Showing 1 words to 3000 words out of 53964 words

Chapter 1 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

758

??????>??  l?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????h????

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?Root Entry???????? ?FmWordDocument?????
0Table????????*
Data
????????????????????? P???KSKS??
JV???????pp????]q??Y??








$u ?' *p??

????
Q ?qQ 
q
Q q

?q 

SARA SA SASSA?A...

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)

YOUNG TALENTED WRITE'S ASSOCIATION



P1

15 ga watan Ogusta, hadari ya yi ganganko a sararin samaniya, babu abin da ake iya gani face hasken wal?iyyar da hadarin yake ta yi babu ?a??autawa. Haka zalika babu abin da kunnuwa ke iya ji, banda sautin rugugin cidar hadarin nan.
Ri?e yake da hannun matashin yaron da hannu Waya, hannunsa Waya kuma ri?e da kaya, su na ta sauri, suna ratsa tsakanin zangarniyar hatsi, da ta yi tsawo, kasancewar tsakiyar damuna ne, amfanin gona ya fito ya yi kyau.
Da kyar yaron yake cira ?afafuwansa, duk da saurin da mutumin da ya ri?a masa hannu yake yi.
Zuciyarsa Wauke da wani nauyi da yake barazana ga numfashinsa, haka yake bin mutumin, yana jin kansa tamkar ba shi ba. Sannu a hankali yayyafi ya fara sauka kaWan-kaWan, a daidai lokacin da wal?iyya ta haska wata ragargajajjiyar hanya mai tarin kwazazzabai da da ramuka suka fito.
Mutumin ya kalli yaron, zuciyarsa na wani irin raWaWi, tamkar mai ci da wuta, raWaWin da yake tasowa daga zuciyarsa har ma?ogwaronsa yake ji, tamkar zai tsage,ya ja ya tsaya.
A raunane ya dubi yaron ya ce "Ka yi ha?uri, tun da na fito da kai hanya, maza ka yi sauri ka bar garin nan, kar ka bari gari ya waye su cim maka, ka dai ji abin da suka faWa da kunnenka. Idan Allah ya ?addara saduwarmu a gaba, sai mu sake haWuwa.
Ya dam?awa yaron ?ullin kayansa, sannan ya zura hannunsa a cikin aljihunsa, ya ciro kuWi ya dam?a masa.
"Ga wannan, maza ka ci gaba da tafiya, idan ka samu guri ka laSe kar ruwa ya dake ka"
Tun da ya fara maganar, yaron yake bin idanunsa da kallo ta cikin hasken wal?iyar da ake yi.
Jikinsa a sanyaye ya ce "Ka tafi sumale, kar su same ka" Ba tare da ya furta uffan ba, yaron ya juya ya fara takawa, bai fi taku biyar ya yi ba, ya tsaya ya waiwaya, ya ga mutumin ya kama hanyar komawa cikin ?auyen. Ya tsaya ya zuba masa ido, a dai-dai lokacin da ruwa mai ?arfin gaske ya Salle, ya fara zuba a jikinsa.
"Zan dawo, tabbas zan dawo, gobe, jibi, ko kuma gata? Ban sani ba, amma dai na san zan dawo" Ya furta yana haWiye wani raWaWi da yake yi masa Waci a ma?ogwaronsa.

*****

Gari ya yi tsit, babu abin da ke tashi, sai sautin kai komon ababen hawan jami'an tsaro, tituna babu kowa sakamakon dokar ta Saci da aka sanya, saboda gudun tashin tarzoma a daidai lokacin da ake shirin sanar da sakamakon ?arshe na zaSen shugaban ?asa. Galibi mutane na cikin gida, da radio wasu da waya wasu talabijin, wasu da na'urar buga lissafa, su na lissafin yawan ?uri'un da wanda suke so suka samu, su na dakon faWin sakamakon, daga hukumar zaSe mai zaman kanta.

****
Dattijo ne Wan shekaru sittin da takwas, wanda hutu da jin daWi ya Soye tsufan nasa, ya koma tamkar Wan shekaru hamsin.
Yana tsaye ya zubawa hotuna uku da suke jikin katafaren Wakin ido. Hoton shugaban ?asa, da gwamna sai kuma sarkin garin. Bayansa kuma wasu manyan dattijan ne sa'aninsa, a zazzaune sun yi shiru, su na dakon abin da zai ce.
Ya juyo a hankali, ya ?are musu kallo Waya bayan Waya, ya Wan yi gyaran murya sannan ya ce "Ha?i?a ya ?etare iyakokin da muka gindaya masa, ba tare da duba mu muka Wora shi a kan mulki ba. Motar kawai muka ba shi, amma sitiyari yana hannunmu. Dan haka zamu murza sitiyarin da fasinjojin zuwa inda muke so. Idan ya so a mutu har liman in dai lissafin siyasarmu ya fita shikenan"

"Wannan gaskiya ne" suka amsa cikin girmamawa.

"Za mu ?ir?iri abin da zai hana shi mulkin nan cikin kwanciyar hankali, zamu Wora daga inda muka tsaya a wancan karon, zamu haWe koko giya, zamu saka masa pressure da hankalinsa zai koma kan kawo daidaito, a dai-dai lokacin da zamu saka a matsa masa lamba"

?aya daga cikin mutanen ya ce "Amma ta yaya kenan ranka ya daWe?"

Mutumin ya ?ara murtuke fuska ya ce "Amfani da tsaro mu sanya tsoro!!!"

*****

MAFARI...

Masu iya magana na cewa tushiya masomar dawa, kuma duk wanda ya bar gida gida ya bar shi. Kowace halitta na alfahari da tushiyar da ta samar da ita, sai da tamu tushiyar, ta ginu a kan wata mummunar a?ida da muka buWi ido, muka ga iyaye da kakaninmu a kanta, ba tare da sanin yadda aka yi ta fara ba, sai jin wai wai a cikin labarai da su kan bamu.
Har gaban abada majigin abin da ya faru, ba zai taSa barin allon zuciyata ba, hakazalika zuciya ba zata gushe ba, tana raWaWi da sanya idanu zubar hawaye, a sanadiyar gadon bashin gabar da iyaye da kakaninmu zuwa kanmu, babu abin da muke yi bayan lissafa asararta.

?auyenmu na can wani yanki a can cikin ?auyukan wata jiha a arewacin ?asarmu. Inda ?abilu uku zuwa huWu ne muke rayuwa a guri Waya. Kowane ?abila a cikinmu, akwai nau'in sana'ar da suka ?ware a kai.
Sai dai wannan zama da muke guri Waya, bai zame mana Alkhairi ba, domin ?abila Waya daga cikin ?abilu uku, sun fi mu yawa, da ?arfi dan haka sun mayar da mu tamkar bayinsu. Sauran ?abilun nan ta ?arfin tsiya suka bar tsakiyar garin Yelwa, su ka bar garin baki Waya, zuwa nesa kaWan su ka kafa nasu garuruwan, aka bar ?abilu biyu a cikin garin.

Bari na gajarce muku dogon labari zuwa gajere, domin hana shi gundurarku, labarin da nake son baku, ya fara ne daga wani lokaci.

Damuna uwar albarka, in ji masu iya magana, kasancewar ta lokaci da al'umma ke amfana da tarin alkhairan da take tattare da ita.
Yanayin garin ya canza da sassanyar iska mai samar da nutsuwa.
Korayen bishiyu masu kyawun kallo ga idaniya, kuma abinci ga dabbobin tudu da na Daji.
Tumbatsar tekuna, da samun wadataccen ruwa, ga mutane da dabbobi, ga uwa uba na du?e tsohon ciniki, kowa ya zo duniya kai ya tarar, wato noma da ake a wannan yanayi, domin samar da abinci.
Zukatan makiyaya tare da manoma, yana cika da farin ciki, a dai-dai lokacin da damuna ta kankama.

Cak na tsaya na Waga kaina, ina kallon yadda garin ya yi duhu, hadari yake ta rugugi, wanda idan har ya zubar da ruwa, zai zama ruwan farko da ya zuba a wannan damunar.
Duk da son yanayin na damuna da nake yi, ?asan zuciyata a cike yake da zullumi da tashin hankali. Domin daga lokacin da damunar ta kankama ya kan zama tamkar zagoyawar jijjiga tsohuwar gaba, da mummunan tashin hankalin da yake tsakanin ragowar ?abilu biyun da ke rayuwa a ?auyen Yelwa.
Adadin yadda garin yake ?ara duhu, haka tashin hankali da mummunar fargaba, ke ?ara mamaye lungu da sa?o na zuciyata.
Ina kallon yadda mahaifina ke kaiwa yana komowa a tskar gida, yana magana da Innarmu, sai dai a muryarsa nake iya karanto damuwa da rashin nutsuwa.

"Kai abin nan da mamaki fa, ina Iro ya shiga a wannan tsohon daren, ga gari na damina fisabilillahi, ai ko yawon zai je, ya bar wa gobe. Kwata-kwata yaushe ya dawo ma, da zai yi nisa haka? Ke Mairo, ba ni tagiyata na zagaya ko Allah zai sanya na gan shi" Ya yi maganar cikin damuwa.
Innarmu ta amsa masa da to, ta ba shi hularsa ya karSa? ya fita.
Ban san dalili ba, na ji jikina ya yi sanyi, na ji tamkar ?afafuwana ba za su iya Wauka na ba. Haka nan zuciyata ta din ga bugawa, da wata irin matsananciyar fargaba da ban san ta mece ce ba.

Daki-daki nake tuna abin da ya faru.
Kwanaki biyu kenan, da dawowar Iro daga kiwo da ya tafi, ya shafe watanni huWu, ba ya garin da dabbobinmu.

Na dawo daga rafi, ina tafe ina ta karanta wasi?ar Jaki a zuciyata, da tunanin ta inda zan samu nasarar abin da nake kwana nake tashi da shi a cikin zuciyata. A dai-dai lokacin? na hangi kyakyawan murmushi a kan kyakyawar fuskarsa. Ban yi ?asa a gwiwa ba, na mayar masa da martanin murmushin na ce " Wannan kwalliyar da ka sha haka? Ina aka nufa?"

Ya gyara tsayuwarsa ya ce "Kin aike ni ne?"

Na girgiza na ce "Ai gani na yi bamu gama ganin ka ba, amma har za ka fita. Ko zance za ka je?"? Na ?arasa maganar ina yin ?asa da muryata.

Da?uwa ya yi mini ya ce "Wuce ki shiga gida, idan na dawo akwai tarin labaran da zan baki. Kuma ki kula da karsanar nan dan Allah, alamu sun nuna, ta kusa haihuwa"

Na jinjina kai na ce "Sai ka dawo. Ina jiran ka zo ka bani labarin, dan ka san duk inda labari yake ina gurin, kuma bana raina saurarensa, komai ?an?antarsa. Dan akwai darasi a cikin kowane labari.

Tun daga wannan fitar, har wannan lokacin, kusan ?arfe sha Waya da rabi na dare, bai dawo ba.

Sallamar Baffa ta katse mini tunanin da nake yi, sai dai gabana ya yanke ya faWi, ganin Baffa shikaWai ba tare da Iro ba.

Tun kafin Baffa ya furta komai, bugun zuciyata ya ?aru, abin da ya furta kuwa ya kusa katse mini numfashi.

"Na je duk inda nake tunanin zan gan shi, ban same shi ba"

Inna ta Wora hannu a ka ta ce "Innalillahi wa innalillahi raji'un, ina yaron nan ya shiga haka? Iro bai taSa irin wannan ba"

Ni dai tamkar an shuka ni, domin gani nake su da suka haife shi ma, ba su kai ni tashin hankali da fargaba ba.

A hankali kunnuwana su ka fara jiyo mini hayaniya sama-sama, na kalli su Baffa ko sun ji, amma na ga babu alamar suna jin hayaniyar.

Sai daga Baya Baffa ya Wan yi shiru ya ce "Kamar hayaniya nake ji fa"

Da sauri na ce "Nima haka"

Jin hayaniyar na ?ara kusantowa, ya sanya Baffa yin waje da sauri, ba mu jira komai ba daga ni har Inna, mu ka rufa masa baya, hannunmu Wauke da cocilan.

Dandazon mutane mu ka gani, Wauke da cocilan a hannayensu, da sanduna su na ta hayaniya.

Kafin mu ?arasa tuni Baffa, ya ?arasa ya kutsa cikin dandazon mutanen.

Tsananin azalzalar son sanin abin da yake faruwa ya ingiza ni, na taka da gudu, ba tare da tunanin komai ba, nima na kutsa? domin ganin abin da yake faruwa.

Sai dai kafin idanuna su gane mini komai, sautin salatin Baffa ya karaWe kunnuwana, fiye da hayaniyar mutanen, wanda ya yi daidai da ganin Ironmu a kwance, cikin jini jikinsa futu-futu da taSo, sai zubar da jini yake yi.

Dur?usawa na yi jikina na karkarwa, tamkar ana kaWa mini mazari.

Baffaa ya rirri?e Iro, ya fashe da kuka yana tambayar "Me ya yi muku? Me Iro ya yi muku daga dawowarsa Sale?"

Ba tare da Sale, ya duba adadin furfurar kan Baffa ba, ya haske shi da fitila ya ce "Au tambaya ma ka ke yi? Hukunci ne da muka zartar a kan wanda yake tunanin karansa ya kai tsaikon da zai iya taSa ahalinmu. Kai ku ja shi a ?asa, ku Waure shi a jikin bishiyar nan, ya zama izina, ga duk wani wanda ya gaza Soye ?walamarsa a kan 'yan matan manoma"

Ras gabana ya yi mummunar faWuwa, me Saleh yake nufi? Me yake Irona ya aikata da har ya cancanci wannan tozarcin?

Na yi kukan kura, na dam?e jikin Iro, da ba ni da tabbacin akwai rai a gangar jikinsa, ina kuka, na gaza furta komai.

Saleh ya haska ni da fitilar hannunsa nima,? ya saka hannunsa ya fizge ni daga jikin Iro, ya yi jifa da ni gefe Waya, ya hankaWe Baffa, ya ja Iro a ?asa, sauran matasan suka rufa masa baya, wasu na dukan Iro da ?afa, wasu na kwaWa masa sandunan hannunsu.

Ma?wabtanmu suka fito, su na yi wa Saleh magiya, a kan ya yi ha?uri, a yi magana a sansanta, a ji me Iron ya yi musu, amma ya ce duk wanda ya kuma yi masa magana, sai ya haWa da shi.

Na tashi na kuma nufar su, ina gurshe?en kuka, amma babu wanda ya saurari kuwwa da magiyarmu a cikin matasan nan. Aka rirri?e ni, saboda kada Saleh ya cutar da ni. Mu na kallo su ka Waure Iro a jikin bishiyar darjebiya.

Cikin isa da bayar da umarni Saleh ya ce "Ku je gidan su, ku kwanto mini dabbobin da suke garken gidansu, zai zamana tamkar diyyar abin da ya aikata mana. Kuma wallahi duk wanda ya kwance shi daga jikin bishiyar nan, sai na yi masa abin da ya yi mana.
Ba wannan ba ma, ina mai sanar da ku da jaddada muku, wannan hukuncin shi ne zai biyo bayan duk wanda ya aikata irin laifin da Iro ya aikata.
Mun kama shi da yin?urin haikewa Waya daga cikin yaranmu a bayan gari, dan haka wannan sai ya zama izina ga duk mai yin?urin aikata laifi makamancin wannan.
Suman zaune na yi, da jin maganganun da suka fito daga bakin Saleh. Ko rantsuwa na yi ba na tunanin kaffara za ta hau kaina, ?arya yake yi wa Ironmu.
Innarmu tuni ta sume dama, mu na ji mu na gani aka kaWo dabbobinmu, aka shiga cikin gidanmu aka burkice komai, suka tafi suka bar Iro Waure a jikin bishiyar nan.

Na yi kuka, na yi gunji, na yi yin?urin zuwa inda Wan uwana yake, amma aka tare ni aka hana ni, saboda gudun abin da ka iya biyo bayan zuwa gurin nasa.

aka kece da ruwan sama, ma ?arfin gaske, haka mu ka yi kwanan ba?in ciki da takaici, zukatanmu da na kusa da mu cike da ba?in ciki da Sacin ran, da baki ba zai iya bayyana nauyin da zukata ke Wauke da shi ba.

Da Asubar fari, muka fito, babu alamar rai a jikin Iro.

Har rana ta fito ta take, babu wanda ya iya zuwa inda Iro yake, saboda tsoron abin da ka iya faruwa. Kamar yadda tun tasowarmu, haka muka tarar da iyayenmu na rayuwa a cikin wannan tsoron, da ya yi wa rayuwar su dabaibayi, ake yi musu cin kashi yadda aka ga dama, mu ma kuma su ka haife mu, muka tashi a haka.

Sai da rana ta take, sannan Saleh ya taho da tawagar sa, Wauke da wasu miyagun sanduna.

Su ka kwance Iro, yadda ya faWo timm, ya ?ara tabbatar mana da babu rai a jikin Iro.

"Ka biyo mu bayan gari, ka binne wannan najastaciyyar gawar Wan naka, dan ba za a sallaci mazainaci a cikin garinmu ba, ka je ka ha?a rami ka binne shi, a can bayan gari shikaWai, dan wannan ?azamar gawa ce, ba ta cancanci sutura ba".

Duk da ?ulli gami da ?udurin da yake cikin zuciyata tun bayan da na tasa, na fara mallakar hankalina kaina, a yau na ajiye alwashina a gefe, na fito gaban mutane na sanya gwiwoyina a ?asa, cikin magiya da hawaye a gaban Saleh, muryata na rawa na ce "Ka duba girman zatin Allah, ka yi ha?uri a yi masa sutura a binne shi kamar yadda addini ya tanada, ko wani laifin ya aikata, musulmi ne shi, dan Allah"

Ya zura mini ido na wani lokaci, daga bisani ya bushe da wata irin mahaukaciyar dariya, mai cike da rashin Wigon imani ya ce "Jikar makiyaya, har kin karaya? Har kin manta alwashin da ki ka yi a kaina? Yau ke ce a gabana ki ke neman alfarma? Na so a ce zan iya yi miki wannan alfarmar, ko dan du?a mini da ki ka yi, sai dai kash Wan uwanki fasi?i ne, kuma da ya tashi bai gwada halin nasa a kan kowa ba, sai a kan ahalinmu, dan haka wannan shi ne abin da ahalinku ya cancanta"

Ina kuka su ka tasa Baffa shikaWai ?wal, suka ja gawar Iro a ?asa suka nausa cikin daji.

Duk dandazon mutanen da suke gurin, babu mutum Waya da zai iya faWa a ji, balle ya tsawatarwa Saleh.

'Yan uwan mahaifina, su ka haWa kai su ka tafi gidan su Saleh, wanda mahaifinsa ne, jagoran garin namu baki Waya, amma suka dawo gwiwa a saSule, saboda yadda ya goyi bayan abin da Wan sa ya yi. Tare da Jaddada cewar, an kama Iro da yin?urin aikata wannan mummunan laifi, ba ?azafi aka yi masa ba.

Duk da ba yau aka saba danne mu, da yi mana mulkin kama karya a ?auyenmu ba, amma wannan karon an bar mana wani mummunan miki da zai dauwwama a cikin zukata har gaban abada.
A iya sanina da Wan uwana, mutum ne mai taka tsantsan da gudun duniya, kullum hankalinsa yana kan, yadda zai kiyaye mu, ya kiyaye mutuncinmu mussaman ni da Akuyata ta yi kuka a garin, kuma nake takun sa?a da Saleh.
Kullum cikin nasiha yake yi mini, da ja mini kunne, a kan na yi ha?uri da abin da Allah ya hukunta mana, na rayu cikin salama da aminci.
Baba ya yi niyyar haWa Iro, shi da 'yar Baffanmu Mariya aure, amma ya nuna shi ba ya bu?atar aure a wannan lokacin, kasancewar Babanmu mutum ne mai son 'ya'yansa, sai ya ?yale Iro bai sake yi masa maganar ba.

Sai dai na damu matu?a da son sanin, wace yarinyar ce wannan, da har ake cewa ya yi yin?urin ketawa haddi? Mutumin da ya shafe watanni huWu ba ya gari, yaushe ya dawo da har ya yi yin?urin haikewa wata?
"Wace yarinyar ce a garin nan? Dole na nemo wace ce, sai ta WanWana abin da Iro ya WanWana, kuma ko a mutu ko a yi rai, jinin Wan uwana Iro ba zai tafi a banza ba. Amma wace ce wannan yarinyar?" Na sake tambayar kaina.

Ghost writer 12/7/....

A hankali ta ja guntun tsaki, ganin a inda labarin ya tsaya, ta kai ta komo a cikin group Win, amma babu ci gaba.

****

Dandazon 'yan makarantar islamiyya ne suke ta fitowa daga cikin makarantar, wasu sun tsatstsaya su na ?o?arin tsallaka titi da ababen hawa ke ta kaiwa su na komowa.
Matashiyar yarinya ce, a?alla za ta yi shekaru sha huWu zuwa sha biyar, hannunta ri?e da jakar islamiyyarta, tare da wasu yaran, su na ta surutu, suka tsallaka titi, suka gota wani matashi a tsaye su ka wuce.
Sosai suke dariya cike da nishaWi, suna hirarrakinsu. Ta waiwaya ta hango shi a bayansu yana tafiya. Ba ta damu ba, suka ci-gaba da hira da ?awayenta. Suna tafe duk wadda aka zo kan kwanar gidansu, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login