Showing 27001 words to 30000 words out of 79064 words

Chapter 10 - Meke Faruwa Book Compelet

unguwa ce?Magaji ya kafa kofin ruwa yana sha,sai daya gama sannan yace,nan fa daya,wallahi bansan komai kan yarinyar ba,hasalima sau daya na taba ganinta.Ibrahim yace,to kai batayi maka kwatance bane?Magaji yace,nifa Bauchi muka ganta.Yarima ne ke sonta shine duk ya daga min hankali,yanzu haka gobe yake son jin ko ita wacece.Ibrahim yace,gaskiya ya baka aiki,Zaria tana da yawa,ta ina zaka soma nemanta?Magaji yace,shi yasa na biyo ta kanka tunda kaine dan gari.Babban misalin dazan iya badawa na yarinyar kawai shine,kyawunta nasan saboda tsabar kyanta bazata bata a unguwar da take ba.Ibrahim yace,to kafin a gano unguwar da take fa?Magaji yace to bari dai in mukayi Isha%??i sai mu soma tun yau.Haka kuwa,suna idar da salla suka shiga gari.Da G.R.A suka soma don zaton Magaji na ko %??iar wani mai halince,gida-gida suka dinga bi cikin G.R.A sune har sha daya da rabi.Washegari ko suka soma da T/Wada,S/ Gari,haka sukayi ta yawon neman inda zasuji labarin Bily,amma shiru.Bayan sunyi sallar La%??isar,suka shiga Ojo da har zasu wuce amma MGJ yace su shiga.
[8:47AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 31??}_

La'asar, suka shiga ojo da har za su wuce amma magajin yace su shiga anguwar.
Kai tsaye kusa da wasu samari suka yi dayan ko sai rantsuwa yake yi. Ibrahim yayi musu sallama suka amsa. In ban da dayan da yake ta zuba bai ma san ana sallama ba. Ibrahim yace, bayin Allah muna tambaya ne ko Allah yasa kun sani? Biyu suka hada baki gurin cewa,to magaji ya matso don Allah cikin ku ko akwai Wanda yasan wata Bilkisu? Yaci gaba. Yarinyar tana da kyau na ban mamaki. Samarin suka ringa kallon magaji kamar sunga wani sauna. Dariya ma ya basu, inda dayan yace Malam, Bilkisu suna da yawa a unguwar nan, kuma akasarin su kyawawa ne.Magaji ya yi shiru, can yace ita fa kyanta dabanne, kuma ta gama makaranta. Gaba dayan su suka sa mishi dariya har ma ya ji haushi zai tafi, sai daya daga cikin masu musun kwallon nan mai surutun tsiyan yace, Aa ko dai yana nufin Bilkisun gidan marina? Nan take samarin suka ce ita ce ma, don duk unguwar nan ita ce best a kyau. Magajin Malam da jin haka sai ya dawo yana cewa, don Allah yaro zo mu muje ka gwada min gidansu.Yace,to Magaji ya saka hannu cikin aljihu ya debo kudi %??ian naira ishirin ya mika musu ba tare da ya kirga ba,yace na gode fa,suma suna ta godiya.Ibrahim yace,bari na zauna baya shi ya shiga gaba saboda zai dinga yi maka kwatancen inda zaka bi.Magaji yaji dadin haka,don yana son ya yiwa yaron tambayoyi musamman ma da yaga yaron zaiyi surutu.Ya dubi yaron,sannan yaci gaba da tuki,yace abokina kusa kuke dasu kenan? Yaron yace,E,gida biyu ne tsakaninmu dasu.Amma gurinta zaka?Magaji yace,eh,yaron mai suna Sule,yace ai ina ganin fa bata nan tana Kaduna,aikin gidan TV takeyi,ko bauta ma kasa naji %??ian gidanmu suna cewa, suna zuwa yace da Sule ya shiga ya tambaya ko tana nan.Bayan fitar yaron ne Ibrahim yace da Magaji abokina zaka iya samun labarinta gurin yaron nan,don naga yana da surutu.Magaji yace nima na lura.Sule ya dawo da sakon cewa tana KD.Magaji yace,amma ka tabbata nan ne gidansu?Sule yace,nan ne,ko ba wata doguwa ba?Fara mai kyau?Magaji yace,itace,nan ne gidansu nan yaro ya labarta ma magaji labarin bilkisu
Bayan sun gama magaji ya kawo kudi ya bashi suka maida shi inda suka dauko shi suka tafi yana mamakin inda take zaune dan shi in ta tashi ne diyar wani hamshaki ce dan shi a zaton sa in ba'a samu gidan su a GRA ba toh cikin dai shahararrun unguwannin masu kudi take
Magajin Malam da ya gama ba Yarima labarin Bilkisu kamar yadda yaji sai Yarima yace,ka bincika sosai ko?Magaji yace duk wanda ka saka ba zai zo maka da sama da wannan labarin ba,sannan ga number dinta nan zan turo maka,wane saurayi ke nemanta?Bata dashi.Yarima yayi wani murmushi aransa kuma fadi yake,yarinyar nan ta cuce sa data ce ta sansa har kuma ta mammaida masa da maganganu.Layinta ya soma kira,amma sai aka ce ba zai je ba,nan take ya soma kiran sabon layin da Magaji ya tura masa,wayar ta soma ringing lokacin Bily tana tsaka da yin nafila,bata kalli wayar ba sai data idar ta sallame sannan ta dauko wayar cike da mamaki tace,to wanene wannan?Domin tasan ba kowa bane yasan layin,kuma wane mahaukaci ne da kiranta cikin dare haka?Tana dauko wayar ana sake kira,bata gane number din ba don shima bada wancan layin ya kira ta ba,sannan duk da(+)din data gani batayi tunanin cewa Yarima bane,duk da tasan cewa bata da wanda zai kirata daga wata kasa.Cikin mamaki ta saka wayar akunnenta,kafin tayi magana ya soma cewa,ke!%??iar gidan masu rinin tsumma,%??iar kauyen kayau,%??iar talakawa tilis,%??iar gidan ginin kasa.Kin cuceni da kika ce kin sanni,sai na saka brush na wanke bakina sosai saboda furtawa da nayi na cewa zan aureki.Wanene kike ikrarin kina dashi wadda mahaifinki Malam Mamman ke rini,uwarki ke aikatau?.....kai jahili! Ta katsesa da zafin rai,tana huci tace,kai jakin ina ne?Da baka san talaka da mai kudi da mai sarauta duk Allah ne ya halicce su ba?Kuma babu wanda Allah yafi so face wanda yafi bauta masa,kana zaton wayonka ne yasa Allah ya sakoka cikin gidan sarauta?Je ka shiga Islamiya,kana da bukatar sanin ilmin Tauhidi.Na biyu kuma duk da talaucinmu ba muzo roko gidanku ba,sannan Ubangijina shine wanda ya tsaya min,dashi nake takama,sannan baka san hakkin dan Adam ba da zaka min waya cikin dare.....ya katseta ni kika kira jahili?Tace ,eh.Zaki ga aikin jahilci,zan baki mamaki donni na wuce da tunaninki %??iar matsiyata kawai.Ya kashe wayarsa duk su biyun sun batawa juna rai,sun gaya ma juna maganganu masu zafi.

Yarima saboda shi namiji ne zufa ya shiga yi tare da yin jifa da wayarsa,yayinda ita kuma ta hau kan gado ta dora hannu akai ta saki kukan bakin ciki,bata iya fada ba,bata taba fada ba,don haka sai abin duk ya zamar mata sabo,don haka kwana tayi tana kuka,kafin gari ya waye fuskarta ta kumbura suntum,haka nan da ciwon kai ta farka,da kyar tayi sallah.Shirun da Mansu taji shiyasa ta fitowa,tasan babu lafiya don tasan Bily da yanzun tana kitchen.Ganinta cikin bargo yasa ta karasawa gaban gadon da sauri taga yanayin da bilyn take ciki hankali tashe tace Billy baki lfy ne ta daga kai kawai ta kamata zuwa jikinta tana mata sannu tace bari toh na kawo maki wani abu ki taba sai muje ko asibiti tace sam ita ba zata ci komai ba mansu Tai banza da ita ta tafi ta hado mata abincin amma sam billy sam taki ci sai kuka take tayi lallashin har ta rasa ya zata yi mata

Mansu ta kalli Faruk tace,baban dady na rasa yanda zanyi da Bily,dama so nake ka gama cin abinci in shaida maka yau ko fita batayi ba,bata ci komai ba sai kuka nayi tambayar duniyar nan taki ta gaya min damuwarta.Ya mike da sauri zo muje,tana zaune ta hada tagumi suka sameta,sannan duk da zafin da akeyi tasha rigar sanyi.Faruk ya jawo kujerar gaban madubi ya zauna agabanta,Mansu kuma ta zauna kusa da ita,ta dafa ta tare da cewa,Bily tunda ni kinki sanar dani damuwarki,ga yayanki nan sai ki gaya masa domin tun kafin in haihu nasan kina da matsala,boye min kawai kikeyi.Kada ki manta fa ni dake ko %??ian biyun da suka fito ciki daya alokaci daya basu kaimu shakuwa ba,ga zatonki bansan kina da damuwa ba?Bily ta kalleta da idanunta da sukayi jajir suka kumbura,sannan ta kalli Faruk tayi wani dan guntun murmushi wanda yayi sanadiyar zubowar hawayen da take kokarin makalewa.Muryarta tana rawa tace kada ku damu,ba wani dogon abu bane ya faru.Ta saka hannu ta kama hancinta ta dan ja iska,sannan taci gaba kun san wani lokaci abu kalilan ne yake bata ma mutum rai,domin zagin da Yarima yayi min wallahi anyi min gomansa amma ban damu ba,sai nasa.Faruk suka kalli juna shida Mansu,sai suka ji zancan wani banbarakwai,Faruk ne ya soma magana,wane Yarima?Ta nuna sa Yarima naka,taci gaba saboda Yarima na canza layi,amma bansan inda ya kuma samun layina ba ya kirani jiya yayi min tatas,harda gorin talauci.Babu abinda yayi min ciwo irin yanda ya zagi uwata.Faruk har suna hada baki da Mansu gurin cewa zagi?Tace zagi dai,Faruk yace tun dama menene ya hada ku?Bata boye ba,nan ta warware masa komai game da mafarkinta da Yarima zuwa ganin data masa,ta masa magana har zuwa sa-in-sar da sukayi dare jiya.Abin yayi matukar bata ran Mansu,Faruk ko cewa yayi sai ya kirasa yaci masa mutunci,nan Bily ta jajirce kan cewa kada ya kirasa,ya kyalesa in halinsa ne zai hadu da daidai shi.Mansu ko kallon Faruk tayi sannan tace,wai shin shi Yarima wanene shi?.
[8:47AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 32??}_

YARIMA MODIBBO cikakken sunansa shine Al%??imin Isma%??il Abdullah,shine da daya tilo namiji da iyayensa suka mallaka bayan sun haifi %??iaya mata ishirin da biyu.Sarki Isma%??il ya gaji sarauta ne gurin Babansa Abdullah tun yana da rai ya sauka yaba dan nasa Isma%??il mulki.Modibbo shahararren Malami ne mai tarin ilmi,su aminan junane shida mai martaba sarki Abdullah,tare suka taso wannan dalili ne yasa daya baya aiwatar da komai sai da shawarar daya,don haka lokacin daya kawo masa shawarar sauka daga kan mulki,Modibbo ya amince tare kuma da bashi shawarar yayi wa dannasa aure hadi da nadin sarauta.Sarki Abdullah yace shima nufinsa kenan,kuma yana so ne ya hadasa da %??iar wajenka Sa%??i.Modibbo yace,wannan dama tasa donna gani cikin lamarin aurensa danayi istihara.Shekara daya jal da auren hadi da nadin sarautar ta sintilo %??iarta mai kyau inda taci sunan matar Modibbo mahaifiyarsu Sa%??i,wato Salma.A takaice sai datayi mata shida sannan ya auri %??iar sarkin yankin Katsina,itama %??iaya hudu duk mata.Lokacinne sarki Abdullah,Allah yayi masa rasuwa,Wazirinsa shima tsakaninsu sati daya,sai dan Wazirin mai suna Hafiz shima ya gaji mahaifinsa bayannan ya kara mata biyu jere banda sadaka ga kuma kwarkwarori bakin abinda Allah ya halatta masa,duk babu wadda tayi koda barin namiji.Al%??imarin daya daga masa hankali kenan,saboda yasan mace ba zatayi mulki ba yana son magaji,haka yake kullum cikin damuwa har girma ya fara shiga,domin da yawa %??iayan nasa ya aurar dasu.Umma mai babban daki haka suke kiran Haj.Sa%??i,tana tausayawa mijinta kullum tana addu%??ir Allah yabawa mijinta da namiji koda ba agurinta ba,ko gurin sauran kishiyoyinta ne.Lokaci yayi nisa,haihuwa ma harta tsaitsaya musu,ba wai sun tsufa bane,Allah ne kurum ya tsaida musu ita.Kwatsam!Sai ga ciki jikin Umma mai babban daki,batayi saurin sanarda mai martaba ba saboda tasan tana sanar dashi yanzun nan zai daga hankalisa,sannan ya hana idanunsa bacci yana rokon Allah yasa da namiji ne.Cikin hakane wani dare takai ziyara gurin mahaifinta Modibbo take sanar masa cikin dake gareta.Modibbo yace,na ganki cikin mafarki kina shayarda wani yaro namiji,sai dai ba yana nufin lallai namiji zaki haifa ba,domin mafarkin Annabawane kurum yake zama gaskiya.Murna ta cika ta tace,a taya mu da addu%??i,sannan bana son mai martaba yasan da cikin nan.Modibbo ya dubeta yace,saboda me?Tace zaya damu ne,yace wannan ba dalili bane,ki sanar dashi.Sai dai kada ki sanar dashi game da mafarkina,domin karya saka rai.Umma tace,to Modibbo na gode,Allah ya kara lafiya da nisan kwana,sukayi sallama ta dawo gida.Cikin satinne matar waziri Hafiz ta haifi danta namiji,mai martaba yayi murna tamkar shine aka haifamawa.Inda waziri yayi kara yasa ma yaro sunan mahaifin mai martaba,wato Abdullah.Da yake anfi kiran mai martaba Abdullah da Malam,saboda yana da ilmi na addini,don haka sai ake kiransa Magajin Malam,wato jaririn da aka haifa.Wannan yasa mai martaba kara son yaron,Umma mai babban daki ta sanar da mai martaba cewa tana da ciki,murna sosai ya shiga yi tare kuma da rokon Allah.Gefe daya kuma zuciyarsa tana cikin damuwa inya tuna shi bashi da kwan da zai samar da namiji kamar yanda wasu Likitocin suka shaida masa lokacin daya shiga neman taimakonsu.Amma ya dai mikama Allah lamuransa,ya kan tuna kalaman Modibbo da yake cewa,lallai kada ya zama daga cikin bayi masu cire rai daga rahamar Ubangiji.Haka dai ciki yayi ta girma har zuwa lokacin da aka haife sa.Ranar wata Juma%??i an tafi masallaci,an haifesa ne awani asibitin kudi dake nan cikin garin Bauchi bayan Umma tasha wahala.Mai martaba yana Fada Jakadiya ta iso masa da albishir,zancen daya saka mai martaba farin cikin da Fadawa suka jima basu gani ba,nan take yace da Jakadiya ya bata kujerar Makka.Kafin mai jego ta dawo gida labari ya karade garin Bauchi da kewaye.Yanda asibitin ya cika shine dalilin sallamarsu zuwa gida.Tun ranar ake shagalin yanke-yanke har zuwa ranar suna,inda mai martaba ya saka sunan Modibbo yace tunda waziri yayi masa kara ya saka Magajin Malam Sai dai yana fatan inya sake samun wani namijin ya saka masa Abdullah,ko kuma in Modibbo ya girma yayi aure to yana fatan Allah ya barsa da rai yaga ya saka masa sunan Abdullah.Faruk ya dubi su Mansu yace,bazan iya sanar daku gatan da Yarima ya samu ba,duk abinda yakeso shi zaiyi shi zai ci,haka nan shi zai sa,banda yayi sa%??ir iyaye masu tarbiya da ilmi hadi da sanin yakamata,to ko daba karamar shagwaba zaiyi ba,ko ince daya lalace,tun yana karami yake zuwa Fada,mai martaba yasa ake kawosa.Wannan abin yasasa girman kai ganin yanda ake zubewa gabansu.Yarima wani yaro ne dan kwalisa mai tsananin tsafta tun yana karaminsa,ga manyance tare da son girma,yana da matukar wahala kaga y shiga harkar wani,haka nan baya son ashiga tasa,halayensa rabi na Turawa ne,ko ince na tsarin Musulunci ne,misali;yana da cika alkawari,in har yayi maka alkawarin abu tabbas ne babu go nd come,sannan ko kai waye karya ne ya zageka abayan idanunka shi dan karara ne ko kaji dadi ko kada kaji bashi da yawan hayaniya,shiyasa nayi mamakin sa- insarku.Ya dan dakata kafin yaci gaba,ya taso shi wani tauraro ne cikin kafatanin %??ian gidansu,haka nan gurin Kakanmu Modibbo bai hadasa da kowa ba,to haka yake cikin dangi kowa yana sonsa.Yayi karatun Nursery da Primary a (C.N.I)wata makaranta ce mafi tsada a Bauchi.Secondary yayi tane akasar Spain,yanzu kuma yana Malesia yana karatun Likita ne fannin mata.Bansan yanda zan gaya muku halin Yarima ba,shi dai dabanne komai nasa dabanne,bansan yanda zanyi muku bayaninsa ba,yana da tsattsauran ra%??iyi,haka nan baya son duk wani abu da zaya zubarda mutuncin gidansu,yana da alheri.Kada kuce ina yabonsa hakane halinsa.Bily tace,niko baban dady banga haka ba,Faruk yace ni kaina nasha mamakin lamarinku,shi ba mai shiga cikin lamarin wani bane,baisan fa bacin rai ba.Bily tace,shidai ya sani.Mansu tace,kadai gaya masa ya kiyayeta,ai talaucin ba bawa yake dorama kansa ba,haka nan don kana da kudi ba yana nufin Allah yafi sonka bane ya baka,wani kudinma in mai su baiyi hankali ba sai su kaisa wuta.Yace zan kirasa.
[8:47AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 33??}_

Bily tace,a%??i don son Manzon Allah(S.A.W)kada ka masa magana,bana son kace masa kala!Nifa ya wuce agurina,kada ma yaga kamar ma na damu dashi ne koda abinda ya faru,please forget about him,na bar maganar.Faruk yace shikenan.

Mai martaba ya kalli Umma mai babban daki,sannan yace,Sa%??idatu menene na damun kanki don kawai nace mun yanke shawara za%??i nemawa Yarima aure?Ranka ya dade,bawai na damu bane,ina duba karatunsa ne,sannan shekaru ashirin da hudu duka nawa yaron yake?Yayi dan murmushi.To ni banda Modibbo ya tsaidani da tuni ma anyi auren.Amma yanzun ma bazai dauki lokaci ba,Yarima yana bukatar aure.Shiru tayi domin tasan maigidan nata baya zartar da wani al%??imari sai da shawarar mahaifinta masani mai tarin ilimi,haka nan tasan suna da dalilinsu.Ta dubesa sannan tace,ina fata Yarima bawani shirmen yakama ba?Mai martaba yace,a%??i yana da kyau dai muga %??iayansa in Allah ya nufa zamu ga hakan,tace hakane,a ina ya samu matar?Mai martaba yace,wannan yana ga Modibbo,yace shine zai zabawa takwaran nasa mata.Umma tace,to Allah yasa mu dace,mai martaba yace amin. Duk da takaicin da Yarima yakeji na yarinyar,amma yana jin gara ya yarda kwallon mangwaron ya huta da kuda,don ba zai iya auren yarinyar ba,taje taci sa%??i domin yaso ne ya aureta ya wahalsheta.Yanzu kuma baya jin auren nasu zai yiwu,tunda yaji ita wacece.Sannan ya jinjina ma karfin halinta kasancewarta mace kuma %??iar talakawa har kuma ta iya ja dashi,tunda ya gano cewa ita din abin tausayi ce to ya barta.Haka Yarima yaci gaba da harkokinsa,ahankali har ya warware ya ma manta da batun wata Bily.

Ga Bily itama tuni ta saka damuwarsa gefe ta shiga harkokinta.Takaicinta daya shine yanda har yau ta kasa yakar mafarkinta,don har yau tana mafarkin Yarima.Kara zage damtse tayi gurin addu%??i,Allah ya rabata da mafarkin Yarima,ta tattara komai nata ta barma Allah,ta kuma sha alwashin tabar kara zuwa gurin Modibbo tunda suna da alaka da Yarima,duk da yanda zuciyarta ke son tsohon
Kai ko Faruk sai taji tana jin haushinsa domin tasan dole ne yafi son Yarima da ita,tunda Mamansa da Maman Yarima uwa daya uba daya,wata kusan kuwa ai tafi wata.Wani sashe na zuciyarta ma har yana zargin koma shine ya gaya ma Yarima wacece ita?Amma ta kasa yarda don tasan Faruk bazai mata haka ba. Kawu yayi sallama ya shiga wurin Modibbo,cikin girmamawa ya zauna gaban mahaifin nasa,sannan ya sunkuyar da kai yace,ina yini Modibbo?Lafiya lau,ka dawo lafiya?Yaya kasuwa?Kawu ya amsa da Alhamdulillah.Modibbo yace,to madalla.Ka shiga ciki inka gama harkokinka sai ka fito zan aike ka gidan mai martaba kayo min iso,gobe in muna cikin masu rai zanzo gurinsa.Kawu yace,yanzu bana komai bari naje inna dawo sai na shiga gidan gaba daya.Modibbo yace,to shikenan,in baka gajiba.Amma da kadan huta,kawu yace,ban gaji ba,bari in tafi kawai.Ana shirin tashi daga Fada,kawu ya isa.Ya nemi iso aka shigar dashi Fada.Nan ya isar da sakon Modibbo ya dawo.Mai martaba sam baya son Modibbo yana zuwa da kansa,yafi son ya aiko masa cewa yana nemansa,shiya dauki Modibbo mahaifi ba suruki ba,don haka misalin karfe tara ya fice ta kofar baya inda Magaji ke jiransa cikin mota.Duk gidan babu wand??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a yasan ya fita,sai ko Magaji da suka fita tare,shima bai san inda zasu je ba,ya dai kirasa awaya yace masa ya amshi mota ya jirasa bakin kofar baya.Sun hau titi sosai,sannan yace Babana gidan Modibbo zamuje,Magaji yana mamakin mai martaba sosai,sam shi bashi da girman kai,sannan duk inda zaije aboye shiya zaba don ya rakashi.Magaji ne ya shiga yayo iso,babu kowa sai Modibbo yana ta jan carbi.Mai martaba ya zauna daura dashi,Modibbo ya mika masa hannu da suyi musabaha kamar koyaushe,mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0