Showing 24001 words to 27000 words out of 53964 words

Chapter 9 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

762

dan ni gaba Waya ban yarda da shi ba, yanayinsa gaba Waya na marasa gaskiya ne, ina nan ina bibiyar lamuransa, ta ?ar?ashin ?asa zan yi maganinsa sai ya bar unguwar nan. Sannan dole ni zan nemawa Alina wanda ya dace da ita, saboda gudan abin da ka iya zuwa ya dawo"

Nadiya ta numfasa ta ce "Maganganun ka gaskiya ne, amma Alina ba soyayya take yi ba, kawai dai jininsu ya haWu ne. Ina saka ido sosai da sosai nima a kanta"

Kawai ya yi dariya ya kwanta, ya ce " za kuwa ta baki mamaki, za ki ce na gaya miki. Na saka masa ido ta kowace fuska yanayinsa da ?irarsa ta marasa gaskiya ce, amma ina nan ina bin diddiginsa"

Alina ce tare da Mamman, tsaye a Wan madaidaicin shagon provision Win da Alhaji Sadi ya buWe masa a cikin layin, ya ce ya din ga zamar masa a ciki.

Cikin washe baki Alina ta ce "Allah ya sanya maka albarka, ya sanya daga wannan ka buWe plaza ?atotuwa, kamar rabin unguwar nan"

"Amin 'yar ?walisa" Ya yi maganar yana dariya.

Ta ce "?an albarka"

"Na'am"

"To yanzu shikenan ka daina wanke mini takalmina, wa zai din ga wanke mini kenan"'?"

Ya din ga kallon idanunta, har sai da ta sunkuyar da kai ta daina kallonsa.

Can ya ce "Na daina gyaran takalmi, ko wankin takalmi,sai naki kawai" ya yi maganar yana kallonta.
Ta yi dariya tana rufe fuska.

Can kuma ta Wago ta ce "To ka gaya wa mamanka ta yi maka addu'a, an buWe maka shago?"

Ya jinjina kai ya ce "Tun jiya, na kuma ba ta labarinki, ta ce na gaishe ki. Ta kuma gode da ciyar da ni da ki ke yi"

Ta faWaWa murmushinta ta ce "Ka ?i bani ita mu gaisa, ina son ta yi mini addu'a, na ji ya ake ji"

Cikin rashin fahimta ya tattara hankalinsa a kanta, ya ce "Kamar yaya kenan?"

Ta yi shiru jikinta a sanyaye ta ce "Ban san mamanmu da babanmu ba, Yaya ya ce mini dai ni kama ta Waya sak da mamanmu, shi kuma da babanmu yake kama"

Mamman ya ce "Ban fahimce ki ba, sun rasu ne?"

Ta gyaWa kai.

"Oh Allah, ki yi ha?uri ki din ga yi musu addu'a, Allah ya gafarta musu" Maimakon ta amsa sai ya ga ta fashe da kuka.???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?

Sai ya rikice ya yi ?asa da murya ya ce "Ki daina kuka dan Allah, ki rufa mana asiri kar a ce ko wani abin na yi miki ma, ki yi ha?uri mu yi musu addu'a" Ta jinjina masa kai tana share hawayenta.

"Yauwwa kar ki saka yaya ya zo ya zane mu"

Ta saki murmushi ta ce "Haba dai, ba zai zane mu ba, sai dai ni ya zane ni, kuma nima Win baya dukana ai"

"Hmm ke ba zai zane ki ba, amma ni fa"

"Kai ma ba abin da zai yi maka"

Suka ci gaba da hira cike da sha?uwa.

*****
'yan boarding su na cikin walwala da farinciki, kasancewar yau ranar visiting ce, makaranta ta cika ta batse da iyayen da 'yan uwan yara. Tun da Rahama ta ga azahar ta wuce ba ta ga Baffa ba, ta fitar da ran za a zo mata.
'yar kwanarta Anty Ru?ayya ce, ta janyo ta cikin 'yan uwanta, suke ta hira kamar tare aka zo musu. Dan tun Rahama na jss 1 Ru?ayya ke bayar da labarinta a gidansu, idan an zo visiting ko hutu ma su na haWuwa da 'yan uwan Ru?ayya. Maman Rukayya na son Rahama, mussaman da ta ji labarin, daga ?ungurmin ?auyen da babanta ya ya sadaukarwar kawo ta makaranta, kasancewarta 'yar boko.
Maman Ru?ayya ta ce "Rahama ni wannan kunyar taki ta yi yawa, ko dai a cikin yayyen Ru?ayya wani ki ke so ne?"

Rahama ta sunkuyar da kai tana murmushi.

"To matso nan mu ci abinci tare, ke dole ma a yaran nan zan yi miki miji. In dai Baffanki zai ba mu ke. A ba wa Abdallah ko Ammar"

Kamar ta nuste, haka ta Wan cakali Abincin nan, saboda Rahama akwai gudun Duniya da abin hannun mutane. Ga su Rukayya kuma masu kuWi ne sosai da sosai. Idan za a zo mata visiting sai an yi nata na package Win. Har Baffan Rahama 'yan gidansu Ru?ayya sun sani.

Mami ta mi?a wa Rahama wayarta da take ringing. Ru?ayya ta ce "Waye"

"KarSi ki duba mana"

Ru?ayya na ganin sunansa, ta yi murmushi ta koma gefe ta Waga.

"Yaya Mubarak"

"Na'am shalelen, ashe su Mami sun ?araso, na so zuwa ayyuka ne suka yi mini yawa sosai, kin san yayyen nan namu, sai su cinye mutum idan bai yi abin da suke so ba"

Ta yi murmushi ta ce "Take your time ka yi aikinka a hankali, kawai idan ka samu time ka zo na ganka"

Mubarak ya ce "Wanne dole ne, dan ba zan iya shafe wata uku ban ganki ba, zan zo in sha Allah." Sun yi hira sosai kafin su yi sallama.

Yana zaune a cikin mota, ya kwantar da kujera, ya Wora ?afarsa Waya a kan Waya, ya Wora a saman sitiyari yana Wan kaWa ta, hannunsa Waya ri?e da waya yana magana.

"Wallahi Ummi ce ta sako ni a gaba, wai sai an zo wa yarinyar nan visiting, daga zuwana gidan na Wan huta, dan dai ba yadda zan yi ne"

Daga cikin wayar mai amsa wayar yake magana, cike da kamala, da har kamalar tasa take nuna isa isa. Yayinda nauyin muryarsa ya sanya in da da wani mutum a cikin motar bayan shi zai iya jin abin da yake faWa, duk da wayar ba a hansfree take ba.

"To mene ne a ciki dan ka je wa Ru?ayya visiting, I wish ina da little sister da za ta ga gata"

Na cikin motar ya kwashe da dariya ya ce "Ta ga gata, ko ta ga gwale-gwale, kai da gidanku gidan maza ne, Ummi ce kaWai mace, da kuna da ?anwa azaba za ta sha ne kawai"

"Alfa zan zage ka wallahi"

Alfa ya ce "Ware, gidan nan naku imaninku da sau?i wallahi, ku kanku ganawa kanku azaba ku ke yi" Ya yi maganar yana ?ya?yata dariya.

Tsaki wancan ya ja ya ce "Stupid"

"Kai tsaya, ga su can ina ga sun gama tafiya za mu yi, zamu yi waya anjima take care"

"Take care like? Mace ne ni da za ka wani ce mini take care?"

"Zan zage ka fa, ma yi waya dai. Don't care, stay wrecked tun da baka da mutunci"

"Am wrecked already ai" ya katse wayar yana Wan tsuke fuska.

Ummi ce ta fara ?arasawa gaban motar ta ce "Ammar ba dai ba?in hali ba, for more than 5 months bana tunanin kun haWu da yarinyar nan, ka fito ka gana da 'yar uwakka amma ka Wauki motar ka tafi gantali ta zo baka nan"

Ya kalli Rukayya, ta risuna ta ce "Yaya Ammar Ina wuni, ya aiki?"

"Lafiya kalau, ya karatu?"

"Lafiya kalau Alhamdillah."

"To a mayar da kai a yi karatu da kyau idan ana son a ga daidai." Ta yi murmushi ta ce "In sha Allah thanks"

"Ina wuni" Rahama ta faWa daga bayan Ummi a tsorace.

"Lafiya sannu" Ya yi maganar yana sake mayar da hankali kan wayarsa.

Ummi ta ce "Wannan wace irin amsa ce? Haka ka amsawa 'yar uwakka? Ka daina irin haka. Ita ma ?anwarka ce ai"

Ya jinjina kai ya ce "To hajjaju, tuba nake." Ya ciro kuWi ya mi?a wa Ru?ayya kuWi ya ce "Ga shi nan ki ?ara, a kula da karatu sosai"

"Ita Wayar me ta yi maka?"

Ya ce "Wa?"

"Ban sani ba" Rahama kuwa tuni ta juya za ta tafi, amma Ummi ta kira ta, ta saka Ammar ya ba ta kuWi ita ma. Sai dai da fari ?in karSa ta yi, sai da Ummi ta haWe rai.

Su na tafe a hanya Ummi na yi wa Ammar faWa."Ammar ba ka kyautawa abun da ka ke yi, yaran nan ?annenka ne, su na sonka su na ?aunarka, su yi ta murna idan za ka zo, amma ka yi ta wulakanta mini yara dan baka da kirki?"

Ammar ya na kallon hanya ya ce "Ummi kin san raini ne ba na so, amma nima ina murnar ganinsu ai"

"?arya ka ke yi, kuma dan wula?anci har da ba?uwa, yadda ka amsawa Rahama gaisuwar da ta yi maka ya bani haushi"

Ammar ya waiwaya ya ce "Wace Rahama?"

"Yarinyar da suka zo da Ru?ayya mana, Junior Win ta ce, wula?anci ba shi da daWi ai"

"To Ummi, ban san yarinya ba sai na din ga washe mata baki kamar wani shashasha"

"Kai ubanka, ina yi maka magana kana kawo mini useless excuses Win ka"

"Allah ya baki ha?uri"

"Amin. Ba?in hali ba abin yi ba ne Ammar, ba a san inda rana za ta faWi ba"

?asa-?asa ya ce "A yamma mana Ummi" jin ta yi shiru ya Wan waiwaya ya ga tana hararsa ya kawar da kansa ya ci gaba da tu?insa.

Rahama a ?asan zuciyarta ta ji babu daWi rashin zuwan Baffa, tare da rashin sanin dalilin da ya hana shi zuwa. Da daddare da suka koma Hostel, kowa yana ta murna, Rukayya na ta ?o?arin ganin Rahama na walwala amma da ta hau kan gado sai da ta yi kuka.

*****

Dattijo ne a ?alla mai shekaru hamsin da takwas, yana zaune a kan buzu, hannunsa ri?e da Alqur'ani bugun warsh, yana karantawa. Opposite Win sa wata irin ?atuwar rumfa, shimfiWe da tabarmi da alluna a jijjingine, almajirai sun tafi bara.

Sallama ya yi wa dattijon, ya nemi guri ya zauna a gefensa. Dattijon ya kai aya, sannan ya amsa sallamar suka gaisa.

Ya dubi dattijon ya ce "Malam ?ayyabu ko?"

"Eh nine"

"Dan Allah tambaya na zo na yi maka, kai malamin Alqur'ani ne. Ma'abocin Alkur'ani kuwa za a same shi da gaskiya da tsoron Allah. Kuma yanayin dattakunka, ya sanya mini yarda da komai zai fito daga bakinka, gaskiya ce"

Malam ?ayyabu ya jinjina kai ya ce "Wannan gaskiya ne, in sha Allah yadda ka kyautata mini zato, ina sanya ran gaya maka gaskiya da yardar Allah"

"Akwai wani matashi da ya tare a unguwarmu, ya ce shi Walibinka ne, ya yi sauka a hannunka, daga baya kuma ya sake dawowa garin nan, neman kuWi. To ina son tabattar da hakan daga gare ka ne, saboda yana Wan bibiyar 'yar uwata ne, ina tsoron wani abin da ba a so ko fata ya faru, na ga yakamata lallai na bibiya"

Malam ?ayyabu ya ce "Wannan gaskiya ne, ka yi kyawun kai, mussaman zamanin nan da ya lalace. Amma ka ga tun ban fi shekara ashirin da biyar ba, nake harkar Walibai, dan haka wanne daga cikin Waliban nawa?"

Ya ce "Sunansa Mamman, ban san sunan garinsu ba, amma ga hotonsa".

Ya yi maganar yana ciro wayarsa ya Wan daddana, ya mi?a wa malam ?ayyabu. Hoton Mamman ne a zaune yana wankin takalmi, Alina na gefensa a kan dakali tana magana.
Malam ?ayyabu ya karSi wayar ya yi shiru yana kallon wayar, ya numfasa ya ce "Wannan ce yar uwar taka?"

"Ba a kanta mu ke magana ba malam, wannan mutumin da ya ce shi Walibinka ne, nake magana a kai"

Malam ?ayyabu ya yi shiru ya zuba wa hoton ido.

"Malam ka yi magana mana" Ismail ya yi maganar yana kallonsa.

Malam ?ayyabu ya Wago kai yana kallon Isma'il.

Ismail ya ce "Ina ?ara tuna maka, ka dubi girman mai littafin da yake gabanka, ka gaya mini gaskiya"

"?alibina ne" Ya yi maganar yana gwama numfashi.

Ismail ya yi shiru yana nazartar fuskar malamin.

"Ka tabattar Walibinka ne?" Ya jinjina masa kai yana Wan zazzare ido.

"Idan akasin gaskiya ka gaya mini, mai Alqur'anin nan ba zai bar ka ba"

"Me zai sanya dattijo kamar ni, ya yi maka ?arya, alhalin baka sanni ba ban kuma sanka ba? Mamman Walibina ne, sai dai ya sauke ya haddace, dan haka ya kai munzalin da zai zaSi abin da yake so, kuma ina da ya?inin mutumin kirki ne, ba zai cutar da kowa ba"

Ismail ya jinjina kai ya ce "Gaskiya ne,na gode sosai da sosai Malam" Suka yi musabiha, ya tashi ya tafi. Yana tafiya jikin Malam ?ayyabu ya yi sanyi, wani irin gumi ya fara tsatstsafo masa, ya kalli Alqur'anin da yake gabansa ya furta "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, da wani bakin zan nemi gafarar Allah"

'yar ?aramar wayarsa da ke cikin aljihunsa ce ta fara ringing, ya ciro ta, yana kallon yadda kira yake shigowa babu suna kuma babu lamba.

Hannunsa na rawa ya kara wayar a kunnensa.

"Aikinka ya yi kyau, idan aikin naka ya ci gaba da kyau, shikenan ka tsira, idan kuma aka samu matsala salin alin zamu Satar da kai"....

Ayshercool
08081012143
SARA DA SASSA?A...

AYSHERCOOL

YOTA/002

Page 8

Sannu a hankali ya ajiye wayar, jikinsa na ci gaba da tsuma, ya tashi tsaye a hankali yana waige-waige, ya ga ko zai hango wani a gurin, da ko shi ne ya bayar da rahoton zuwan matashin, amma bai ga kowa ba. Zuciyarsa ta raya masa haWin baki ne, ana sane aka turo shi, dan a gani ko zai faWi wani abu ko ba zai faWa ba. Ya sanya hannu ya Wauki Alqur'aninsa ya tafi yana ta istigfari.

*****

Tana tsaye daga nesa da shagonsa kaWan, ya buWe ?ofar ya tsaya yana kallonta. Doguwar riga ta saka, da wani Wan ?aramin mayafi, hannunta ri?e da flask Win Abinci. Tun kan ta ?arado, ?amshin turaren da take yi, ya karaWe ilahirin gurin. Ta saka jam baki a bakinta, idanunta kuma ta saka kwalli.

"?an Albarka"

"Mmm 'yar ?walisa"

Ta yi murmushi ta ce "Bacci ka ke yi ne?" Ya girgiza mata kai alamar a'a.

"Me ki ka dafa mana ne yau?"

"BuWe ka gani" Ta yi maganar tana mi?a masa flask Win Abincin, ya karSa ya buWe, ya ga tuwon shinkafa da miyar wake. Ta mi?a masa ledar hannunta ta ce "Ga zoSo mai muslmin sanyi kuma"

"Na gode sosai 'yar ?walisa"

Cikin jin nauyinsa ta ce "Nima na gode, sai anjima"

Ya Wan yi gyaran murya ya ce "Ina kuma za ki je?"

"Zan je titi ne sayo wa Antynmu abu"

"'Yan mata mayafin nan ya yi ?arami fa, ana ganin jikinki. Kuma ga shi kin yi kyau sosai da sosai"

Ta rufe fuska ta ce "Dan Allah ka daina bani kunya mana"

"Hmm ba kunya nake baki ba, gaskiya na faWa, kuma mayafin nan ya yi kaWan, ba ki san kin fara girma bane?"

Ji ta yi tamkar ta nutse saboda kunya da ta mamaye ta. Ta Wan kwaSe baki ta ce "Yanzu zan dawo fa" Ta yi maganar a Wan shagwaSe.

"A dawo lafiya, na gode sosai da abinci" Ta juya ta tafi, ba tare da ta sake cewa komai ba.

Yana zaune bayan ya gama cin abincin, ya jiyo hayaniya a waje, sarai ya Wauki muryar Isma'il sai bala'i yake yi, har ya basar saboda ya riga ya fuskanci Ismail masifaffe ne lamba Waya. Sai dai tuna cewa ba a jin kansa, idan ba Alina aka taSa ba, ya sanya ya tashi da sauri ya le?a.
Aikuwa kamar yadda ya yi tsammani, wani matashi yake yi wa hargowa, tun daga titi ya gano shi, ya bi Alina yana yi mata Wan kira, ya biyo su a babur sai da suka shigo cikin layi, ya rutsa su yana zazzaga wa matashin bala'i. Tuni mutane suka taru su na ba wa Isma'il ha?uri. Alina kuwa yanayin fuskarta ya nuna rashin jin dadin tijarar da yake yi wa matashin, ga jama'a ya tara musu, sai Waga murya yake yi. Takaici ya sanya ta wuce gida ta bar su a gurin.

Da kyar aka ba shi ha?uri, matashin ya tafi.
Mamman ya girgiza kai kawai yana murmushin gefen baki.

Kamar guguwar ba?in hadarin kaka, haka Ismail ya shigo gidan yana ci gaba da bala'i.
"Wallahi Alina idan ba ki kiyaye ni a kan gayyar mazan nan da suke bibiyarki ba, a gabansu zan naWa miki duka wallahi. Ke ba ki san halin da ?asar nan ke ciki ba na rashin tsaro, kowa ba abin yarda ba ne, amma da yake kin fi kowa mutunci kowa sai ya biyo ki yana yi miki surutun banza kina washe baki, mara hankali kawai da ba ta san ciwon kanta ba"

"Yaya wallahi ban san shi ba, biyo ni kawai fa ya yi"

"Rufe mini baki ina magana kina magana" Yadda ya yi maganar cikin ?araji, ya sanya babu shiri, ta shige bayan Nadiya tana Suya.

"Ki ci gaba kar ki fasa. Wataran sai kin janyo mana abin da ya fi ?arfinmu, ko tilasta mana komawa inda muka fito yadda mu ma za a kashemu kamar yadda aka kashe iyayenmu. Shi kansa wannan Wan iskan da ki ka saki jiki da shi kamar ubanki, ki ka li?e masa kallonki kawai nake yi. Gaba Waya mutumin nan da ganinsa ka san munafuki ne ba shi da gaskiya. ?irarsa da idonsa duk na miyagun mutane ne, babu ta inda ya siffantu da wani almajiri, amma kin li?e masa, na rasa uwar da yake gaya miki. Amma za ki ga matakin da zan Wauka a kanku"

Alina ta fashe da kuka, Nadiya ta rungume ta ta yi ?asa da muryarta ta ce "Ki daina kuka rabu da shi, ya yi faWansa ya gama, kar ma ki sake kare kanki, ?yale shi"
Bayan fitar Ismail Alina ta ce "Antynmu ni shikenan haka zan zauna, yaya ya korar mini ?awaye, ya hana ni hulWa da kowa? Kuma wallahi Mamman mutumin kirki ne, ai kema kin san ba zan je inda zan lalace ba, ai ina bin nasiharku ba zan baku kunya ba. Kuma ni ba saurayina bane"

"Na sani Alina, amma duk wanda zai so mu, ba zai kai yadda Yaya yake sonmu ba. Duk abin da yake yi, yana yi ne, domin ya bamu kariya kar wani abu ya cutar da mu, ki yi ha?uri wataran sai labari" Alina ta jinjina kai.

"Alina" Nadiya ta kira sunanta tana nazartarta.

"Na'am"

"Son Mamman ki ke yi ko?"

Alina ta Wago da sauri ta ce "So kuma? Haba Antynmu, ni wallahi ba son shi nake yi ba, kina ganin mutuncin da yake yi mini, ni kawai dai mun saba ne. Yana da kirki kuma yana koya mini karatu"

Nadiya ta jinjina kai tare da yin murmushi ta ce "Shikenan tashi ki je"

Ismail kuwa yana dawowa daga sallar isha'i, ya manta da faWan da ya yi wa Alina, sai da bai ganta a tsakar gida ba, ya tambayi Nadiya ta tuna masa ai ta yi bacci tun faWan da ya yi mata.

Bayan kiran sallar asuba na farko, Mamman ya buWe ?ofar Wakinsa domin kama ruwa ya yi alwala, kawai ya yi tozali da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login