Showing 9001 words to 12000 words out of 53964 words

Chapter 4 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

772

maka baho da ruwa ka wanke?" Ya jinjina mata kai.

"To bari na je gida" Ta ajiye kayan, ta nufi gidansu. ?asan zuciyarsa cike da fargaba, kuma sai gargaWinsa zuciyarsa take yi, da tuna irin abin da yayanta ya yi masa, da kuma kashedin da ya yi masa a kanta.

Ba a yi mintuna biyar ba, sai ga ta Wauke da baho ta sha?e shi da ruwa a ciki. Yana tsaye yana kallonta, ta Wauki yalon nan ta juye a bahon duk ta Wauraye su, ta zuba masa a cikin bagcon sannan ta zubar da ruwan.

Ta yarfe bahon ta dube shi ta ce "Allah ya tsare gaba"

"Amin" Har za ta tafi ta ji ya ce "Na gode" ta tsaya ta waiwaya ta kalle shi, amma jikinta ya yi sanyi, saboda yadda ya tsare ta da manyan idanunsa. Jinjina kai kawai ta iya yi, ta nufi gida.

*****

Ramata na zaune da wayarta a hannunta, ta tattara hankalinta tana sauraren radio a cikin wayar. Tana zaune hannunta ri?e da biro da takarda, ga kuma fitila a ci balbal tana haska mata littafin gabanta.
Cak ta tsaya da rubutun, ta ?ara tattara hankalinta a kan sauraren bayanan da mutumin cikin radion yake yi, yadda turawa suka mamayi Afrika.
Yadda suka fara zuwa African ta jirgin ruwa, su kan zo gaSar teku domin yin cinikayya a ?arni na sha biyar. Su na kasuwancin zinare, hauren giwa da makamatansu. Daga baya aka fara cinikayyar bayi, mussaman tsakaninsu da sarakuna, yadda suke dibar mutane daga Afrika su tafi da su ?asashen su, su yi musu bauta.
Daga bisani a ?arni na 16 suka fara kafa sansanoninsu, da kawo coci-cocinsu, da Asibitoci da makarantu a Afrika. Suka daina tsayawa a gaSar teku suka fara watsuwa a cikin ?asashen Afrika.
Cinikayyar bayi da yarjejeniyar bogi, tsakaninsu da sarakunan Afirka, shi ya fara kawo rarrabuwar kawuna a Afrikan tare da kawo koma baya.
A ?arni na 19 alif dubu Waya da tamanin da takwas, manyan ?asashen nahiyar Turai suka yi taro, suka rarrabawa kansu ?asashen Afirka ba tare da sanin ?asashen Afrikan ba.

Ramata ta ri?e haSa, jin an tafi talla. Ta dubi Baffa da yake gefenta yana sauraren radion shi ma.

"TaS Baffa"

"Na'am Ramata"

"Tabbas ba a taSa cin gari har abada ba tare da Wan gari ba. ?ulafuci da son zuciyan sarakunan Afrika na ?arnukan baya, na daga cikin dalilan da ya sanya muke cikin wahala haryanzu, kuma muke ?ar?ashin mulkin turawa ta wasu fuskokin"

Baffa ya yi murmushi ya ce "Ba an ce mun samu 'yanci ba? Kuma duk da haka mutanen wancan ?arnukan ai sun fi na yanzu wadatar zuci ma da amana. Duk da ni ba wani gane kan wannan abubuwan nake yi ba"

Jiki a sanyaye ta ce "Baffa, duk da ba na nan abubuwan nan suka faru, na san Al?awarurrukan da turawa suka yi musu, baya rasa nasaba da basu tarin dukiya, ko kuma wani abu da za su amfana ba tare da kallon makomar al'ummarsu ba. Ban da haka ya za ku din ga Waukar junanku ku na sayarwa mutanen da ba ma launin fatarku Waya ba, daga wani guri suka zo, ba ma yankinku Waya ba, alhalin su ba sa sayar muku da na su mutanen, tun a lokacin sun nu na ba su san ciwon kansu ba fa kenan?

Baffa ya kwashe da dariya, ya ce "Ramatu kenan. Ga shi nan sun dawo daga tallan ai, bari mu ci gaba da jin meyafaru"

"Assalamu alaikum " su ka ji an kwaWa sallama.

Baffa ya amsa sannan ya kalli Ramata ya ce "Maza shiga Waki"

Ta tashi tsam ta shige Waki, Baffa ya sake cewa "Bismillah"

Tamkar korarre haka ya faWo gidan, Baffa ya mi?e yana yi masa sannu da zuwa, ya nuna masa gefen tabarmar da yake kai domin ya zauna.
Yana zama Juma ta fito kanta da lulluSi, ta dur?usa ta gaishe shi ya amsa, sannan ya mayar da idonsa kan Baffa.

"Wato kai dai ba zaka taSa hankali ba ko Jibo?"

Cikin rashin fahimta ya ce "Yaya lafiya kuwa?"

"Ka tambaye ni ko lafiya mana, to ba lau ba. Saboda tsabar Wan kanka ne kai, mun ha?ura mun zuba maka ido kana yadda ka ke so. Ban da rashin mafaWi har dukiyarka zaka tattare idan ka mutu Ramata ta ci gaba da yahudanci ko? To baka isa ba wallahi. Babu wannan maganar na soke ta. 'ya ce dai tun da ba zaka aurar ta ba, mun zuba maka ido, a garin nan dai ka san babu mai auren ta. Ka Wauke ta ka kai ta can wata uwa duniya ta yi kwana da kwanaki babu wanda ya san inda take da abin da take yi, babu wanda zai aure ta dan haka sai ka ji?a ta ka sha"

Baffa ya kalli Juma, ta tsuke fuska tana kawar da kai. Ya girgiza kai ya ce "Yaya haryanzu ba ku fahimci manufata ba, ana ta samun ci gaba a duniya, mu mu na guri Waya duk a dalilin rashin ilimi. Ko mulkin kama karya da ikon da ake yi mana a garin Yelwa rashin ilimi ne ya haddasa mana shi."

"Ni rufe mini baki, 'yan bokon ba su ne suke kashe-kashe ba, suke mulkin ?asar gaba Waya ba, wane zalunci ne su ba sa yi. Sau nawa ana kai ?orafin abin da yake faruwa a garin nan, amma su ke goya musu baya. Wallahi idan baka yi wasa ba, yadda ka fifita yahudanci a kan aurar da Ramata, sai ka zubar da hawaye a dalilin bokon nan, sai ta zame muku masifa daga kai har ita"

Ras gaban Ramata ya faWi, jin yadda Wan uwan mahaifinta ke janyo musu jafa'i ga shi dattijo. Ta jingina da jikin katangar ?asar da ke Wakin, zuciyarta na bugawa da sauri.
Baffa ya ce "Ba za a yi haka ba in sha Allah, Alkhairi za ta zame mana baki Waya"

"Wannan kuma matsalarku ce" Ya tashi ya kaWe rigarsa ya fice.

Baffa ya dubi Juma ya ce "Kin kyauta, na gode sosai da sosai" Ta tashi sumi-sumi ta wuce Waki tana ?un?uni.

****

Ko da Alina ta taso daga makarantar dare, ba ta ga mutuminta ba, ta yi ta tunanin ko ya ?afarsa, ko ya warke? Haka ta yi ta sa?e-sa?e, har ta koma gida.
Daga nan sai da aka kwana biyu, sannan ta sake ganinsa.
Sai dai kan ta ?arasa inda yake ta yi magana, ya shige Wakinsa. Duk sai jikinta ya yi sanyi.

*****
Dan?areriyar mota ce ?irar higlander take ta zuba gudu, sai dai jikin motar babu lamba.
Yana zaune a bayan motar, fuskarsa a rufe da rawani, sai idanunsa kawai ake iya gani. Sai rarraba idanu yake lokaci zuwa lokaci, wasu lokutan kuma sai ya sunkuyar da kansa ?asa yana duba agogon hannunsa.
Check point suka tarar a hanya, wanda tilas direban motar ya yi slow, ya ja ya tsaya.
Sojoji ne su uku a a check point Win, ya yin da wasu ke zaune a cikin mota, babban cikinsu ya ?araso, ya kalli direban ya ce "Daga ina?"

Direban ya amsa da "Maigida ne ya aike mu"

"Waye mai gida?"

"Lamba Waya"

A Wan hasalae sojan ya ce "Malam ka yi mini bayani, daga ina kuma ina za ku je? Sannan suwa ka Waukko, ga motar ta ku babu lamba, kai ba ku da gaskiya."

A hankali ya sauke gilashin motar, ya yi wa sojan alama da ya ?arasa. Ya ?arasa daidai tagar yana son ganin fuskar mutumin.
"Kacalla Sumale, shugaban manyan ?ungiyoyin ta'addanci na yankin nan, da ku ke nema babu dare babu rana, shi ya aike ni. Manyanku sun saka a Waukko ni domin wata yarjejeniya" Ya yi maganar yana ?are wa sojan kallo, ya sauke rawanin fuskarsa, kyakykywar fuskarsa fari sol ta bayyana.

Ya sake duban sojan ya ce "Ka buWe mini hanya zan wuce" Sojan ya Wana bindigarsa yana ?arewa fuskar matashin kallo. Shi ma matashin ya tsare shi da nasa idanunsa da suka da kalar ja.
Ba tare da ya Wauke idanunsa daga kan sojan ba, ya ciro wayarsa ya daddana, ya saka ta a hansfree.

Daga cikin wayar wata murya ta ce "Ya aka yi ne?"

"Ka janye mutanenku sun tsare mini hanya, ko kuma su riga rana faWuwa" Waro ido sojan ya yi, jin muryar mai maganar, saboda duk wanda yake cikin battalion Win su, babu wanda bai san wannan muryar ba.

"Argungu are you with me?"

Cikin rawar murya ya ce "Yes Sir"

"Clear the road"

"But Sir"

"I said clear the road"

"Ok sir" Tamkar soko haka ya ja da baya a hankali, yana kallon motar. Ya yi wa sauran alama da hannunsa, suka buWe hanya motar ta wuce.

*****

"Alina, wai bacci ki ke yi da la'asar Win nan?"

Alina ta amsa da "A'a idona biyu" ta fito tsakar gida ta ce "Sa?a nake yi, safa da hula zan sa?a idan ki ka haihu mu saka wa jaririyar"

Nadiya ta yi murmushi ta ce "Alina kenan. Kin ga gobe in Allah ya kaimu litinin ki zo ki kai wankin takaliminki, ga nawa ki haWa da shi a yi mini round, na yi wa Yaya maganar ya manta"

Alina ta ce "To bari na saka hijjabina" Ta yi maganar tana Wan yin hamma, sai kuma ta katse hammar da ta tuna mutumin nan da ko sunansa ba ta sani ba yana gyaran takalmi. Da sauri ta janyo hijjabin ta zura, ta Wauki takalman ta fita.
Sai dai baya gurin da yake zama, dan haka ta je ?ofar Wakin da yake kwana cikin tsoro, ta fara bugawa.

Har ta sare ta fara tunanin baya nan, kawai ta ga ya buWe ?ofar, sai da ta razana ta Wan ja da baya tana kallonsa. Ya ?ura mata ido, a Wan rikice ta ce "Ahh da..da..dama gyaran takalmi na kawo maka" Ta yi maganar tana nuna masa takalman hannunta.

Ganin ya tsaya yana kallonta, ya sanya ta sha jinin jikinta, tsoro ya ?ara bayyana a fuskarta. Kawai ta ga ya koma, ta tsaya sororo tana kallon ?ofar, har za ta juya ta tafi, ta ga ya sake buWewa ya fito da kayan gyaran takalmin. Ta yi ajiyar zuciya ya samu guri ya zauna, ta gaya masa abin da zai yi wa takalman, sannan ta koma gefensa kan dakali ta zauna.
Ya du?ufa yana wanke takalmin, ya din ga jujjuya takalmin Alina, tomes na 'yan makaranta ba?i, mai tsadar gaske. Ta Wan zuba masa ido, haka kurum ta ji tana son ta ga fuskarsa, amma ya tara uwar ?asumba dogon hancinsa kawai ake iya ganewa sai manyan idanunsa da suka fi komai razana ta. Bayan haka ga wata uwar hula da yake sakawa a kansa ya rufe, ga uban kwalli da yake rambaWawa a idonsa. Kayan jikinsa sun sha jiki, dark bluen yadi ne a jikinsa, amma ya koma sky blue saboda tsufa.

"Ciwonka ya warke?" Ta yi maganar ba tare da ta shirya ba.

"Ya warke" Ya faWa a ta?aice.

"Allah ya ?ara sau?i, ya kiyaye gaba"

"Amin" Yayi maganar yana ci gaba da abin da yake yi ba tare da ya Wago ba.

Ya gama gyaran takalmin, ya wanke mata nata, sannan ya mi?o mata.
Ta karSa ta Wan yi murmushi ta ce "Kai ya naga takalmina ya koma sabo? Wannan ?yallin ai sai na gano fuskata a ciki saboda kyau da she?in da yake yi" Ta yi maganar tana Waga takalmin tana kallonsa. Ga mamakinta sai ta ga ya Wan kalle ta ya yi murmushi.

Ita ma murmushin ta sake yi sannan ta ce "Nawa ne?"

"A'a ki bar shi"

Alina ta ce "A'a ai sana'a ka ke yi, Yayana ya ce a duniya kar ka zalunci mai sana'ar hannu".

Ya ce "Idan kin kuma kawowa sai ki biya"

"To Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya ji?an magabata, idan su na raye Allah ya ja kwanansu"

Ya amsa da "Amin na gode"

Ba ta kai ga tashi ba, sai ga Isma'il ya shigo layin a kan babur, idonsa na sauka a kansu, ya tsuke fuska kamar ya ga bala'i...




SARA DA SASSA?A...

AYSHERCOOL

YOTA/002

BRIGHT PENS

P4

Bai kula su ba kawai ya wuce, Alina ta tashi ta ce "Sai anjima na gode"

Cikin fargaba ta shiga gida, ta tarar da Yaya Ismail a tsaye yana jiran isowarta.
Aikuwa ya tare ta da "Meye haWinki da mutumin nan? kin kawo mini ?ara na je na tsawatar masa, yanzu kuma na ganki a gurinsa me ya kai ki gurinsa kuma?"

Alina ta nuna masa takalman hannunta A Wan tsorace ta ce "Gyaran takalmi na kai masa, ni fa dama babu abin da yake yi mini Yaya, tsoronsa kawai nake ji da, kuma daga baya na gane mutum ne, shi ne na kai masa gyaran takalmanmu, nawa da na Anty"

Ya ce "To dai ki din ga kula da kyau, kuma ki din ga addu'a"

Alina ta jinjina kai, ta ajiye takalman.

*****

Yau Juma'a, da yamma li?is Ramata ce sanye da Winkin riga da skirt na yadi, ta yi wa fuskarta ado da jam baki da kwalli, ta yi kyau. Ta tsaya dai-dai jikin wata bishiyar tsamiya, tana Wan le?e-le?e.
Wanda ta gani yana tahowa ne, ya sanya ta tsuke fuska, gabanta ya tsananta faWuwa, idanunta suka fara kaWawa, ta ji tamkar ta juya ta zura da gudu. Tun daga nesa yake wage baki yana dariya cike da ?eta, ya ?araso inda take tsaye, jikinsa sanye da kayan farauta, da karnuka su na bin sa, sai abokansa su biyu.

Ya ?are mata kallo ya ce "Jikar makiyaya wannan kwalliyar fa?" Ta ?ara tsuke fuska tana jin yadda zuciyarta ta fara tafasa, ta haWiye wani abu mai Waci a ma?ogwaronta, tana kallonsa.

Hannu ya mi?o zai kai jikinta, cikin zafin nama, ta buge hannun ta ja da baya tana huci.

Ya sake kwashewa da dariya sannan ya ce "Kafiya da taurin kai tamkar mahaifinki Ramata. Daga nan shiyyarku na so shiga domin na ganki a bar ?aunata, sai dai na taki sa'a na yi gamo da ke a nan. Ko akwai wanda ki ke jira ne?" Ta tsare shi da idanunta da suka kaWa suka yi jawur.
"Idan shiyyarmu ki ke son shiga, ki shiga babu wanda zai yi miki komai saboda ki na da ni. Gaya mini wa ki ke jira? Hanne ko kuma Bukar?" Ras gabanta ya yi mummunan faWuwa. Ta Waga ta sake kallonsa.
Ya kwashe da dariya, ya ce "Kin Wauka babu wanda ya sani ko? Yaro man kaza"
Ya sassauta murya ya matso daf da ita? ya ce "Idan ki ka bari abin Soye ya fito fili, kin san ke da zuriyarku ne za ku karSi hukuncin, babu wanda zai hukunta Bukar. Kamar yadda Iro ya karSi hukuncinsa da shi da Hanne" Sake ware ido ta yi, ta ja da baya, tana ?o?arin magana amma maganar ta gagara fitowa.
"Ya ki ke ja da baya, kullum ?o?arin nuna ke ta Allah ce ki ke yi, bayan kowa ya san yadda son abin Duniya ya sanya Babanki kai ki birni nema masa kuWi, ta hanyar karuwanci.. cikin ?warin gwiwar da ba ta san tana da shi ba, ta Wauke shi da wawan mari, sakamakon yin?urin taSa ?irjinta da ya yi lokacin da yake maganar.

A zafafe ta fara magana, duk da siririyar murya ce da ita ta ce "Kai kuma za ka karSi hukuncin kaf laifukan zuriyarku muddin ina raye, shashasha kawai" karnukansa ne suka fara yi wa Ramata haushi, abokansa kuma suka yin?uro, amma ya dakatar da su.
"Marin soyayya ne, tukuicinsa kuma Bukar ne zai biya" Ya yi maganar yana ci gaba da dariya.

Ramata ta ce "Wannan kuma matsalarku ce, dama idan mutum yana mugunta, idan bai yi wa kansa ba, bai iya ba, kuma da sannu wannan zaluncin da ka ke yi, zai waiwayo ku, matsa ka bani hanya kan na ?ara maka wani marin" Yana murmushi ya yi taku biyu, ya bata hanya ta wuce fuuu tana zubar da hawaye.

"Gaskiya ka bada maza, mari fa, mace ta mare ka kana kallonta?"

"Shhh, kar na sake jin bakin wani daga cikinku" Gaba Waya suka yi shiru, ba su sake cewa komai ba, suka bar gurin.

Ramata ta yi tafiya mai nisa, ta ji muryar Bukar na ?wala mata kira, kamar ta share shi ta wuce, amma ta fasa ta ja ta tsaya, ta share hawayen fuskarta.
Ya ?araso yana sauke numfashi ya ce "Ramata, na fi awa biyu a rafi ina jiran zuwanki, ga shi yau juma'a ban ganki ba"

Ta numfasa ta ce "Hanyar tsamiya na je na jira ka yau mu tafi tare, kuma ban ganka ba"

Jiki a sanyaye ya ce "Ramata meyafaru ne, na ga fuskarki wani iri" Ganin ya rikice ta ?a?alo murmushi ta ce "Babu komai fa, ka san duk lokacin da zan koma makaranta sai na ji kewar gida"

Ya yi murmushi ya ce "Yakamata a ce kin saba zuwa yanzu fa. Na so mu haWu yau mu sha hira sosai da sosai, na san sai kin yi watanni uku zuwa huWu ban sake ganinki ba, kuma kin hana ni zuwa makarantar taku"

"To ai da nisa sosai ba kaWan ba, kuma ba na son a gida a gane kana zuwa. Bari na ?arasa gida"

Bukar ya Wan tsare ta da ido sannan ya ce "Da alama dai wani na damunki, ban so mu rabu a haka ba, amma shikenan Ubangiji Allah ya tsare ya bada nasara. Ga sayayyarki nan ba yawa ki ?ara, zan yi kewarki abar ?aunata" Ya yi maganar yana mi?a mata ledar hannunsa. Ta tsaya tana kallon ledar.
Ya sake mi?a mata ya ce "KarSi mana" Sai da ta risuna sannan ta karSa ta ce "Na gode sosai da sosai. Wai ni kuwa ina Hanne? Tsawon lokacin nan ka ce mini ta yi tafiya, haryanzu ba ta dawo ba?.

Ya Wan girgiza kai ya ce "Ba ta da lafiya ne, jinya take yi sosai"

"Allah sarki, idan ka je gida ka gaya mata? ina gaishe ta, kwana biyu na daina ganinta, kuma ka gaya mata abin Soye na shirin fitowa fili. Na so zuwa da kaina na duba ta, amma ina jin tsoro saboda yadda ala?a a tsakaninmu ta ?ara yin tsami" Ta ?arasa maganar tana murmushi mai ciwo.

Ya ce "Kamar yaya kenan?"

"Idan ka gaya mata zata gane" Daga haka ta wuce ta bar shi a tsaye, yana kallonta.

Ramata ta gama haWa komai na tafiyarta, dan washegari Baffa zai mayar da ita makaranta.
Ta Waukko wayarta Tab,, da ta samu kyautarta a lokacin da ta ci gasar lissafi. Da fari Baffa cewa ya yi bai yadda ta yi amfani da ita ba, saboda an ce tana lalata tarbiyya, sai dai ya saya mata irin tasa mai madannai.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login