Showing 3001 words to 6000 words out of 53964 words

Chapter 2 - Sara Da Sassaka Hausa Novels free By Ayshercool

14 Jun 2026

746

su yi sallama ta tafi, har ya rage saura su biyu. Suka ?arasa wata mararraba, ta dubi Wayar Ta ce "To sai kuma Allah ya kaimu gobe, ki ri?e dai-dai inda ki ka tsaya mini, za ki ?arasa bani labarin, ni idan Yaya ya kama ni da karatun littafi ina ga kashe ni zai yi, amma duk yadda za a yi ki karanto ki zo ki bani labari"

?ayar ta yi dariya ta ce "Nima a Soye nake yi, sai kowa ya yi bacci, nake haska fitila ?asa-?asa, ki gaida gida da matar Yaya"

"Za ta ji in sha Allah, ki gaida su baby" Tana ?o?arin shiga wani layi, ta waiwaya baya suka sake yin ido huWu da matashin nan. Dogo ne launin fatarsa ba za ka kira shi ba?i ba, kuma kai tsaye ba za ka ce fari bane. Fuskarsa na Wauke da yanayi na samartaka, yana da Wan jiki, sai dai fuskarsa a cike da ?asumba, ya sanya wata uwar babbar riga duk ta yamutse babu guga, yana da manyan idanuwa sai dai ba farare bane, sun sirka sun yi ja, haka kurum ta ji tsoro na neman ya shige ta. Da sauri ta shiga layin nasu, amma da ta yi nisa ta waiwaya sai ta sake ganinsa. Ba shiri ta fara sauri tamkar za ta tashi sama. Ta sake waiwayawa cikin tsoro, sai ta ga ba taga gan shi ba. Ta yi ajiyar zuciya, ganin layin babu kowa, ya sanya ta kyalla da gudu ta ?arasa gida.

"Assalamu alaikum" Ta yi sallama daidai lokacin da ta faWo tsakar gidan.

Matashiyar mata ce a tsaye, tana kwashe shanya ta ce "Yaya? Ke da wa?"

Ta Wan waro ido "Wani mutum na gani, tun daga ?ofar islamiyyarmu yana bina"Ta yi maganar fuskarta na bayyanar da tsoro.

Matar ta yi turus tana nazarin maganganunta. "Yake binki saboda me?"

Ta ce "Ina na sani, daga baya dai da na shigo layin nan, ya daina bina, dan da na waiwaya ban gan shi ba"

Ta yi murmushi ta ce "Alina kenan, ?ila ma hanya ce kawai ta biyo da shi, ki ka sani ma, ko saurayi ki ka yi, gani yayi yana so ya biyo ki? Amma ki ke ta guje-guje kamar ba budurwa ba"

Ta waro ido tana ?iftawa ta ce "Kai rufa mini asiri, kar Yayanmu ya ji wannan maganar ma, wai a ce na zo da saurayi ai sai ya kusa kashe ni, rufa mini asiri. Amma an rage abinci?"

Matar ta? tsuke fuska ta ce "To acici, ai kya fara zuwa ki cire kayan ki nutsu tukuna"

Alina ta nufi Wakin tana murmushi ta ce "Kin san ina da tsutsar ciki ne, da na ci take cinyewa"

"Ke ce tsutsar ai" Ta yi dariya tana shiga Waki.

****

Tana tsugunne a cikin turken awakin da ke tsakiyar ?aton tsakar gidan. Ta share turken tsaf, ta din ga kama dabbobin tana Waurewa Waya bayan Waya. Ta gama ta zuzzuba musu abinci da abin sha.

"Sannu da aiki Ramatu" ta Wago ta kalli farin dattijon, da yake zaune a kan tabarmar kaba, gefensa da radio yana saurare.

"Baffa dan Allah ka din ga gaya mini sunan zamani, tun da ka je mini visiting, ka faWi Ramatun nan, ake tsokanata"

Ya yi dariya ya ce "To Ramata"

"Kash ana jika dai kunamar bebe Baffa, ka ce Rahma"

"Na ?i" ya yi maganar yana dariya. Ta ?arasa ta zauna a kusa da shi a kan tabarmar.

"Idan kin huta, zan baki magani ki kai wa Talatu, an ce yaronta yana masassara"

Ramata ta rausayar da kai "To Baffa" ta yi maganar tana Wan sunkuyar da kai.

"Ramata, na san abin da ki ke tunani, babu ruwanki da su, da kin kai ki dawo, kar ma ki tsaya ki ji me za su faWa"

Ta jinjina kai ta ce "In sha Allah Baffa, amma dama...

"Dama me?"

Ta Wan daidaita nutsuwarta ta ce "Baffa zan samu ci gaba da karatun kuwa?"

Ya Wan yi shiru, sannan ya dube ta "Ramata, zan yi alfahari na ga kin yi karatu mai zurfi, wata?ila albarkacinki, mu samu ci gaba da mafita a garin nan, amma kina kallo a haka ma, su na nema su kafirta mu, saboda makarantar da ki ka yi. Ki yi ha?uri a manemanki, ki samu wani ku daidaita ko ba yanzu ba, idan da rabo sai ki ga kin ci gaba a gaba. Amma ba na so baki ya yi mini yawa a kanki. Duk da na san ko a yanzu mun ciri tuta kaf rigar garin nan, babu wadda ta samu ilimin da ki ka samu, na shiga kundin tarihi ginis rikol suke cewa a radio ko me?"

Ramata ta tuntsire da dariya ta ce "Baffa guinnes world record ake cewa. Kar ka damu ko kai ba ka shiga ba, ni zan shiga, zan rubuta littafi mafi tsawo a duniya, ko kuma wani abu mai ban mamaki dai, da sai duniya ta tafawa Ramatanka"

Baffa ya yi dariya ya ce "Ko a yanzu dole na tafa miki ai. Ai ni tun da aka nuno mini ke a salalula, kin ci gasar lissafi, sannan na ji sunanki da nawa a radiyo, na ce haihuwa mai rana, dalilin ramatuna ga sunana a radiyo"

Wata mata ce ta fito, daga Waya daga cikin jerin bukkokin da suke harabar gidan, tana jan guntun tsaki, da surutai ?asa-?asa. Ta harari inda su Ramata ke zaune suna hira.

Ramata kuwa hankali kwance suka ci gaba da hira da Baffanta. "Yanzu ka ga Baffa, da karatun boko ka yi, tsaf za ka zama farfesa, kana da saurin gane abubuwa da ri?e su"

Suka yi dariya baki Waya.

*****
Su na zaune da daddare su na cin abincin dare.

"Alina" ya kira sunanta

"Na'am Yaya"

"Tunanin me ki ke yi ne?"

Ta ce "Ba komai, abinci nake ci"

Yaya ya ce "FaWi gaskiya dai"

Matar Yaya ta yi murmushi ta ce "Alina na faWa"

Ta Wago ta ce "Me?"

"Abin da ki ke tunani mana"

Alina ta yi dariya ta ce "Ai babu abin da nake tunani"

"A'a fa, Yaya saurayi ta yi shi ne...

Da sauri Alina ta ce "Innalillahi, wallahi yaya ba haka aka yi ba, haba Anty idan ya zane ni fa?"ta ?arasa maganar a shagwaSe, kamar za ta yi kuka.

Ta kwashe da dariya ta ce "Yaya ka san ba zan yi mata ?arya ba ko? Siriki ta samo maka"

Cikin tsoro ta ce "Wallahi ni ba saurayina ba ne ba, kin gan shi kuwa, ?azami da shi fuskarsa duk gashi" Ta yi maganar duk a ruWe, da ?o?arin kare kanta, kar yayan ya Wauka da gaske ne.
Ganin ta ruWe shi ma ya ce "A'a mutuniyar gaya mini gaskiya, idan aure ki ke so ai ba wani abu, ki turo shi mu gaisa mana"

Kawai ta hau kuka "Ni wallahi ba saurayina ba ne, ba aure nake so ba"

Gaba Waya suka hau yi mata dariya, ya ce "Ni dai kin san bana son kwana-kwana, abin da ki ke so shi nake so. Masoyiyya ina ga zan ba ki kuWi a fara sayayya"

"A'a da wasa nake yi, haba Alina daga wasa sai kuka, ba mai yi miki aure yanzu, sai mun gama jin Wumin juna ko ?anwar yaya?"

Ta yi maganar tana janyo Alina jikinta.

Ya yi dariya ya ce "Wai kukan take da gaske?"

"Wallahi kuka take yi"

Ya mi?e yana faWin "Babu ruwana, ai kun fi kusa, Kano da jigawa in ji kanawa, ke ki ka haWa zancen"

Da kyar ta rarrashe ta ta daina kukan.

****

Uniform Win makarantarta sun sha karin guga, tana tafe tana ta ?ara karkaWe ?ura daga jikin uniform Win, idan ta karkaWe uniform, sai ga koma karkaWe jaka, ta koma kan goge takalmi. Ta Waga kai zata shiga lungun da zai ?arasa sadar da ita da titi, kawai ta gan shi a tsaye cak yana kallonta, da manyan idanunsa tamkar za su faWo, yau ma da wannan Koriyar babbar rigar a jikinsa, wadda take duk a yamutse.
Gabanta ya yi wata irin faWuwa ta tsaya cak.

1k

SARA SA SASSA?A...

AISHA ADAM (AYSHERCOOL)
YOTA 002

Wannan littafin 1k ne a telegram via 0069685771
Aisha Adam stanbic
Shaidar biya ta 08081012143

Page 2

Ganin yadda ta tsaya tana kallonsa, ya sanya shi yin gaba ya bata hanya dan ta wuce. Haka kurum ta ji jikinta ya yi sanyi, kawai ta canza hanya zuwa wata hanyar daban. Tana tafe tana waige-waige cike da matsanancin tsoro, dan gaba Waya ba ta yarda da mutumin ba.

Ana tsaka da assembly sannan ta shiga cikin makarantarsu, sai da ta ga ta shiga tukuna, sannan hankalinta ya kwanta ta samu nutsuwa.

****

Tana zaune ta yi shiru, ta lula a duniyar tunani, hankalinta da tunaninta ya yi nisa sosai da duniyar da muke ciki. Daga can sama-sama ta jiyo muryarsa "'Jikar makiyaya hattara, idan shanunki suka yi mini Sarna, da ke zan tafi a maimakon Sarnar da suka yi mini"
A firgice ta waiwayo dube shi, ta yi ajiyar zuciya. Ya zauna a kusa da ita yana murmushi.

Cikin damuwa da sassanyar muryarta ta ce "Wallahi ka tsorata ni, na Wauka da gaske ne, har na fara tunanin Sarakar da zata iya faruwa, a dalilin hakan"

Ya girgiza kai ya ce "Haba dai, Ubangiji Allah ya kawo mana ?arshen wannan tashin hankalin in sha Allah duk zai zama tairhi wataran. Ni ki ke jira ne ko ya ya?"

Ramata ta dube shi, dogon matashi ba?i. Ta rausayar da kai ta ce "Bayan kwana biyu ko ka neme ni"

Ya lumshe idanunsa yana kallon kyakykyawar fuskar Ramata, mai Wauke da siririn bille "Kin san ba na son a gano mu ne, kar a samu matsala, amma ki na nan Wi na" Ya yi maganar yana nuna mata saitin zuciyarsa.

Ta kwaSe fuska ta ce "Ni na yi fushi" Ta yi maganar tana tura baki, tare da kawar da kanta gefe, dan ba ta iya haWa ido da shi.

Ya haWa hanneyensa biyu ya ce "Tuba nake yi, ki yi ha?uri dan Allah hasken rayuwata" Ya yi maganar yana murmushi.

Ta yi murmushi ta ce "Ka san ba zan iya fushi da kai ba ai" Ta yi maganar cikin ?o?arin faranta masa rai, duk da matsananciyar kunyar da take ji.

Ta saka hannu ta Waukko wayarta da take ajiye a gefenta, ta duba.

Ta dube shi ta ce "An saki sakamakon jarrabawarmu, ka ji yadda ?irjina ya buga da sauri kuwa?"

Ya le?a fuskar wayar, kamar zai iya gano wani abu a ciki ya ce "A'a ki kwantar da hankalinki, khairan in sha Allah, ina da ya?inin za ki cinye duka jarrabawar"

Jikinta a sanyaye ta ce "Allah ya sa, ka san jarrabawa ikon Allah ce kawa. Aikuwa dole gobe in Allah ya kaimu in tafi cikin gari na duba."

Bukar ya dube ta ya ce "Babu wanda zai dubo miki sai kin je har cikin gari da kanki?"

Ramata ta ce "Gara na je da kaina, ba lallai wanda zai je ya iya duba mini yadda nake bu?ata ba"

Bukar ya ce "To ko na jira ki a bayan gari mu tafi tare?"

Ta girgiza kai da sauri ta ce "A'a Baffa zai raka ni. Idan kuma Allah bai sanya na duba yanzu ba, sai kuma idan na koma makaranta tun da su can kafe ta ake yi gaba Waya, wannan kuma a computer ko waya ake dubawa. Bari na je gida na gaya masa ma, Ubangiji Allah ya sanya sakamakon nan ya yi kyau, na sanya shi farinciki" Ta yi maganar tana tashi tsaye.

Shi ma ya tashi tsayen ya ce "Amin ya rabb, Allah ya sa sauran mutanen ?auyen nan, su yi koyi da baffanki a kan jajircewa, a yi ta samun yawan wanda za su nemi ilimi."

Jikin Ramata ya yi sanyi ta jingina da jikin bishiya ta ce "Yaya Bukar"

"Na'am Ramata" ya amsa cikin nutsuwa yana kallonta

"Duk da yadda muka sha?u,na san babu lallai aure ya yiwu tsakaninmu, ka ga a garin nan su na ce mini karuwa, saboda Baffa ya kai ni birni makarantar kwana, kuma na kai wannan shekarun Baffa bai yi mini aure ba. Ga kuma abin da yake tsakaninmu da zuriyarku na rashin jituwa, ba za su taSa bari mu yi aure ba ko?"

Bukar ya gyara tsayuwarsa ya ce "Ramata, ki ?arfafa zuciyarki ki yi koyi da Baffanki a kan jajircewa. Kar mu bar wata gaba da rashin jituwar da ba mu san lokacin da aka fara ba, su hana mana cikar burinmu. Sai dai ban sani ba, ko ba za ki iya aurena ba, saboda ni ba Wan boko ba ne kamar ke"

Ta dur?usa ta Wauki sandar kiwonta, ta kalli Bukar ta ce "Karatun boko baya cikin sharuWan aure, kuma boko ba ta sanya na sauya da komai ba, sai abin da na san ba daidai ba ne"

Bukar ya ce "Gaskiya ne. Muje na taka miki zuwa kan iyaka" suka tafi su na ci gaba da hira.

Ko da ta koma gida, ta shigar da shanun turke, tana tsaka da yi musu haya?i, Baffa ya fara ?wala mata kira.

"Na'am Baffa"

"Wai ke kina 'yar boko amma ba za ki fasa fita kiwo da shanu ba, ba kya gudun a samu matsala ma"

"Baffa ba za a samu matsalar komai ba da yardar Allah, na kula da komai yadda yakamata" Ta yi maganar tana fitowa daga cikin turken.

"Kina dai bawa 'yan boko kunya, ina Wan boko ina yawo da nagge"

Ramata ta yi murmushi, ta ci gaba da karkaWe hannunta.

"Idan kin gama, ki zo mu je ki raka ni zan duba marasa lafiya"

"To Baffa"

*****
Matsakaicin gida ne, mai Wauke da 'yan madaidaitan Wakuna.
Wata mace ce take ta kai wa tana komowa a tsakar gidan, tare da wasu 'yan mata su uku, biyu na ta aikace-aikace Waya kuma na zaune tana kallon waya tana tsifa.
Ta dubi ta zaunen ta ce "Mariya, tashi ki je gidan su Bilal, ki ce idan ta haWa ?anzon ta baki ki kawo mini. Sai ki biya ta shagon iliyasu ki karSo man wanke baki, ki sayo sugar sonake zuwa gobe in Allah ya kaimu zuwa jibi an gama haWa mata kayan komawa makarantar nan"

Mariya ta tsuke fuska ta ce "Mama wannan makarantar, in dai za ta koma duk sai kin Waga mana hankali, kamar ita kaWai ce 'ya" Ta yi maganar tana harar Nana da take wanke-wanke.

Naja ta yi murmushi ta ce "Kwantar da hankalinki, idan ba za ki je ba, ni idan na gama wanke-wanke na je na karSo"

"Dama hakan aka yi, da ke da Yaya duk lokacin da ku ka zo hutu, idan za ku koma duk sai ta tashi hankalin kowa, idan kun tafi ma ba ta da aiki sai zancenku"

?aya yarinyar da tun da aka fara ba ta yi magana ba, ta dubu Mariya ta ce "malama ki tashi ki je aiken da aka yi miki"

Mariya ta tura baki tana tashi tsaye.

Mama ta ce "Ai Hafsan ita ce daidai ke, tun da ni kin raina ni. Taho mini da wayata idan ina da Wan canji na kira yaron kirki na ji ya yake"

Mariya ta fito ri?e da hijjabinta, da wayar Mama ta mi?a wa mama wayar.

Ta karSi wayar ta daddana, ta saka a kunnenta ta Wan yi shiru ta ce "Alhamdillah ta shiga"

A nutse ya yi sallama, fuskar Mama ta faWaWa da murmushi ta ce "Soja mazan fama"

Tamkar yana gabanta, haka ya risuna ya ce "Mama ina wuni?"

"Lafiya kalau Harisu, ka tashi lafiya?"

"Alhamdillah Mama, ya su Naja ya shirye-shiryen komawarta makaranta kuma?"

"Kana lissafe kenan, Alhamdillah ga shi mu na ta yi"

Harisu ya ce "Ma sha Allah, Mama ku yi ha?uri dai, haryanzu ba a biya albashi ba, na so a biya mu kan ta koma, a ?arasa mata sayayya, amma Allah bai nufa ba. Ki ba ta ha?uri, idan na samu yadda nake so bayan salary abin da ba a saya ba zan je da kaina na kai mata har school"

Mama ta ce "A'a, ka kwantar da hankalinka ma, na haWa mata abin da ya samu, kai ma ka kula da kanka, ku na barikin ne?"

"A'a mu na daji fa a yi mana addu'a, ban gaya miki bane kar damu kanki" Kan Mama ta yi magana Mariya ta ce "Yaya dan Allah idan an yi muku albashin ka sayo mini nama"

Hafsa ta ce "Ka ji mahaukaciya"

Harisu ya ce "In sha Allah ko ban samu zuwa ba, zan aiko da shi a saya miki. Mama bani Naja zan yi mata magana"

Mama ta mi?a wa Naja wayar, ta karSa tare da yin sallama "Hello Yaya"

"Sallama dai ko"

"Yi ha?uri. Assalamu alaikum"

"Wa'alaikum salam, ya shirin koma wa makaranta?"

"Alhamdillah Yaya ya aiki"

Harisu ya ce "Lafiya ?alau Alhamdillah, ki na ji na Naja, ki yi ha?uri da abin da ya sauwwa?a, in sha Allah abin da bab zan zo har makarantar na kawo miki. Ku yi ha?uri in sha Allah wataran sai labari zai wuce, za mu zame wa Mama ababen alfahari. Duk wannan wahalar za ta wuce"

Naja ta yi murmushi cikin nutsuwa ta ce "Yaya dan Allah kar ka damu, wallahi ko ban tafi da komai ba, zan ci abincin makaranta na rayu, karatu kuma da yardar Allah ba zan baku kunya ba"

"Alhamdillah barakallah, Allah ya yi mana albarka, ba wa ?anwata wayar" Ta mi?a wa Hafsa ita ma su ka gaisa, Mariya ma ta karSa tana ta rashin hankali, wayar ta katse katin ya ?are.

Soyayya da tausayin da suke nuna wa junansu ba ?aramin sanya Mama farin ciki yake yi ba, ba ta jin tana damuwa da halin da suke ciki na babu, idan ta ga yadda Allah ya ba ta su shiryayyu.

Harisu kuwa bayan ya ajiye wayar, Suleiman ya dube shi ya ce "Wannan duk ?annenka ne Haris"

"Eh Oga, ?annena ne su uku ne Abbanmu ya rasu ya bar mini, su haWu ma zan ce har da Mamanmu"

"Wow, kai kaWai ne na??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????miji kenan?"

"Eh nikaWai ne"

"Allah sarki, Allah ya baka wuyan Wauka Haris, zan zo Mama ta bani Waya na aura"

Haris ya yi dariya ya ce "Girmanka ne oga an riga ma an baka" Ya ?arasa maganar yana murmushi.

*****

Tun da Alina suka rabu da su Hafsa ta nufo hanyar gidansu, kawai gabanta ya hau faWuwa, da tuna mutumin nan da take gani, da ta fara tunanin ko mahaukaci ne, yake bin ta.
Ta fara addu'a a zuciyarta, da fatar Ubangiji Allah ya tsare ta daga sharrinsa koma wane iri ne shi Win. Sai dai ganin har ta shiga layinsu, ba ta gan shi ba, hankalinta ya Wan kwanta. Sai dai tana sake waiwayawa ta hango shi a ?ofar wani Wan Wakin langa-langa, da ke ?ofar wani gida, yana Winke takalmi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login