Showing 27001 words to 30000 words out of 53964 words

Chapter 10 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

757

Isma'il a tsaye kamar bayyanar aljan.

A tsorace ya ce "Lafiya kuwa?" Ya yi maganar yana kallon Isma'il.

"Ba lafiya ba, gurinka na zo"

Ya ajiye butar hannunsa, ya ce "Allah ya sanya ba laifi na yi ba"

Ismail ya ce "Na je gurin mutumin da aka ce ka yi karatu a hannunsa,? ya tabattar mini da kai Walibinsa ne, sai dai Haryanzu ni ban ji na yarda da kai ba. Amma na san komai girman gona akwai kunyar ?arshe. Na fuskanci amfani da ?arfi gurin raba ka da kanwata, zai iya zama cutarwa a gare ta, ka yi amfani da yaudara ka sanya kusanci tsakaninka da ita. Kuskure mafi girma da za ka yi shi ne fara soyayya da Alina, na kuma fuskanci idan ban yi da gaske ba abin da zai faru kenan. Ka sani akwai layin da idan ka ?etara a kan Alina zan iya sadaukar da rayuwata na yi zaman prison na har abada saboda ita"

Mamman ya kalli Ismail ya yi murmushi ya ce "Ban san dalilin da ya sanya ka tsane ni har haka ba. Ni da Alina zaren ba kalar yadin bane ba, kawai mutumtaka ce a tsakaninmu. A Sangarena na yi maka al?awarin, kare martabar Alina, ba zan faWa soyayya da ita ba, sai dai ban yi maka al?awarin hana ta sona ba" Wani mugun kallo Ismail ya yi masa ta hasken fitilar solar gurin, ya yi ?wafa ya juya ya bar gurin.

Gari ya fara haske, Ismail ya yi sallama a ?ofar Wakin Alina, ta amsa masa murya ?asa-?asa. Ya Waga labule ya shiga. Ta tashi zaune daga kwancen da take, ya zauna a gefen katifarta yana kallonta.

"Alina fushi ki ke da ni, ko gaisuwa ko?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a zan gaishe ka, tsoro nake ji, kar na je wani laifin na sake yi ne"

Ya Wan jinjina kai, tare da kaWa ?afafuwansa da ya mi?e, ya ce "?anwata, na san maybe kin yi fushi da Yaya, amma duk abin da Yaya yake yi, ?o?ari yake bawa halittu mafi soyuwa a gare shi kariya, wato Fatima da Nadiya, a duniya yanzu ba ni da kamar ku, gurin baku kariya daga duk abin cutarwa, sai inda ?arfina ya ?are.
Ke yarinya ce Alina, haryanzu ba kya banbance mene ne daidai da akasin haka, kuma kina kan shekaru mafiya hatsari na ruWin ?uruciya, zuciyarki a buWe take, duk abin da ya yi mata daWi, ko ya burge ta, karSa za ta yi. Shiyasa nake taka tsantsan gurin tantance miki aya da tsakuwa. Ni gaba Waya mutumin nan bai yi mini ba, yana da sifofin munafukai marasa gaskiya. Amma ba na son Sata miki rai shiyasa nake ta saka muku ido. Ki yi ha?uri faWan da na yi miki, amma ki yi a hankali kar ki kawo mana abin da zai kawo mana barazana ga kwanciyar hankalinmu."
Har ya yi magana ya gama, Alina ba ta ce uffan ba, ya tashi ya fita.
Gaba Waya jikinta ya yi sanyi, ba ta son abin da za ta Sata wa yayanta rai, amma gefe guda sun sha?u da Mamman, rana tsaka ta daina kula shi ba ta kyauta ba. Ga shi gaba Waya cikin abin da bai fi wata Waya da satuttuka ba, suka yi wannan sha?uwar.

*****
Ru?ayya ce ta ?ura wa Rahama ido, yadda take ta juya abu a kofi ta kasa sha.
"Rahama ya ne? Me yake damunki ne?"

Ta Wago ido ta kalli Rukayya, ta sunkuyar da kanta.

"Ke kalle ni, mene ne?"

Ta girgiza kai alamar, babu komai.

"A'a da komai, mene ne?"

"Baffa bai zo ba, bai kuma kira kowa ba a gaya mini dalilin rashin zuwan nasa, a tsorace nake" Ta ?arasa maganar hawaye na cika mata ido.

Ru?ayya ta ce "Haba Rahama, wata?ila wani abin ne ya hana shi zuwa, amma da yardar Allah zai zo"

Rahama ta Wan rausayar da kai ta ce "Duk da ?aunar makaranta da nake yi, a duk lokacin da na taho, hankalina a tashe yake. Saboda rashin sanin abin da yake faruwa a garinmu. Garinmu babu cikakken zaman lafiya da kwanciyar hankali".

Rukayya ta dafa kafaWarta ta ce "Babu abin da yake faruwa sai alkhairi. Share hawayenki ki gama ci, ki zo mu je Clinic akwai marasa lafiya" Ta jinjina kai ta kammala abin da take yi suka bar Hostel Win.

A clinic Win suka tarar da wata Waliba da ?ofa ta ji wa rauni, zai yi mata Winki. Yana ganin Rahama ya hau murmushi ya ce "Ai yanzu nake saka ran na aika a nemo mini ke, na ga yau ban ganki ba"

Ru?ayya ta ce "Yaushe za ka ganta, tana can tana shagwaSa, wai Baffa bai zo mata visiting ba, tun da yan gidanmu da suka zo mata dodanni ne"

Ya Wan yi dariya ya ce "Ai ba a shiga tsakaninku, ina ga idan ki ka yi Candy sai kin jira Rahama"

"Wannan dole ne" Ta yi maganar tana dariya ta wuce Wakunan da ake ajiye Walibai idan ba su da lafiya"

Rahama kuma a gefen Likitan ta zauna, tana ci gaba da yi masa tambayoyi kamar yadda ta saba.

*****

Misalin ?arfe biyu da rabi na dare, yana tsaye a jikin tagar Wakinsa, yana shan sigari, ya sha ta kai uku. Sannan ya dawo ya canza kayan jikinsa, zuwa shirt da dogon wando, ya samu wani mayafi, ya rufe fuskarsa, ya Waga ?asan fulonsa, ya Wauki abun da zai Wauka, ya Wau ?aramar wayarsa, da wata wallet, ya rufe Wakin ya fita.

Da safe Ismail na kallon Alina nata rawar jikin kai wa Mamman Abincin safe, wanda da wani abin ne ya nuna baya so, da tuni ta bar abin, amma nasihar da ya yi mata ba ta shige ta, dan bai ga alamar za ta ja baya da hulWa da mutumin nan ba. Shi dai fargabarsa Waya kar Alina ta faWa soyayya a shekarun ?uruciya, mussaman da mutum irin wannan da haryanzu ya kasa nutsuwa da shi.
Ba ta fi mintuna uku da fita ba ta dawo, tana faWin "Antynmu ga Abincin Mamman, baya nan ko ina ya tafi da sassafen nan, idan ya dawo ya ?wan?wasa miki ya karSa, ko ki aika masa idan Wan malam ya zo karSar nasa" Ta ?arasa maganar tana Waukar jakarta.

"Yayanmu na tafi" Ya Waga kai ya kalle ta, ya yi shiru bai amsa ba.

Ta Wan tsaya cak tana kallonsa, ta sake cewa "Yaya na tafi"

"Sai kin dawo" Ya furta a ta?aice, jiki a sanyaye, Alina ta fita. Sai ta ji gaba Waya duniyar ta yi mata babu daWi, ganin fushi da damuwa ?arara a fuskar Yayanta.

*****
Rahama na zaune a class Win su, kasancewar lokacin prep ne, tana zaune tana karanta wani littafi, da yake ?unshe da yadda turawan mulkin mallaka suka mamayi Afrika, da sace musu wasu daga kayan tarihinsu, da kuma mallke musu kadarorinsu. Kawai ta din ga jin zafin abubuwan da suka gudanaz saboda yadda ta yi zurfi a karatun gani take kamar a gabanta abin ya faru.
"A Yelwa" da sauri ta Waga kai.

Prefect Win da ta kira sunanta ta ce "Ki je ofishin pc ana neman ki"

"Tom"
Ta amsa tana tattare litattafanta tana zuba wa a cikin jakarta, ta yin?ura ta tashi ta fita. Hannunta na cikin hijjabinta tana tafiya a hankali.
Muryar Baffa ta jiyo, su na magana da principal Win su. Da sauri ta ?arasa cikin ofishin. Murmushinta ya gaza Soyuwa. Ta gaisa da Principal sannan Baffa ya fito suka keSe.

"Baffa na zata ba za ka zo ba, hankalina a tashe na fara tunanin ko wani abin ne ya faru a gida"

Jikin Baffa a sanyaye ya girgiza kai ya ce "Babu abin da ya faru, sai dai tsoron faruwar tasa ne ya sanya na kasa zuwa ko ina."

Rahama cikin kaWuwa ta ce "Baffa mene ne?"

"Ramata dama akwai wata ala?a a tsakanin ki da yaran manoma ban sani ba?"

Ras gaban Ramata ya faWi, ta hau tambayar kanta, ya aka yi Baffa ya sani, duk Soye-Soyen da take yi.
"Kin yi shiru Ramata, ke yanzu ba kya duba mana halin da muke ciki ko? Sai kin janyo ke kaWai Win da ki ka rage mini, kema na rasa ki ko wata fitinar ta tashi ko?"

Ramata ta yi ajiyar zuciya, ta gyara zamanta ta Wan kalli Baffa ta sunkuyar da kai ta ce "Baffa abin da ka faWa ba ?arya ba ne, Bukar ya daWe yana bibiyata tun ?awancen da nake yi da Hanne. Sai dai na saki jiki na ba shi dama ne, ba domin komai ba, sai dan na san wacece wadda ake zargin Ironmu a kanta, na tattara hujjar da zan bi hakkinsa" Ta ?arasa maganar tana kallon Baffa.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ramata yaushe ki ka koyi ba?in taurin kai haka? Ni da nake ubansa na ha?ura na fauwwala wa Allah, ke da ba ke ki ka haifar mini shi ba, ki dage sai kin Wauki mataki, a gurin wa za ki Wauki matakin? Ramata kar ki Sata mini rai , ki yi abin da za ki janyo mana tashin hankali, ba zan iya kirga iya tashin hankali da barazanar da na gani a rayuwata a zamana a garin nan ba, yakamata na huta haka"

Rahama ta yi shiru tana goge hawaye, saboda yadda komai yake dawo mata tun daga cikin kwanyarta har zuwa cikin idanunta. Baffa ya koma yi mata nasiha, ya bata abin da ya ri?o mata ya tashi ya tafi.
Gudun kar hankalin malamansu ya dawo kanta, a zo ana tambayarta lafiya, ko su zata kukan tafiyar Baffa take yi, su yi mata faWa, dan haka ta goge hawayenta ta tashi ta tafi. Sai dai da aka tashi daga prep, ta kai kayan kwanarsu ta ajiye, ta tafi keSanttacen guri ta zauna tana tunani.
Tabbas tana son bin jinin Wan uwanta, amma ta fuskanci yanayin shari'a a ?asar nan ka na bu?atar ilimi, kuWi da kuma hanya, idan ba haka ba wahalar banza za ka yi ta sha, idan ba Allah ya tarfawa garinka nono ba. Mussaman ita da ga ?arancin shekaru kuma ba ta da tabbacin samun cikakken haWin kan mutanen garin, kowa cewa zai yi babu ruwansa saboda tsoron manoma da ake ji a garin.

*****

Yana ri?e da leda a hannunsa, yana ?o?arin shiga layin, ya ga daidaita sahu na ?o?arin fitowa, da Alina a ciki a kwance a jikin Nadiya. Da sauri ya tare a daidaita sahun ya ri?e ?arfen yana kallon Nadiya ya ce "Lafiya kuwa?"

Nadiya ta ce "Alina ce babu lafiya za mu je Asibiti"

A Wan rikice ya ce "Subhanallah, Asibiti kuma meya same ta"

Cikin basarwa Nadiya ta ce "Tana da ciwon kai mai tsanani ne, mai Napep mu je, kar ta ci gaba da galabaita" Mai baburin ya ja suka tafi. Mamman ya tsaya yana bin adaidaita sahun da kallo, da tunanin ina yayanta za su tafi Asibiti sukaWai? Kuma kwanaki uku kan ya yi balaguron da ya yi, lafiyarta ?alau.

Wayarsa ya Waukko mai madannai, ya daddana, sannan ya ?arasa shagonsa ya shiga.

Ya gama abin da zai yi ya fito ya zauna a bakin hanya, ko zai ga dawowarsu, amma bai gani ba, dan ya yi mamaki a yadda yake da Alina, babu yadda za a yi ya yi magana ba ta Wago ba.

Wata ma?wabciyarsu, da take jikin gidansu Alina, ya gani ta fito daga layin, ta ri?o kwando da kwanukan Abinci. Ya tashi ya ?arasa, suka gaisa. Ya ce "Dan Allah Asibiti za ki jegurin su Alina?"

Ta ce "Eh zan kai musu Abinci ne"

Cikin damuwa ya ce "Subhanallah, wane Asibitin ne?"

"Bright ne, a can suke kwanciya idan ba su da lafiya"

"Dan Allah kar ki ce na dame ki, dama tana yawan rashin lafiya ne?"

Maman Hanan ta ce "Gaskiya dai dan kwana biyu ma Alina ta yi lafiya, amma tana da yawan rashin lafiya"

Ya jinjina kai ya ce "Shikenan na gode sosai"

Alina na kwance a kan gadon Asibiti, Idanunta a lumshe, Wakin an kashe fitila, saboda ba ta son haske, idan ciwon kan ya tayar mata.

"'Yar ?walisa"? Ya kira ta a hankali.

A hankali ta motsa ta buWe idanunta a saboda hasken fitilarsa da ya haske mata fuska. Sai dai idonta ya yi ja sosai.

"Sannu" Ya furta yana ?asa da muryarsa. Ta mayar da idanunta ta lumshe, ta ce "Ina ka tafi babu sallama, nake ta neman ka?" Ta yi maganar cike da kasala da rashin ?warin jiki.

"Na je gida ne, kin san Innata ba ta da cikakkiyar lafiya ita ma."

Ta jinjina masa kai kawai.

Cikin tausasawa ya ce "Me yake yi miki ciwo ne?" Ta Waga hannunta a hankali, ta nuna masa kanta. Kawai ta ga ya saka hannu yana share mata gumin da yake tsatstsafowa a goshinta. Ta buWe idanunta tana kallon fuskarsa ta hasken fitilar wayarsa. Ji ta yi zuciyarta ta fara bugawa da sauri da sauri, har numfashinta ya fara fita da sauri.
Idanunsa da suke ba ta tsoro ya tsare ta da su. Ga kusancin da yake tsakaninsu, wani irin ?amshi jikinsa yake fitarwa mai kwantar da hankali. Hakan ya ?ara sanya mata kasala da wasi-wasi.

"Yaya Mamman" Bai amsa ba sai kallonta da yake yi.

"?amshin turare ka ke da ?aurin wani abu, kamar... Sai kuma ta yi shiru."

Ya Wan ja dogon hancinsa, ya basar, ya ce "Tashi zaune ki ci abin da na kawo miki" Kafin ta yin?ura ya riga ta ya Waga ta zaune.

"Wayyo Allah kaina, ka yi mini a hankali mana, zai rabe biyu" Ta yi maganar muryarta na rawa.

Ya jinginar da ita, sai dai gaba Waya a tsorace take, idan ban da Yaya babu wani namiji da ya taSa gangancin kai hannunsa jikinta, ko da kuwa samun kusanci da ita ne. Bayan rashin ?warin jiki da take fama, wani irin yanayi take ji a jikinta da ya ?ara kashe mata jiki fiye da da.

Ya janyo ledar da ya zo da ita, ya fito da yoghurt, ya fito da fruit, ya ce "Wanne za ki ci?" Tsura masa ido ta yi, tana tsoron kar wani ya shigo ya gan su a haka, saboda yadda yake zaune daf da ita, gaba Waya a tsorace take. Ta zuba wa wuyansa ido, idan ba gizo idanunta suke yi mata ba, sar?a ce a wuyansa, sai dai ba ta fitowa sosai, tana cikin rigarsa, tana son ta yi magana amma ta kasa.
Ya ci gaba da bin ta da kallo, da mamakin abun da yake gani a tare da ita.
Ya buWe robar yoghurt Win ya ce "Na baki a baki ne?" Ya yi maganar yana kallon ta. LaSSansa take kallo a hankali, kamar yau an canzo shi gaba Waya. Idan su na magana bai fiye son su din ga haWa ido ba, kuma yana ?o?arin kiyaye duk wani abu da zai sanya ko hannunta ya taSa, ko zama ta yi yana nesa da ita, amma yau kamar zai rungume ta. Ba haka ba hatta muryarsa tamkar an canza ta. Muryar ta ?ara buWewa, kuma babu alamun wasa a cikin muryar tasa.

Babu tsammanni su ka ji an buWe ?ofar Wakin gaba Waya.
SARA DA SASSA?A...
Ayshercool

YOTA/002

P9

Aka kunna fitilar Wakin, da sauri Alina ta rufe idanunta, saboda ba ta son haske idan tana wannan ciwon kan.
Nurse ce ta ?araso tana turo trolley. Ta ce "Yi ha?uri Alina, zan ba ki magani ne"

Ta gaida Mamman ya amsa, ya sake duban Alina ya ce "Kar Si ki sha kafin ta baki maganin"

Ta girgiza kai ba tare da ta Wago kanta ba, ta ce "Ina Anty ta tafi?"

Nurse Win ta ce "Ta je sayo miki magani, ba a samunsa a nan haka"

Ya sake tausasa muryarsa ya ce "'yar ?walisa daure ki sha ko kaWan ne"

Ya yi maganar yana ajiye mata a kan cinyarta. Idanunta a rufe ta fara laluben cokalin dan ta sha. Ya Webo ya kai bakinta. A hankali take karSa, amma idonta a rufe. KaWan ta sha ta ce ta ?oshi amai take ji, ba za ta iya ci gaba da sha ba. Nurse ta kama hannunta, ta buWe cannula ta fara yi mata allura. Alina ta kawar da kanta gefe ta rintse idonta, saboda yadda ba ta son allura. Ya fakaici idonta, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro sirinji, ya kalli Nurse Win da idonsa, ta koma gefe ya kama hannun Alina, cire sirinjin da ta saka mata, ya saka wanda ya ciro a aljihunsa ya fara yi mata. A gigice ta buWe idonta ta kalle shi.
Sai dai ba ta yi magana ba, jikinta ya saki ta fara bacci, a hankali ya gama zuba ruwan allurar a jikinta, sannan ya gyara mata kwanciyarta, ya kalli Nurse Win ya Waga mata babban yatsansa alamar jinjina.
Sannan ya yi mata alama da ta tafi. Ta juya da trolley Win ta fice. Ya ciro babbar waya a aljihunsa, ya Wauki hotunan Alina.
Ya kwashe sauran kayan ya fice ya bar Wakin da sauri.

Ba a yi mintuna goma da fitarsa ba, Nadiya ta shigo Wakin, ta ?arasa gaban gadon Alina tana faWin. "Fatima, haryanzu ba ki tashi ba?" Ta yi maganar tana dafa goshin Alina.
Ta ajiye magungunan da ta sayo, sannan ta ciro wayarta da ke ta ringing.

"Hello masoyi"

"Na'am ya jikin nata?"

"Jiki Alhamdillah, tana ta bacci, ka san ?a'ida sai ta yi kwana biyu tana fama"

"Na kusa shigowa garin ai nan da awa biyu in sha Allah"

"Wai dawowa zaka yi da gaske? Aikin fa"

Ismail ya ce "Kin san hankalina ba zai kwanta ba, ba na son ciwon kan nan da take yi, na kusa shigowa in sha Allah. Kin samu magungunan kuwa?"

"Eh na samo su, amma da kyar aka bani su, wai ba a sayar da su barkatai"

"To Alhamdillah, da ta tashi a bata ta sha, kuma su yi mata duk abin da yakamata, su tattara mini bills ina dawowa zan bayar, dan bana tunanin akwai isassun kuWi a file Winmu"

Nadiya ta jinjina kai tana faWin "Ai ka san ko babu ko sisi, za su yi mana duk abin da yakamata, sai ka ?araso"

Ya amsa da "To shikenan" Ya katse wayar.

*****

Tun da Baffa ya zo, Rahama ta rasa nutsuwarta gaba Waya, kanta har wani ciwo yake yi mata. Tabbas babban dalilin da ya sanya ta karSi soyayyar Bukar, amfani da shi ne ta gano ha?i?anin wace ce wadda aka tozarta mata Wan uwa saboda ita. Amma daga baya ta fahimci kamar shi ma bai san wace ce ba, sai dai kyawawan Wabi'unsa ya sanya ta saki jiki da shi, har take jin ta fara sonsa. Ta sake tuna maganganun da Saleh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login