Showing 42001 words to 45000 words out of 53964 words

Chapter 15 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

761

murar da ta kama ta, bayan tunanin Baffa da ya addabe ta, babu abin da ya dame ta, irin rashin suturar kirki da ke jikinsu, ga ?arti a kewaye da su.
Kumburin da ?afafuwanta suka yi kuwa, ba su riga sun sace ba, saboda dafin ?ayoyin da ta din ga takawa.
Tana zaune ko kwanciya ta kasa yi, ta du?un?une jikinta, tana kallonsu a zube a daji kamar dealer gwanjo.
?aya daga cikin maharan nasu, da suke tsaronsu, ta lura da yadda yake takura mata da yawan kallo, hakan ya ?ara takura ta, mussaman rashin cikakkiyar sutura da take jikinta.

****

Tana zaune a kan gado, tana shan tea, ta kammala ta sauka daga kan gadon ta fita falo, kawai ta tarar da shi a zaune a ?aton falon, ya mi?e ?afafuwansa ya jingna da jikin kujera. Kai tsaye ta nufe shi tana faWin "Mr. President a gida zaka kwana kenan, ai ban san ka shigo ba" Ya yi shiru bai ce mata komai ba.
Ta zagaya ta zauna a kan kujera ta ce "Bikin 'yar gidan ministan al'adu da za a yi, ina son sabuwar mota gaskiya latest mai kyau. Kalli lace Win da zan yi order shi nake son sakawa, 5.5million wannan sar?ar ma direct daga Dubai na sayo ta"

Cike da takaici ya ce "Dan girman Allah Fatiyya ki rabu da ni na ji da abin da yake damuna. An sace yaran mutane a makaranta, na rasa ta ina zan fito na taushe su, yaran mutane na inda ba a ma sani ba, kuma duk da matsayinkii a ?asar nan, ko sau Waya ba ki nuna dmauwarki ko kin yi wata magana ta kwantar da hankali ba. A lokacin da ?asar nan ke fama da rashin kuWi? dur?ushewar tattalin arziki, ga Walibai an sace a mulkin mijinki a gaSar ne ki ke shirin saka kayan miliyan biyar. Ke ko gudun magana ba kya yi?"

Fatiyya ta Sata fuska ta ce "To wai dan Allah mu muka sace su ne? Abin da zai faru ya riga ya faru, Allah ya kuSutar da su, amma dan an sace yara kuma shikenan ba za mu yi walwala ba?"

Ya ?are mata kallo tsaf ya ce "Anya kuwa ke uwa ce Fatiyya? Kin ga je ki ki bani guri ne, kar ki sake dagula mini lissafi"

KwaSe baki ta yi ta fice ta bar shi a gurin a zaune.
Duk da yadda yake samun masu rarrashinsa a kan abin da ya faru, amma ya takura ?warai da matsin lambar da yake fuskanta daga jam'iyyun adawa, ?asashen ?etare da uwa uba al'ummar ?asa da su ka fara Allah wadai da mulkinsa.

*****
Laila na zaune ta idar da sallar la'asar, ta yi shiru. Sadam ya shigo da sallama Wakin ya Wora da kiran sunanta.
"Ke Laila, amma dai da wuri yau za ki Wora mana girkin dare ko? Dan ni wallahi ba na ganewa taliyar nan ko minti sha biyar ba ta yi a cikina, nake jin wayam ba komai" Sai dai ya ga ta yi shiru bata amsa ba.
?arasawa ya yi inda take, ya taSa kanta, kawai ya ga tana sharSar kuka wiwi. Cikin mamaki yake kallonta ya ce "Lafiya?"

Jin sheshshe?ar kukan nata, ya sanya Mama shigowa da sauri tana tambayar kukan me take yi.

Laila ta goge hawayenta cikin ?unar rai ta ce "Wallahi tunanin 'yan uwana da aka sace nake yi?"

Sadam ya ce "Wane 'yan uwan naki aka sace?"

"?aliban makarantar nan mana" Ta ba shi amsa tana share hawaye. "Ko a tarihi ban taSa jin wannan masifar ba, yaya za a yi a ce an sace Walibai mata har cikin makaranta kamar wasu kayan sakawa"

Saddam ya yi tsaki ya ce "Ji banza, shi ne ki ke wa mutane kuka har haka? A gidan uban wa suka zama 'yan uwan naki? Kawai kin saka gabana ya faWi a banza"

Mama ta ce "Ni wallahi kin bani tsoro"

Ta girgiza kai ta dube su ta ce "Sai ranar da ya zamana an sace da ni, za ku ji babu daWi? Idan Walibai a makarantu ba su tsira ba, ni wane tabbaci nake da shi zan tsira?"

"Ke dalla yi wa mutane shiru da wannan falsafar banzar taki. Ba nan ki ke zama kina video kina goyon bayan gwamnatin ba. Dalla tashi ki Wora mana tuwo"

Mama ta ce "Kai dakata mini, Laila na da gaskiya. Duk inda iyaye da yan uwan yaran nan suke, hankalinsu a tashe yake. Ubangiji Alla??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????h ya tseratar da su cikin Aminci. Ni kaina abin ya tsaye mini. Har da yarinyar wata class mate Winmu aka sace wallahi abin gwanin ban tausayi. Tare muka yi islamiyya da ita"

Sadam ya Sata fuska ya ce "Ahh lallai aiki ya ganku, gara na fita tun wuri na nemi abin da zan ci, tun da naga alamar zaman makoki zaku yi yau, ba za ku dafa abinci ku bani ba"

*****
Tamkar marasa amfani, haka suke hantarar Waliban.
Su na jere a zazzaune, ana raba musu buredi a wula?ance, mai rabon buredin ya mi?a wa Ramata. Ta mi?a hannu za ta karSi buredin, ya haWa da hannunta ya ri?e yana ?are mata kallo. Jikinta ya yi sanyi ya hau rawa, ta fara ?o?arin ?wace hannunta. Amma cike da rashin Wa'a ya fara shafa hannun nata da Waya hannun nasa, har zuwa damtsenta. Jikinta ya hau rawa cike da tsoro tana ?o?arin ?wacewa, amma ya tsare ta da ido da ba?ar fuskarsa yana sauke numfashi.
"Kai kar fa ka kuskura ka yi abin da ba shikenan ba, kar ka ja mana tashin hankali" cewar na kusa da shi, da suke raba buredin tare.
Ya yi murmushi tare da sakar mata hannunta, yana yi mata murmushi.
A hankali Rahama ta yi ajiyar zuciya, dan tsoro ne ya shige ta, ta zata wani abin zai yi mata.
?arar sautin kusantowar babura ce ta cika gurin, gaba Waya suka zuba wa inda suke jiyo sautin ido. Su goma sha biyu ne suka zo a kan babura kowannensu ri?e da miyagun makamai.
Idan da sabo, ya ci a ce Rahama ta saba da ganin tashin hankali, amma a wannan karon ma sai da tsoro ya shige ta, ganin uban bindigun da suke hannun maharan kamar za su ya?in duniya.
Cikin girmamawa suke gaishe shi, ya din ga jinjina musu kai, ya din ga ?arewa 'yan matan kallo, ya tsayar da idanunsa a kan Rahama. Ya yi shiru yana ?ara ?ura mata ido, tamkar mai son hango wani a kan fuskarta.
Sai dai ita ma ta Wan tsura masa ido, ba ta kai ga janye idanunta ba, ya tako a hankali nufo ta, da sauri ta sunkuyar da kanta ?asa ta daina kallonsa. Ya ?arasa ya tsuguna a gabanta yana kuma ?are mata kallo, tun zuwansu ya lura da yadda take ta kare jikinta da hannunta.

"Kalle ni" Ya faWa cikin kakkausar murya.

Tamkar zuciyarta za ta faso ?irjinta ta fito, saboda luguden da take yi, haka ta Wago idanunta da kyar ta kalle shi. Ta mayar da kanta ta sunkuyar.

"Kin sanni ne?" Ta girgiza kai a hankali.

Ya saka hannu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Da gaske? Kalle ni dai, na ga kina kallona kamar kin sanni ko?" Ya yi maganar yana murmushi.

Ta sake girgiza masa kai tana sunkuyar da kanta ?asa, ba tare da ta kalle shi ba.

"A jam fullo?" (Ke Bafulatana ce?"

Ta jinjina kai alamar eh.

""ko honWun wuro njahaa?" (Daga wani gari ki ke?"

"Yelwa" Ta faWa a tsorace.

Ya waro ido tare da yin murmushi ya ce "Daga Yelwa aka kai ki makarantar kwana? gaskiya ne, lallai makiyayan Yelwa sun waye, an samu gagarumin ci gaba Sannu ko, ku kwantar da hankalinku babu abin da za mu yi muku, za ku koma gida lafiya in sha Allah, za mu ajiye ku ne nan da wani Wan lokaci, domin cikar muaradanmu da na iyayen gidanmu. Da mun kammala za mu sake ku. Kun kafa tarihi a duniya, Walibai na farko da aka yi garkuwa da su. Ya yi maganar yana murmushi.
Ba tare da ta san ita yake kallo ba, ta sake Wagowa ta kalle shi, fari ne sai dai ba tas ba, idanunsa sun sha farin kwalli rabajau, yanayin fuskarsa da yadda yake magana, ba ka ce ko kwari da baka zai iya Wauka ba, balle bindiga.

"Za ki ce wani abu ne?" Ya yi maganar yana kallon ta. Ta girgiza kai da sauri tana sake sunkuyar da kanta.

"Ya sunanki?"

"Rahma" Ta furta kamar mai raWa cikin tsoro.

"Ramata" Ya furta yana guntun murmushi, ya mi?e tsaye ta kalle shi da mamakin jin yadda ya faWi sunan da ake gaya mata a gida, Alhalin ita ba ta san shi ba, ba kuma ta taSa ganinsa ba...

Ayshercool
08081012143


SARA DA SASSA?A...
AYSHERCOOL
YOTA/002
BRIGHT PENS

13
Murmushi ya yi ganin yadda alamun mamaki suka bayyana a fuskarta baki Waya, a lokaci Waya.

*****

Fuskar Ummi Wauke da matsananciyar damuwa take kallon Ru?ayya, tana kwance a gadon Asibiti sai dai ba ta magana. Sai dai Likitoci sun tabattar wa su Ummi cewar, tsoro ne kawai da razani suke damunta. Haka suka karSo ta suka tafi da ita, da niyyar su canza mata Asibiti, zuwa na kusa da su can cikin gari.
Babu yadda Ammar bai yi ba, ya samu release ya je gida, ya ji halin da ake ciki game da Ru?ayya amma aka hana shi, sai dai su yi waya ya ji ya jikinta, saboda su na daji ma a lokacin.

*****

Nadiya ta takura wa Alina a kan lallai sai ta koma makaranta, dan idan Yaya ya dawo, ya tarara ta jingine zuwa makaranta, sai ya yi mata faWa.

Ko da ta shirya ta je makarantar ma, jikinta duk a sanyaye yake, malamai da Walibai su na ta yi mata jajen Satan yayanta.
Hafsa ta yi ta rarrashinta tana bata ha?uri, ji ta yi kamar ta gaya mata ha?i?anin abin da ya faru, amma tamkar wadda aka asirce ta kasa furta mata komai.

Haka ta je Islamiyya ma, tana tafe tana jan ?afarta jikinta a sanyaye. Ta jiyo muryarsa "'yan mata" Kamar ta yi banza ta tafi sai kuma ta tsaya cak. Ya ?araso yana faWin "Alhamdillah, kin koma makaranta kenan? Ai hakan ne ya dace zama a gidan damuwa zai ci gaba da saka ki"

Ta Wago idanunta ta zuba masa, tare da haWiye wani abu mai Waci, idanunta ya cika da hawaye.

"Lafiya mene ne kuma?" Ta yi shiru tana bawa hawayen idanunta damar zubowa.

Jiki a sanyaye ya ce "Ki na ji 'yan mata, ki yi ha?uri, ki yi ha?uri ki ci gaba da addu'a in sha Allah zai dawo cikin ?oshin lafiya da aminci"

"Yaushe? Zuwa yaushe zaka dawo mini da shi?"

Ya yi saroro yana kallonta. "Ka gaya mini yaushe za ka dawo da shi? Na ganka fa, na ga komai, amma na kasa gayawa kowa, ina ta kallonka in ga ko za ka dawo da shi, amma ka ?i. Na san kai da Yaya ba kwa jituwa amma abin da ka yi ya yi tsauri"

"Me ki ke nufi?"

"Na ganka, na gani, a kan idona ka Waure shi kai da wasu ku ka tafi da shi Da daddare ranar na dawo daga makarantar dare. Ta can baya na zagayo ina tsaye a bakin lungun can, na ganka. Dan Allah Mamman dan darajar iyayenka ka dawo mini da yayana dan Allah" Ya waiwaya layin ya ga babu kowa, ya sassauta murya ya ce "Ni fa ban gane me ki ke nufi ba"

"Ka sani wallahi ka sani, kai ka Waure Yaya da igiya ku ka tafi da shi" Ya girgiza kai ya ce "Gaskiya ba ni ba ne ba, dan ranar da ki ke magana bana garin nan, na je gurin Inna"

"Kai fa ma'abocin karanta Alqur'ani ne, bai kamata ka yi ?arya ba, dan Allah dan Annabi ka dawo mini da shi"

"Amm ina ga ki je gida kawai, wata?ila damuwa ce ta yi miki yawa ki kr irin wannan tunanin, amma gaskiya ba ni ki ka gani ba." Ya wuce ta ya bar ta a tsaye a gurin.

Sai da ta yi kuka mai isarta sannan ta ?arasa gida, ko da ta je gidan ta tarar Nadiya ta fita, dan haka ta samu cikakkiyar damar yin kuka.

*****

"Ha?i?a mu na yabawa yadda mr. President yake ta ?o?arin ganin yaran nan sun kuSuta, mun san ayyuka sun yi maka yawa, kuma duk wani abu da ka ke yi, domin al'immarka ka ke yin su. Amma Allah wadai da fadarka ta yi da sace Walibai, ta bakin mai magana da yawunka ta yi kaWan. Ko ba ka je da kanka ba, ka rarrashi al'ummarka mussaman iyayen waWanda aka sace Win nan, za su ji daWi, komai ?an?antar abin da zaka gaya musu kuwa za su ji daWi domin kai uba ne ga kowa. Please ka ce wani abu ko babu yawa, za mu ji daWi"

A hankali ya ja ajiyar zuciya, bayan kammala kallon videon da ta wallafa, gaba Waya ?asar ta ruWe, ko ta ina bring back our girls ake posting.
Ji ya yi ya samu ?warin gwiwa da kalamanta, ko da maganarsa ba za ta yi tasiri ba, akwai bu?atar ya yi magana da bakinsa, ba a ji iya ta bakin mai magana da yawunsa ba.

Halilu ne ya shigo ofishin, hannunsa ri?e da takardu. Cikin matu?ar girmamawa, suka gaisa. Bayan an yi masa iznin zama, ya dubi Kankiya ya ce "Mr. President, tafiyarka taron kasashe masu arzikin man fetur fa jibi ne, ina yi maka tuni duk da na ga ka yi busy da yawa."

"Na soke tafiyar"

Da sauri Halilu ya dube shi ya ce "Mr. President ka soke kuma?"

"Eh, hankalina na kan batun yaran nan, ba zan iya komai ba"

"Haka ne, amma akwai bu?atar ko wakilci a naWa ka tura"

"Babu bu?ata, mutanen nan hawan ?awara suke yi mana kawai, wannan shekarar ba zamu halarci taron ba, hanyoyi da yarjejeniyoyin da za su dur?usar da mu, su azurta kansu kawai suke yi"

"Amma Your excellency, ?in halartar zaman, ya saSa da yarjejeniyar da tsohuwar gwamnati ta saka hannu, kafin karSar bashin biliyoyin da aka yi a shekarun baya, za su iya hukunta mu, ta hanyar janye mana wani tallafin, ko kuma sanya mana takunkumin da zai dur?usar da tattalin arzikinmu ma baki Waya"

Ya Wan yi shiru yana matsa yatunsa, ya dubi Halilu ya ce "Ina bu?atar zama da shugaban hukumar ya?i da cin hanci da rashawa. Ina bu?atar bincikar yadda aka gudanar da wannan ma?udan kuWaWen, da ainihin kwafin yarjejeniyar basussukan da aka karSa. Dan yanzu haka ma, ?asar ba za ta tafi ba sai an ciyo wani bashin, kuWaWen da suke asusun ?asar nan, ko jihohi goma ba zai ri?e ba"

Halilu ya risuna ya ce "In sha Allah, za a yi yadda ka ce, amma mr. President ka sake nazari a kan batun taron nan" Kai kawai ya jinjina. Bayan fitar Halilu ya sake Waukko wayarsa yana dubawa.
Comments ne na rashin kyautawa, da cin zarafi aka cika Laila da shi. Cin mutumci har da iyayenta, cin mutunci mai matu?ar muni ga ita da iyayenta, ban da ?azafi da kushe mata halitta a ?o?arinta na bawa gwamnatinsa kariya.

A hankali ya dafe goshinsa yana Wan murzawa a hankali. Yana tunanin meya kamata ya yi.

*****

YELWA
Duk da dakiya da juriya irin ta Baffan Rahama, sai da ya yi wata irin muguwar rama, dan ko lokacin da aka kashe masa Wa, bai shiga mummunan tashin hankali kamar yanzu ba. Ko Abinci baya iya ci, baya iya bacci, 'yar kasuwar da yake Wan zuwa ma ya daina saboda matsananciyar damuwa da kuma tashin hankali.
Tashin hankali da damuwa da yake ciki, bai hana jama'ar garin zunWensa ba, har da masu yi masa dariya da Allah ya ?ara.

Hanne na zaune a Wakinta, tana sa?ar mafici, Bukar ya faWo Wakin kamar an jefo shi. Ta Waga kai ta bi shi da kallo tana mamakin me ya faru.

"Hanne, kin san me yake faruwa kuwa?"

Ta girgiza kai tana tsare shi da ido, tana jiran ?arin bayani.

"Su Ramata aka sace s makarantar boko"

"Kamar ya ya aka sace su? Ta ya za a sace mutum? Ko dai ba ka ji dai-dai ba ne?"

Bukar ya tsuke fuska ya ce "Zan yi miki ?arya ne? Da gaske nake an sace su Ramata a makaranta, ba a ma san inda suke ba"

Hanne ta dafe ?irji tana nanata "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wannan wane irin abu ne? Allah sarki Baban Ramata, anya akwai wanda Allah ya taSa jarabta a garin nan kamar sa? Amma ni ta yaya za a ce an sace mutum"

Cikin damuwa Bukar ya ce "To nima dai haka na ji"

"Gaskiya zan je gidan nasu, zan sake tambayar Baffan"

"A'a babu ruwana, kin san a ?ar?ashin takunkumi ki ke, kuma a gan ki a gidansu Ramata?"

Hanne da idanunta suka cika da hawaye ta ce "Wallahi ko za su kashe ni sai na je, har Duniya ta naWe Ramata da ahalinsu su na bin mu gagarumin bashi, ba zan iya jurewa ba sai na je"

*****

Sosai Waya daga cikin masu tsaron su Rahama, yake ?o?arin kai musu farmaki. Da ?o?arin fito da zalamarsa a fili a kansu.
Duk dare haka ake Waure musu ?afafuwa, domin kar ma a samu mai yin?urin guduwa.
Idanun Rahama biyu, tana rarraba su a cikin duhu, ta ji wani abu mai sanyi, yana bin ?afarta. Ta Wan motsa ?afarta a hankali, ta ji abin ya daina bin ta. Wata irin ?ara ta saki, bayan jin wani irin raWaWi ya ratsa ?waurinta zuwa cikin ?wa?walwarta ta gigice.
Cikin hanzari masu tsaronsu, suka yo kanta su na haskata da fitila, su na yi mata tsawa. Tuni gumi ya wanke ta, sai dai kafin su yi magana suka hangi wani irin ?aton ba?in maciji ya bar gurin.
Su ka haska ?afar Rahama, ga shaidar gurin da ya cije ta, jikinta sai wata irin tsuma yake yi.
Da yawa daga cikin Waliban, har da wanda suka fara bacci, duk su ka zubo mata ido, su na yi mata sannu. Ya yin da tsoro ya shige su, kar ya kuma cizon wani.
"Dare ne yanzu babu abin da za mu iya yi, zuwa da safe a sanar da sadauki" cewar Waya daga cikinsu.

Babu wanda ya damu ya ba ta wani taimakon gaggawa, kawai suka koma mazauninsu, suka bar ta. Rahama kuwa ji take yi tamkar ranta ne zai bar gangar jikinta, saboda azaba da raWaWin da yake ratsa ta.
Duk yadda ta so gwada jarumta sai ta kasa, ta fara kuka mai sauti, mai nuna tsantsar azaba da galabaita.

"Ke ki rufe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login