Showing 12001 words to 15000 words out of 53964 words

Chapter 5 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

749

Sai da malamansu suka gaya masa, za ta taimaka mata a gurin karatu, sai kuma ya amince ta ri?e. Dan wasu lokutan har koya masa yadda ake amfani da ita take yi. Ta daWe tana Wan rubuce-rubuce sannan ta ajiye ta yi shiru tana tunanin maganganun da Sale ya gaya mata Wazu. Kamar yadda Iro ya karSi hukuncin Hanne?
"Kai ba zai yiwu ba" ta furta a fili tana kashe Tab Win gaba Waya. Ta tattare komai ta gyare Wakin nata, ta nemi guri ta kwanta tana ta tufka da warwara ba dan makaranta d???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?a za a mayar da ita ba, tabbas tana bu?atar ?arin bayani a kan wasu abubuwa da suka saka ta a duhu.

Duk da zuciyarta a cunkushe ta kwanta, hakan bai hana ta ganinsa a mafarkinta ba yau.
Tana tsugune tana wanki a rafi, ta Waga kai ta gan shi a tsaye a cikin rafin. Yana sanye da tufafi na birni kamar yadda ta taSa ganinsa. Fuskarsa babu yabo babu fallasa. Babu shiri ta mi?e tsaye tana faWaWa murmushinta, cike da farin ciki. Sai dai bai ce mata komai ya juya ya tafi ya Sacewa ganinta.
Ta buWe idonta a hankali, duhu ya mamaye ko ina na cikin Wakin nata. A zahiri tana son Bukar. Amma wannan kyakykywan matashin ya addaba wa rayuwarta. Har wani farin ciki take shiga, a duk lokacin da ta kwanta bacci ta yi mafarkinsa. Sai dai ta san har gaban abada ya fi ?arfinta, ba za ta taSa samunsa a matsayin miji ba.
Tun a ganin farko da ta yi masa, yake yawan zuwa mafarkinta a kai a kai.

Washegari.

Ramata na cikin motar haya, Baffanta na daga gefenta, hannunsa ri?e da carbi yana ta tasbihi. Ya nisa ya ce "Ramatu bacci ki ke yi ne?"

"A'a Baffa idona biyu, kewar gida nake yi ne, duk lokacin da zan koma makaranta sai na ji na damu"

Ya yi murmushi ya ce "Ranar da aure kuma ya zo ya za a yi Ramatun Baffa? ?ila ma Allah ya kawo wanda zai fito da ke daga Yelwa zuwa birni. Abin da nake so da ke dai, abu ne da nake nanata miki kullum. Ke ba 'yar kowa ba ce face makiyayin daji, ki ri?e mutuncinki, sannan ki ji tsoron Allah. Ba wai ina zarginki ba ne a'a ita dai tunatarwa tana da kyau ga mumini. Ramata ko bangon duniya za ki je ke kaWai, ba dan hadisin Annabi Sallallahu alaihi Wasallam, da ya ce bai halatta ga wata musulma ta yi tafiyar sama da kwana uku ba tare da muharraminta ba, da Ramata zan bar ki saboda yardar da na yi da ke. Amma a matsayina na uba, ina sake nanata miki ki ji tsoron Allah, kuma ki yi addu'a."

Baffa kenan bai samu wani ilimin addini ko na zamani mai zurfi ba, tsabar ala?a da radio ce, ta sanya shi sanin rayuwa, har yake iya wa'azi. Sai dai duk da rashin ilimin nasa nutsatsen dattijo ne mai dattakun gaske. Haka suka ci gaba da tafiya yana ta yi wa Ramata nasiha.

?arfe Waya na rana suka isa makarantar 'yan mata ta kimiyya da fasaha, da Ramata take yi, ana ta mayar da Walibai ranar.
Baffa suka gaisa da malaman su Ramata, cikin girmamawa Ramata ma ta gaida su.

Vice ya dubi Ramata ya ce "B Yalwa, kin duba jarrabwarki kuwa?" Cikin tsoro Rahama ta girgiza kai.

Ya yi murmushi ya ce "Kin ci jarrabawa, kuma mun yi ?o?ari, an bar mana ke a nan reshenmu, dan ba zamu gama rainonku ba, a yi posting Winku wasu makarantun ba, su fi mu amfanarku ba, muna alfahari da ke Rahama Bashir Yelwa"

Cikin matsanancin farin ciki ta ce "Alhamdillah, Allah na gode maka"

Baffa ma cikin farin ciki ya wahse baki ya ce "Ma sha Allah, malam ta yi nasara kenan, za ta ci gaba da bokonta babu wata matsala?"

"?warai kuwa, ai ko ba ta yi nasara ba, za ta ci gaba da boko, sai dai nasararta a wannan jarrabawar yana nufin za ta ci gaba da karatu ?ar?ashin makarantu na mussaman na koyar da ilimin kimiyya da fasaha"

Baffa ya ce "To ma sha Allah, Ubangiji Allah ya sanya albarka"

?awayen Ramata suka zo gaida Baffa, babban dalilin da ya sanya suke son zuwa gaida Baffa, duk yanayinsa na ?auyanci wasu lokutan, ya din ga kwarara musu addu'a kenan. Addu'ar uba da 'ya'ya, addu'a da nasiha mai shiga jiki.
Farkon zuwan Rahama makaranta ta fuskanci ?alubale, saboda ?auyancinta, hakazalika babanta ya zama abin bayar da labari, kasancewarsa makiyayin ?auye typical, dan takalmin nan nasu na roba da makiyaya da ake cewa fillo tomes shi yake sakawa. Abin yana sosa mata zuciya sai dai ba ta bari hakan ya zama rauninta ba. Da alfahari take nuna mahaifinta ga kowa bata Soye asalinta. Tamkar kar su rabu, haka ta Wan raka Baffa zuciyarta cike da karaya ta juyo.
Ta Wauki kayanta, tare da ?awayenta, suka nufi hostel cikin farinciki, kasancewar galibi sun ci jarrabawarsu, kuma ba a yi musu transfer zuwa wasu makarantun ba.

*****
Sannu a hankali ya sanya ?afarsa a cikin katafaren falon, ya tsaya cak yana ?arewa falon kallo. Set Win kujeru kawai uku ne a ciki, ga wani irin sanyi da yake ratsa ko ina.
Ya saki wani irin murmushi, ya sake gyara zaman takunkuminsa ?afarsa sanye da takalminsa ya shiga falon.
Wanda yake yi masa jagorancin, ya yi gaba suka wuce wannan falon, suka Wan yi tafiya sannan suka shiga wani.
Shi ma wani falon ne a can ?uriyar gidan, an yi masa da ado da dukiya mai yawan gaske. Ya sauke idanunsa a kan agogon Wakin, ?arfe biyu saura mintuna goma na daren juma'a.
Babban mutum ne dattijo a zaune, ya mi?e tsaye yana murmushi ya ce "Barka da zuwa kacalla Sumale"
Ya tsaya ya Wan ?arewa mutumin kallo da falon, sannan ya yi taku biyar ya tsaya, ya ce "Ba mai gida bane, yaron mai gida ne, Sadauki nake, amanar kacalla Sumale mai Allah" Ya yi maganar yana sauke rawanin fuskarsa.

Mutumin ya yi turus. "Amma meyasa Sumale zai yi mana haka? Ya zan yi magana da shi, kuma ya turo mini wani daban?"

"Ka shirya har?allar, ko na juya na tafi?" Ya yi maganar yana tsuke fuska.

Ya jinjina kai ya ce "Bismillah zauna"

Ya samu guri ya zauna a ?asan carfet ya mi?a ?afafuwansa. Ya Wago idanunsa da suka sha uban farin kwalli ya dubi mutumin ya ce "Shi madugu, hawainiya ne, idan ya juyo nan a wannan kalar, idan ya juya can a wata kalar za a gan shi. Haka zalika kullum a tafe muke mu, bama zama guri Waya. Yau zaka iya ganina gobe ka ga wani daban. Amma ka kwantar da hankalinka, ni karSar aikin ne nawa, aiwatarwa kuma tasa ce. Ina jinka.

Mutumin ya ce "Ko kana bu?atar wani abu na ci?"

Sadauki ya ce "A'a faWi har?allar kawai" Ya yi maganar yana kunna karan taba sigarinsa.

Dattijon ya gyara zamansa cikin nazarin matashin ya ce "Amma na san ka san waye ni a ?asar nan ko?"

"A'a" ya ba shi amsa kai tsaye yana jingina da kujerar da take bayansa.

Dattijon ya yi saroro yana kallonsa, yana ganin amsar tasa kamar rainin wayo.

Mutumin ya dake ya ce "Amm to ni ne...

Sadauki ya tari numfashinsa ya ce "Ba gabatar da junanmu ne ya kawo ni ba, yarjejeniyar aiki ce ta kawo ni, Kacalla ya san yadda zai ji da komai"

Dattijon ya yi murmushin ?arfin hali sannan ya ce "Gaskiya ne. Ha?i?a muke ri?e da sitiyarin ?asar nan, mune muke juya lamura yadda muke so. A duk lokacin da aka kawo abin da yake saSanin tsarinmu, muna iya karkata motar mu kifar da kowa. Nan da na gayyace ka, ina magana ne da yawun wasu mutane da ba lallai sai ka san suwaye ba. Mu na son a Sata ruwa ne ba dan a sha ba. A mayar da tsaro tsoro, a gwamutsa gari da ?asa."

Ya yi murmushi ya dubi dattijon ya ce "Aikinmu ne wannan, gwari-gwari ku na so a yi kururuwa a gabas sai kuma a koma yamma a tayar da ?ura a gabas?"

Dattijon ya yi murmushi ganin ya Wau haske ya ce "Gaskiya ne"

"Mene ne sadakin aikin?"

Za a yi raba dai-dai a ganimar, mu ne sitiyari ku ne injin mota, sai an bi mu sannan komai zai tafi yadda ake so.

Sadauki ya mi?e ya ce "Za ku yi magana da Madugu, yallaSai ku na sararawa fa, irin wannan duniya haka, mu muna dawa muna ri?e muku ?asa" Ya yi maganar yana ?ya?yata dariya.

Dattijon ya mi?e ya ce "Za a baka sa?onka a hanyar komawarka gida"

"Yayi" Ya furta yana nufar hanyar fita.

Ya bi bayan Sadauki da kallo, muddin wannan ba shi ne Kacalla Sumale ba, to shi ma ba ?aramin tsagera ba ne ba....

*****

Yau kasancewar Asabar ce, kuma an yi hutun islamiyya, Alina ta nemi izinin Yaya, ta tafi gidansu Hafsa.
Wuni suka yi wasanninsu, da shiriritarsu ta yara. Yayar Hafsa da suke satarwa littafi su karanta, ta saka Alina a gaba, sai da ta yi mata kitso, saboda kullum kanta a tsfefe yake babu kitso.

Bayan sun keSe a Waki su na hirarrakinsu, Hafsa ta ce "Alina kin san wani abu?"

"A'a"

"Babanmu ne ya ce mu na gama makaranta aure zai yi mini, wannan Wan abokin nasa ne wai sona yake yi, ni tsoro nake ji"

Alina ta ce "Meyasa ki ke jin tsoro, ba kya son sa ne?"

Hafsa ta ce "Nima ban sani ba, ba na son na yi aure ya din ga zagina kamar yadda babanmu... Da sauri Alina ta rufe wa Hafsa baki tana girgiza mata kai. Tuni hawaye ya cika wa Hafsa ido, ya fara gangarowa. Jiki a sanyaye ta sauke hannun Alina, ta ce "Dan Allah Alina Yaya yana zagin Antynku? Ai kamar ma su ba sa faWa ko?"

Alina ta ce "Wallahi ban sani ba ko su na yi, amma bai taSa zaginta ba, dan Allah kar ki gaya wa kowa Baba na zagin Ummanku"

"Wallahi Alina ji nake ba na son shi, idan na ga ya zage ta tana kuka, jiya har miyar kuka mai zafi ya watsa mata. Idan kuma abin ya wuce, sai na ji na fara son sa, idan ya kuma yi mata sai raina ya Saci.
Ba na son na yi aure mijina ya din ga zagina ko dukana, wallahi zan iya mutuwa, Alina ba na son na yi aure tsoro nake ji"

Cikin kulawa Alina ta saka hannu tana share mata hawaye ta ce "Ba zai din ga dukan ki ba ko zaginki in sha Allah, ki yi addu'a. In sha Allah rayuwa za mu yi irin ta littafin da muke karantawa"

Hafsa ta waro ido ta ce "Novel fa ba gaske bane"

Alina ta Wan yi shiru ta ce "Haka ne, amma dai ai idan muka ro?i Allah zai bamu" da haka suka koma hirar littafi, suka bar waccan maganar.

Sai bayan magariba Alinan ta taho gida, sai dai ta san sai Yaya ya yi mata faWa, ?ila ma ya haWa mata da ran?washi ko murWe kunne. Tana ta sauri, ta zo daf da inda za ta karya ta shiga layinsu, aka Wauke wuta. Ta ja ta tsaya, tana Wan waige-waige. Kamar mai tsoron shiga duhun, ta Wan yi jimm sannan ta shiga. Daga bayan ta ta ga an kunna fitilar waya ana haska hanyar.
Ta yi ajiyar zuciya, tana bin gefen hanya tana tafiya a hankali, da son bawa mai fitilar damar wucewa, amma ta ga idan ta rage sauri sai ya rage, idan ta ?ara sai ya ?ara kamar dai ita ake haskawa fitilar.
Ta nemi guri Waya ta tsaya, tare da waiwayawa, dan ta fara tsorata da tunanin ko bin ta ake yi. A hankali ya ?araso yana haske mata fuska. Ta saka hannu ta kare tana Wan motsa baki za ta yi tsiwa.
"Wai waye?" Ta yi maganar tana tura baki. Bai amsa ba, sai da aka yi wasu sakanni, sannan ya haska mata fuskar sa da fitilar wayar.

Ajiyar zuciya ta yi tare da faWin "Wai dama kai ne, ka bani tsoro fa"

Bai ce komai ba, ya ci gaba da haska mata hanya. "To na gode" Ta faWa tana bin bayansa ganin zai wuce ta.

"Amm ?afarka ta gama warkewa?"

"Eh" ya furta a ta?aice.

Ta ce "To ina ka tafi kwana biyu na daina ganinka?"

Ya amsa da "Gida"

"Ina ne gidan naku?"

"Wani guri"

Ta sake cewa "Ina ne gurin, nan unguwar ne, ko wani gurin?"

"A'a"

"To ya ka baro 'yan gidan naku?" Ya yi shiru bai amsa ba, dai-dai lokacin da suka shiga layinsu.
Ta dube shi ta ce "Na gode sosai da sosai"

Ya ce "Mu je na ?arasa haska miki"

Alina ta ce? "Idan ka hasko mini ma daga nan zan hango har cikin soronmu" Gaba ya sake yi ya bar ta, a dole ta sake bin sa tana cewa "Ai da kar na wahalar da kai ne, amma shikenan"
Daga tsallaken ?ofar gidan ya tsaya yana haska mata har cikin soron su.

Ta tsaya ta waiwayo ta Waga masa hannu "Na gode sosai da sosai, sai da safe"

Shi ma ya Waga mata hannu, ya tsaya har ta shige.

Ya juya zai tafi, ya yi karo da Isma'il a tsaye a bayansa yana kallonsa.


SARA DA SASSA?A

YOTA 002

P5

A tsorace Ya yi turus yana kallonsa, jikinsa a sanyaye yana jiran cin mutuncin da Isma'il zai yi masa a wannan karon.
Sai dai ga mamakinsa bai yi masa magana ba, ya raSa shi ya wuce. Wata irin ajiyar zuciya ya sauke, ya juya ya tafi.

"Alina" ya shiga gida yana ?wala mata kira.

"Na'am" Ta yi maganar tana fitowa daga Waki.

"Me ya haWa ki da mutumin nan?"

A shagwaSe ta ce "Yaya har ka bani tsoro, na dawo daga gidan su Hafsa, aka Wauke wuta a hanya, shi ne ya haska mini fitila"

"Gidan su Hafsan ne ki ka je ki ka yi zamanki har isha'i ko Alina? Wallahi da na san ba ki dawo ba, har gidan su Hafsan zan je na same ki, na zane ki tun daga can mara ji kawai"

Ta risunar da kai ta ce "Ka yi ha?uri dan Allah"

"Ni ?yale ni, sai kin yi laifi ki wani kwantar da kai kina a yi ha?uri kamar kyanwa"

Ta yi shiru tana sunkuyar da kai. A gida ya yi sallar isha'i, sannan Nadiya ta zuba masa Abinci.

Ganin yana jin haushinta, ya sanya Alina ba ta yi masa surutu ba kamar yadda ta saba, ta ja bakinta ta yi shiru.

Can Alina ta ce "Antynmu ni ko na tambaye ki mana"

"To tambai, me za ki tambaya?"

Alina ta karkace ta ce "Anty wai dan Allah ku na faWa da ke da Yaya?"

Nadiya ta ce "Ai ga yayan naki a nan tambaye shi mana" Alina ta no?e kafaWa.
Nadiya ta yi dariya ta ce "Meyasa ki ka tambaye ni?"

"Hafsa ce take cewa babansu na zagin mamansu. Ya ce aure zai yi wa Hafsa da ta yi candy, shi ne ta ce ba ta son ta yi aure, mijinta ita ma ya din ga zaginta"

Nadiya ta numfasa ta ce "Duk yadda muke sonki ba kya laifi mu yi miki faWa?" alina ta jinjina kai.

"To babu zamantakewar da babu saSani, amma fahimtar juna ke kawo zaman lafiya.? Ni da yayanki...

Yaya ya katse su a fusace "Shiyasa ba na son yawace-yawacen nan, a can ake gurSata miki tunani. Babu wani mijin kirki da yake zagin matarsa. Ni kin taSa ganin na zagi Masoyiyya?" Alina ta girgiza kai.

"Amma idan ta yi laifi, ina yi mata faWa, shi ma ba kullum nake yi nata a gabanki ba, haka mijin arziki yake. Dan haka baban ?awarki mahaukaci ne"

Nadiya ta ce "Subhanallah baban ?awarta ne fa"

"To babanta ne? Mahaukaci ne mana, banda mahaukaci ya za a yi yaranka su san kana zagin babarsu a gabansu dan hauka. Ke tashi ki tafi ki je ki kwanta. Kema tashi mu tafi" Alina ta tashi sumi-sumi ta tafi Wakinta.

Ko da suka shiga Waki Nadiya ta ce "Yaya
Masoyi, ka din ga gaya wa Alina gaskiya fa. Idan mu soyayya muka saka a gaba lallai ne ta samu miji irirnka".

Ya haye kan gado yana faWin "Na raini yarinyar na aura maka, ka zagar mini ita, da kuwa na fasa wa mutum baki wallahi. Balle a ce duka sai na kusa binne mutum da ransa ba"

Ta tuntsire da dariya ta ce "Allah mai 'ya"

Ya ce "Sa wasa, ai yau ko da wani aka kama Alina, gara ya sako mini ita salin alin, a kan ya taSa lafiyarta ko ya zage ta. A yadda Alina take babu yadda za a yi ta yi wa mutum laifin da zai dake ta ko ya ci mutuncin ta. Babu abin da ya yi mini zafi da laifin da ta yi, na aura wa mutum ita ya wulakanta mini sai ya gwammace mutuwarsa wallahi. Idan ta yi ba daidai ba, gara mutum ya dawo mini da kaya ta ta fasa auren"

Nadiya ta ce "Ohh anya zaka iya aurar da ita kuwa?"

"Eh mana, shiyasa ke ma nake ?ara lallaSa ki masoyiyya, saboda kar na zaluce ki, wani ya auri ?anwata ya cutar da ita
Allah ya ba wa Alinana wanda so ta ya kula mini da ita kamar yadda nake sonta. Shiyasa sai na dirje na tantance yadda yakamata zan ba wa mutum" Ya yi maganar yana kwanciya a jikinta. Ta so ta furta abin da ke ranta, amma ta san tana maganar za su yi faWa, a dole ta haWiye ta yi shiru ta rungume shi.

****

Yana daga kwance ya dafe kansa, da sallama ta shigo bakinta Wauke da sallama, ya amsa ba tare da ya Wago ba.

"Ashe kana nan, ina ?asa ina ta bulayin neman ka ai"
Ya sauke hannun a hankali ya gyara kwanciyarsa ya ce "Ina nan"

Ta zauna a kusa da shi, ta ce "Ni wai dan Allah ya maganarmu ne?"

"Wacce kenan?"

"A'ah maganar motocina mana, waWanan fa tsofaffi ne wanda waccan first ladyn ta yi amfani da su ne, a cikin allowances Wina ka bayar da umarnin a sayo mini sababbi, wannan na rarrabawa mutanen da suka yi mana wahala"

"Dan Allah ni dai a yanzu ki ?yale ni, mene ne aibun motocin nan, daga zuwanmu sai mu saka wa dukiyar al'umma wawa"

"Haba dan Allah, ba batun saka wawa bane ba, abu ne da yake a rubuce fa, ni dai gaskiya ka yi wani abu a kai, ni wannan motocin sun yi mini tsufa gaskiya"

"Shikenan na ji, zan yi magana da Halilu su duba"

Ta sauke numfashi tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login