Showing 18001 words to 21000 words out of 53964 words

Chapter 7 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

771

a cikin jama'a.
Kiri-?iri 'yan makarantar su maza, ba sa shiga harkarta, tun da wani yaro ya ce yana sonta tun a Jss 2, yaron yana Ss2, daga ta ba wa Nadiya labari, ta gaya masa yaje har makarantar, ya zane yaron, case har da iyaye da zuwa gurin 'yan sanda. Samari na cikin unguwa kuwa, babu wanda yake shiga harkarta, ko kula ta, da ka nuna alamar sonta ka ke yi ko da gaisuwa ce ta fiye haWa ku, sai Ismail ya yi wa mutum tijara ya ce za a lalata masa ?anwa, ba zai lamunci hakan ba. Ita kuma Allah ya hore mata farin jinin mutane, saboda yawan fara'arta da kuma surutunta, da wuya ka yi zaman minti goma da ita ba ku saba ba.
Ko da Isma'il ya je masallaci, sahu Waya Ismail ya yi salla da mai gyaran takalmin nan, kallo Waya ya yi wa Isma'il, ya sunkuyar da kansa, ya ?arasa azkar Win sa ya tashi sumi-sumi ya fitaya bar masallacin. Yana cikin tafiya ya ji an dafa kafaWarsa. Babu shiri ya waiwayo a tsorace.

Ismail ya tsare shi da ido ya ce "A tunaninka haWa sahu da kai da na yi kawai faruwa ya yi ne haka kurum? Gurinka na zo ne ai. Ba kuma tsawaita magana zan yi ba. Hawainiyarka ta kiyayi ramat??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a. Shi ne kawai abin da zan iya gaya maka" Ya sakar masa kafaWa ya kewaye shi ya wuce.
Yaje gida ya tarar da Nadiya da Alina sun kewaye rake, su na sha su na hira. Sai da Alina ta gan shi, sannan ta tuna ma a yadda ya fita. Sai dai bai kula su ba, ya shiga Waki.

*****

"Barwa" Ya kira sunansa.

"Na'am sir"

"Ka ce yaronsa ya aiko maka ba shi ne ya zo da kansa ba?"

Barwa "Eh ranka ya daWe"

"Dole mu yi taka tsantsan da mutanen nan, amma abin da muke so ba zai yiwu ba, sai da su dole. Ka gaya musu mun amince da dukkanin bu?atunsu, za kuma mu yi, su fara aiki kawai"

"Amma ranka ya daWe, yarjejeniyar ta yi tsauri da yawa fa, kuma za a kashe kuWaWe ne ba kaWan ba"

Dattijon ya yi murmushi ya ce "Ai yaro bai san wuta ba sai ya taka, bamu za mu biya kuWin aikin ba, gwamnatin da kanta za ta biya kuWin aikin da za a ya?e ta, ka zuba idanu ka gani, sannan kuma na nemi haWin kan ?usoshin tsaro, komai zai tafi dai-dai babu gargada. A hanzarta shirya yarjejeniyar kamar yadda suka bu?ata"

Barwa ya ce "Shikenan ranka ya daWe, an gama da yardar Allah"

"A hanzarta domin Allah, dan bamu da lokacin Satawa, a gaggauce yakamata mu yi komai. Ba na son ya rufa shekara guda, lissafi bai ?wace masa ba. Anjima zamu zauna da su Ade, da zarar yaran nan sun fara aikinsu, akwai bu?atar dala ta yi ?aranci a kasuwa"

Barwa ya kwashe da dariya ya ce "In dai lissafi ne a bar maka YallaSai"

"Kash, kai dai ka zuba ido, ka ga yadda za mu mayar da komai baibai ai Jagora ya tsaya mana, sai mu ga da mu da shi, wa zai ha?ura ya bi wani. Ta?amarsa ko da mu ko babu mu, yana da soyayyar jama'a yana da ya?inin zai sake komawa gadon mulki, tun da mun tura motar zai bule mu da haya?i, amma mu zuba mu gani...

*****

Baffa na zaune bayan sallar asuba yana lazumi, ya kashingiWa da jikin gado, yana jan carbi. Yana jin Juma ta shigo, ta kawo masa madara ta ajiye ta fita, amma bai motsa ba. Ya rasa wace irin fargaba ce take ratsa shi har haka, komai baya yi masa daWi. Tun da ya mayar da Rahama makaranta, ya rasa mene ne yake ba shi tsoron ko saka shi fargabar ji yake yi tamkar ya koma ya Waukko ta kawai.

Rahama kuwa na zaune a Wakin karatunsu na makaranta, tana duba wani littafi, ta ci karo da ta?aitaccen tarihin sir isaac newton, da ake yi wa la?abi da father of modern physics. Masanin kimiyya ne sosai da sosai. Yana cikin wanda suka bayar da gudummawa a harkar lissafi. Duk da bincike ya nuna kai tsaye ba za a ce shi ne kaWai father of physics ba, tun da ga Albert Einstein, ga Galileo Galilei.
Shi ya samar da law of motion, bincike ya nuna Isaac newton introvert ne, ana kyautata zaton yawan ta'amalli da chemical ne ya yi sanadiyar mutuwarsa. Babban abin da ya fi Waukar hankalin Rahama shi ne, da aka ce bai taSa aure ba, babu kuma ?wa?a?warar hujjar da take nuna, ya yi soyayya a rayuwarsa.

Kawai ta yi murmushi tana tunanin, ?ila da ya yi soyayya, ko da yana da aure, da wannan nasarorin bai cin musu ba, dan Sai ya fi mayar da hankali a kan gina iyalinsa, haka zalika da yana da yawan surutu babu lallai ya cimma abubuwan da ya cimma.
Saboda mata na son attention, da kulawa, babu lallai ya din ga samun isasshen lokacin tunani, da bawa ?wa?walwarsa damar samar da abubuwa.
Ta yi ajiyar zuciya tana tuna Bukar, tabbas mata na son kulawa da attention,? sai dai ta su soyayyar na fuskantar barazana, du da ?o?arin da Bukar yake yi a kan hakan. Sai dai gudun faruwar matsala ya sanya a Soye suke haWuwa. Sai dai sam ba ta jin irin wannan zunzurutun soyayyar tasa a cikin ranta. Babban abin da ya sanya take tare da Bukar tausayinsa ne da take ji.
Sai kuma ta mayar da tunaninta kan Hanne, tare da son tabattar da abin da Saleh ya faWa gaske ne?

"Kenan idan ina bu?atar yin nasara a rayuwata, dole na fara ajiye batun wannan gurguwar soyayyar tawa da ban ga ta inda zata haifar da Wa mai ido ba." Ta yi maganar a zuciyarta.

"To wani hali Bukar zai shiga? Idan na jingine batun soyayyarmu" Wata zuciyar ta tambaye ta. Gaba Waya sai ta ji ta gaji, ta daina fahimtar abin da take karantawa, kawai ta rufe littafin ta kwanta.

"Bacci a Library Rahama" Ta buWe idonta, sannan ta tashi zaune a hankali ta kalle shi ta ce "Ba bacci nake yi ba sir"

"?arya na yi kenan?"

Ta girgiza masa kai, tana sunkuyar da kai.

Ya ce "Me ku ka shirya presenting ne, next week in Allah ya kaimu?" Ta Waga kai tana kallonsa.

"Press club i mean"

"Introvert" Ta faWa a ta?aice.

Ya yi dariya ya ce "Rahama B Yelwa, Introvert kawai? Meye ala?ar introvert da presentation na press club? Ko da yake akwai ala?a ai. Amma you went deep, ko personality Winki ki ke son yi wa mutane bayani a kai?"

Ta girgiza kai ta ce "No sir, ai am not introvert, za mu rubuta mu kawo maka ka duba" Ta yi maganar tana murmushi.

"To shikenan ina jiranki"

Ta tashi ta tattare litattafanta, ta fice daga Libraryn.

*****

Yau a makarantar dare, Alina bacci ne ya dame ta, dan haka ana tashi babu wanda ta tsaya jira, ta rungumo jakarta ta fito hanya. Tana ta uwar hamma, katse hammarta ta yi ganinsa a tsaye a ?ofar makarantar, ya saka ?ofar makarantar a gaba.
A hankali ta ?arasa inda yake tsaye, tana Wan layi saboda baccin da yake kanta. "Wani ka ke jira ne?" Ta yi maganar tana kallon Walibai da suke fitowa daga cikin makarantarsu.

Ya kunna fitilar hannunsa ya ce "Wucewa zan yi, sai na ga an Wauke wuta"

Dariya ta yi ta ce "Saboda ina tsoron duhu ko? To na gode sosai da ka tuna da ni, ka taimake ni mu tafi" Ya jinjina kai su ka jera yana haska musu hanya.

Alina ta Wan dube shi ta ce "Ka ce mini ka je garinku, ina ne garin naku? Kullum na tambaye ka baka gaya mini"

"Can wani guri"

"Ina?"

Ya ce "Wani waje ne, can ?auye"

"To meyasa ka baro garinku ka dawo nan?"

Ya Wan yi shiru sannan ya ce "Almajiri ne ni"

Alina ta ce "Almajiri kuma? Babba da kai haka, ba 'yan yara ne suke almajiranci ba? To ina ce makarantar ku?"

Ya Wan yi jimm, jin yadda take ta jero masa tambayoyi kashi-kashi kamar shari'a. Ya numfasa yana tunanin amsar da zai bata daidai da hankalinta. Ya ce "Eh, na yi sauka ne, tuntuni, neman kuWi nake yi, shi ya zaunar da ni, amma ina zuwa makarantar haryanzu ai ba a girma da neman ilimi ko?."

"Laa nima na kusa sauka fa, mu na kammala haddar izifi ashirin za a haWa mu yi bikin sauka, Yaya ya ce zai saya mini ?aton rago idan na yi sauka" Ta faWa cikin farincikinki.

Ya Wan yi dariya da gefen bakinsa ya ce "Hakan na da kyau, Allah ya sanya albarka"

"Amin. To yaya sunanka?" Ta yi tambayar daidai lokacin da suka ?araso layin.

"Bawan Allah"

Ta Wan Sata fuska ta ce "To ai kowa bawan Allah ne, sunanka fa da ake kiran ka da shi, sunanka na gaskiya"

"Mamman" Ya faWa a ta?aice.

Ta yi murmushi ta ce Muhammad dai ko? Tun da a birni ka ke. Ni kuma sunana...

"Alina" ya ?arasa mata.

Ta yi turus ta ce "A ina ka san sunana?"

Bai bata amsar ba ya ce "Sai da safe" Ta yi murmushi ta ce "To ai ba shi ne sunana na gaskiya ba, sunana na gaskiya Fatima".

Ya Wan yi turus yana kallonta, fuskarsa Wauke da murmushi.

"Ya na ga kana murmushi?"

"Sunan Innata ne da nake matu?ar so, duk da ba ita ta haife ni ba"

Alina ta yi dariya ta ce "Ashe kai Wana ne, to Wan albarka zan din ga ce maka"

Jinjina kai kawai ya yi, yana murmushi, ita kuma ta shiga gida. Murmushi ta Wan din ga yi, da ta tuna saboda ita ya je makarantar su, saboda ya haska mata hanya. Da ta tuna abin da Yayanta ya yi masa sai ta ji babu daWi, kasancewar yanzu ta fahimci yana da kirki, kawai dai Wabi'unsa ne wasu lokutan kamar mara gaskiya.

Mamman kuwa bayan ya shiga Wakinsa, ya zare rigar jikinsa, ya gyara shimfiWarsa, ya fito da indomie a leda, ya zazzage a wani kwano, ya cinye ya sha ruwa. Ya Waga ?asan 'yar katifar da ke Wakin, ya din ga kallon ?asan katifar sannan ya mayar da katifar ya gyara ya kwanta yana Wan yin mi?a.
Ya ciro wayarsa daga gefen katifarsa, ya tura wasu code zuwa ga wata lamba. Ya juya ya kwanta.

*****

YELWA

Baffa ne ya yi zuguum yana sauraren radion da ke gabansa, yanayin fuskarsa ya nuna ruWewa da tsoro.
Ya numfasa ya ce "Juma"

"Na'am" Ta amsa tana tattara hankalinta a kansa.

"Ki na jin wata masifa ko?"

"A ina?"

"A radion nan da nake ji"

Ta girgiza kai ta ce "Me aka ce?"

"FaWan manoma da Makiyaya a can wani yanki, an yanka manoma yankan rago su kusan goma sha biyu da sunan Waukar fansa"

Juma ta waro ido ta ce "Yankawa kuma?"

"Wallahi yankawa, ga shi ina ji a radio"

"Innalillahi, yanzu Jauro sai a yanka mutum, kuma da wu?a aka yanka su ko da me?"

Baffa ya ce "Ina zan sani, abin da dai suka ce kenan. Wallahi abin nan yana bani tsoro. Mu ma kusan irin wannan rikicin muke fuskanta tsawon shekaru, ina tsoron ya rikiWe ya zama wani abu daban."

Juma ta ce "Babu abin da zai faru sai alkhairi da yardar Allah"

Baffa ya jinjina kai ya ce "Haka nake fata, amma haryanzu ina ha?ur?urtar da samarinmu, a kan lallai sai sun Wauki fansar abin da aka yi mana. Ke dai Allah ya kyauta kawai".

*****

Rahama ce ke zaune a bakin kwanarsu, tana kallon 'yan hostel Winsu, sun sha kwalliya su na ta raye-raye kasancewar weekends ce. Sun saka bokitai da jarakuna su na ta kaWe-kaWe. Littafi ne a hannunta amma tana kallon littafin tana kallonsu, saboda abin da suke yi Win yana saka ta nishaWi.

"Yelwa, kin no?e kina wani murmushi, taso ki taka"

Cewar wata senior Win ta.

Rahama ta hau dariya tana girgiza kai.

Ru?ayya? ta ce "Idan Rahama ta yi rawa, na yi al?awarin bayar da kyautar sadine gwangwani goma wallahi" Shewa suka hau yi, Rahama kuwa rufe fuska ta hau yi tana dariya.

"Ai wallahi Ru?ayya kin san sadine Win nan ba zai ciwu ba, in dai sai Rahama ta yi rawa za a ci shi. Ita a makiyayan ma ma irin na 1980s Win nan ne."

Suka din ga tsokanar Rahama, ?arshe ta bar musu Hostel Win. Naja ce ta biyo bayanta tana faWin "Yaya Rahama" Rahama ta tsaya ta waiwayo ta ce "Na'am Nana".
"Dan Assignment ne da ni, na kasa ko za ki koya mini"
Rahama ta ce "Me zai hana na koya miki, wanne subject ne?"

Naja ta ce "Your favourite Maths"

Rahama ta ce "Mu je Library, sai mu yi a can" Naja ta jinjina kai, ta karSi litattafan hannun Rahama suka tafi. Boarding kenan, gidan ka zo na zo, amma duk ?in ka da mutane haka zaka haWu da wanda za ku rayu tare tamkar yan gida Waya.
Duk da akwai ?alubale, amma ana koyon darussan rayuwa.

*****

"Assalamu alaikum. Salamu alaikum" Cikin bacci yake jin 'yar muryar na yi masa sallama. Da kyar ya iya motsawa, ya tashi ya saka rigarsa, ya buWe ?ofar. Da idanunsa ta fara tozali, ta Wan ja da baya a tsorace.
"Ahh, ka yi ha?uri, ban san bacci ka ke yi ba, da dam..dama takalimina na kawo, yi ha?uri." Ya mi?a mata hannunsa yana tsare ta da ido. Jikinta na Wan rawa ta mi?a masa takalaman nata.
Ya fito tare da kayan aikinsa, sai dai yau ta ga fuskarsa a tsuke sosai da sosai. Ta lura da yadda yake aikin yau a hankali sosai da sosai.

So take ta tambaye shi ko lafiya, amma ta kasa sai satar kallonsa da take yi. Gani ta yi ya tsaya cak da wanke takalmin, yana Wan rintse idanunsa.

"Meyafaru?" Ta faWa a Wan rikice tana kallonsa.

Da hannunsa ya nuna mata cikinsa, ya tashi, ya ajiye komai a gurin, ya koma Wakinsa. Jikinta na rawa ta tashi ta tafi gida. A kitchen ta samu Nadiya tana aikin girki. Cikin damuwa ta ce "Antynmu idan ki na da maganin ciwon ciki ki bani zan ba wa Mamman cikinsa ne yake ciwo"

Nadiya ta tsaya ta ce "Waye hakan?"

"Mai gyaran takalmi"

"To? ba shi da lafiya, to Allah ya ba shi lafiya, duba jakar magungunan ki gani idan akwai" jikin Alina na rawa ta shiga Wakin Anty, tana duba jakar da suke ajiye magunguna, ta dubo maganin ciwon ciki. Ta fito tana faWin "Anty na samu, amma akwai sauran kunu? Kin ga ba zai sha magani bai ci komai ba"

Nadiya ta ce "Eh gaskiya ne, amma dai da yayanki na ajiyewa kunun, kin san zai iya nema da rana ya ce zai sha"

Cikin marairaicewa ta ce "Dan Allah Antynmu ki kawo a ba shi, sai ki cewa Yayan kununan ya ?are.

Nadiya ta ce "To Alina, a ba shi Allah ya sauwwa?e, ya sanya kaffara"

Ta tsiyaye kunun gyaWar a kofi mai murfi, ta yi waje da sauri. Nadiya ba ta kawo komai a ranta ba, saboda sanin halin Alina. Wasu lokutan a hanya za ta tsinto almajiri, ta kawo shi gida ta ce sai a ba shi Abinci ko ta ce sai Isma'il ya ba shi kuWi. Duk da rashin mu'amala da ita da samarin unguwar ba sa yi, amma tana shiri da alamajirai sosai da sosai. Saboda tana son bayar da abu.

Cike da wauta da ?uruciya, Alina ta faWa Wakin Mamma, ba tare da sallama ko neman izini ba. Da wani irin mugun zafin nama, ya saka filo akan wani abu ya rufe. Idanunta ba su kai ga tantance mata abin da ta gani ba, ya rufe da fulon.

Ta Wan sororo amma ta basar ta mi?a masa kofin kunun ta ce "Ga kunu sai ka sha, sai ka sha maganin. Tsigar jikinsa duk ta tashi, saboda azabar ciwo har wani gumi ne yake tsatsafo masa ta kan karan hancinsa. Ya saka hannu ya karSi kofin. Kunun? da zafinsa ya kafa kai ya din ga zu?arsa. Bai shanye ba, ya mi?a mata hannunsa, ta saka masa maganin ya Salle ya haWiye ba tare da ko ya haWa da ruwa ba.
Ta tsaya cike da rashin sanin abin yi tana jera masa sannu. Bai amsa mata ba, sai yatsun ?afarsa da ta ga yana ta lan?wasawa, alamar yana cikin matsanancin ciwo.
Ya juyo da fuskarsa a hankali, duk gumi ya tsatstsafo masa, wasu irin jijiyoyi sun shata a goshinsa raWa-raWa, sai idanunsa da suka yi jawur.
"Je ki" Ya furta da kyar. Maimakon ta fita sai ta tsaya tana kallonsa, ganin kamar zai fita hayyacinsa.

"Ki fita!" Ya yi magana cikin tsawa, yana nuna mata hanyar fita. saboda rikicewa ba ta san yadda aka yi ta ganta a waje ba. Ta kwashe takalmanta ta nufi gida a tsorace.

Nadiya ta ce "Alina yanzu nake shirin fita na ga ko lafiya, ki ka daWe, kin san fa fita zan yi, zan je Asibiti"

Alina ta ce "Lafiya ?alau, sai kin dawo" Ta shige Waki. Nadiya ta bi Alina da kallo tana mamakin meya tsorata ta haka, ba ta sake magana ba ta fita. Cike da tausayawa Alina take tuno yanayin da ta bar shi a ciki, amma da tuna tsawar da ya yi mata, sai ranta ya Saci gaba Waya, ta ji haushi ba kaWan ba"
Sai dai ba ta daina tantama da zuciyarta ba a kan abin da ta gani a Wakin nasa ba. Idan ba gizo idonta ya yi mata a kamar dai bindiga ta gani a Wakin ya saka pillow ya rufe. Sai dai ta ?i yarda da hakan ta gani, ta basar ta ci gaba da kokwanton ba bindiga ta gani ba.

Sai dai hakan bai hana ta lokaci-lokaci ta din ga le?a ?ofar gida ba, ta ga ko za ta hango ya fito ba.

*****

Kacalla ne tsaye a cikin dokar daji, tare da Sadauki, gabansu wani buhu ne a ajiye.
Ya dafa kafaWar Sadauki yana kallon idonsa.
"Sadauki amanar kacalla"
ya yi murmushi ya ce "Allah ya taimaki Uban Wakina"

"Ka ga dai yadda lamari ya kaya, na yarda da kai na san ba za a samu kowace irin matsala ba da yardar Allah. Ka je ka ?arasa shirya komai da mutanenka, duk abin da ake ciki, mu yi waya."

Sadauki ya ce "An gama shugabana, ka yi layar zana, ka bi ta gabasa zan Kudu da kayan, ka saka a gyara mana hanya"

"Shikenan babu damuwa, Allah ya tsare"

"Amin" ya saSa buhun nan a kafaWarsa ya yi gaba.

*****

ALINA

wunin ranar ba ta sake ganin gilmawarsa ba, abin ya din ga damunta, ta din

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login