Showing 21001 words to 24000 words out of 53964 words

Chapter 8 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

748

ga tunanin ko yaya yake.
Monday da ta fito makaranta, ta tarar da Wakinsa a rufe, amma bai saka mukulli ba.
Har guri ta samu ta Wan tsaya, ta gani ko zai fito, amma shiru ta gaji ta tafi, dan sai da ta makara ma.

*****

YELWA

Baffa ne yake tafe sannu a hankali, yaje ya bawa wani yaro maganin maciji, saboda maciji ya sare shi a ?afa, ya duba ya ga wani mara lafiya da ya yi wa Worin karaya, daga nan ya biya kasuwa, ya Wan yi sayayya ya nufo gida.
Yana ta sauri, ya ji ana yi masa sannu da zuwa, ya tsaya ya waiwaya ya ga wane ne, kawai ya ga Saleh. Baffa ya yi shiru bai ce komai ba, ya sa kai zai ci gaba da tafiya.
"Ba za ka amsa sannu da zuwan nawa ba? Babu faWa mai ya kawo gaba?"

Baffa ya tsaya, ya kalle shi ya ce "?an samari, ina gama ka da Allah, idan ka san shi. Kana kuma tsoron sa, ka fita daga harkata" Ya yi maganar idanunsa suna yi ja, muryarsa na rawa.

"Baba tun da Allah ya haWa mu zaman guri Waya, ai haraka ta zame mana dole. Abin da zai iya cutar da kai na gano, na ce bari na sauke hakkin ma?wabtaka"

Baffa ya tsaya cikin rashin fahimta yana kallon Saleh. "Duk da lokaci ya so ya ?ure, amma ina tausayawa yadda ?addara ke bin ahalinku, mussaman ma kai.
Duk da Ramata ba ta gari, amma kana iya Waukar mataki."

Baffa ya ce "Ramatan kuma me ta yi muku, yarinyar da tana makaranta ma?"

"Tana soyayya da Wan uwana Bukar, wanda ka sani na sani, babu ga maciji a tsakaninmu da ku, duk abin da ya faru ka kuka da 'yarka, na gaya maka ne ka yi wa tufkar hanci, kar ita ma ka rasa ta"

Cikin mamaki Baffa yake kallon Saleh, sai dai ya gaza cewa komai, sai bin sa da yake yi da ido baki buWe cikin mamaki. Sam bai ji maganganun Saleh sun shige shi ba. Yarinyar da ba ta garin ma, ga ta da gudun magana yaushe za ta je ta yi wannan katoSarar. Kawai ya sanya wa zuciyarsa ?arya Saleh yake yi.

*****

Bayan kwana biyu.

An taso 'yan makarantar su Alina, Hafsa ta ce "Ke na sato mana littafi, yau zan karance shi cikin dare in sha Allah"

Alina ta ce "Haba dai ya sunansa?"

Hafsa ta Wan yi shiru ta ce "Na manta, amma dai zan karanta mana"

"To shikenan, sauran gobe in Allah ya kaimu, ki ?i ba ni labarin. Allah dai ya sa an zuba soyayya a ciki"

Hafsa ta yi dariya ta ce "Ai da ganin bangon littafin ma, ke dai ki jira, zan karance mana shi, shi kuma mu ji me aka yi a cikin sa"

Alina ta ce "Kin san littafi idan da soyayya a ciki, subhanallah har wani nishaWi yake sakawa."

Hafsa ta gyaWa kai ta ce "Ina ta ?o?arin ganin na sake da yaya Hafiz Win nan, nima mu din ga soyayyar nan na kasa, kunya ma nake ji wallahi"

Alina ta kwaSe baki ta ce "Ke kenan, da aka bawa damar ki yi soyayyar ma, ni duk wanda ya ce yana sona zagi yake sha a gurin Yaya ya kore shi, wai ni yarinya ce. Idan aka ganni zata ake babba ce ni"

Hafsa ta ce "Kuma ga maza na sonki, amma wata?ila sai kin yi candy zai bari"

"Mhmm ai ni na zubawa sarautar Allah ido ne ma, na bar Yaya da halinsa"

Tun da Alina suka fito daga makaranta, take ankare da yana bin su a baya, amma ta basar, suke ta hira da Hafsa. Amma a ?asan zuciyarta, ta ji daWin ganinsa da alamar ya warke. Suka yi sallama da Hafsa ta bi hanyar gidansu, Alina ma ta bi tata hanyar.

"'yar ?walisa" Ya yi maganar yana Wan ?ara sauri.

Sauri ta ?ara ita ma, ta ?i ko waiwayowa, ta basar da shi.

"Alina" ya kira sunanta. Ta tsaya tana zumSura baki, ta? waiwaya kai tana kallonsa.

"An taso?" Ya yi maganar yana kallonta. Ta yi shiru tana kawar da kanta gefe.

Ya sake cewa "Amm dama zan ce miki na gode ne"

"Da aka yi me?" Ta yi maganar tana tattaro jarumtar kallon idonsa amma abu ya gagara.

Ya Wan ja numfashi ya ce "Maganin ciwon ciki, da kuma Abinci da ki ka bani"

?an murguWa baki ta yi ta ce "Daka yi mini tsawar" Ta yi maganar tana tura baki.

Ya Wan rungume hannayensa ya ce "Ohh zafin ciwo ne fa, kuma ina jin tsoron kar a zargi wani abu, mussaman yayanki, na san ya ganki a Wakina zai iya yi mini duka ma"

Idanunta ta Waga tana ?are masa kallo, sai dai ba ta kalli idonsa ba, ta tura baki ta ce "Tun da abin alkhairi na yi maka, sai ka gaya mini a hankali ai. Amma ka yi mini tsawa. Kuma ni ba na son a yi mini tsawa, sai da na tsorata"

Ya yi shiru yana kallonta.
Ba tare da ta kalle shi ba a shagwaSe ta ce "ka bani ha?uri to"

Ya yi turus yana kallon 'yar abar da da kaWan ta fi ?ugunsa, tana i?irarin ya bata ha?uri, kuma yanayin fuskarta ya nuna da gaske take abin da take faWa har zuciyarta...

Ayshercool
1k ne via 0069685771
Aisha Adam stanbic
Sai shaidar biya ta 08081012143

https://whatsapp.com/channel/0029VaPywxs8kyyIhWtuvh3g

SARA DA SASSA?A...

YOTA /002

P7

Ganin ya ?i magana yana ?are mata kallo, ya sanya ta yi gaba ta bar shi a gurin, Tana ?un?uni, da mita ?asa-?asa.

Bai san lokacin da murmushi ya suSuce masa ba, ganin tsagwaron ?arfin hali irin nata.

*****

PRESIDENTIAL RESIDENCE.

Garin ya yi shiru, ba a iya jin motsin komai, tamkar babu halitta mai numfashi a gurin. Sannu a hankali yake kaiwa yana komowa a cikin katafaren ofishin. Ya koma ya dafa kan kujera yana juya ta a hankali da hannunsa.
Ya kalli agogon office Win, ?arfe uku saura mintuna goma. Yana sauke idanunsa, aka buWe ?ofar ofishin aka shigo.

"Halilu ka ?araso?" Ya yi maganar yana ajiyar zuciya.

Cikin girmamawa kamar ya dungura ya ce "Yes sir na ?araso, a yi mini afuwa, ina fatan ban Sata maka lokaci ba?"

Ya girgiza kai ya ce "A'a. Bismillah zauna"

Halilu ya ja kujera ya zauna, yana daga tsaye ya tura wa Halilu jarida ya ce "Ina fatan ka ga wannan, na san ma wata?ila ka riga ni gani?"

Halilu ya ja jaridar ya fara dubawa. Ya shafi goshinsa, da yake jin kansa na yi masa wani irin ciwo. "Da na san abin da zan tarar kenan a ?asar, da ko a mafarki ban nemi mulki ba. Tun bayan rantsar da ni, babu abin da na cimmawa mai muhimmanci sai ma koma baya da na fara fuskanta a ?asar. Wannan case Win shi ne na uku da ya faru a tsukin kwanakin nan, dole mu yi wa tufkar hanci, kafin lamuran su fi haka ?azanta. Wancan yankin na yamma satar mai ya ta'azzara, gabas kuma rikicin manoma da Makiyaya, da rikicin ?abilanci. Gobe in Allah ya kaimu ka tara manema labarai, ka sanar musu na ?o?arin Waukar matakan inganta tsaro, ka dai san abin da yakamata ka yi a kai. Sannan a shirya mini zama da shugabannin rundinonin tsaro, gobe da misalin ?arfe tara na dare. Za kuma mu naWa wakilai su je ta'aziyya gurin da abin ya shafa"

Halilu ya numfasa ya ce "Shikenan sir, za a gabatar da duk abin da ka ce, na bar ka lafiya"

Jinjina kai kawai ya yi cikin ?arfin hali.

*****

Tana zaune a kan kujera, ta Wora wayarta a kan ?aramin table Win gabanta, tana kallon paper gabanta, da ta yi rubuce-rubuce a jiki, tana rehearsal.

Ta bayanta ya ?araso yaka le?a paper, ya ja guntun tsaki ya ce 'Yar wahala, ke dai kin ga ta kanki Laila" Ya yi maganar yana dungure mata kai.

Ta Wago tana murguWa baki ta ce "Ba ruwanka da ni, na gaya maka ka fita daga sabga ta"

"Da ruwana da ke, ke ba ki san yanzu haushinki nake ji ba, kamar na sha?e ki na huta"

"To sai ka kashe ni ka huta ai"

Mama ce a gefe, a kwance a kan fulo hannunta ri?e da counter, ta Wago tana faWin "Sadam ba ruwanka da ita dan Allah, ka ?yale ta"

"Mama ke ki ke goya mata baya dama, kiri-?iri yarinyar nan, Wan aikin nan da ta samu, Wan abin da ake ba ta yana taimakawa, amma saboda ba?in hali, ta ja an kore ta, ta dawo wahala wai content creation. Ko uban wa ya gaya mata Wan jarida yana Waukan side ya shiga siyasa oho mata"

Laila ta ce "Ni fa ba siyasa na shiga ba, tun da an kore ni, i decided to take another decision. Dama can ina content Wina. Beside yanzu na samu cikakkiyar dama na yi abin da nake so, a hankali zan yi building pages Wina na fara samun kuWi"

Sadam ya yi tsaki ya ce "Aikin banza ?iba a kunne, comment section Win ki ban da zaginki ma babu abin da suke yi"

"Duk da haka ba zan gaji ba, masu yaba mini sun fi masu zagin yawa. Sannan masu zagin ma taimakona su ke yi gurin pushing ayyukana. Ni fa na gama gane ka. Kuma ina yawan gaya maka, da arziki a garin wasu gara a gidanku."

"Gidanku ke a wa? Da ya ci president Win uban me ya tsinana miki, kullum cikin ?ona datarki ki ke a banza, da hauragiya ba a san da ke ba ma"

Laila ta yi murmushi ta ce "Mu siyasar a?ida muke yi. Ko bamu samu komai ba, muddin al'umma na amfana shikenan. Ko kowa ya watse ya bar tafiyarsa, nikaWai zan tsaya a bayansa ?uri'ata tasa ce"

Wani uban tsaki ya ja ya ce "Su na can su na satar kuWin talakawa su na ci, yaran talakawa ku na nan kuna wahalar banza"

"Idan Allah ya tsayar da kai ranar shaida, zaka nuna abin da ya sata?"

A hasale Mama ta ce "Ko dai ku daina wannan musun banzan da na wofi, ko ku fita ku bar mini Waki. Sadam ba ka da girma sai na jikinka. Kawai ku zauna ku cika mini kunne ku hana ni sakat ni da gidana. Ko a yi mini shiru ko ku fita ku bar mini Waki na huta, iskancin banza kai"

Laila ta yi masa gwalo, ya galla mata harara, ya fita. Ta saita wayarta ta kunna video ta fara recording.

Mama ta ce "Malama ki yi ?asa-?asa kin cika mini kunne, ko kema ki fita yanzun nan ki bani guri"

Laila ta ce "Na fuskanci videon nan ne dai ba kya son na yi, bari na tafi tsakar gida"

"Eh sauka lafiya. Haba wannan abu har ina, kai da gidanka ba zaka huta ba"

Laila ta kwashi kayan videonta, ta fito waje.

****
"Amanar kacalla"

"Allah ya bar mini kai Madugu"

"Ya ake ciki?"

"Kaya sun zo hannu, an samu shanu Wari biyu da goma sha biyu. Ga kuma tumaki da raguna guda Wari"

Kacalla ya numfasa ya ce "Ku kaWa su boda, akwai tireloli su na nan su na jiranku, za su karSa su bar ?asar da su"

Sadauki ya ce "To ina fatan sun gyara mana hanya, saboda aka samu kuskure zubar ruwa za mu yi kan mai uwa da wabi"

Kacalla ya ce "A huce haka Sadauki, na kula da komai, an share hanya ku saka kai kawai"

"Allah ya bar mini kai ubangidana, ina sanya ran zuwanmu nan da kwana biyu"

"To shikenan, duk yadda a ke ciki mu yi magana kawai. Ka kiyaye da lokutan kirana"

Sadauki ya ce "Na kiyaye"

*****

?angaren Alina ta daina gaida Mamman, ta kuma daina kai masa wankin takalmi, idan ta zo wucewa ma sai ta kawar da kanta gefe tana haWe rai, da zumSura baki. Yana zaune a bakin hanya, ta zo ta wuce shi za ta tafi makaranta, ta yi nisa sosai wani almajiri ya biyo ta yana ?wala mata kira. Ta tsaya tana kallon yaron.

"Ga shi in ji wani mutum ya ce a baki" Ta kalli takardar da ya mi?o mata, ta karSa ta buWe. Shiru ta yi tana kallon rubutun ajamin da yake jiki.

"Na yi ba daidai ba, ba zan sake ba" Ta waiwaya ta ga yaron ya tafi,? ta Wan yi murmushi ta ninke takardar ta saka a jakarta.

Bayan an tashi daga makarantar boko sun fito tare da Hafsa, da shi ta fara cin karo a waje, a ?ofar makarantar yana jiran ta. ba ta ce masa komai ba, suka wuce shi da ita da Hafsa. Sai da suka yi sallama da Hafsa suka rabu a hanya sannan ta tsaya. Ya ?araso yana tsare ta da ido. Tsiwa ta so ta Wan yi masa amma kuma sai ta kasa, idanunsa suka Waure ta, ta gaza cewa komai.

A hankali ya ce "Kin ga sa?ona?"

"Na gani" Ta amsa tana juya masa ?eya.

"To ya wuce?"

Alina ta jinjina kai.

Ya Wan yi murmushi ya ce "To ki juyo mana"

Ta Wan Wago, amma ba ta bari sun haWa ido ba. Ta rufe fuska tana murmushi.

Ya sake kwantar da murya ya ce "Ina fatan za a ci gaba da kawo mini wankin takalmin, kuma za a daina fushi da ni?"

Tana ?o?arin yin murmushi tana mazewa ta ce "Zan kawo maka ma idan na taso daga islamiyya"

Ya ce "To ya yi, yaushe ne saukar ne?"

"Mun kusa in sha Allah"

"Allah ya sanya albarka"

"Amin na gode sosai"

"Idan da taimakon da ki ke bu?ata, ko inda ba ki iya ba, ki gaya mini na koya miki"

"Kai amma na ji daWi sosai, na gode." Ya jinjina kai ta wuce gida. Ya tsaya shiru yana bin ?ofar gidansu da kallo. Yana sake nazarinta.

Kamar yadda suka yi da ita, bayan ta dawo daga islamiyya ta kai masa wankin takalmi, ta kai masa har da abinci.

Ya kalli flask Win Abincin ya kalle ta, ta yi shiru tana jiran ta ji me zai ce. Sai kuma ta ji ya ce "Yayanki ba zai yi miki faWa ba?"

Ta jinjina masa kai, jiki a sanyaye ya karSa, dan ya ga alamar idan bai karSa ba akwai daru.

"Yaya Mamman" Ta kira sunan shi, hannunta ri?e da ?ulu tana sa?a. "Ba ka gaya mini sunan garinku ba."

Ya numfasa ya ce "Ai ko na gaya miki ba ki san ina ne ba"

"To da ka yi ciwon cikin nan ka je Asibiti ne?"

Ya amsa da "A'a"

"Meyasa?"

"Ba ni da kuWi"

"Ka je a duba me yake damunka, idan aka rubuta maka magani sai na bawa yaya ya saya maka"

Mamman ya kalle ta ya ce "Idan zan mutu yayanki ba zai saya mini magani ba"

Ta ce "Wallahi zai saya maka in dai na kai masa. Yana da kirki fa, kawai dai saSanin fahimta ne ku ke samu da kai da shi"

Tun yana biyewa surutun Alina, har ya yi shiru, dan da alama ita ba gajiya take yi ba. Ya gama wanke mata takalminta, ya bata abin ta. Sai dai a wannan karon ma bai karSi kuWin ba.

Godiya ta yi masa cikin harshen turanci tana murmushi, sai dai yadda ta lan?wasa harshenta ta yi magana, tamkar baturiya"

Sai da ya kalle ta da mamaki, duk da makarantar da take zuwa ta boko, mai tsadar gaske ce. Amma abu ne mai wuya a ce a nan iya wannan turancin. Ya numfasa ya ce "Ina fatan dai ba zagina ki ka yi ba, tun da kin san ban iya yaren nasara ba"

Ta yi dariya ta girgiza kai ta ce "Godiya kawai na yi maka fa, yaya za a yi na zage ka ma?"

"To ai na ji turancin ma, ba irin na 'yan nan ba, kamar na turawa ki ka yi, ya aka yi ki ka iya irin wannan?"

"British Academy na yi Nusery da primary, daga baya na ce bana son makarantar, Yaya ya dawo da ni nan" Ta yi maganar tana karkaWe gefen rigarta.

Ya yi murmushi ya ce "Lallai yaya attajiri ne, British Academy ki ka je?"

"Wai kai ma ka yi Makarantar boko ne?"

Ya yi murmushi ya ce "A'a, na san dai makarantar turawa ce, kuma tun da makarantar turawa ce, za ta yi tsada sosai"

"Aikuwa da tsada sosai, har breakfast da lunch ake bamu fa, malamanmu har da turawa, sai da muka tashi daga waccan unguwar ga nisa, ga wataran Yaya baya gari, nima dai na ce ba na son makarantar, aka dawo da ni wannan"

Ya jinjina kai ya ce "Lallai yaya ya yi ?o?ari sosai, yana son ki yi karatu"

Ta ce "Eh mana, kuma ina yi sosai da sosai ba"

Sannu a hankali, wata irin sha?uwa ta din ga shiga tsakanin Alina da Mamman mai wankin takalmi.
Wanda har ta kai Alina ta saka masa kwanon abinci, a gidansu safe rana dare, duk abin da aka dafa sai ta zuba ta kai masa. Tun tana Wan jin War-Wari, saboda jarabar Yaya Ismail, har ta rage jin tsoron. Hatta ala?arta da Hafsa sai da ta ja baya, saboda Mamman. Ba ta taSa zaman mintuna ashirin ba ta yi zancensa ba.
Idan ta taso daga Islamiyya, sai ta tsaya a gurinsa, su yi hira ya jiye mata hadda. Wataran kuwa a ?ofar makarantar take tarar da shi su tafi tare.

Nadiya nata bacci, ta yi juyi kawai ta ga Ismail a zaune a kan gado. Ta kai hannu ta shafa bayansa ta ce "Masoyi ya dai na ganka a zaune, kai ba salla ba meyafaru ne?"

"Alina" ya ba ta amsa a ta?aice.

"Me ta yi kuma?"

Ya ja numfashi ya jingina da allon gadon ya ce "Ala?arta da mutumin nan ce ba na so ko kaWan, alamu sun nuna na yi sake sha?uwa ta shiga tsakaninsu, na kuma fuskanci idan na matsa, za ta iya jin haushina. Na fuskanci yadda magana Waya biyu a gidan nan sai ta ce Mamman, hatta yadda take rawar jikin kai masa abinci duk ina ankare da ita, kallonta kawai nake yi"

Nadiya ta tashi zaune ta ce "Masoyi, ko muna so fa ko ba ma so, dole Alina a ce ana sonta, kuma dole a aurar da ita, yawan hana ta kula samari da ka ke yi, kar ya zame mata matsala fa a gaba. Sai dai kuma idan abin da nake so tsoro ne zai faru"

A kausashe ya ce "Za ki fara ko? Sau nawa zan gaya miki ki daina Warsa wannan shirirtar da a ranki? Alina yarinya ce ?arama fa, soyayya kuma barazana ce ga mutum mai ?allafa abu a rai kamar ta. Idan Alina ta kamu da soyayya za ta sha wahala, kuma ban shirya bawa ?as?antaccen mutum kamar wannan auren Alina ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login