Showing 33001 words to 36000 words out of 53964 words

Chapter 12 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

773

mini sai na sayo mata?"

"Ina na san mata, ka san idan ta ga dama ta yi sa?ar ta sayar, ko ta kyautar. Dan kai ta gado a ungo"

Ya yi guntuwar dariya ya ce? "Ta sa?a wa Mamman hula ta ba shi, ya saka ta yaje masallaci da ita. Abin da nake gudu ya faru, amma zan Wau mataki na ?arshe a kai"

Da sauri Nadiya ta ce "A'a masoyi, kar ka...

"Shhhh" Ya katse ta yana zare mata ido, tare da tsuke fuska tamkar bai san yadda ake dariya ba.

*****

Daga nesa kaWan yake tsaye, yana hango ?ofar gidan Malam ?ayyabu, da rumfar almajiransa aka shimfiWa tabarmi ake zaman makokin rasuwarsa.
Duk wanda yakamata ya tambaya, da binciken da yakmata ya yi, amma babu wani gamsashen dalilin rasuwar malamin, kowa yana faWin ya kwanta bacci lafiya kalau, aka wayi gari da gawarsa.!

Alina ce a tsaye, hannunta ri?e da takalmanta na makaranta, tana tsaye a bakin shagon yana ta sallamar mutane.
Ya yi ?o?arin sallamarta, amma ta ce masa ya gama tukuna.

Kasancewar yamma ce, ana ta zuwa sayayya.

"Nifa na gaji da tsayuwa" Ta yi maganar tana tsuke fuska.

"To ai ke ki ka ce na sallame su, bari na ?arasa ranki ya daWe"

Ya sallami kowa, ya fito yana gyara zaman hularsa da ta sa?a masa. Ya saka hannu zai karSi takalman, ta janye abin ta, ta Soye a bayanta.

"Meyafaru kuma?" Ya yi maganar yana kallon ta.

Ta harare shi, ta kawar da kanta gefe.

"Subhanallah me na yi?"

"Ka sallami kowa ka ?i kula ni, kuma kana sallamar su, kana yin murmushi" Ta ?arasa maganar tana kawar da kanta gefe fuskarta Wauke da damuwa.

Ya yi dariya ya ce "Ni ne nake murmushin? Rigima dai ki ke ji, amma ban da ke kin ga ina yi wa wani murmushi? Ai ba na dariya murmushin ma ke kawai nake yi wa"

Ta Wago kanta suka yi ido huWu, kawai ta hau dariya, wanda hakan ya sanya shi ma ya yi guntuwar dariyar.

"?an albarka"

"Na'am 'yar ?walisa"

"Yaushe za ka cire gashin nan na fuskarka ne? Ina son na ga fuskarka sosai da sosai"

Mamman ya shafa fuskarsa ya ce "Yanzu ba kya ganin fuskartawa?"

"Eh mana, gashi ya fi yawa, idan ka aske sai ka fi kyau"

Ya jinjina kai ya ce "Ai abin da Mumsy take so shi nake so, zan aske ki ganni sosai"

Ta kalle shi ta ce "Mumsy, amma dai Mamman ka yi karatun boko?"

Ya girgiza kai ya ce "Ai ba sai mutum yaje boko ba zai san wani abin ba, amma bari na din ga ce miki Inna"

"Ni wallahi ba Inna ba ce" Ta yi maganar tana dariya. Ya karSi takalmanta, tana zaune ya goge su ya yi musu mai.

Wayarsa ce ta fara ringing, ya ciro wayar ya kalla, ya kalle ta sannan ya Waga ya yi sallama.

Ba ta san me ake ce masa a wayar ba, ta Waga takalminta tana kallo, ta ga ya sauke wayar a hankali, fuskarsa babu walwala.

"Ya dai meyafaru? Ko jikin Innar ne?"

Ya girgiza kai ya ce "Ma?wabtan ?auyenmu ne, aka yi rikici da manoma, da maharba, an karkashe mutane"

Cikin razana ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ubangiji Allah ya ta?aita. Ko za ka je gidan to ka gani?"

Jiki a sanyaye ya ce "Sai abin da Allah ya yi"

"A'a gara ka je, irin wannan kuskuren Yaya ya yi. Ya ce mu garinmu rikicin manoma da makiyaya ake yi, ba su Wau abin serious ba, sai da ya yi yawan da muka rasa iyayenmu, kuma aka kori wanda suka rage daga garin. Shi ne su suka taho nan, ya ce mukaWai muka rage a gidanmu. Kafin mu zo nan a gidan su Antynmu muka zauna, har ya aure ta, ita ma aka yi ta rikici a garinsu, aka kashe musu yan uwa muka taho nan. Duk an ?arar da danginmu, daga Allah sai yaya muke da shi." Ta yi maganar tana sanya tafukan hannayenta, ta rufe fuskarta tana fashewa da matsanancin kuka.
Ya yi shiru yana nazarinta, ya jinjina kai, sannan ya yi ?asa da muryarsa.
"Ki yi ha?uri 'yan mata, bayan yaya, gani kuma, in sha Allah zan kula da ke, idan yaya ya bani cikakkiyar dama, zan ba ki kulawa fiye da yadda ya baki. Amma ban san meyasa ba ya so na ba"

Ta share hawayenta ta ce "Ba sonka ne ba ya yi ba, baya son kowa ya raSe ni ne, saboda baya son ya rasa ni nima. Allah ya ta?aita muku yaya Mamman rashin ahali ba shi da daWi"

"Ki daina kuka, ko ki na son ki saka ni kuka nima? Ki daina"

Ta jinjina masa kai.

"Ba ki ga hulata ba ne?"

Ta yi murmushi ta ce "Na gani, ta yi maka kyau sosai da sosai"

Ya tashi tsaye ya Waukko biro da takarda, ya yi rubutu a jiki, ya mi?a mata.

"Wai a ina ka iya rubutu?"

"Koya na yi" Ya ?arasa maganar yana dam?a mata takardar.

Ta buWe takardar tana kallo, ta Waga idonta ta kalle shi, ta ga ya tsare ta da ido. Kawai ta tashi tsaye tana murmushi, ta kwashi takalmanta ta yi waje. Ya bi bayanta da kallo yana murmushi. Sai da ta Sacewa ganinsa sannan ya tashi ya shiga cikin kantin, ya Waukko wata wayar daban, ya danna wasu lambobi, ya saka a kunnensa.

A ?ofar gida ta tarar da Yaya a ?ofar gida a tsaye.

"Wankin takalmin ne sai yanzu?" Alina ta yi shiru tana sunkuyar da kai. Bai ce mata komai ba, ya yi gaba ya bar ta.

*****

Ana ta jarrabawa, saura guda Waya a kammala, Rahama na ta shirin gida.
Bayan sun dawo daga night pref. Ta je ta yi wanka, ta shafa alamun Win ta, ta yi shirin kwanciya bacci.
Tana jin Ru?ayya na ce mata, ta taso su ci abincin dare, amma ta ce ta ?oshi, saboda wani irin bacci da take ji yau.
Dogon wandon skin tied ta saka, sai vest doguwa har gwiwa, sai da ta hau kan gadonta, sannan ta cire hijjabinta ta kwanta, kasancewar lokacin yanayin na zafi ne, garin da zafi sosai.

Duk da tana jin bacci, ta janyo littafinta a jakarta, ta kunna fitilarta tana haskawa.

Tarihin gwagwarmayar karSar 'yancin take karantawa. Gudunmawar da su Sir Ahmadu bello
Dr. Nnamdi Azikiwe
Chief obafemi owolowo
Sir Abubakar tafawa Salewa suka bayar gurin karSar wa ?asa 'yancin kai.

Yanayin yadda mulki ya fara gudana, a wancan shekarun. Yanayin yadda sir Abubakar tafawa Salewa, ya zama priministre? na farko, yadda ya fara gudanar da mulkinsa. Gaba Waya ba dukiyar ?asar ce a gabansu ba, ?asar suka yi ?o?arin ginawa da dukkanin karfinsu. Sai dai kash an yi juyin mulki a alif dubu Waya da Wari tara da sittin da shida 1996 a sha biyar ga watan January. Juyin mulkin da wasu tawagar sojoji suka yi, ?ar?ashin jagorancin wani soja Major Chukuma Kaduna Nzeogwu, da wasu sojoji irin su Major Emanuel Ifeajuna. Inda aka je har gida aka tafi da shi. Daga bisani kuma aka tsinci gawarsa an kashe shi. Kisan Sir Abubakar tafawa Salewa ya kawo rikici a ?asar a wancan lokacin. Daga nan General Aguyi-Ironsi ya karSi mulkin ?asar.

"Kash mtseww"

Ru?ayya na daga gadonta na ?asan Rahama ta ce "Rahma lafiya kuwa?"

"History nake karantawa"

Rukayya ta yi dariya ta ce "Na zata kin daWe da yin bacci ai. Ina mamakin abin da ya haWa Walibar kimiyya da karance-karancen tarihi"

Rahama ta ce "Anty Ru?ayya zama guri Waya tsautsayi in ji kifi, kuma shi karance-karancen na karawa mutum ilimi. Tarihin mazan jiya nake karantawa yadda aka faro kafa ?asar nan da samar mata 'yanci, da yadda aka fara mulki. Da an bi tafarkin da suka Wora ?asar tun da farko, da tuni mun fi haka ci gaba. But so sad an zubar da jini da yawa, an yi wa Sir Abubakar tafawa Salewa coup an kashe shi, despite all his efforts. Ba ki ji zuciyata ba" Ta ?arasa maganar a Wan shagwaSe.

Rukayya ta saka dariya ta ce "Lallai ma Rahama, ita kanta Duniyar, da ?asashen da suka kai inda suke yanzu da zubar da jini suka kafa ta. Ki ci gaba da karanta tarihin akwai abin da ya fi wanda aka yi masa ma"

Rahama ta yi guntun tsaki ta ce "Ni na karaya ma. To ina sojojin da suke tare da shi, suka bari har aka shiga aka Wauke shi, aka tafi da shi aka kashe dan Allah?"

"Rahama kenan, ba a cin gari ai sai da Wan gari. Galibin juyin mulki da ake yi, da sanin masu tsaronsu. Da Yaya na nan da kin sha bayani. Babu yadda a aikinsu ko kaWan. Wataran zan haWa ki da Yaya Ammar, ki sha labari"

Rahama ta ce "Daina bani labarin nan, zuciyata za ta karye da yawa. Sai da safe bari na yi azkar na kwanta" Ta yi maganar tana sauke ajiyar zuciya. Ta lumshe idanunta ta Waga hannayenta tana karanto addu'a kwanciya bacci.

*****

"Kangiwa, kana ganin yadda al'amura suke neman fin ?arfinmu a ?asar nan ko? Dama haka mulkin yake? Wallahi da na san haka yake ba zan yadda na karSi ?asar nan ba"

Kangiwa ya ce "Haba mr. President kar ka saka mu karaya mana, ka daure mu ga abin da za mu iya yi"

"An dabaibaye komai fa, yanzu kalli uban bashin da ake bin ?asar nan. Trillion Wari da hamsin da biyu da Wigo huWu fa"

"Mr. President, ?asashen da suka ci gaba a duniya, ai duk da basussuka suka gina ?asashensu"

"Amma Kangiwa su ?asashensu suka gina, mu kuma wasu ne suke gina kansu. Ana maganar billion sau billions ne fa. Me da me aka yi a ?asar na wannan uban kuWin haka? Ga uban kuWin ruwan da ake lafta mana. Yanzu babu ta inda za mu yi kasafin kuWin shekara mai zuwa fa, babu komai a ?asar nan, kai shaida ne da muka zo mulkin nan account Win ?asar babu komai sai abin da ba a rasa ba"

Kangiwa ya jinjina kai cikin damuwa ya ce "Your excellency, bamu da wata mafita da ta wuce mu ranto kuWin da zamu yi kasafin kuWin baWi"

"Kangiwa bashi again?"

"Mr. President bamu da wata mafita idan ba wannan ba, harajin da muke samu, ba zai samar mana da wannan kuWin ba. Ga Wanyen mai ya faWi a kasuwar duniya, ga satar mai da ake yi da yake ?ara kassara mu. Ciyo bashin nan ne kawai mafitarmu"

Kankiya ya kashingiWa yana cije lips Win sa, ya buWe idanunsa da kyar ya kalli Kangiwa ya ce "Ina tausayin al'ummata. Amma kafin mu kai ga wannan gaSar, zan zauna da shugabanin hukumar ya?i da cin hanci da yi wa tattalin arzikin ?asa zagon ?asa. Dole a matsa tsofaffin wanda suka ri?e madafun iko, a matsa duk wanda aka kama da ha'inci, su dawo mana da dukiyar da suka sata."

Kangiwa ya yi murmushi ya ce "Wannan ma dabara ce, bari na je meeting Win da ka sanya ni, na ga lokaci ya yi"

Kankiya ya ce "To shikenan babu laifi"

Kangiwa na baro office Win, ya ja ya tsaya, ganin kiran Makama na shigo wayarsa.

Ya Waga yana faWin "Ranka ya daWe"

"Ka yi ganawar sirri da Kankiya, me ku ka tattauna?"

Kangiwa ya waiwaya bayansa, sannan ya ce "Na naWi komai zan tura maka yanzu in sha Allah"

"Ina saurarenka"

*****

Alina zaune a ajinsu ta ajiye Alqur'aninta a gabanta ta zuba masa ido, sai murmushi take yi.
Hafsa ta taSa ta ta ce "Lafiya, murmushin me ki ka yi haka ne? Karatun kuwa ki ke yi?"

Alina ta girgiza kai ta ce "Wani abu na tuna"

"Yaya Mamman Win ne? Alina wai Mamman Win nan saurayinki ne? Soyayya ku ke yi? Ke kuwa me za ki yi da mai wankin takalmi, provision store Win ma fa ba nasa bane ba"

Alina ta Sata fuska ta ce "Ce miki na yi mu na soyayya ne? Mutunci kawai muke yi"

"Kuma shi ne kullum sai kin yi zancensa, ko ya biyo ki Islamiyya ku tafi tare?"

"Wai ke Hafsa haka aka ce miki? Babba ne fa ya kusa Yayanmu"

Hafsa ta ce "Ke wallahi soyayya ku ke yi, kuma Yaya Ismail ya sani?"

Alina ta kwaSe baki ta ce "Yaya ba ya son ala?ata da shi, amma yana yi mini kirki ne kawai"

Hafsa ta addabi Alina a kan lallai sai ta yarda soyayya suke yi da Mamman, amma Alina ta share ta.

Ko da aka tashi daga Islamiyya, su na fitowa daga gate Win makarantar, suka hango shi a tsaye hannunsa ri?e da wayarsa mai madannai.
Hafsa ta taSo Alina da ke sayen Agwalima, ta ce "Ga saurayinki can ya zo yana jiranki"

Alina ta Waga kai, ta gano Mamman yana nufo su. Hafsa ta Wan ja baya, saboda tsoro yake ba ta.

"Nawa za a sayar mana da agwalumar nan gaba Waya" Ya yi maganar yana kashewa Alina ido. Sai da ta Wan rikice, tare da kallon Hafsa ko ta ga abin da ya faru. Wani irin sassanyan ?amshi ne yake tashi daga jikinsa, gaba Waya suturar jikinsa ba ta dace da ?amshin turaren da yake yi ba. Idan ba ta manta ba, lokacin da yaje Asibiti irin wannan ?amshin yake yi, amma ya ce mata shi ba shi ba ne ba.

"Inna mu saya duka ne?" Ya yi maganar yana karSar ta hannunta da ta ri?e.

"Inna ko?" Ta yi maganar tana hararsa.

Ya yi murmushi ya ciro Wari biyar a aljihunsa, ya mi?a wa mai agwaluma ya ce ya zuba mata ta 500.

"Ta Wari biyar ai ta yi mini yawa, ta Wari zai bani, kuma guda biyu manya"

Mamman ya ce "A Wari za a baki biyu manya, ga wannan ?ara mata" Ya ?ara ciro Wari biyar ya ba shi.
Ta Waga kai za ta yi masa magana, amma ya harare ta, aka cika mata ba?ar leda da Agwaluma suka tafi.
Hafsa kamar ta bi Alina da gudu ta sha?e ta, ta tsaya jiranta, ita kuma ta yi tafiyarta ta bar ta.

Ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro leda ya ce "Ungo" Ta saka hannu ta karSa ta ce "Na waye?"

"Nawa ne" Ya yi maganar yana basarwa.

Alina ta ce "Yi ha?uri, nawa ne?"

"Mmm babu yawa"

"Na gode sosai da sosai ?an albarka, amma dan Allah ka daina kashe kuWinka haka, ka ga...

"Kin raina kyautar almajiri ko?"

Da sauri ta girgiza kai ta ce "A'a ba haka ba ne, na gode sosai da sosai"

Har ?ofar gida ya raka ta, sannan ya juya ya tafi shago.

Ko da ta shiga gida, ta tarar da Nadiya kamar ita take jira ta ce "Kin dawo? Dama ke nake jira"

Alina ta ajiye kayan hannunta, ta ce "Meyafaru?"

"Leda za ki karSo mini, da zan ?ulla tuwo. Sai da na gama tu?awa na duba na ga bani da ita. Meye wannan a hannunki?"

Alina ta mi?a mata ledar tana faWi. "Mamman ne ya saya mini agwaluma, sai kuma wannan ledar, da nake son ganin mene ne a ciki". Ta ?arasa maganar tana zaro turare a cikin kwalinsa.
Ta ce "Wow kin ji ?amshinsa" Nadiya ta karSi turaren, tana jujjuya shi tana kallon Alina. Ta ce "Amma kuwa ya yi ?amshi sosai, je ki ki karSo mini ledar" Alina ta karSi kuWin ta sake fita.

Ismail ya fito daga Waki ya ce "Yanzu kin yadda da abin da nake gaya miki ko?"

Nadiya ta jinjina kai, jikinta a sanyaye.

"Jibi in Allah ya kaimu, huWun Asuba za mu bar garin nan,kar ki gaya mata ma, ba zan jira ta yi saukar ba ma" Nadiya ta jinjina masa kai. Tana jujjuya turare.

Wani matashi Alina ta hango a cikin shagon a tsaye, zai yi Mamman a tsaye, har ?irar jikinsu iri Waya, sai dai ba ta taSa ganinsa ba sai yau.

Ba ta damu da shi ba, ta shiga ta tsaya, sai dai ta ji ta a takure saboda mutumin.

Mamman ya ce "Na zo ne?"

Ta girgiza kai ta ce "A'a leda ba?a ?anana ta saka tuwo zaka bani"

Ya ce "Waye ya yi tuwon, ke ko Antynmu?"

"Anty ce, Yayanmu ya ce nata ya fi daWi, ni jagwalgwalo nake yi"

"Ni kuma naki ya fi daWi a bakina. Ya ki ka ga kyautar tawa, ta burge ki?"

Alina ta jinjina kai tana murmushi, ta karSi ledar, ta mi?a masa kuWi, ya ?i karSar kuWin. Na cikin kantin na ta son ya kalle ta, amma ta juya masa baya ta fita.

Tana fita ya tuntsure da dariya ya ce "Allah wadaran naka ya yi expire"

Mamman ya tsuke fuska ya ce "Fita ka bar gurin nan ka tafi dan Allah"

"Ba zan tafi ba, ji wata riga a wuyanka kamar korarre, saboda tsabar mutuwa har ta fara gari za ta koma audugarta" Ya yi maganar yana ?ya?yata dariya"

Mamman ya ce "Dalla malam ware, dan Allah ka tafi"

"Kai wallahi ba zan tafi yanzu ba. Kai tsaya wai kai ne ka ke kashewa yarinya murya haka kana mata wani kallon iskanci anya kuwa kai ne?"

Mamman ya ja guntun tsaki ya ce "Bari kawai, sai shashashanci nake da yarinyar da na haife ta ko? Ni kaina kamar na yi wa kaina shegen duka"

"Ka haife ta a ina? Gyambo sarkin girma?"

Mamman ya yi tsaki ya ce "Za ka wuce ka je ka shirya abin da ya dace, ko kuma zaka ci gaba da rashin mutuncin ne?"

Da kyar yake ?o?arin controlling Win dariyar da yake yi, ya ce "Na ji. Amma sace yarinyar za a yi kenan?"

"Ina tunanin haka, sai dai yadda plan ya kasance. Ka ga a zahiri babu alamun kuWin nan a tattare da su. Amma dai na tabattar da duk abin da yakamata na tabattar.

Matashin ya jinjina kai ya ce "Daren yau ko na gobe za mu ?addamar da aikin?"

Mamman ya fito ya ce "Mu je hanya mu ?arasa"

"Amma yarinyar nan fa, kamar sonka take yi fa. Kai amma tun da aka haife ni ban taSa ganin abin da ya bani dariya kamar yau ba. Madakin maza a cikin tsummokara yana kashewa yarinya murya Allah ya isan maza"

Ashariya Mamman ya Wura masa yana hankaWa shi waje, amma ya ma?ale yana ?ya?yata dariya.

*****

Duk da nisan da baccinta ya yi, amma haka kurum ta kasa jin daWin baccin. Banda miyagun mafarkai marasa daWi babu abin da take yi. Wata irin hayaniya mai razanarwa ta din ga ji a saman kanta, ta kasa tantance wace irin hayaniya ce haka, kuma ta kasa farkawa daga mummunan mafarkin da take yi.

Sautin murya kawai take ji ana ?wala mata kira "Rahama!Rahama!"
Kamar daga sama ta ji an dan?ota an yo ?asa da ita daga kan gadon. Sai a lokacin ta buWe idanunta, ta din ga jin guje-guje da iface-iface a zahiri. Hostel Winsu ya hargitse, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login