Showing 18001 words to 21000 words out of 79064 words

Chapter 7 - MEKE FARUWA BOOK COMPLETE BY HALIMA K. MASHI.doc

cikin bahon wankan mai cike da kanshin sabulai kaloli masu sa santsin jiki da laushin fata, kwance yake ciki ya yi lamo zuciyarshi dam da sha'awar yarinyar yar mutanen China, yau sati daya da haduwarsu kullum sai ta neme shi da yawa tana son shiga harkarshi musamman da ta San in yana makaranta to karatu yazo abin da bata sani ba makaranta tana cike ne da yammatanshi sai dai sun san baza ya kula su a school ba in kin matsu isko shi gidan shi sau biyu suna rigima da Vicky.
[8:46AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 21??}_

Bilkisu sun shiga shekara ta karshe a makaranta , da kyar da sidin goshin da taimakon su Abban Mansura ta gama Degree na farko, ta samu damar zama yar jarida, suna gida sai jiran bautar kasa, cikin yardar Ubangiji da sa'a Kaduna aka tura ta, farooq kam yace ba wata bautar kasa da Mansu zata yi saboda tsohon cikin dake gare ta tuni ma ya tafi da ita Kaduna gidanshi na can, don haka gidan su Mansu take son zama kamar yanda suka yi da Mansu, ta waya,

Dama cikin shekara hudun nan Mansu a shiririta take karatun, course din da aka bata ba shi ta nema ba, gidan farooq ya kama a malali na sani same road, ya yi kusa da sakatariyarsu, Bilkisu duk da cewa sai ka hau mashin, ranar da ta soma saka kayan NYSC zaku ganin tamkar tafi kowace mace sa'a Mansura ta ce kin yi kyau wlh Bily, ta dubi Mansu, ina tunanin yaya zanyi na fita da wando? Zan dinga saka after dress idan zan fita in naje zan cire.
zaune kofar gidan Yarima, magajin Malam ne tunda ya sauka ya iso gidan a kulle,ya sani kamar wannan lokacin Yarima yana makaranta, zaman kusan awa uku sai ga Yarima shi da yar mutan??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an China, hannuwansu rike cikin na juna, magajin Malam yace toh! Abu ya kara gaba, tunda yanzu har cikin gari yana yawo rike da mace, abin damuwa ba ne, ya tsaya cike da matukar mamaki ganin magajin Malam ya iso yana cewa, abokina tun yaushe ka ke a nan? Magajin Malam ya mike Yana dan karkade rigarshi, nafi awa biyu ina jiranka fa, suka yi musabiha rike da hannun juna suka nufi cikin gida, tana biye da su Yarima, ya ce jiki na fa ya yi sanyi da ganinka, Allah yasa ba hukuncin mai martaba ba ne zan fuskanta, magajin Malam yace barin na huta nayi sallah, to yi bari na amso mana take away suka fita shi da chelen don yanzu ta zamar mishi jaka, ko ina tana manne dashi ga tsinannan kishi, dama tana yawan gaya mishi su a dokar kasarsu mutum ba zai yi mata biyu ba.

Yarima kam ya ce mata shi sai dai tayi hakuri da shi, soyayyah zai yi da mata da yawa, amma macen aurenshi daya ce, ta kan ce ita ce? Sai yace mata ba zai iya sani ba, zaune suke tsakiyar falon Yarima da magajin Malam, yan ciye ciye suke yi tare da yan hirarraki ya matsu yasan Dalilin zuwan magajin Malam shi ko magajin Malam sai ja mishi rai yake yi, tare da tsokanarshi, Yarima don Allah magajin Malam yi min bayani mana, mikewa ya yi ya shiga bedroom din Yarima Ya dauko jakarshi irin wacce ake ratayawa , yazo ya zauna ya zage ta ya ciro envelop ya mika ma Yarima gashi in ji mai martaba sakon kenan yace lallai ka duba in je mishi da amsa, ya mike rike da jakarashi duba ina zuwa bari na maida jakar.

Daya bayan daya yake bin hotunan da kallo, ya'ya ne na sarakuna da na manyan attajirai, kuma yan juhohi daban- daban, domin ya gani a bayan hoton magajin Malam ya dawo ya zauna kusa dashi cike da tashin hankali mai tsanani Yarima ya dubi magajin Malam, wai martaba yana nufin in zabi mata? Ina zaton haka ne in ji magajin Malam, Yarima Ya ce gaskiya ba amin a dalci ba, 24 years shi ne zan yi aure? Gaskiya ba zan iya ba, kwana kadan mutum ya tsufa, ya tara yara magajin Malam yace to yanzu ya zaka yi?

Nasan dai ba zaka yi gangancin fada mishi wadannan magananun ba? Yarima zufa yake yi, ya dubi magajin Malam ni gaskiya ko da aure zan yi ban sha'awar matanmu na nigeria, musamman. 'Yan arewarmu kauyawa ne, ya watso ma magajin Malam hotuna duba fa ka gani, kalle su bana son irin mutanan gaskiya ni kuma bana da sha'awar Auren mata da yawa, mata daya jal zan yi dan bana son a cika min gida da yara yanda mazan hausawa suke yi, kallon shi kawai magajin Malam ke yi cike da mamaki.
[8:46AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 22??}_

Yace Modibbo kana bani mamaki in na ce ka canza kana min musu yanzu har da haihuwar ce ba ka so? Yace eh bana so ko ka taba ganina na dauki wani yaro iya tsawon rayuwarka? Shin ko wasa kaga ina ma yara? Magajin Malam yace to tunda ka ce baka son matan nigerian sai yan wace kasar, yan China? Cikin gatse ya tambaye shi. Yarima yaja tsaki ni yanzu kawai ka ce mishi cikin su babu wadda ta min, kallon hotunan magajin Malam ke yi cike da mamakin yarima, yanmata ne kyawawa, ya dube shi matan sauran kasashin farar fata ba su fi namu kyau da cikar halitta ba,farin ne kurum amma matan arewa sune matan da ya dace mu aura sabo..... Yarima ya katse shi, please wannan ra'ayinka ne ni basu min ba, magajin Malam yace ni ko kaga akwai yarinya da nake so amma ina shakkar tunkararta. Yarima ya dube shi, wannan wace yarinya ce har da zata daga maka hankali? Magajin Malam yace sumayya yar gidan Umman gombe, tsaki Yarima yaja, sannan yace kai dai soko ne, yanzu dama wannan yar yarinya ce har kake wani kana shakkar ta? Kada ka bani kunya mana, ni nan shi yasa na ke matukar burge kaina, duk yanda mace ta kai da tsaruwa tayi kadan in tsaya ina wani binta ko in lallabata ba ayi ta ba, kuma ba za'a yi ta ba, in da na gagara kenan, magajin Malam yace ai matan sun fi son irin Ku masu wulakantasu, ni dai zan kai kaina gurin sumayya da naso ne in jira yi zuwan ka sai ka ja min gora muje, da sauri Yarima ya kalle shi muje INA? Gidan su can gomben cewar magajin Malam, god forbid, ba zan iya zuwa gidan su da sunan na raka ka tadi ba, sai dai in gaida Umman gombe naje kai ni fa ko matan nan da suke da daraja a idona sai dai su biyo ni, ba dai ni na biyo su ba, ni suke ya yi ba su nake ya yi ba.magajin Malam yace ba zaka gane ba ne, matanmu na arewa suna da kamun kai natsuwa da kuma kunya ba za su taba binka ba,sai dai in an dace da masu ra'ayinka su daban ne, tsaki Yarima yaja sannan yace ba a wata mace da zan so ta ba, kaf Nigeria, na fada da babbar murya, magajin Malam ya yi dariya sannan yace daina zafafawa shi Allah ba yanda bai iya ba, in yaso sai ya dauko wuyan ka ya mika ma yar nigerian ta yi ta juyi da kai son ranta, Yarima ya mike tare da fadin wannan kam tatsuniya ce irin ta mutanen da, ko cikin mafarki bana zaton zai yiwu bare a gaske, kai dai kai mishi hotuna ka ce basu yi ba, shi kenan magajin Malam yace in kuma shi yaga wadda ta yi ya zaba maka da kan shi fa? Murmushin takaici Yarima ya yi sannan ya shiga bedroom din shi don yin wanka.

***************************

Cikin sa'a Bilkisu ta soma aikin bautawa kasa, an fi turata gidan radio station na Kaduna, fannoni daban daban duk tana tabawa, wani sa'in ma har gefen TV sukan turata, yau kan news zata yi a dauka duk ta kasa sukuni saboda zata yi wani Abu ne da bata taba zaton zai zo kanta ba, duk da tana sha'awar hakan. Mansu ita da farooq dinta suna ta karfafa mata gwiwa tun a gida, sai da aka dora mata kyamara ta yi addu'a samun nutsuwa nan take natsuwa tazo mata, ta shiga karanto cikakkun labarai cikin harshen turancinta din nan dan gaske, Masha Allah haka duk wadanda suka kalli labaran litinin din yau suke cewa, saboda ganin kyau tare da zazzakar muryarta tana dawowa, Mansu ta rungume ta tana cewa kin ganki kuwa? Tamkar dama kin dade kina yi kina karantowa kina dago kai tare da juya kyawawan idanuwanki, Bilkisu ta ce har ma da sharri wane juya ido kuma? Abokan aikinta ma sun sha mamaki tare da al'ajabin kwazonta cewa suke Allah kin yi kokari Bilkisu Muhammad Salis.

A Zaria kuwa babansu haushin mama yake ji nashi ganin ta tura ya karuwancine a Kaduna, in ma ta sake ta debo ciwon zamani ba dai gidan shi ba,su Ladiyo ma haka suke cewa, ta tafi yawon dandi suna zuga shi yana faman fada. Goggo Amarya kuwa cewa ta yi Allah ya isa tsakaninta da Fatima kuma tayi bakin cikin hada zuri'a da ita, auduga Mamanmu ta sa ta toshe kunnenta tana yiwa 'yarta fatan alkairi ne ta tsaya tsayin daka dan yiwa 'yar tata addu'a saboda Allah yana saurin karbar addu'ar iyaye ga ya'ayansu.

***************************
Lokacin rakiyar magajin Malam filin jirgi ne suke tattaunawa a mota, Yarima yana me kara jaddada ma magajin Malam sakonshi gurin mai martaba, fadi yake yi don Allah kace mishi duk cikin su babu wadda ta yi min, yar dariya magajin Malam ya yi kafin yace wlh ba zan iya cewa mai martaba haka ba, jin ka kawai nake yi, dama shiru na maka in na shiga jirgi in duba hotunan wadda ta kwanta min a rai sai na ce mishi ga zabinka, Yarima yace tab ka ce kaso dai ka kulla min tsiya? Magajin Malam yace tabbas domin kuwa ina fada sai a shiga biki, sai dai kaji an gama.Yarima ya yi parking gefen titi yace da ka cuce ni yanzu to yaya zan yi ne ma? Magajin Malam yace oho, ni dai ba zan iya yiwa mai martaba rashin kunya ba, domin wannan rashin kunya ne, kai ka kira wayarshi ka sanar dashi cewa babu wace tayi maka. Yarima yace kasan ko da wasa ba zan iya ba, to shi ne ni ka ke son in je gaban shi in gaya mishi haka, kimarshi ta wuce nan a gurina, ni kawai ka kai ni kada lokaci ya kure, jirgi ya barni a tasha, wayarshi, ya shiga Neman layin mai martaba, a zuciyar shi kuma yana kisima me zai CE mishi? Yarima yayi sallama lokacin da ya ji an dauka, mai martaba ba ya amsa sannan ya soma gaishe da mahaifin nashi cikin girmamawa, mai martaba yace ina fata kuna lafiya? Lfy lau in ji Yarima sannan yace am dama shi kenan dai dama zan gaishe ka ne, mai martaba yace kayi magana Modibbo nasan akwai abin da ka ke son cewa Aa ba komai ranka ya dade, yace shikenan kaga sakon gurin magaji ko? Yace na gani ka zabe ne? Mai martaba ya jeho mishi tambaya, eh am...Aa ban amma dai kawai Ku zabar min don ni banga wadda ta kwanta min ba.

Yarima ka duba sosai kuwa? Cewar mai martaba, na duba amma Ku duba min duk wadda kuka ga ta yi shi kenan, ni nawa bi ne In'sha Allah, to ko dai auran ne ba ka so? Ina nufin ya yi wuri? Aa in ji Yarima, ni duk yanda kuka yi shikenan zan bi, shirun dan lokaci sannan mai martaba yace shi kenan tunda ba su yi ba za a duba maka wasu sai dai ina maka nasiha da cewa kazama na kirki a duk in da ka ke ka guji zina saboda ita babban zunubi ce ka sani in ka yi da yar wani sai anyi da taka in ko da matar wani kayi haka nan za'a yi da taka, ka zama na gari wannan shi ne yace to na gode Allah ya kara maka nasara, magajin Malam yana nan zuwa yanzu zai taso yace Allah ya kawo shi lfy.

Ya dubi magaji cike da fara'a na ci nasara, kai mugu har kana min dariya, suka tafa ya kai shi filin jirgi suka tashi ya juyo gida cike da nishadi prince kenan.

Watanni shida kenan da fara service din Bilkisu, sallah ce ta zo babba, sun samu dan Hutu na kwana uku su Mansura gombe zasu je sallah sun matsa mata da cewa lallai da ita za suje tace bari in munje zariya kila in je, haka ne kuwa, Allah yasa tana da rabon zuwa, Mamanmu ta ce kuje mana ba zai yiwa ba ma in hana ki zuwa, suna zaune a falon Mansura na gidansu a can gomben tsarar rangida ne da a ka ganshi cikin family house din su farooq an sauke su da kalolin abinci masu dadi dangin farooq suna matukar son Mansura,
[8:46AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 23 ??}_

Yammatan gidan su hudu ne kannan farooq, sumayya ce kurum suke ciki daya dashi,sauran duk uban su daya amma kansu hade yake.Suna girmama mansura sun shiga dakin su suna labarin kyan Bilkisu.Da dare suna zaune dakin hajiyar farooq wadda take matukar jin nauyin mansura,da Bilkisu kadai take hira itama jefi jefi tace,yar nan na zata kin yi aure?Bilkisu tayi murmushi tace Allah bai kawo lokacin ba,ta dube ta cike da kulawa,to Allah ya kawo na alkairi kada ki yi ruwan ido ko ki ce sai wane kin ji ko?Bilkisu tace to hajiya,ni dai ma ban samu bane in na samu mai so yaushe ma zan tsaya cewa sai wane? Haka kawai ta ji hajiyan farooq ta kwanta mata a rai har ma tana sha'awar ta gaya mata matsalarta,hajiya ta gyara zama,me ke faruwa ne da ke 'yar nan? Bilkisu tace wlh ban sani ba hajiya,ni dai tunda na taso da sunan wasa ban taba ??samun wanda yace ina sonki Bilkisu ba. Al'ajabi ne ya cika hajiya tare da tausayinta,tace ke ko da za ku jima ne ai da kun je bauchi in kai ki gurin mahaifinmu,shi malami ne waliyin Allah,
In'sha Allah matsalarki tazo karshe, mansura dake gefe tana jin su,da farko har ta ji haushin Bily menene na tona ma kanta asiri? Amma jin haka sai tace hajiya zamu je don batun aiki kiyi waya ki ce baki jin dadi, nima farooq yasha gaya min ko zamu je gurin kakansu a bauchi, in na gaya mata sai tace mu bar komai hannun Allah hajiya tace to sai ya kai ku in'sha Allah za'a warware matsalar kada ki damu,godiya suka yi sannan suka ci gaba da dan tattaunawa, ran jajibari suka zo gombe washe gari ranar idi suka dauki hanyar bauchi, gidan Modibbo Al'amin Dattijo mai ran karfe nan suka sauka, gida ne na alfarma ginin zamani da 'ya'yanshi suka tsara mishi,farkon gidan,shi ne a sasan farko mai dauke da tafkeken falo da dakunan bacci guda biyu,daga ciki dan autan shi ne jafar tare da iyalinshi tsohon yana da yara kusan guda 16, shidanne maza yayin da goman suke mata, ya'yanshi duk suna da rufin asiri matan kuma duk suna auran masu rufin asiri. Farooq ne yayi musu jagora zuwa falon Modibbo yana zaune kan wata lallausar darduma kan kafet, tsohon mai yawan shekaru ba yada rudu sam tuni matanshi sun jima da rasuwa,farooq ya zauna kusa dashi yana cewa,barka da war haka Akaramakallahu,ka ko shaida mu?Su mansura duk suka zauna gefe,ya dago ido ya kalle shi sannan ya kalle su?Yayi dan murmushi,Ummmarul faruku duk da baka zuwa gaishe ni ai ba zan manta ka ba,wadannan dai su ne ban san su ba, kila iyalinka ne,cikin yar dariya suka gaishe shi, farooq yakara shige mishi sannan yace ka min uzuri saboda nisan garin da nake aiki, amma ai ina yo maka aike ko?Aiken ka baya damuna nafi son kazo ka gaishe ni fiye da sakon ka,yace to zan kula,ni kaina ina son zuwa ka dinga sa min albarka,yanuna mansura ga mai dakin na nan,ya tashi yadauko dady,yana bacci ma yadora mishi akan cinya,ga kuma danka nan tsohon ya rungume shi masha Allah,yayi girma to ka kai su ciki gurin kawun naka,ya mike ko mu shiga ciki mace mai kirki da son mutane ta sauke su cikin farin ciki
da la'asar Farooq yana son ganawa da tsohon amma mutane sun mishi yawa,da yawa 'yan gaisuwar sallah ne, manyan attajirai ne tare da malamai,farooq ya shiga cikin gidan yace ku shirya muje mu gaida umman gidan mai martaba,hajiya fati tace gaskiya ne suma dai nasan gidan yau yan gaisuwar sallah sun yi yawa, amma gara yau akan gobe,tunda gobe hawa gaban bilkisu ya fadi tace a ranta dama farooq suna da dangantaka da gidan sarki?gidan su yarima kenan,sun shirya bilkisu cikin jallabiyya baka ta zagaya dan gyale tamkar yanda larabwa suke yi,takalmin ma baki ne.Hajiya fati ta yi ta yabon kyan bilkisu da tsarinta, mansura cikin shadda galila suka sha anko ita da farooq suka nufi kofar fada. Tsararran gida ne ginin zamani duk da girman gidan harabar cike da motoci na alfarma suka yi parking sannan suka fito me yasa gaban bilkisu yake faduwa? Sun shiga kofafi faluka kashi-kashi, kafin su ka shiga wani tafkeken falo, yana shimfide da carpet kirar china me shegen laushi,
[8:46AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 24??}_

Ga kujeru na alfarma kusan gefe uku kowacce da kalarta kuma ta dace da gefen da aka jera su, wata Dattijuwa ta nufo su da fara'a tana cewa Aa umar farooq kune a gidan ina gajiya?yace babu gajiya hajjo umma tana ciki kuwa?Tana nan bari ayi muku iso,ta fito tace gata nan zuwa, sai nan ta shiga gyara mata inda zata zauna,ma'ana ta shiga kakakabe kujerar duk da ba ko kura akanta,kyakkyawar mace ta fito sanye cikin wani leshi na alfarma, gwala-gwalai ne suke kyalli a yatsunta a hannun da na kafa, zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login