Showing 30001 words to 33000 words out of 53964 words

Chapter 11 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

776

ya gaya mata. Ji ta yi tana son ta haWu da Hanne ko ta halin ?a?a. Litattafan da suke gabanta ma, sai ta ture su a gefe, ta nemi guri ta kwanta saboda ba ta jin dadin komai.

Sai dai tana Warsa batun son Bukar a zuciyarta, sai mutumin nan ya bujiro mata, ya mamaye ko ina.

*****

Mariya na zaune tana goge uniform Win ta na Islamiyya.
Mama ta dube ta ta ce "Mariya, dan Allah idan kin je, ki ba wa malam ha?uri, in sha Allah a satin nan za ki kai kuWin makarantar ya ?ara ha?uri"

"Tom zan gaya masa in sha Allah"

Hafsa ta shigo Wakin da sallama tana cire hijjabinta.

Mama ta amsa ta dube ta ta ce "Yaya?"

"Na fita kenan Yaya ya kira ni, ya sako mini dubu uku, ya ce mu yi ha?uri mu lallaSa, ya je wa Naja visiting shekaranjiya ba kuWi a hannunsa"

Mama ta ce "Hafsa ba dai gaya masa ki ka yi cewa bamu da komai a gidan ba?"

"Haba Mama kema kin san ba zan gaya masa ba. Dama ba son zuwa gurin Kawu Babballen nan nake yi ba, da an taSa shi shi ma cewa zai yi ba shi da shi, mu je yaya ya bamu"

Mariya ta ce "Ya ma haWa ka da masifa ma"

Mama ta ce "Allah sarki yaron kirki, Ubangiji Allah ya tsare mana shi, ya yi masa jagora. Allah dai ya saka masa da alkhairi. Mariya kan ki tafi makarantar nan karSo mana gari kowa ya sha, mu cancana kuWin"

"To Mama" Haka ta ci gaba da yi musu addu'a da fatan, Allah ya haWa mata kan su.

Mi?a ya Wan yi, idanunsa jawur saboda gajiya, ya cire bindigarsa ya ajiye yana duba wayarsa.
"Haris yane? Ka zo mu je cin abinci, rana ta yi fa"

"Oga Suleiman ka je kawai, bacci nake ji ne"

"Kai Haris, bacci a yanzu, shikenan bari na je"

Haris yana jin yadda cikinsa yake ?ugi, saboda yunwar da yake ji, amma ya rage kayan jikinsa ya nemi guri ya kwanta.

*****

Alina ce ta yi shiru tana tunanin da gaske Mamman ya zo, ko kuwa mafarki ta yi? Cikin kulawa Yaya yake ta jera mata sannu cike da kulawa.

Ta jinjina masa kai, tana ?ara ri?e hannunsa a cikin nata.

"Sannu Alinan Yaya, Ubangiji Allah ya yaye miki wannan ciwon kai, ya yi miki maganinsa"

Suka amsa da Amin.

"To yanzu ya ki ke ji?"

Ta Wan yi shiru ta ce "Kan ya daina ciwo, ni yanzu mu tafi gida kawai" Ta yi maganar da sigar magiya.

Ismail ya ce "A'a ki yi ha?uri ya ?ara sakinki tukuna"

Ta kwaSe fuska ta ce "Yaya gobe in Allah ya kaimu Asabar, idan ba a ji karatuna ba, makina zai iya yin ?asa a cire ni daga cikin yan sauka"

Nadiya ta ce "Alina ai larura tana gaban komai, ki bari dai mu gani"

Ta shagwaSe tana yi musu magiya.

Ismail ya ce "Ina ganin hakan za a yi, tun da haka take so. Bari na je na ji nawa ku ka ci"

Nadiya ta ce "To shikenan"

Ya fito reception, suka gaggaisa da ma'aikatan, kasancewar sun san shi sosai, patient Win su ne, mussaman saboda yawan rashin lafiyar Alina.

Ya ce "Hajiya duba mini file Winmu, nawa ku ke bi na, nawa Alina ta ci?"

Aka ciro file, ya sake cewa "I??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????na ga wancan karon bai fi dubu uku ce ta yi saura a file Win ba"

Matar ta Waukko file ta duba, ta kalli Ismail ta ce "Ai ba a binku ko sisi, kun biya"

Ismail ya ce "Hajiya ya idon ne? Duba dubu uku ce a cikin file Win, sun kawo Alina kwanansu biyu yau. Ki ga nawa suka ci na saka muku yanzu" Ya yi maganar yana daddana wayar hannunsa.

"Da gaske fa nake, an biya har da canjin dubu talatin a file Win." Ya kalle ta, ya ja file Win gabansa ya fara dubawa. Shekaranjiya ranar da aka kai Alina Asibiti aka saka kuWi dubu saba'in a file Win, kuma da sunansa a saka. Ya yi shiru.
Ya kira Nadiya a waya, ya ce ta zo reception. Ba a jima ba sai ga ta ta iso.

"Masoyiyya, waye ya biya kuWin Asibitin Alina?"

Nadiya ta ce "A'a ba a biya ba"

Ya ce "To zo ki ga"

Ta ?arasa ta kalli file Win, ta ce "Gaskiya ba su biya ba"

Aka kira wayar wanda ya yi duty ranar, ya ce ta POS kawai ya ga transfer, ya ga sunan Isma'il a jiki, da narration, dan haka ya yi setting bills Win.

Ismail ya yi shiru yana tunani, bai sake cewa komai ba, ya ce Nadiya ta haWa kayanta su tafi.

*****

Babbar mace ce, za ta shekara Arba'in da uku, ta sha kwalliya, ta fito katafaren falonta, ta yi turus ta Wan tsaya tana kallonsa.

"Baba Mai Kano saukar yaushe?"

"Ko na koma ne?" Ya yi maganar yana Wan kallonta.

Ta gyara zaman gilashin fuskarta, ta ce "Wane mutum inji mutuwa, barka da sauka"
Bai amsa ba ya nufi fridge, ya buWe ya Wauko coc mai sanyi, ya Wauki glass cup, a saman fridge Win, ya zuba ya sha. Ya dawo falo ya zauna. Ya dube ta ya ce "To kina lafiya?"

"Mmm ba gani kana gani ba, Alhamdillah na godewa Allah"

"Ya jikinki fa?"

Ta yi murmushi ta ce "Alhamdillah"

"Allah abin godiya. Amm na ce duk takardunki masu muhimmanci su na nan a ajiye inda na sansu ko?"

"Eh me za a yi?" Ya mi?e tsaye ya ce "Abu nake nema"

Ta dube shi ta ce "Me za ka yi ne?" ya yi gaba cikin hanzari ba tare da ya ce komai ba.

"Mai Kano me za ka yi ne wai? Kai ba ka zo gurin mutum ba, a yi ta maka magana ka mayar da mutum iska, ba za ka amsa ba"

Ya shige bedroom Win ta, wardrobe ya buWe, ya din ga duddubawa ya ciro wata takarda, ya din ga kallon takardar a tsanake, daga bisani ya tashi ya mayar da wardrobe Win, ya fito falon ya tarar da ita a zaune, da remote a hannunta, tana canza tasha.

"Sai anjima" Ya furta yana nufar hanyar fita.

"Ina fatan baka hargitse mini Waki ba?"

"Ki saka a gyara miki" Ya yi waje da sauri.

BAYAN KWANA HU?U.

Tun daga nesa ya zuba mata ido, har ta shigo cikin kantin nasa.

Guri ta samu ta tsaya tana hararsa.

"'Yar ?walisa, ya aka yi ne, ya jikin?" Ta murguWa baki ta yi shiru.

Ya fito daga cikin kantin, ya zauna a gefenta a kan bencin da yake ciki.

"Me na yi miki ne?"

"Sau Waya ka zo duba ni, baka sake nema na ba?" Ta yi maganar tana tura baki.

Ya yi murmushi ya ce "Ki yi ha?uri, tsoron yayanki nake ji, kin san ba ya son ala?ata da ke, amma kina raina na damu sosai da sosai, kamar na cire miki ciwon".

"Ba wani nan" Ta yi maganar tana zumSura baki.

"Da gaske nake 'yan matan Yaya"

Ta Wan Wago ta saci kallonsa, ya kashe mata ido, kawai ta hau dariya. Shi ma ya yi dariyar. Ya ce "Kin rame sosai, me yake saka miki ciwon kai haka?"

Ta gyaWa kai ta ce "Nima ban sani ba, tun ina ?arama, wani Likita dai ya ce Magrine headache sunan shi. Ka san ranar da ka zo duba ni Win nan, bayan ka tafi...

Ya katse ta da cewa "Waye ya zo duba kin?"

"Kai mana, lokacin da ina Asibiti fa"

Ya girgiza kai ya ce "A'a ban zo ba"

Ta yi saroro ta ce "Ka zo mana, na manta kalar kayan da ka saka, amma ka manta ka zo. Har ka kawo mini yoghurt"

"Ta yaya zan zo bayan yayanki yana yi mini kashedi a kanki"

Cikin mamaki Alina ta kalle shi, ta Wan dafa kanta ta ce "To mafarki na yi kenan? Har ka Waga ni zaune fa, lokacin Antynmu ta je sayo mini magani"

Ya ce "Anya kin gama warkewa kuwa, ko dai a koma Asibitin nan? Gaskiya mafarki ne, yanzu me zan Waukko miki da za ki ci?"

Ta girgiza kai ta kasa cewa komai, saboda mamakin da ya cika ta.

Ta tashi tsaye ta ce "Ni ba na son cin komai, ga wannan" Ta yi maganar tana ba shi leda.
Ya saka hannu ya karSa yana faWin "Me na samu?" Ya buWe ledar ya fito da abin da yake ciki.
Hankici ta sa?a mai kyan gaske, ta sa?a shi fari da ja, ta rubuta ?an albarka, sai kuma hular sanyi ita ma ta rubuta Wan albarka a jiki. Sai uban ?amshi suke yi. Sosai yake murmushi, ya Wago ya kalle ta, ya tsare ta da idnaunsa, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "'Yar ?walisa, wannan duk nawa ne?"

Ta ce "Eh, ka din ga canza hula, tun da na ga kullum da hula ka ke zama, ko ka na da san?o ne?" Ta yi maganar tana dariya.

Kawai ya yi wata 'yar gajeriyar dariya, jin abin da ta faWa. Ya cire hular kansa, kansa cike da suma ya ce "Ba ni da san?o, ina dai saka hular ne ina rufe kaina"

"Eh na gani ka bani gyaWa zan koma gida na yi bacci, magungunan nan bacci suke saka ni, duk su kashe mini jiki"

Ya mi?e ya Waukko bokitin gyaWar ya ce "?auki iya wadda za ta ishe ki"

Ta Wauki ?ulli biyu ta ce "Wannan ta isa"

Ya kalli kantin, ya dube ta ya ce "Sai kuma me zan baki?"

Ta girgiza kai ta ce "Wannan ta ishe ni"

"Kai 'yan matan, na rasa me zan ce miki ne ma gaba Waya, amma na gode sosai da sosai Lina, Thank you in ji turawa. Nima yakamata ki din ga koya mini turancin nan"

Ta ce "To shikenan, zan din ga koya maka, amma ka daina wannan godiyar ta yi yawa. Ai ba zan biya ka Wawainiyar da ka ke yi da ni ba"

Ya saki murmushi ga ta yarinya sai manyance, da iya tsara magana.

Ya Wan lumshe idanunsa, yana nazartar fuskarta. "Ke ki ke Wawainiya da ni ai, ki bani abinci, ki taya ni hira, ga kyauta kin bani, kuma... Sai kuma ya yi shiru.

Ta Waga kai suka haWa ido, ta yi saurin sunkuyar da kanta ?asa.

"Sai ka ce na baka wata duniya, ai ba yawa,na gode nima" Ta fice daga kantin, tana tafiya a hankali. Ya zura mata ido, har ta Sacewa ganinsa.

*****

"Sadauki"

"Allah ya taimaki Madugu"

"An gama saita komai?"

"Na gama Madugu, umarninka kawai muke jira"

"To ku jira ni daga yanzu zuwa kowane lokaci, ku saurare ni, ina jiran a gama gyara mana hanya ne, saboda ba a son kuskure a aikin, sama ta ka zamu kai mamayar"

Sadauki ya ce "Allah ya bar Kacalla Sumale, kai mu ke saurare"

"Good"

*****

Sosai ya zuba wa kayan da Alina ta ba shi ido, yana murmushi.
Ya din ga jujjuya hular, ta sa?u sosai da sosai, sai ?amshin turare take yi, ga handkachief Win ma ya yi kyau sosai, har beza ta yi masa da wani abu mai ?yal?ali. Ya kai hancinsa ya sha?i ?amshin turaren da suke yi, irin wanda take yi ne. Ya yi murmushin gefen baki, ya haWe su a guri Waya, ya Waga ?asan kayansa ya saka su.

*****

YELWA

Tarin makiyaya ne maza, dattawa da matasa, su na zazzaune, a kan wata ?atuwar tabarma, su na tattaunawa.

Moddibo da ya kasance shi ne jagora a Sangren makiyayan garin, ya yi gyaran murya yana magana "To tunatarwa ce dai da muka saba yi duk shekara, yanzu ma ga mu mun zo da ita.
Mun san wasu za su dawo da dabbobi gida, wasu kuma za su fita da su. To ga kuma labarai marasa daWi da muke samu, ga kuma rigimgimun cikin garin nan. Saboda haka nake ro?onku, duk inda za ku je, ku kasance mutanen kirki, duk inda ku ke ku wakilan makiyaya ne, makiyayi kuma ba a san shi da tashin hankali da neman rigima ba. Domin girman Allah ku kula da dabbobi, kar su shiga su yi wa kowa Sarna. Sannan wanda za a bari a gari, kuma ina ro?on waWanda za a bari a gida, kowa ya kula da dabbobinsa, kar ya bari su shiga gonar wani su yi Sarna.
Hausawa sun ce; kowa ya kwana lafiya shi ya so. Kun san mutanen nan sun fi ?arfinmu ta kowacce fuska, tsokanarsu ko neman rigima da su, ba zai haifar mana da Wa mai ido ba. Mu na sane da tabon da yake zukatanmu, na cutarwa da suke yi mana, da har abada ba zamu warke ba, dan haka kowa ya kula dan Allah"
Duk suka amsa masa da In sha Allah. "Ko akwai mai magana"

Baffa ya Waga hannu, Modibbo ya ce "Mu na saurarenka Jibo"

Baffa ya mi?e ya ce "To 'yan uwana Assalamu alaikum, ni Worawa zan yi abin da ka faWa. Mu na jin yadda al'amuran rikicin manoma da makiyaya ke komawa wani abu daban. Duk ma'abocin jin radio, ko wanda yake shiga birni, na san yana da labarin hakan. Saboda haka nake sake ro?onmu mu ?ara kulawa sosai, dan kamar jira suke yi wani abin ya haWo mu ma su far mana. Sannan duk wani abu da muka gani ba?o da bamu yarda da shi ba, mu sanar da junanmu...

?an uwan Baffa? ya ce "Dan Allah Modibbo, idan an gama taron nan mu tafi, ya tashi sai iyayi yake yi mana. Koma mene ne ba Wanka ne yaje ya tsokane su ba, ya ?ara tayar mana da tsohuwar gabar nan ba, da bai je inda 'yarsu take ba, ai da abin bai ?ara tsauri ba."

Wani a gefe ya ce "Gaskiya ne, yo mutumin da bai iya kula da gidansa ba, ya Wauki yarsa ya kai wata uwa duniya ne, zai wani tashi yana mana surutu da sunan shawara?"

Sai jikin Baffa ya yi sanyi. Maddibo ya tsuke fuska ya ce "Jatau, Iro meye haka? Iro da aka kashe mana, ai ba Jibo kawai aka yi wa ba, mu aka yi wa. Kisan gillar da aka yi masa zuriyar makiyaya aka yi wa. Kuma ba domin mu na son zaman lafiya ba sai mun bi kadin jinin iro. Batun kai Ramata birni wannan abu ne da shi ya shafa. Mu na jinka Jibo ci gaba da magana"

Baffa ya girgiza kai, fuskarsa Wauke da murmushin ?arfin hali, ya ce "Ahh dama shikenan maganar tawa, na gode" Ya nemi guri ya zauna yana ya?e.

****

"Vice"

"Ranka ya daWe"

Ya yi taku biyu da sanda a hannunsa, ya nemi guri ya zauna, ya Waga idanunsa, ya saka a cikin na kan Kangiwa.

"Na san ka san faWin tashin da muka yi, muka kawo ku kan mulki ko?"

"Na sani Allah ya baka yawan rai"

"Masu iya magana sun ce, Wan halal baya manta alkhairi, sai dai farawa da bismillah, Kankiya yana ?o?arin nuna mana, an tura motar zai bule mu da haya?i, ba tare da sanin direban da yake tu?in motar namu ne ba. Tun da ya nuna zai mana butulci, ba zai yi mana biyayya ba, zamu yi masa yaren da zai gane. Idan ka amince ka bamu haWin kai Wari bisa Wari, zamu mayar da shi fanko, ka jagoranci ?asar, zuwa lokacin zaSe mu hankaWe shi, kai mu Wora ka."

Cikin mamaki yake kallon Makama, murya na Wan rawa ya ce "Ta yaya hakan zai faru ranka ya daWe?"

"Wannan aikinmu ne, kai dai ka zama mai biyayya kawai, idan ba haka ba daga kai har shi, zaku rasa zamu nemo wanda za mu tsayar, dan ba za ku yi tazarce ba, dabara ta rage ga mai shiga rijiya. Idan ka shirya ka amince, zamu hargitse ?asar kai kuma ka ji da sauran...

Ayshercool
08081012143





SARA DA SASSA?A...
YOTA 002
P10
AYSHERCOOL


Kangiwa ya yi shiru yana lissafa maganganun a cikin zuciyarsa.

Ya jinjina kai a hankali ya ce "Shikenan, zan je na yi shawara"

"Ina saurarenka"

Kangiwa ya tashi sumi-sumi ya fice.

Ya zuba lemo a kofin gabansa, ya Wago kofin ya kai bakinsa yana zu?a a hankali, yana jujjuya lemon a kofin yana kallon katafariyar talabijin din da ke cikin Wakin.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya Wauke ta a gefensa, ya kalli lambar bai santa ba, ya dai Waga ya kai kunnensa ya yi shiru bai yi magana ba.
Jin an yi shiru ya sanya shi cewa "Waye a kan layi?"

"Kacalla Sumale"

Da sauri ya ajiye kofin hannunsa ya ce "Yaya ake ciki ne? Mu na ta nemanka a waya ba mu samu ba, kai fa muke jira"

"Ba na gaggawa a aikina, ya?in sun?uru ka ce a yi, dan haka kar ka shigar mini aiki." Cikin mamaki mutumin ya buWe baki, jin yadda ba?auyen Wan ta'adda yake yi masa magana gatse-gatse.

"Ba zan ci gaba da ?addamar da hari ko ta ina ba, nima aikina lissafi nake yi. Na kira ka ne na jaddada maka na kuma ja maka kunne, kar ka kuskura ka saSa yarjejeniyar mu. Kuma ka ce za ka kula da Sangaren kwaWin nan, idan aka kashe mini mutane, ko aka kama wani zan yi fyaWar 'ya'yan kaWanya ne, har iyakar da bai kamata ba sai na ci. Kuma wannan kwantiragin, ko a mutu ko a yi rai ne, ka tabattar ka kula da Sangarenka. Idan da wani abu, ko kana nema na, ka tuntuSi Sadauki... ?it ya kashe wayarsa.

*****

"Masoyiyya" Ismail ya kira Nadiya.

"Masoyi"

"Jikina yana bani wani abu"

Cikin rashin fahimta ta ce "Wani abu me kenan?"

"Haryanzu ina mamakin wanda ya biya kuWin Asibitin Alina kuma da sunana, wannan ya tabattar mini da akwai wani abu a ?asa"

Nadiya ta ajiye ninkin kayan da take yi, ta dube shi ta ce "Nima dai abin ya Waure mini kai, sai dai bana tunanin akwai wanda zai din ga bibiyarmu, saboda me ma to za a bibiye mu, ni nafi tunanin ko mistake aka samu"

Ya yi dariya ya ce "Mistake? Ba kuskure ba ne, wani abu ake ?o?arin gaya mini da hakan. Ina tunanin Alina na yin sauka, zamu bar garin nan, shi ma dan na ga yadda ta ?allaffa ranta a kan saukar Alqur'anin ne. Kawai ina jin akwai matsala zamanmu a nan"

Nadiya ta ce "Amma duk shekarun da muka yi, ba a samu matsala ba, sai a wannan karon? Ina zamu koma?"

Ya ce "Alina, Saboda Alina dole mu bar garin nan, da daga ni sai ke ne, babu inda za mu je, tun da bamu takawa kowa ba, ba kuma mu zubarwa kowa ba a garin nan. Amma ba na son duk wani abu da zai kawowa ?wa?walwarta cikas, kin san me nake nufi ai"

Nadiya ta numfasa tare da sauke numfashi.

Ya sake numfasawa ya ce "Wai me mutuniyar ta sa?a ne, da ulun da ta addaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login