Showing 6001 words to 9000 words out of 53964 words

Chapter 3 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

745

Ta na tsayawa, su na haWa ido, ta ji wani irin abu a jikinta. Ya yi mata dabaibayi da manya-manyan idanunsa, da suka surka da kalar ja. A take ta hau tsuma, ta kwasa da gudu ta ?arasa gida.

Daga cikin Wakin Ismail ya ji Alina ta faWo gidan ya ce "Yaya mene ne haka za ki faWo gida haka da gudu kamar an sako shanuwa?"

Cikin fargaba ta ce "Ni wallahi Yaya wannan mutumin kullum sai na gan shi, tsoro yake bani"

Ba shiri ya fito daga Wakin fuska a murtuke yana faWin "Waye shi, me ya yi miki?"

Tana Wan rarraba ido ta ce "Bai yi mini komai ba, tsoronsa kawai nake ji, kuma kusan kullum sai na gan shi"

"Mu je na ji dalilin da ya sanya yake tsorata ki" Ya yi maganar yana zura takalmansa a fusace.

Anty Nadiya ta ce "Haba masoyi, kamar ba ka san shirirtar Alina ba, ban da shirirta ya za a yi haka kurum kawai ta din ga jin tsoron mutum, ka san ta saba irin wannan rashin kan gadon, kar ka je ta saka ka ji kunya."

Sai kuma ya Wan sassauta tsuke fuskar da ya yi, ya dubi Alina ya ce "Babu ruwanki da shi, muddin ya yi miki wani abu na rashin kyautawa, kawai ki gaya mini" ta jinjina kai, sannan ta nufi Wakinta.

Kwanaki biyu a jere, Alina duk lokacin da za ta fita, za ta ga mutumin nan, a ?ofar shagon nan, yana gyaran takalmi. Ta din ga ?o?arin koyawa kanta rashin jin tsoronsa, amma ta kasa mussaman idan ta tuna idanunsa, muddin suka haWu suka haWa ido, sai gabanta ya yi mummunar faWuwa gaba Waya sai ta rikice.
In dai za ta fita har addu'a take yi, Allah ya sa kar ta haWu da shi.
Cikin sa'a yau har ta je makarantar boko, ta je islamiyya ta dawo ba ta gan shi ba, sai da aka taso daga makarantar dare sannan ta gan shi a ?ofar makarantar su. Sosai abin ya fara damunta, ga shi tana tsoron jarabar Yaya, da sai ta sake gaya masa. Ta lura gaba Waya yanzu mutumin a layinsu ya tare, da safe zuwa azahar ya yi gyaran takalmi zuwa yamma ta ga ya kasa wani abin daban.
A daren ranar ma dai da gudun ta shiga gida, ta laSe a bayan ?ofa ta daidaita nutsuwarta, sannan ta shiga cikin gidan, dan haka babu wanda ya gane halin da take ciki.

Da safe kuwa tamkar ta ce "Ba za ta je makarantar bokon ba, ko ta ce Yaya ya rakata. Yau ma sai da ta makara sannan ta fita, amma kamar yadda ta yi tsammani, yana jikin gidan da yake kallon nasu, ya zubo wa ?ofar gidan su ido kamar mai jiran tsammanni.

Babu shiri ta koma cikin gidan, tana Sata fuska da rarraba ido.

Yaya ya ce "Wai me yake damunki ne? Kin makara fa mene ne haka ne?"

Kawai ta fara hawaye "Wallahi Yaya mutumin nan kullum sai na gan shi, tsoro nake ji, na fara tunanin ko gamo na yi ma nikaWai nake ganinsa, ni tsoro nake ji"

Cikin rashin fahimta ya ce "Gamo kuma? Wai wane ne? Wane mutumin ne?"

Nan Alina ta sake yi masa bayani, tun ranar da ta fara ganinsa.

Tamkar zai dake ta ya ce "Kuma shi ne baki gaya mini ba, uban waye mu je ki nuna mini shi"

Anty Nadiya ta ce "A'a Masoyi, ka tsaya a bi a hankali"

"Ba ruwanki" ya yi maganar yana kallon Nadiya a hasale.

Ya tasa Alina a gaba suka fita.

Ko da suka fita, suka tarar da shi a zaune, yana ta kokowa da wani takalmi zai yi masa round ya gyara shi. Yaya Ismail bai jira komai ba, ya yi fatali da kayan gayarn takalimin matashin, ya dam?i kafaWarsa ya tashe shi tsaye.

"Malam waye kai? Meye haWinka da yarinyar nan ka ke bibiyarta?" Ya yi maganar yana nuna masa Alina.
Ya kalli Yaya ya kalli hannunsa da ya ri?e shi, ya juya yana kallon Alina da ta yi tsuru-tsuru, tana rarraba ido kamar a ce kyat ta gudu.

"Waye kai malam?" Yaya ya ?ara maganar cikin Waga murya, yana ?ara ri?e kwalar mutunin.

"Wallahi ni ba kowa ba ne, kuma ba bin ta nake yi ba" Ya amsa da wata dakakkiyar murya, mai cike da nutsuwa da kamala, tamkar ba daga gangar jikinsa mai Wauke da wannan yamutsatsun kayan maganar ta fito ba.

"?arya ka ke yi, kusan sati biyu kenan, tana maganar wani yana bin ta, mene ne ala?arka da ita, idan ma wani abin ne a ranka, ko mugun nufi ne da kai a kan yarinyar nan, wallahi wani abin ya same ta, sai ka zubar da hawaye a kan matakin da zan Wauka a kanka na gaya maka"

Jiki a sanyaye ya ce "Ka yi ha?uri dan Allah, wallahi ni babu abin da zan yi mata" Ya yi maganar yana Waga hannunsa alamar saranda.

Tuni mutane suka fara taruwa, suna tambayar ba'asin abin da ya faru. Maigidan da mutumin yake zaune a Wakin langa-langar da ke ?ofar gidansa, ya fito yana tambayar hayaniyar me ake yi, aka taru a ?ofar gidansa haka?

Yaya Ismail ya ce "Rana tsaka mun ga mutum yana kwana a ?ofar gidanka, ba tare da mun san waye ba, yana bin Alina, bamu san daga ina yake ba, wallahi aka yi mata wani abin daga kai har shi ba za ku ji daWi ba. Dan mummunan mataki zan Wauka a kanku baki Waya"

A rikice mutumin ya kalli matashin mai gyaran takalmi ya ce "Me ka yi mata, meyasa ka ke bin ta?"

A rikice ya ce "Wallahi ba bin ta nake yi ba, hanya ce kawai take biyo da ni, sai ta yi zaton bin ta nake yi, amma ba bin ta nake yi ba, ni wucewa kawai nake yi"

Mutumin ya sassauta muryarsa ta ce "Kana ji malam Isma'il, dan Allah ka yi ha?uri,? wannan da ka ke gani, almajiri ne kawai ya Wan zo ci rani ne, aka ro?i na ba shi dakin nan na masu gadina tun da babu kowa, ya zauna tun da yanzu ba ni da masu gadi, kan ya samu gurin zama, amma ina da ya?inin mutumin kirki ne, ba zai cutar da kowa ba. ?alibin Alqur'ani ne"

Yaya Ismail ya sakar masa wuya, yana zazzare ido, tare da yi masa wani irin mugun kallo.
Yana sakinsa matashin ya dur?usa yana tattaro kayan gyaran takalminsa, da Isma'il ya yi fatali da su. Gaba Waya sai jikin Alina ya yi sanyi, ta yi dana sanin gaya wa Yaya Ismail, ba ta ji daWin yadda ya Wauki abun da zafi har haka ba. Sai ta ga kamar mutumin ya muzanta da yawa.
Ya ce "Gara dai da na yi magana, tun da mu bamu san wane iri bane kawai ka kawo shi ka ajiye, babu bayani. Wallahi duk abin da ya faru ba zan lamunta ba"

Alhaji Sadi ya ce "Da yardar Allah babu ma wani abu da zai faru sai alkhairi, in sha Allah"
Ismail yadube ta ya ce "Wuce muje" ya ri?e hannunta suka yi gaba, ta waiwaya ta ga ma?wabcin nasu na yi wa mai gyaran takalmin magana, yayin da shi kuma yake ?arasa harhaWa kayan sa da Yaya Ismail ya watsar, Ya Wago suka haWa ido ita , ta yi saurin kawar da kanta suka shiga gida.




SARA DA SASSA?A
AYSHERCOOL


BRIGHT PENS
YOTA 002

Arewapen ayshercool

Page 3

Da sauri ya sunkuyar da kansa, sai dai sa?on da ya aika mata ta idanunsa, sun yi tasiri jikinta ya yi sanyi, har ta Wan rasa nutsuwarta. Da sauri ya tashi ya kwashi kayan aikinsa da ya tattare, ya shige Wakin da yake kwana ya rufo ?ofar.
Gaba Waya sai Alina ta ji babu daWi, a ce babba kamar wannan, Yaya Ismail ya yi masa tijara a gaban mutane, har sai da fuskarsa ta nuna yanayi na damuwa, sai ta ji sam ba ta ji daWi ba, har ta ji dama ba ta gaya wa yayan ba.

*****

Ramata na tsugunne, tana ta aikin wanki, yayin da Juma ke ?o?arin tu?a tuwo, Baffa ya yi sallama. Suka amsa masa gaba Waya. Ramata ta yin?ura ta tashi ta je ta karSi kayan hannunsa.
Juma ta kalle shi ta ce "Sannu da zuwa"

"Yauwwa sannu da gida"

Bayan Ramata ta ajiye kayan ta ce "Baffa sannu da zuwa"

Baffa ya ce "Yauwwa Ramatuna autar Baffa, Ubangiji Allah ya raya mini ke, ya sanya rakiyarmu ta yi tsawo tare"

"Amin Baffana" Ta yi maganar cikin murmushi.

Juma ta ce "Nima Allah ba mantawa ya yi da ni ba, da bai bani haihuwa ba, da kullum sai ka saka Ramata a gaba ka na ce mata 'yar auta, domin ka goranta mini"

Baffa ya kalle ta ya Wan Sata fuska ya ce "Haba Juma ya za a yi na yi miki gori ma, ke ce dai ki ke tunanin haka, amma ni ban yi miki gori ba" Juma ta tsuke fuska tare da yi masa banza.

Bayan ya zauna a kan tabarma ya buWe Waya daga cikin ledojin da ya zo da su ya ce "Ramatu, ga man shafawa da man wanke baki, da sauran abubuwa na shirye-shiryen komawarki makaranta na fara sayo miki, sati mai kamawa za ki koma ko?"

Cikin farinciki ta ce "Eh Baffana. Baffa kana yi mini addu'a ko? An kafe jarrabawarmu fa"

Baffa ya ce "Ba nima na gaya miki na ji a radiyo, an sako jarrabawar ba? Ai Allah ba zai kunyata mu ba Ramata, in sha Allah sai kin zama abar alfahari da kwatance a garin nan"

Ramata ta ce "Allah ya amince Baffa. Amma Baffa zan ci gaba da karatun kuwa?"

Baffa ya Wan yi shiru sannan ya ce "Ramata zan so hakan, domin shi ne cikon burina. Amma kina kallon tambarin da aka yi mana a garin nan, saboda karatun da ki ke yi. Ni na san ko iya haka ki ka tsaya Alhamdillah kwalliya ta biya kuWin sabulu. Amma idan Allah ya kawo damar ki yi karatun, ko bayan raina ne, zan bar wasiyya a abin da na bari, a ware wanda za a biya miki, ki ci gaba da karatu, ko ma ni ma ware da kaina.

Juma ta juyo ta zuba masa ido, daga bisani ta taSe baki ta ce "TaSWi abin na yi ne ashe"

Ba su kula ta ba, Baffa ya sake cewa "Ramata ga wannan saiwoyin, ki dafa su da kyau, gobe in Allah ya kaimu zan je duba mara lafiya"

Ramata ta yin?ura ta tashi tana faWin "To Baffa"

*****

Alina ce ta shigo da sallama, ta Wora da cewa "Anty na dawo"

"To sannu da zuwa, ya makarantar?"

Alina ta amsa da "Lafiya ?alau, Yaya bai dawo ba?"

"Ban da abin ki Alina, dama yana da ?a'idar lokacin dawowa ne? Amma dai Wazu ogansa ya kira shi, zai je ya dubo masa wasu kaya, ya ce idan bai dawo ba, mu rufe ?ofa wata?ila sai Allah ya kaimu gobe"

Alina ta Sata fuska ta ce "Ni wannan ogan nasa ya fiye matsala, ni ba na son wannan aiken da yake yi masa"

Nadiya ta yi murmushi ta ce "Kin fiye rigima ke kuma ba. Alina shi ne babban yaronsa, duk sauran cin amanarsa suke yi. Kuma idan bai je aiken ba da me zamu rayu, tun da a ?ar?ashinsa yake nema"

Jiki a sanyaye Alina ta ce "Antynmu tafiye-tafiyen nan ne da yake yi fa ba na so"

Cikin mamaki Nadiya ta ce "Saboda me?"

"Ba na son bin manyan hanyoyin nan, ba na son ya yi hatsari"

Da sauri Nadiya ta ce "A'uzubillah, wace irin magana ce haka Alina?"

Tuni idanun Alina suka cika da hawaye ta ce "Kullum ya yi tafiya hankalina ba ya kwanciya sai ya dawo, ina jin tsoron ya yi hatsari wataran a hanya. Duk ranar da aka ce babu ke ko Yayana a duniya ya zan yi?" Ta yi maganar hawaye ya wanke mata fuska. "Na san dole hakan za ta faru watarana, amma b a na fatan ku riga ni barin duniyar nan, Allah ya sanya zamu daWe tare"

Nadiya ta ce "Alina, shi ajali ba sai na kan titi ko na cikin Waki ba, yana iya faruwa a kan kowa, sai dai mu yi addu'ar Allah ya sanya rakiyarmu ta yi tsawo tare da juna, kamar yadda ki ke fara. Bari a yi sallar magariba, sai na kira miki shi ki ji muryarsa" Alina ta jinjina kai tana share hawayen fuskarta. Ta nufi Wakinta Nadiya ta bi ta da kallo, har ta shige,? sannan ta yi ajiyar zuciya ta ci gaba da abin da take yi.

Washegari da yamma, Yaya Ismail ya dawo gida, Alina ta rirri?e shi tana murna har da hawaye. Nadiya ta ba shi labarin abin da Alina ta yi jiya, da ta dawo ta tarar baya nan.

Ya kalli Alina, cike da matsananciyar ?aunarta ya ce "?anwata, da gaske ki na tsoron na mutu na bar ki?" Ta jinjina masa kai cikin damuwa.

"Aikin gama ya gama, mutuwa dole ce Auta"

Cikin kuka Alina ta ce "Dan Allah ka daina faWa ba na so, dan Allah ka gaya wa oganka ya daina yawan aikenka guri mai nisa ?anwarka tsoro take ji"
Rungume Alina ya yi yana murmushi tare da rarrashinta. "Babu abin da zai faru sai alkhairi, idan na zauna da ya ya zan kula da ku? Ki yi ha?uri ki din ga yi mini addu'a kin ji ko?"

Ta jinjina masa kai, ta share hawayenta ta ce "Bari na je na shirya, na gaya wa Anty zan je sayo cardboard paper, zan yi assignment"

Ya ce "To a dawo lafiya, ta baki kuWi ko na ?ara miki?"

"?ara mini" Ta yi maganar tana mi?a masa hannu. Ya yi dariya ya zura hannunsa a aljihu, ya ciro Wari biyar ya bata.
Bayan fitar Alina, ya dubi Nadiya ya ce "Masoyiyya ya dai?"

"Alina fa yanzu ba yarinya ba ce ba, lokaci kaWan ya rage ta shiga shekara goma sha biyar" Ta yi maganar tana tsuke fuska.

Cikin rashin fahimta ya ce "To meyafaru?"

Nadiya ta ce "Ina maganar rungume ta da ka ke yi, wannan ba dai-dai ba ne ba, ba abu ne da ya dace ba"

Ya ?are mata kallo ya ce "To abin ya motsa kenan, shaiWan zai yi miki kururuwa"

Ta girgiza kai ta ce "ShaiWan bai yi mini kururuwa ba, ina dai gudun kai ya yi maka ne"

Ya shafa sumar kansa ya dube ta ya ce "Nadiya, ?a'idar ba za ta canza ba, a kan Alina, zan iya lalata komai ciki har da ?a'idar, shi kansa shaiWai Win ya san na fi ?arfin ya yi mini kururwa a kan Alina. Alina ?addarata ce, kuma jarrabawata. Kin san bawa ba ya gujewa ?addararsa, a ?o?arin gujewa ?addarar mutum ka iya halaka ba ki Waya. Dan haka dole ki yi ha?uri ko domin gudun halaka. Nadiya ta dube shi cikin ?unar rai, amma ta yi shiru ba ta sake cewa komai ba.

Kasancewar ba a daWe da idar da sallar la'asar ba, rana ba ta gama yin sanyi ba, balle masu zaman majalissa su fara bin dakali da tebura su na zama.

Alina na fitowa hanya, ta tarar da shi a tsaye a bakin titi, hannunsa rungume da bagco yana ?o?arin tsallakawa, su na yin ido huWu, cikin azama ya yin?ura zai tsallaka titi, dan yanzu kamar tsoron ganinta ma yake yi tun da Isma'il ya tijara shi a gaban mutane. Yana ?o?arin tsallakawa wani matashi ya taho a kan babur da gudu, ya buge shi. Take ya faWi, bagco hannunsa ma ta faWi, yalo ne fal a cikin bagcon, aikuwa ya watse a ?asa, a kan ?aramin titin cikin unguwar. Matashin da ya buge shi kuma, ya ja baburinsa ya zura da gudu, ba tare da ya tsaya ba
Da sauri Alina ta bi yalon da gudu, ta fara tsintowa, tana sakawa a hijjabinta, saboda yadda suke ?o?arin shiga kwata. Sai da ta tsince su tsaf, sannan ta? nufo inda yake, a Wan tsorace ta ce "Sannu" sau Waya ya kalle ta, ya sunkuyar da kansa ?asa.

Ta Wauki buhun, ta tattare ta zuba masa a ciki. Ta sake cewa "Sun Saci da ?asa sai dai ka wanke. Still ya yi shiru bai ce komai ba. Sai ta fara tunanin ko kurma ne. Sai kuma ta tuna ranar da Yayanta ya je yana yi masa faWa a kanta ya yi magana.
Ta sake cewa "Ko ba zaka iya tashi ba?" Bai Wago ba ya yin?ura a hankali ya tashi tsaye. Sai dai ya ji rauni a babban yatsansa na ?afa farcen ya Wago, sai zubar da jini yake yi. Da sauri ta yamutsa fuska saboda ba ta ?aunar ganin jini, yanzu hankalinta zai tashi.
Ya mi?a hannu zai karSi bagconsa, ta girgiza kai ta ce "Muje na kai maka" Bai sake magana ba, ya Waga ?afarsa ya fara takawa a hankali. Da kyar yake taka ?afar, saboda ya bugu, ga jini na zuba. Gaba Waya sai tausayinsa ya mamaye ta, da ta kalli ?afar sai ta yamutsa fuska ta kawar da kanta gefe.

Tana tafe yana biye da ita, ta ja ta tsaya ta ce "Laa ka ga chemist Win Albarka ya fito, muje ya duba maka, ko jinin zai daina zuba kar jininka ya ?are ko tetanus ta shiga ciwon, duk da kwalta ce ba ?arfe ba. " Ta yi maganar tana nuna ?ofar shagon. Ya Wan kalle ta, yadda take magana Allah ya hore mata iyayi. Daki-daki take maganar tana demonstration, dai 'yar siririyar muryarta mai kauWi tamkar tsuntsuwa.

Kansa a ?asa ya basar ya ce "Ba ni da kuWi"

Ta ce "Mu je da kuWi a gurina"

Bai sake cewa komai ba ya bi bayanta.

Da sallama ta shiga, mai chemist Win na ganinta ya hau murmushi. "Alinan Yaya, ina Yaya?"

Ta yi murmushi ta ce "Yaya yana gida. Dan Allah ka duba masa ?afarasa babur ne ya buge shi, kuma ya gudu"? Mai Chemist ya tashi yana faWin Subhanallah.

Ya dudduba ciwon sannan ya wanke masa ciwon, ya yi masa allurai, da magunguna.

Alina ta ce "Nawa?"

"Dubu uku da Wari biyu" ya bata amsa.

Ta waro ido ta ce "Dan?ari, to ka sakawa Yaya a cikin lissafinsa"

Mai chemist ya ce "To amma ki yi masa bayani"

Ta ce "Zan yi masa in sha Allah"

Daga haka suka fito suka tafi, sai da suka je ?ofar Wakin da yake zama, ya tsaya yana kallon kayansa da ke hannunta, bai ce ta ba shi sai kallonta da yake yi.
Ta mi?a masa ya karSa, ta ce "Ko na kawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login