Showing 48001 words to 51000 words out of 53964 words

Chapter 17 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

777

kowa sai ya zarge ta da laifin faruwar komai dalilinta, dan babu irin kashedi da jan kunnen da Yaya bai yi mata ba a kan Mamman.
Tun safe Alina ke kallon Nadiya daga kwance, tana harhaWa musu kayansu a bagco.
Ta dubi Alina cikin kulawa ta ce "Sannu ?anwar Yaya"

Alina ta jinjina kai ta ce "Anty ina zamu ne, na ga kina haWa kaya?"

"Tafiya zamu yi" Ta bata amsa.

"Ina za mu je?"

"Garin nan zamu bari"

Cikin rashin fahimta Alina ta ce "Mu je ina? Idan yayan ya dawo kuma fa?"

Nadiya ta ce "Alina kin fiye tambaya, ki zuba ido za ki gani, ci gaba da zamanmu a nan ba shi da wani amfani, Yaya kuma duk inda muka shiga, in dai ya dawo zai neme mu"

Alina ta sake cewa "Ta yaya zai san ina muka tafi, ko kin san inda yake ne?"

"Alina, ki kwanta ki yi shiru ki samu bacci, wannan ciwon kan ya sake ki, idan abin ya ci tura kin san sai mun je Asibiti abin da ba kya so" Alina ta jinjina mata kai kawai ta lumshe idanunta, sai dai ?asan zuciyarta tana ci gaba da mamakin ina za su bar garin nan su tafi, su da ba su da kowa.

*****
Tun da sadauki ya tafi, Rahama a cikin fargaba take, idan ta kalli babbar rigar da ya saka mata, ga shi ya suturta nata jikinta da take ta Soyewa, amma a mugun tsorace take. Ga rigar sai ?amshin turare take yi. Da ta tuna yadda ya harbe Sabi'u sai ta razana kamar hankalinta zai gushe.
Sai dai Sangaren ?afarta da maciji ya sare ta, a hankali ta saki ta daina yi mata wannan mugun zugin da take yi mata.
Daga nesa kaWan suka din ga jin ?wale-?wale, sai dai ba su san me ake yi ba. Ko a tsakaninsu Waliban, ba a bari su yi hira a tsakaninsu saboda gudun kar su ?ulla wani abu a tsakaninsu.

A hankali Rahama ta takure jikinta, saboda wani irin azababben sanyi da yake ratsa ta, bacci Sarawo ya fara Wibarta.
Sannu a hankali take ratsawa cikin ?auyen Yelwa, kai tsaye ta tunkari rigarsu, ta shiga cikin gidansu, ta tarar da Baffa a zaune yana addu'a. Ta ?arasa da gudu ta je gabansa ta zauna tana yi masa magana, sai dai ta ga alamun baya ganinta.
Sadauki ta ga ya shigo gidan nasu, tare da su Saleh a bayansa, da wasu daga matasan garin nasu, ri?e da miyagun makamai. Kafin ta farga kawai Sadauki ya harbe Baffa, jininsa ya watso a fuskarta kamar yadda ya yi wa Sabi'u. Wani irin ihu Rahama ta yi tana faWin "Innalillahi wa Innalillahi raji'un"', Wayyo Allahna Baffa"

Sadauki ne ya ri?e ta da hannayensa biyu, ya mayar da ita ya zaunar da ita. ?ara rikicewa ta yi cikin tashin hankali ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza masa kai "Dan Allah kar ka kashe shi, kar ka kashe Baffana dan Allah bai yi maka komai ba"

"Shhh. Ai kin baro mafarkin, kalli ba gaskiya ba ne" Ya yi maganar cikin sigar rarrashi, yana haske fuskarta da fitila.

Ya sake girgiza mata kai, yana yi mata nuni da ta kwantar da hankalinta.

Ta kalli gurin duhu ya yi sosai, alamar dare ya tsala, ga wuta an kunna a tsakanin su. Sai da ya tabattar da ta Wan nustu, sannan ya saki hannunta, ya janyo wata ledar Viva, ya buWe ya haska mata cikin ledar da fitila. Maciji ne a ciki ba?i ?irin da shi, yana buWe shi ya fasa kai, aikuwa ta zabura ta ja da baya.

Ya yi ?asa da muryarsa ya ce "Shi ne ya sare ki, na yi amfani da dafinsa na nemo miki shi, ya ki ke son a kashe shi?" Ta girgiza masa kai.

"Sai fa an kashe shi, ya ki ke so a yi masa?" Ta takure jikinta tana kallon ledar cikin tsoro.

Kawai ya saka hannu ya dam?o kan macijin, ya jefa shi cikin wutar da take ci a gurin.
Za ta yi ihu ya saka mata kan bindiga a ?afarta, da sauri ta saka hannu ta toshe bakinta, ta ?arfin tsiya ta haWiye ihun. Zuciyarta ta karye ganin yadda macijin yake ta wutsul-wutsul a cikin wuta yana mi?ewa yana neman hanyar guduwa, yana fitar da wani sauti mai ban tausayi. Ya waiwaya ya kalli wutar, sannan ya kalli yadda take kallon wutar hawaye na zuba daga idanunta, ya ciro kwalbar da ya zu?e dafin macijin daga jikinta ya jefa a cikin wutar.
Su na haWa ido, ta sunkuyar da kai, tana jinjina girman rashin imani, da Allah ya dasa a cikin zuciyar Sadauki.

Ya mi?e ya tattaka ya je ya Waukko wani abu, ya zo kanta ya tsaya ya buWe shi,?aton bargo ne mai kaurin gaske ya lulluSa mata a jikinta. Ya mi?e ya yi gaba abin sa.

*****

YELWA

Baffa ya yi iya yin sa, gurin yin tawakalli, da mi?a lamuransa ga Allah, da ?o?arin danne zuciyarsa a kan abin da ya faru. Sai dai a ?ar?ashin zuciyar tasa wuta ke ci, da take ?ona shi shikaWai ba tare da kowa ya sani ba.
Cikin ?arfin hali, yana zaune a ?ofar gida da radionsa da saurarenta ya zame masa jiki. Can ya hango Bukar na nufo inda yake tare da Hanne, hakan ya sanya shi tsayawa cike da tsoro da fatan ba wani laifin ya aikata ba.
Cikin girmamawa Hanne da Bukar suka gaishe shi, ya amsa yana kallonsu da jiran jin abin da yake tafe da su.

"Baba shin da gaske ne labarin da muka samu, na cewa an sace su Ramata a makaranta?"

Baffa ya???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? numfasa cikin ?arfin hali ya ce "Haka ne Hannatu, sai dai ku taya mu da addu'a"

Bukar ya ce "Amma Baffa, Babu wani labari a kan inda aka kai su, ko labarin ?o?arin nemo su?"

Duk da Baba idan ya kalli su Bukar, yana fama masa mikin da ke zuciyarsa, na abin da ahalinsu, suka yi wa zuriyarsa, sai dai ya danne, duba da yadda suka zo yi masa jajen abin da ya faru da 'ya Waya da ta rage masa.

Ya ce "To, ko ma ana ?o?arin nemo sun, ka ga ni ina nan a cikin ?auye, babu lallai na san halin da ake ciki. Amma na bayar da lambata ina tuntuSar malamansu".

Jiki a sanyaye Bukar ya ce "Baffa ka yi ha?uri, in sha Allah Ramata za ta kuSuta cikin aminci da yardar Allah"

Baffa ya ce "To, Allah ya sa"

Hanne ma cikin sanyin jiki ta ce "Za mu ci gaba da addu'a, da yardar Allah Rahama za ta kuSuta cikin aminci"

Baffa ya ce "Ina fatan hakan, kuma yakamata ku koma haka kar a zargi wani abu, ko mu yi laifi daga ni har ku"

Suka yi wa Baffa sallama suka tashi suka tafi.

****

Kwana biyu Mama tana saka wa Laila ido, tare da sake rarrashinta, a kan batun filayensu da aka ?wace, dan tana yawan mita a kan lamarin.

Ranar Talata da yamma, Mama ta fito daga Wakinta, tana yi wa Saddam mitar, Laila tun safe ta fita amma haryanzu ba ta dawo ba.

Ya ce "To ki kira lambar wayarta mana"

"Na kira bata shiga, Ubangiji Allah ya shirya mini wannan yarinya, ni duk godiyata ga Allah da ya zamana ba wani abin ashshan take aikatawa ba, amma 'ya mace dole sai da saka ido ai"

Saddam ya ce "Mhmm, In dai Laila ce, tana can neman abin wallafawa a shafukanta ne, za ta dawo na san, iyaka idan ta dawo ki zane ta wallahi"

"Ba zan dake ta Win ba, ziga zigi"? Mama ta yi maganar tana hararsa.

Ya ce "Daga bayar da shawara? Allah ya baki ha?uri ai kun fi kusa"

Sai dai abu kamar wasa, har magariba babu Laila babu dalilinta, wanda hakan ne ya ?ara Waga wa Mama hankali, ba ita ba har da Saddam, babu shiri ya fita yawon neman ta.
Ga shi ita ba ?awaye ne da ita ba, babbar ?awarta Murja su na gama makarantar Sakandire aka yi mata aure, ma?wabciyarsu ce, da aka yi mata aure sai ta ci gaba da abotar da Bala, wanda yake Yayan Murja, wanda shi ne ya sanya mata sha'awar harkar sarrafa waya da kuma aikin jarida.

Laila ce rufe a cikin cell, sai rarraba ido take yi, ta kalli yadda duhun magariba ya fara yi. Ta jijjiga ?arfe cell Win ta ce "YallaSai ka yi wa Allah da ma'aikinsa ku sake ni na tafi, babata dattijuwa ce ba ta da cikakkiyar lafiya, hankalinta yana nan a tashe na sani. Wannan kamun da ku ka yi mini kun take mini hakkina fa"

Babu wanda ya kula ta, daga cikin office wani Wan sanda ne a zaune, sanye da uniform ya Waga wayarsa ya daddana ya saka a kunnensa.
"Allah ya taimaki honourable"

"Yauwwa ya aikin?"

"Alhamdillah, game da yarinyar nan ne, haryanzu ba ka ce komai ba"

Honourable ya ce "Eh ina sane, ku ajiye mini ita sai na waiwaye ta. Ba dai ba ta da kunya da mutunci ba, za ta gane ba ta da wayo ku ajiye ta sai na waiwaye ta."

?an sandan ya ce "Na fahimce ka sir, amma ka san yarinyar nan mutane sun fara gane ta a shafukan sada zumunta, idan abu ya bayyana ka saka an tsare ta, kar abu ya zama surtu"

"Ba na san aikinka ba ne?"

"Sorry sir"

"Ka ajiye ta sai na waiwaye ta, zan saka maka kuWin mai"

Gidan su Laila kuwa kwanan tsaye Mama ta yi, saboda rashin Laila a gida. Tuni Saddam da Bala suka kai Satan Laila gurin jami'an tsaro.

Da sassafe Bala ya zo musu da labarin tana gurin 'yan sanda, dan haka Saddam ya zo su je.

Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Yanzu Laila ce ta kwana a hannun 'yan sanda me ta aikata har haka?. Ba zan iya zama a gida ba, mu je tare kawai"

Saddam ya dubi Mama ya ce "Dan Allah ki yi ha?uri ki zauna a gida, wallahi ko mun je babu abin da za ki yi, ki bari mu je mu gano tukuna"

"In kwana yarinyar ba ta gida, ta kwana a hannun 'yan sanda ka ce mini ba zan bi ku ba"

Bala ya ce "Saddam ina ga ka bari kawai mu je tare, hankalinta sai ya fi kwanciya"

Ba dan Saddam ya so ba, ya ?yale Mama ta yafo mayafinta suka tafi.

*****

Alina na ta son sake tambayar Nadiya, inda za su tafi idan sun bar garin, amma ta fasa ganin yadda Nadiya ta nuna mata ba ta son tambayoyin.
Sai da Nadiya ta dangana da kai Alina Asibiti, aka bata magunguna da allurai, suka taho gida.
Da kyar Alina ta yi sallar isha'i ta kwanta, saboda baccin da take ji, a sakamakon magungunan da ta sha.

Baccinta ya yi nisa, ta din ga jin motsi da Suruntu a cikin gidan, a hankali ta fara ?o?arin buWe idonta. Gani ta yi an haske ta da wata irin fitila mai matu?ar haske, sai ta kasa tantance mafarki ne ko gaskiya.

Muryar Nadiya ta ji tana faWin "Kar ku taSa yarinyar nan, wallahi ba za ku iya ganin bayan Ismail ba. Babu ruwanku da ita. Ba dai shi ka ke son ka kama ba, ka kama shi, amma kamun da ka yi masa shi ne kuskure mafi girma da za ka aikata a rayuwarka".

"Shut up, da harbina za ki yi kenan?"

"Dole na kare kaina, abin da baka sani ba, tuntuni Isma'il ya san wane ne kai. Kar ka yi abu da ka, baka san abubuwa da yawa ba, zaka aikata mummunan kuskure"

A hankali Alina ta buWe idanunta, ta yin?ura, ta mi?e tsaye a razane da ?arfinta, tana son ganin suwaye suke wannan jayayyar da Nadiya, ammaba ta kai ga hakan ba, ta ji an sha?a mata wani hankici ta baya, take ta ji Wiff ta daina gane komai. Duhu ya ?ara mamaye ganinta.





SARA DA SASSA?A...
YOTA 002
AYSHERCOOL

Page 15



Hankalin Maman Laila ya yi mummunan tashi, ganin a inda Laila take.
A babbar headquarter yan sanda ta jiha aka kai ta. Shi ma sashen da aka kaita, aka gaya musu wanda case Win yake hannunsa baya nan sai dai su jira.

"Yanzu Saddam a gurin nan duk maza yarinyar nan ta kwana? Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Wai laifin me ma ta yi ne?"

Saddam da ransa yake a Sace shi ma ya ce "Mama tare da ke fa muka zo gurin nan, nima ban san abin da ta yi ba, sai dai mu jira mu ji me za su ce"

Bala ya ce "Ki yi ha?uri Mama, da yardar Allah yau zamu tafi da ita."

Duk magiyar da Mama ta yi, aka hana su ganinta. Har azahar su na gurin a zaune, sai bayan azahar wanda case Win yake a hannunsa ya zo, shi ma da ya zo ya ce musu su na da meeting da IG dan haka su ci gaba da jira.

"Wallahi ban da mahaifina ma Wan sanda ne a cikin aikin ya mutu, da sai na tarkata su na tsine musu wallahi yan wahala"

Bala ya ce "A'a Saddam kar ka yi abin da za su ?ara shanya mu, kuma kowane aiki akwai Sata gari, wani abin kuma yanayin aiki ne a haka, ba za a karya dokar aiki domin a burge ka ba"

Saddam ya ja uban tsaki kawai yana sake turSune fuska.

Sai bayan la'asar aka saurare su, aka fito da Laila, fuskarta duk cizon sauro.

Cikin nutsuwa Wan sandan yake kallon Mama, ya ce "Hajiya yarinyarki ba ta ji gaskiya. Ta je ta taSa manyan mutane, ta ce da saka hannunsu ake ?wacen"

Cike da takaici Mama ta ce "Laila, idan ba ki kiyayi rayuwa ba, wataran sai kin janyo an kashe mu. Allah wadaran wannan harkar jaridar taki. Wallahi ranka ya daWe, babu irin jan kunnen da ban yi mata ba, a kan ta yi ha?uri ta bar wa Allah ba, amma ta ?i. Ku dubi girman Allah ku yi ha?uri. Marainiya ce kuma 'yarku ce, mahaifinta tsohon Wan sanda ne yarku ce"

Ya kalli Laila ya ce "Yarinya, kina da ?anan shekaru, ki mori rayuwarki ta hanya zuba ido ga duk abin da ba ki da ikon gyara shi, idan ba haka ba, wahala za ki sha a banza." Laila ta sunkuyar da kai ta ?i magana.

Ya daddana waya ya kira wata lamba ya kara a kunnensa. Bayan sun gaisa ya ce "Honourable batun yarinyar nan ne, dan Allah a yi ha?uri, ga mahaifiyarta tana ta kuka tana bayar da ha?uri, dan Allah su na neman belinta"

"Kar ka kuskura, ba zai yiwu ba, ai sai na banbance mata aya da tsakuwa, ko da wasa aka sake cewa ta fito ta yi soki burutsu irin wannan ba za ta yi ba"

"Amma ga mahaifiyarta a gurin ba dan ita ba...

"Babu ruwana na gaya maka, sai na wula?anta yarinyar nan, za ta ga ?arshen rashin hankali" ?an sandan ya kashe wayar.
Mama ta ri?e haSa, ta ce "Yanzu a kan wannan yar da ya haifa yake i?irarin zai wula?anta? 'yar da ya haife ta? To Allah ya kyauta idan Allah bai wula?anta ta ba, babu wani wanda zai wula?antata"

"Shiyasa ake cewa, ku din ga ja wa yaranku kunne, ku din ga ba su tarbiyya su din ga iya bakinsu"

"Ku yi mata duk abin da za ku yi mata, kai ka ga alamar rashin tarbiyya a tattare da ita? Tsawon shekaru mahaifinmu na yi wa ?asa hidima aikin Wan sanda, Wan abin da ya mutu ya bar mana, wasu sun yi kashe mu raba a tsakanin su, kuma a ce kar mu yi magana ?asa za mu ci mu rayu? Idan hidimar wani ta tashi a cikinmu wani zai yi mana ne". Saddam ya ?arasa maganar jikinsa yana rawa saboda ba?in ciki.
"Kai, ka zo har gurin aikin nawa ka nemi ka gaya mana magana, yaran talakawa tarbiyyar ce da ku? Zan saka a rufe ka wallahi"

"Ba rufe ni za a yi ba kashe ni za a yi" Bala ne ya dan?i hannun Saddam suka yi waje, yana rarrashinsa.

"Saddam mutanen nan, wasu ba mutunci ne da su ba, babu Allah a ransu. Ka rabu da su, na san abin da zan yi, ko ba yau ba zuwa gobe in Allah ya kaimu, Laila za ta fito"

Haka ya rarrashi Mama ma, suka sai Abinci aka ba wa Laila suka koma gida, ya din ga basu ?warin gwiwa a kan yana da hanyar da zai fitar da ita.

Tun da suka koma gida, daga Saddam har Mama babu wanda yake walwala. Duk da Mama na ta faWan halin Laila na azabar kafiya.

Shi kuwa Saddam daga baya bai ga laifin Laila ba, dan yarinya ce mai sau?in kai mara hayaniya, amma akwai kafiya, kuma duk abin da ta wallafa ya san tana da cikakkiyar shaida da hujja a kan abin da ta yi.

Bala kuwa shi ma rubutun ya wallafa a shafinsa, da bayanin cewar an kama Laila, saboda maganar da ta yi da sunayen yan siyasar da kama, da cewar an haWa kai da su ana ?wacewa mutane filaye.
Duk da wasu na jin haushinta, amma kasancewar ayyukan da take yi a shafinta ba siyasa bane kawai, ta kan faWakar, koyarwar addini, girke-girke motivational speaking, idan baka ?aru da ita ta wani fannin ba, za ka ?aru ta wani, dan haka nan da nan mutane suka din ga reposting abin da ya faru.

****"
A hankali ta motsa, ta yin?ura domin tashi zaune, amma ta koma yuuu saboda wani irin azababben jiri da ciwon kai da ya Webe ta. Ta buWe idonta a hankali ta din ga gani dishi-dishi, ga kanta da yake yi mata wani irin azababben ciwo.
Ta koma ta kwanata ta yi lamo, a hankali komai ya fara washewa. Ta kalli gurin Waki ne na Asibiti, da gadaje kusan biyar a ciki, sai dai itakaWai ce a Wakin. Ga hannunta Waya sanye da ruwa.
Hayaniya ta din ga jiyowa sama-sama, ana wani irin yare ana haWawa da broken English.
Sai kuma ta ji Wif an daina sai alamar takun takalma.
?ofar Wakin aka buWe, maza ne suka shigo zabga-zabga, sanye da kaakin soja a jikinsu. Sai dai a wanda suka shigo Win duk ya kere su a tsayi. Wandon sojoji ne a jikinsa, sai riga armless shirt army green. Gefen wandonsa a soke da wata 'yar ?aramar bindiga.
Ya Wan tara suma a kansa, sai dai yanayin askin gaban kan tafi cika, zagayen kuma kwantacciyar suma ce, gwari-gwari dai yanayin askin da ake kira da balatoli. An yi wani abu mai kama da arrow a gefen kan.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login