

*****

Safiyar Lahadi yana zaune a cikin Wakinsa, yana daddana wayarsa, ya ji alamar motsi a bakin ?ofa, ya Wan yi shiru yaga alamar motsi a gurin.
"Waye a nan?" Ya yi maganar yana kallon ?ofar, tare da zura hannunsa ?ar?ashin pillownsa.
?aga labulen ta yi ta shiga, ya yi saroro yana kallonta.
"Lafiya kuwa? Me ki ka zo yi Wakina da sassafiyar nan Alina, sai kin saka a zarge mu?" Ya yi maganar yana ?arewa kumburarriyar fuskarta ido. Allah ya wadata Alina da manyan idanuwa, sai dai sun rine sun yi jawur kamar an zuba mata kala.

Gani ya yi ta dur?usa a kan ?afafuwanta, ta haWa hannayenta biyu, hawaye na rige-rigen zubowa daga idanunta ta ja numfashi da kyar ta ce "Dan girman Allah, dan son da ka ke yi wa Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam, ka taimaka ka gaya mini ina ka kai mini Yaya? Ka san ba mu da kowa sai Allah sai shi, ban san yadda zan rayu babu shi ba, shi ne komai nawa. Dan Allah ka gaya mini inda yake, na kasa gaya wa kowa abin da ya faru, dan Allah dan Annabi ka dawo mana da shi, ka yi ha?uri dan ma wani laifin ya yi maka ka yafe masa dan Allah"

"Alina" Ya kira sunanta yana tsare ta da ido. Ta Waga kanta tana kallonsa.

"Sau nawa zan gaya miki cewar ni ba ni bane ba ki yarda? In Wauki yayanki na kai shi ina?"

"Wallahi kai ne, na ganka da idanuna, kai ne ba wani ba. Dan Allah Mamman ka taimake ni ka dawo da shi. Ba wanda zan gaya wa na ga abin da ya faru, dan Allah ka taimaka. A duniya bayan Allah da ma'aiki ba ni da kowa sai Yayana ka duba rayuwata da maraicina dan Allah"

Wani irin motsi ya din ga ji a ?asan zuciyarsa, ?wa?walwarsa ta shiga kai komo, lissafi na neman ?wace masa, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita ya ce "Zo ki tafi, zan fita"

Jiki a sanyaye ta taso, ta sake nufarsa, amma ya murtuke fuska ya ce "Ki fita ki bani guri" Ta girgiza masa kai tana haWa hannayenta tana kuka, ya kawar da kansa daga kallonta yana nuna mata hanyar fita. Wani irin tsoro ya mamaye ta, ta fita tana jan ?afarta a hankali tana kuka mai sauti.

*****

Yanayin fuskar Laila ne Wauke da damuwa, da alama ta sha kuka ne sosai da sosai.
Cikin yanayinta na nutsuwa ta fara da sallama, kamar yadda ta saba a dukkanin videos Win ta.

"Na ga alamar posting Wina na ?arshe a kan mr. President, bai yi wa da yawan mutane daWi ba. Na ci zagi da ni da iyayena, da masu ce mini karuwa, da masu cewa kuWi ake ba ni, nake kare gwamanti. Ni babu wanda ya bani kuWi na kare gwamanati, hasali ma ba a san da zamana ba.
Son da nake yi wa shugaban ?asa ya faro ne, silar sunansa Waya mahaifina marigayi DSP Faruk Kankiya. Wanda ya rasa rayuwarsa shekarun baya, bayan artabunsa da 'yan fashi, wanda wani case ne daban. Tun Mr. President yana ri?e mu?ami a matakin jiha nake son sa, Saboda son da nake yi wa mahaifina aka kashe shi, kuma 'yan fashin da ya kama aka sake su.
Har Mr. President ya zama shugaban ?asa, ina bibiyar lamarin siyasar sa, ina son shi, yana burge ni, kuma halayensa sun yi kama da mahaifina a wasu Sangarorin.
Ba zan iya daina son sa da ba shi goyon baya ba, son zuciya Wabi'ar zuciya ce, ba zan iya kushe shi dan na faranta muku ba. A ?arshe ina baku ha?urin, duk wanda baya son abin da nake yi ya yi ha?uri, ya daina following Wina, ro?ona Waya ku daina zagin Abbana dan baya raye. Mr. President kuma har abada bana fatan ko shi ko mu?arabbansa, wani ya maganta mini sisinsa ba na bu?ata. Shugaba ne da nake wa kallon Uba, zan yi masa addu'a Allah ya yi ri?o da hannayensa kuma zan ci gaba da goyon bayansa Wari bisa Wari".

Mama na wanke-wanke a tsakar gida, ta ji ana ta ?wala sallama a ?ofar gida.

"Waye?" Ta yi maganar tana kallon hanyar soro.

"Bala ne"

"Shigo" Ta amsa tana Wauraye plate Win hannunta.

Ya shigo yana sake sallama ta amsa masa tana faWin "Dama kai ne ka ma?ale a waje ka na kwaWa sallama?"

"Wallahi kuwa, mutuniyar fa?"

"Ta je karSo caji"

Ya zauna a kan tabarmar da ke shimfiWe, ya ce "Bari na jira ta"

Su na cikin hira, Laila ta dawo, tana ganinsa ta yi murmushi ta ce "Balansy"

Ya Wan tsuke fuska ya ce "Dalla zauna, mai abin haushi" Ta tsuke fuska ta ce "Me na yi?"

"Videon da ki ka wallafa Wazu mana, uban wa ya aike ki? Ina ruwanki da wasu masu Comment da zagi, ko dai ki rama zagin ko ki ?yale su"

Ta sake Sata fuska ta ce "Ni ba zan zama 'yar balaja'u na din ga zage-zage ba"

Bala ya ce "Ina ruwanki da wani balaja'au in dai za ki samu kuWaWenki? Next week akwai yiwuwar dollar ta ?ara tashi, sai ki cire kuWinki"

Ta yi murmushi ta ce "Kai ka ce ina cikin alkhairi, nawa zan samu?"

"Kusan dubu Wari da hamsin a ?iyasi, sai dai yadda ta kaya. Ke ba wannan ba, na ji wai-wai, shugaban ?asa zai zo garin nan, jajen abin da ya faru na Satan matan nan, idan hakan ta tabatta dole ki halarci gurin nan, duk yadda za mu yi, ko hoto ki yi da shi"

Ta waro ido ta ce "Dan Allah? Ni ba sai na yi hoto da shi ba, ko ganinsa kawai na yi"

Mama da ke kitchen ta ce "Bala me ka ke ?ulla mata, ba dai wata tsiyar za ka saka ta kuma aikatawa ba ko? Kun yi ?ulle-?ullen da sai da ta rasa aikinta, yanzu kana kitsa mata wani abin, ni dai kar ku janyo abin da za a zo har gida a same mu, mu shiga uku ina lallaSa rayuwata"

Bala ya ce "Hajiya Mama ba za ki gane ba, idan Allah ya Waga likkafar Laila, sai kin manta duk wata wahala fa, za ki sarara"

Sadam ya fito daga Wakinsa, fuskarsa duk alamun bacci ya ce "Ma?aryaci, wace likkafa kullum cikin wahala ku ke, ba kwa samun ko sisi, sai ma kuka da ba?in ciki da take kwasa"

Bala ya ce "To ina ruwanka? Duk ranar da Allah ya sanya ta fashe mana, muka sha kwana zaka sha mamaki. Mu na nan? zamu fara wallafa ayyukanmu a jaridarmu mai zaman kanta ta online".

Saddam ya yi tsaki ya ce "Jaridar bugaggu ba"

Bala ya ce "Laila, kar gwiwar ki ta yi sanyi, za mu ba su mamaki da yardar Allah"

Ta yi murmushi ta ce "Ba zan gajiya ba, ba kuma zan sare ba in sha Allah"

*****
Can a daji kuwa, Rahama tana yashe a ?asa, su maharan ba su bari an taSa ta ba, kuma ba su taSa ta ba.
?aya ne daga cikinsu ya saka ?afarsa yana taka tata. A hankali ta motsa, ta buWe idanunta da suka yi mat nauyi, sai dai ta ji kanta kamar ba nata ba. Ga shi ba ta gani sosai sai dishi-dishi. Ya yin da ?afar da maciji ya sare ta, take jin ta tamkar ba a jikinta take yi ba. Ga jikinta sanyi ?alau.
Ganin ta motsa ya sanya ya dur?usa a kanta yana kallonta. Ta kalle shi da kyar, amma ta kasa motsi. Ya yi wani irin murmushi yana lashe laSSansa, ya mi?a hannunsa jikinta yana faWin "Ashe dai da sauranki ba ki yi mushe ba?" Ya yi maganar yana neman Wage mata riga a gaban mutane. Tafasar da zuciyarta ke yi, ya bata wani irin ?warin gwiwa da niyyar ta hankaWe shi, amma tana Waga hannunta ya koma ya faWi.

"A'a Halliru, kar ka yi wa yarinyar nan wani abu, kar Sadauki ya zo ya yi mana hauka"

"Shhh" Ya yi maganar yana kallon Salisu, da fuskarsa ke bayyanar da tsoro.

"Ba zai yiwu a bawa kura ajiyar nama a hana ta WanWanawa ba" Ya yi maganar yana Wago Rahama, yana kallonta cikin murmushi.
"Kai ba fa zai yiwu ba, idan na gama sai mu ?arasa ta, mu ce saran macijin ne ya kashe ta kawai"? Ya yi maganar idanunsa na yin ja, jikinsa na rawa, saboda sosai yake ?arewa jikinta kallo, mussaman da kullum cikin takurewa take.

Ayshercool
08081012143

Mun kusa Kammala free pages.
1k ne a telegram via 0069685771
Aisha Adam stanbic
Sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira sai an kammala 1500 za su biya.




SARA DA SASSA?A
YOTA 002
AYSHERCOOL

Page 14

Cikin sauri Sabi'u ya saki Rahama ya tashi, saboda jin ?arar babur a bayansu, ba tare da jin sautin tahowarsa ba.

Ya sauka daga kan babur Win, sauran 'yan bindigar suka nufo shi, su na yi masa barka da zuwa, ya mi?a musu bindigarsa suka karSa.
Ya ?arasa inda Ramata ke yashe kamar abin banza, ya saka hannunsa ya Wago ta zaune. Ya kalli leSenta ya bushe, jikinta sanyi ?alau. Sai motsa hannunta take yi, tana ?o?arin kare jikinta.
Ya dubi Waya daga wanda suka zo tare, ya ce "Ba ni abin nan" Ya ?araso ya mi?a masa wata 'yar ?aramar kwalba. Ya kwance ta ya Waga bakin Rahama ya zuba mata abin da yake cikin kwalbar. Mintuna kaWan ya Waga ta zaune, aikuwa ta fara she?o amai babu ?a??autawa, ta galabaita sosai, sai da ya fuskanci ta gama sannan ya ja ta ya jinginar da ita a jikin bishiya. Sai haki take yi tana sauke numfashi.
"Kina jikar makiyaya, ya aka yi ba ki sha maganin dafin maciji ba?" Ta yi shiru tana bin sa da kallo a galabaice.
Ya kalli inda ?afar da macijin ya sare ta, ya fara kumbura. Ya ciro wata aska ya tsaga gurin, ya tsare ta da idanunsa, da idan ta kalli idon nan nasa da ya sha farin kwalli sai tsoro ya kama ta. Ya dur?usa ya kafa bakinsa a dai-dai gurin. Ji ta yi tamkar yana fizgar wani abu a cikin jikinta. Wani irin wahalallen kuka ta din ga yi jikinta na karkarwa, tamkar za ta shiWe. Ya Wago ya buWe kwalbar da ya bata magani a ciki, ya zuba abin da yake cikin bakinsa. Abun ba?i ?irin babu kyawun gani.
Ya dube ta ya ce "Ki yi ha?uri, in sha Allah macijin zai kawo kansa, za ki ga hukuncin da zan yanke masa. Ya yi maganar yana goge mata gumin da ya tsatstsafo a goshinta. Ya ciro hiramin da yake rufe fuskarsa da shi, ya yagi wani sashi a jiki, ya kama ?afar saman gurin da ya cije ta ya Waure.

Ya sa aka kawo masa ruwa, ya ba ta ta sha, ta rage tana daga zaune ta yi alwala, ta yi sallar asuba a haka a yadda take zaune.

Yana tsugune a gefenta, ta idar aka ba ta waina a cikin leda fal da ?uli-?uli, ta ri?e wainar a hannunta, ta Waga kai tana kallon sauran 'yan uwanta da suke tsare tare, sannan ta kalli Sadauki.

"Nasu abincin yana hanya, idan ba ki ci naki ba, maganin da ki ka sha zai iya halaka ki"

Hannunta na rawa, ta gutsiri wainar, sai dai ta ri?e a hannunta, tana sinne kai ta kasa ci. Ya yi murmushi ya matsa gefe ya kawar da kansa daga kallonta, sannu a hankali ta fara kai wa bakinta tana ci, tamkar tana cin magani.

Sadauki ya Wan waiwaya ya ce "Sabi'u zo ka karSi kwalbar nan, ka ajiye mini zan yi aikinta na kama macijin nan" Ya yi maganar yana mi?a masa kwalbar da hannu Waya, hannunsa Waya kuma ya zura a cikin Aljihunsa.
Sabi'u ya ?araso ya kawo hannu zai karSi kwalbar. Sadauki ya janye kwalbar, Sabi'u ya sake ?arasawa zai karSa, amma Sadauki ya fito da Waya hannun nasa ri?e da bindiga ?irar pistol ya harbe shi har lahira. A take da yawa daga cikin Waliban suka saka ihu cike da tsoro. Jikin Rahama kuma ya hau rawa ta kasa ko ?wa?w?waran motsi saboda jinin sai dai ya Sata mata fuska. Idanunta da suka yo waje suka ?ara bayyanar da tashin hankalin da ta shiga. Sadauki ya Wan tsura mata ido, ganin yadda numfashinta ke kai komo a ?irjinta.
Ya sake ciro hiraminsa ya kamo fuskarta, ya fara goge mata jinin yana faWin "Yi ha?uri na tsorata ki ko? Ya aka yi jinin makiyaya ta kasance cikin matsorata ne? Mu fa ba matsarota bane ba a sammunda tsoro ba" Ya yi maganar yana ci gaba da goge mata fuskarta.
Ya sakar mata murmushi ya ce "Kar ki yi mini mummunar fahimta fa, ni mutumin kirki ne" Ita kuwa ba ma ta gama iya tantance a wani yanayin take ciki ba, balle ta fahimci me yake faWa. Sai da ya gama goge mata jinin sannan ya mi?e tsaye, ya murtuke fuska tamkar bai taSa dariya ba ya ce "Wannan shi ne abin da zai biyo bayan duk wani wanda ya yi yin?urin aikata halin Wan taure a tsakanin yaran nan. Kai Gulafa, ku je ku binne shi, kai kuma je ku ?arasa aikin da na saka ku ku yi mini, saboda zan din ga zagayowa ba tare da na sanar muku ba.
Ya kalli sauran 'yan matan ya ce "Ku kuma ku kwantar da hankalinku, na gaya muku babu wanda za mu cutar" Ya saka hannunsa ya cire babbar rigar yadin da take jikinsa, ya dur?usa ya saka wa Rahama da har a lokacin jikinta bai daina rawa ba. Ba ta iya motsawa ba har ya gama saka mata, shi ma kuma bai sake ce mata komai ba. Ya nufi baburinsa ya hau, suka mi?a masa bindigarsa ya karSa ya tafi.

*****

Laila ce a zaune, ta du?ufa a kan wayarta, hannunta Waya ri?e da biro da takarda tana rubuce-rubuce.
Mama ta shigo Wakin ta tsaya a kanta ta dube ta cike da takaici ta ce "Wai Laila uban me ki ke yi ne a kan wayar nan?"

Laila ta yi mi?a ta ce "Mama aiki nake yi"

"Aikin banza ba, awa ashirin da huWu, kullum idonki a kan waya, ina jin wani likita na magana a radio, ya ce ba da jimawa ba idanun matasan yanzu duk zai mutu, saboda azabar kallon waya."

Laila ta Wan yamutsa fuska ta ce "Bincike nake yi ne, neman kuWi nake yi da wayar nan Mama, dan Allah ki bani dubu Waya zan je wata unguwa ne"

Mama ta dube ta she?e?e ta ce "Shegiyar wayar taki da ki ke wuni a kanta, ki ke neman kuWin da ita, ba ta kawo miki dubu Wayar da zaki yi yawon ba"

Laila ta yi murmushi ta ce "Hajiya Mama kenan, bari na yi wanka na je Cafe Win su Saddam, na san ko ya gama yi mini gori zai bani"

"Tsaya tukuna ma ina za ki je?"

Laila ta hau murmushi ta ce "Ba daWewa zan yi ba, zuwa zan yi na dawo"

"Tambayarki na yi, ina za ki je?"

Laila ta ci gaba da murmushi ta ce "Mamansy, kin san ba zan je inda zan Waukko miki magana ba"

"To wallahi idan ba ki gaya mini ba, ba za ki fita ba"

Ta Wan sunkuyar da kanta, jiki a sanyaye ta ce "Mama zan koma batun filinmu ne, ina ci gaba da bibiya, idan ba za su yi mana adalci ba, akwai yiwuwar na wallafa rubutu a kan lamarin"

Mama ta nemi guri ta zauna ta? dube ta ta ce "Laila, na san an cutar da ku. Wannan filin shi ne abin da muka tsira da shi da wannan gidan, tun da an yi ?arfa-?arfa a kan filin nan ki yi ha?uri kawai. Tun da mun tsira da gidan nan shikenan. Kin ga Wan uwanki da na ba shi baki ya ha?ura, to kema ki bar wa Allah kawai"

Laila ta sunkuyar da kanta, sannan ta Wago kanta idonta duk hawaye ta ce "Mama shikaWai fa muka tsira da shi, kina gani hakkin babanmu abokansa suka ci abin da suka ga dama, suka bamu wanda suka ga dama. Kuma filin da aka saya mana tsawon lokaci, mu na saka ran mu na da kadara mai tsada a ajiye, rana tsaka gwamnati ta ?wace an bamu diyyar da bata kai rabin kuWin kadararmu ba. Kuma an saya mana wani filin shi ma wasu su mallake su ce nasu ne, mu zuba ido"

"Laila ya za mu yi tun da sun fi ?arfinmu? Da aka ?wace filayen mun daina rayuwa ne? Muka rasa mahaifinku ma balle wani fili, mu bar wa Allah kawai. Albarkar Annabi Sallallahu alaihi Wasallam da Alqur'ani filaye idan mu na raye sai dai ku bawa wani kyautar su ma, mu bar wa Allah kawai"
Ba haka Laila ta so ba, amma gudun Waga wa Mama hankali, ya sanya ta jinjina kai ta nuna mata cewar komai ya wuce.

*****

?angaren Alina, abubuwa sun ?ara rikice mata, yadda ta kai ba ta iya sarrafa kanta sosai. Hankalin Nadiya ya tashi sosai, dan Alina ta kwanta rashin lafiya, saboda damuwa wannan ciwon kan ya tayar mata. Ga shi a duk lokacin da ta yi yin?urin gaya wa Nadiya abin da ya faru, sai ta ji ba za ta iya ba, gani take yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login