Showing 39001 words to 42000 words out of 53964 words

Chapter 14 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

775

mini mu?amai na na bawa wasu".

General Jalal ya Wan yi gyaran murya ya ce "Mr. President tabbas wannan kuskurenmu ne, zan iya cewa sakacinmu ne ma da har wannan al'amari ya faru. Amma mu na mai baka tabbacin da yardar Allah, yaran nan za su kuSuta. Amma muna neman alfarmarka mako guda ya yi kaWan...

A fusace ya ce "7days Lieutenant General Jalal, 7days kawai ku ke da shi, akasin haka ku ajiye mini mu?amaina"

"Ok sir" Haka suka tashi sumi-sumi suka fice daga ofishin.

Su na fita Barwa ya ciro wayarsa ya daddana. Ya kara a kunnensa.

"Jagora barka da wannan lokaci"

"Barkanmu dai Barwa, bamu labari"

"Shugaba fa ya Wauki zafi ba kaWan ba, kwana bakwai kawai ya bayar a nemo yaran nan, ko su ajiye masa mu?amansa ciki har da ni"

Ya kwashe da dariya ya ce "?aryar banza ce ?iba a kunne, shi ya isa ma? Zan yi magana da Boss ?agwai, tun da shi ne God father Winsa, dole ya janye wannan maganar. Kana ganin yadda muka fara raba kan ?asar ko? To ba a yi komai ba ma. Sai ya tattara hankalinsa a kan yaran can, za mu sake Sallo masa ruwa, kai dai ku ci gaba da bin abin da aka tsara. Ka kwantar da hankalinka yara dai ba za su fito yanzu ba, ka zuba ido...

*****

Tuni labarin sace Waliban makaranta mata, kimanin hamsin ya cika gidajen rediyo da kafafen watsa labarai da na sada zumunta na ciki da wajen ?asa. Duk inda ka buWe babu abin da ake yi sai maganar, saboda abu ne da bai taSa faruwa ba a tarihi.

Sai da su Rahama suka kwana guda curr, babu ko ruwa a cikin su, a kwana na biyu, aka bi su da ruwa Waya mutum biyu, sai buredi mai yanka-yanka kowa guda biyu. ?afafuwan Rahama suka kumbura sosai saboda azabar tafiyar ?afa da suka yi. Inda suke daji ne sosai da sosai, sai dai saboda tsabar sur?u?insa ko rana ta take, bata wadatar dajin da wadattacen haske saboda tarin dogwayen bishiyu.

****
Alina ta yi wata irin mummunar rama, ta yi zuru-zuru saboda azabar tsoro da kuma tashin hankali.
Tun safe Nadiya ta fita ta koma gurin jami'an tsaro, domin jin ko akwai wani labari.
Alina na zaune ta yi zuru a tsakar gida, ta ji ana ?wan?wasa ?ofar gidan su.
Jiki a sanyaye ta sanya hula a kanta, ba tare da ta tambayi waye ba, ta buWe ?ofar gidan.
Turus ta yi bayan tozali da fuskar Mamman, kawai ta hau bin fuskarsa da kallo.
Fuskarsa Wauke da damuwa ya ce "'yan mata, abin da ya faru kenan? Na je gida duba jikin Innata, na dawo Alhaji yake gaya mini an nemi Yaya Ismail an rasa"
Tsuruu ta yi da ido tana kallonsa, ta ma rasa me za ta ce masa gaba Waya.

"Ya na ga kina kallona a haka?"

Ta sunkuyar da kanta, sai a lokacin hawayen da ta gaza zubarwa ta samu damar zubar da su, zuciyarta na wani irin ?una da tafasa.

Cikin tausasa murya ya ce "Ki yi ha?uri, in sha Allah za a gan shi, an je gurin 'yan sanda an sanar musu?" Ta jinjina masa kai kawai.

"Ki yi ha?uri dan Allah, ki daina kukan nan haka" Ta Waga fuskarta a hankali tana kallon idanunsa masu bata tsoro, a yau ta samu kallonsu da cikakken ?warin gwiwa, amma ta gaza furta komai. Sai dai da ta ?ara matsawa kanta ta fuskanci akwai wata Soyayyiyar fuska a bayan wannan fuskar da yake mu'amalantarta da ita...

Ayshercool
08081012143

1k ne a telegram 0069685771
Aisha Adam stanbic
https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

MORE PAGES AVAILABLE AT AREWAPEN


SARA DA SASSA?A...
YOTA 002
AYSHERCOOL

Page 12

Turus ya ja ya tsaya cikin tashin hankali, bayan da ya kunna wayarsa ya ci karo da batun sace Walibai da aka yi. Cikin sauri ya kira wayar Ummi. Sai dai wayar ba ta shiga.
Cikin tashin hankali ya lalubi wayar Amir, sai dai ta kusa katsewa sannan ya Waga. Cikin hargowa Ammar ya fara yi masa faWa "Wani irin iskanci ne zan din ga kiran wayarka ka ?i Wagawa?"

Amir ya ce "Ba ?in Wagawa na yi ba wayar na mota...

"Dalla ina Ummi take? Me yake faruwa ne?"

"Abin da ka ke son tabattarwa ya faru, an shiga makarantar su Ru?ayya an yi garkuwa da Walibai hamsin, amma Alhamdillah luckily she's not among, mun je Waukko ta ni da Baba Sani, sai dai tana cikin tashin hankali sosai da sosai"
Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya nemi guri ya zauna yana faWin "Amir, ka tabatta tana lafiya babu abin da ya same ta?"
"Eh lafiyarta ?alau, sai dai a tsorace take ne kawai"

"Shikenan take care, zan sake kira in sha Allah " ya kashe wayar yana hamdala.
Wayar ce ta fara vibrating, kira yana shigowa.
Ammar ya Waga wayar ya saka a kunnensa.
"Yaya ake ciki?"

Ammar ya numfasa ya ce "She's safe, ba ta cikin wanda aka sace"

Ya yi ajiyar zuciya ya ce "Alhamdillah"

"Wai komawar ka sake yi da gaske?"

"Eh, ai ban gama ba, alamu sun nuna akwai sauran rina a kaba"

Ammar ya ja guntun tsaki ya ce "Ka na da matsala Mega, wannan Win ma da aka yi, ba wani appreciation na kirki, ana ma doubting idan mai laifin ka kama. Ka kuma koma, ban san me ya mayar da kai ba kuma"

"Ba aikinsu kawai na koma yi ba, wannan aikina ne, ina son gyara Sarnar da na yi"

Ammar ya ce "Kuma sun san da hakan? Sun san ka koma?"

"A'a. Akwai abin da nake bibiya ne, and ban bayar da wayarsa ba, tana hannuna ina son za mu yi aiki a kanta"

Ammar ya ce "Good, keep it safe kar ka kuskura ka dam?a musu ita tukuna, ka fara tsayawa mu ga iya gudun ruwansu"

Mega ya ce "Kai na san abin da nake yi fa, idan na kammala abin da nake yi, idan na tabattar babu sauran wani abu, zan dawo soon in sha Allah"

"Anyway yadda ake ciki, ka yi mini magana. Take care"

"Shikenan" Ya katse wayar.

*****
Yana zaune a ?ar?ashin bishiya, yana shan sigari, gefensa wasu manyan matasa ne su huWu. Ri?e da manyan bindigogi su na kaiwa su na komowa.
Ya ciro ?aramar wayarsa ya duba sa?on da ya shigo.
"Da alama dara ta ci gida, 'yan maza sun shiga hannu"
A sukwane ya mi?e tsaye yana sake karanta sa?on. Da sauri ya fita ya sake danna lambar amma shiru.
Cikin sauri ya buWe bayan wayar, ya zaro layukan da ke cikin wayar, ya kakkarya su, ya watsar ya cillawa Waya daga cikin matasan da ke tsaye a kansa wayar ya ce "Ka jajjage ta yanzun nan, mu bar gurin nan dawa ta Saci" Nan da nan suka je inda suka ajiye baburansu ?irar boxers, suka hau suka bar gurin.

*****

Dattijo ne da shekaru sun ja, duk da hutu da jin daWin da ake ciki, amma yanayin tsufa ya bayyana a tattare da shi, yake zaune a kan kujera 3 seater. President Faruk Kankiya na kan kujerar da ke facing Win dattijon cikin girmamawa.

Dattijon ya ce "Mu na mai jajanta maka, gami da takaicin abin da ya faru a mulkinka, na sace Walibai 'yan makaranta. Amma ina mai tausarka da baka shawara ka bi komai a nutse sannu a hankali, kar ka yi garaje ko gaggawa ko kaWan, idan ba haka ba lissafi zai ?wace maka. Batun bawa rundunar tsaro kwanaki bakwai su dawo da yara ba abu ne da zai yiwu ba. Kai ba jami'in tsaro bane ba Faruku, ka ba su dama su yi aikinsu domin ceto yaran nan cikin sau?i ba tare da an yi asarar rai ba. Duk da a rahotannin da muke samu an kashe masu tsaron yaran, da yarinya guda Waya, amma ba ma fatan a sake rasa rai. Batun za ka sauke shugabanin tsaro ba shi ne mafita ba. Kamar yadda ka ke faWa aiwatarwa ne naka, yiyuwar lamari na Allah ne. To su ma hakan ne, ka ba su dama, ka toshe kunnuwanka da surutu da tashin hankalin mutane za su ruWuka ne kawai. Sai kuma ka je ?afa da ?afa makarantar, ka ga halin da makarantar ke ciki ka kuma jajantawa iyayen yaran da ba su ?warin gwiwa, ka nuna yaran nan da aka sace naka ne"

Jiki a sanyaye Kankiya ya ce "Na fahimce ka ranka ya daWe, na kuma gode sosai da sosai da wannan shawarwarin da ake bani, atleast na samu releif na kuma fahimci kuskuren da na so tafkawa. Na gode sosai da sosai "

"Good, a yi ta ha?uri da yardar Allah komai zai daidaita" Ya jinjina kai ya tashi suka yi musabaha da dattijon ya fice.

*****

Jikin Mama ne yake karakarwa, tamkar mai shirin hawa bori. Hafsa da Mariya sun yi mata ?uri da ido, su na jiran su ji me za ta ce, bayan ta sauke wayar daga kunnenta.
Hafsa ta ce "Mama mene ne? Me aka ce miki?"

Da kyar ta iya ?wato "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ta mi?e tsaye ta fizgo mayafinta a kan gado"

Mariya ta ce "Mama kin ?i yi mana magana, kuma jikinki sai rawa yake yi me aka gaya miki ne?"

"Mariya Naja, Naja'atu an ce ba a ganta a cikin sauran Waliban ba, shiyasa dama na ce da ku bari na je a duba"

Hafsa ta ce "A'a Mama, ko kin je babu abun da zai canza, yanzu ina za ki je?"

"Gurin su Babballe zan je na sanar musu"

Mariya ta ce "Mama babu abin da za su tsinana mana, dama ki rabu da su"

"A'a ku jira ni ni dai na je na gaya musu" Ta nufi hanyar fita, sai dai ta ji jikinta ya yi mata nauyi, da kyar take Waga ?afafuwanta.

YELWA

Can garin su Ramata, tuni labari ya cika garin an sace Waliban makarantar su Rahama. Cikin matsanancin tashin hankali Baffa ya tafi makarantar ,domin duba waWanda ba a sace ba, ko da Rahama a ciki, sai dai cikin Waliban kaf babu Ramata.
Jikinsa na tsuma ya fito ya samu wata baranda ya nemi guri ya zauna yana nanata Innalillahi wa Innalillahi raji'un.

Shugaban makarantar ne, ya nufo Baffa jikinsa a sanyaye ya ?araso gefensa ya zauna. Ya dafa kafaWarsa cikin ?o?arin kwantar masa da hankali, ya ce "Ka yi ha?uri, Malam Bashir mu Wauki wannan al'amarin a matsayin ?addara. Mu kuma yi addu'a. Gwamnati ta bamu tabbacin yaran nan za su dawo cikin aminci. Da yardar Allah za su dawo gare mu"

Baffa ya numfasa ya ce "Na yi imani da ?addara, na sani ko a gida hakan za ta iya faruwa. Ni tunanina Waya Ubangiji Allah ya tsare mana su, ka sani ni ita kaWai ce da ni yanzu" Ya ?arasa maganar cikin rawar murya.

"Ka yi ha?uri, mu ci gaba da yi musu addu'a, in sha Allah za su kuSuta cikin aminci"

Har da jami'an tsaro aka haWu a ka din ga tausar Baban Ramata, duk da akwai sauran iyaye da aka sace wa yara. Amma duk wanda ya ga yanayin mahaifin Rahama dole ya tausaya masa. Idanunsa da farar fatarsa ta yi jawur, jijiyoyi duk su ka fito raWa-raWa a goshinsa saboda tashin hankali. Har tasha wani jami'in tsaro ya kai shi aka saka shi a mota, ya nufi Yelwa.

*****

Tun da Isma'il ya yi Satan dabo, kwana na biyar kenan, mutane na ta shigowa yi wa su Alina jaje, tare da fatan Allah ya bayyana shi.
Sai dai haryanzu abin da yake Waure mata kai, bai wuce yadda Mamman ya nuna damuwarsa a kan Satan Yayanta ba. Ga shi tamkar ya yi mata asiri, ta kasa gaya wa kowa abin da ya faru.
Yau ma da ya aika yaro ta zo, Nadiya ba ta ce komai ba, dan a ganinta, zuwansa na Wan ragewa Alina damuwar da take ciki.
Tun da ta fito ya tsare ta da ido, amma ta sunkuyar da kanta ?asa. "Ya nuna mata gefensa kan barandar gidan, ta nemi guri ta zauna.

"'yar ?walisa, kin ga ramar da ki ka yi kuwa?" Ya yi maganar daki-daki. Ta sunkuyar da kai ba ta yi magana ba.

"Alina, wannan yanayin da ki ka shiga, ba zai haifar da Wa mai ido ba, ki yi ha?uri ki kwnatar da hankalinki. In sha Allah duk inda yake zai bayyana, amma wannan damuwar ba ta kamace ki ba. Tsananta addu'a yakamata mu yi a wannan gaSar"
Ta yi shiru ta kawar da kanta gefe guda.

"Alina" Ya kira sunanta. Ta Waga kai a hankali ta kalli cikin idanunsa. A take abin da ya faru ya fara dawo mata, kuma tana da ya?inin shi ta gani ba wani ba.
Tun da Isma'il ya Sace sai a lokacin hawaye ya samu zubowa daga idanunta.
Cikin sanyin jiki ya ce "Alina kar ki yi kuka dan Allah. Ki yi ha?uri" Tamkar ya ziga ta, ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ta tashi da sauri ta shige gida ta bar shi a gurin a zaune.

*****
YELWA

Duk da yadda 'yan uwan Baffa ke jin haushinsa, na ?in aurar da Ramata ya kai ta makarantar boko, sun shiga tashin hankali da labari ya fara bazuwa cewar an shiga makarantar su Ramata an saci Walibai.
Ko da ya tafi dubawa ko har da Ramata a ka Wauka, bai gaya wa kowa ba sai Juma. Ita kuwa yana tafiya ta je ta gaya wa su Maddibo. Aikuwa hankalin kowa ya tashi. Mussaman 'yan uwan mahaifiyar Ramata da babu yadda ba su yi ba, ya yi mata aure amma ya ?i.

Sai bayan la'asar sosai sannan ya dawo gida.
Aikuwa ya tarar da gidan a cike da mutane.
Su na ganinsa suka yi kansa da tambayoyi a kan ina Ramata.
Jiki a sanyaye ya samawa kansa gurin zama.
"Kai Jibo, ina yarinya take ka dawo kai kaWai?" Modibbo ya yi maganar cikin za?uwa.

"Ramata na cikin yaran da aka yi garkuwa da su" Ya ba su amsa kai tsaye, dan bai ga amfanin Soye-Soyen ba.
Salati suka saka gaba Waya.

Cike da takaici Sambo ya ce "Ka gani ko? Babu irin abin da bamu gaya maka ba, game da kai yarinyar nan can wata uwa duniya da sunan boko, ga shi yanzu ka salwantar da rayuwarta a banza. Ita kaWai dama ta rage maka, yanzu ga abin da ka janyo"

Maddibo ya ce "Ya isa haka, Ramata dai 'yarmu ce, yanzu tayar da jijiyoyin wuya da hayaniya ba namu bane ba, iyaka kawai mu ri?e addu'a Ubangiji Allah ya bayyana ta"..

Baffa ya kwashi takaici da miyagun maganganu a gurin 'yan uwansa, duk da halin da yake ciki.
Yana ji yana gani, abinci ya gagare shi, salla sai ya sallame sau biyu, saboda rafkanuwa. Ya zauna ya ja uban tagumi, ya ji sallamar Wan gidan Iro Yayansa Amiru, wanda aka so haWa shi aure da Ramata, Baffa ya dage makaranta za ta yi.
Baffa ya amsa masa, ya yi masa iznin shiga.
Ya shiga yana sake sallama, Baffa ya yi masa iso, tare da nuna masa kusa da shi ya zauna.
Jiki a sanyaye Amiru ya ce "Baffa ashe tsautsayin da ya faru da Ramata kenan?"
Baffa ya sauke numfashi ya ce "Wallahi kuwa Amiru, an sace su Ramata. Duk ana Wora mini laifin faruwar hakan, amma ni uba ne, ba zan taSa aikata abin da zai cutar da 'yar da na haifa kuma ta kasance itakaWai ta rage mini ba"

Amiru ya ce "Na sani Baffa, kuma na fahimce ka, sai dai mu haWu mu yi ha?uri, mu yi ta addu'a Allah ya bayyana ta"

Amiru ya din ga rarrashin Baffa, sun daWe tare sannan Amiru ya yi masa sallama ya tafi.

Sai dai Baffa bai karaya da lamarin ba, sai da dare ya tsala, ya tuna Ramatansa bai san a inda take ba, bai kuma san a yaya za ta kwana ba.
Tsakar gida ya fito, ya tsaya a tsakiyar farin wata, ya sakawa ?ofar Wakinta ido. Lokacin da ya kai ta makaranta, tare da shugaban makarantar primary Win su Rahaman, sai da aka kai shi har Wakin da aka bata, da gadon da aka bata ya tabattar da tana kauwwame a guri Waya, sannan ya amince wanda tsawon shekarun nan, ko ya kaita makarantar wasu lokutan sai ya yi ta damuwa da rashinta a kusa da shi. Balle yau da ba a san ma a inda take ba.
Ya ja da baya a hankali ya jingina da jikin danga, sai kuma abubuwa daban-daban suka fara dawowa kansa game da garin, baya tunanin kaf garin YELWA akwai wanda ya haWu da masifu kala-kala kamarsa. Haka ya wanzu yana tuna abubuwa daban-daban marasa daWi da suka faru da shi a garin.

*****
Tamkar ba?in hadarin damuna, mai Wauke da iska haka ya murtuke fuska hanunsa ri?e da waya, ya kara ta a kunnensa yana jiran a Waga.
Yana kwance a kan doguwar kujera yana kallon talabijin, kiran wayar ya cika masa kunne.
Kuma wayar da ba kowa kiransa a ita ba, sai mutane na musamman. Ya duba ya ga lamba ce babu suna, ya Waga kai kunnensa. Sai dai shiru ba a yi magana ba.
"Wa ke magana?"

"Sadauki ne"

"Waye hakan?"

"Idan ma ka gane waye, idan ba ka gane ba, Waya daga cikin manyan yaranmu, ya yi Satan dabo, bamu san inda yake ba, kuma Kacalla Sumale na matu?ar ji da shi, dan haka ina fatan babu hannunku a cikin kama mana yaro"

"To kai Wan samari, ta yaya ka ke tunanin zan saSa yarjejeniyarmu ne? Bamu saka an kama kowa ba, hasali ma mu na ta ?o?arin ?ara gyara muku hanya ma"

Sadauki ya ja ajiyar zuciya ya ce "Shikenan, ya yi Satan dabo ne bamu gan shi ba, mu na kyautata zaton ko kama shi aka yi, amma za mu ci gaba da duddubawa. Yaran nan su na nan a tare da mu, ku sako kuWin Abincinsu. Sannan duk abin da gwamanati ke ciki a sanar da mu, dan idan rana ta ?wace tare za ta ?wace mana"

"Ka kwantar da hankalinka, ina da tabbaci a kan shirin da muka yi"

"Shikenan"

"Yauwwa Wan samari, za a kawo muku sa?on, zan turo da lambar motar, da inda za ku je ku karSa"

"Yayi" Sadauki ya faWa a ta?aice ya katse wayar.

Dattijon ya yi dariya ya ce "Idan rana ta ?wace, zata ?wace mana mu da ku a ina? Yaro bai san wuta ba sai ya taka.

*****

Wani irin azababben sanyi ake yi a gurin, Ramata ji take yi tamkar ta fi kowa jin sanyi. Jikinta sai wata irin karkarwa yake yi.
Yunwar da take ji, har ta ci ta cinye ta, abin da ake ba su sam baya isar su. Gaba Waya hancinta a toshe yake,? da baki take numfashi saboda matsananciyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login