Showing 66001 words to 69000 words out of 79064 words

Chapter 23 - MEKE FARUWA BOOK COMPLETE BY HALIMA K. MASHI.doc

kusa harma ya soma tunanin ko ta mutu ne suke boye masa? Yana dira dama daga shi sai kayan jikinsa,yayi wa Magaji waya,wane asibitin?Suka masa kwatance ya nufa, doguwar nakuda Bily tayi likitar tace su kwantar da hankalinsu zata iya haihuwa da kanta. ana cikin haka sai ga Yrm,duk suka cika da mamaki, office din likitar ya nema ya shige ya nemi son ganin matarsa kasancewar tasan aikinsa ne bata musa ba,suna tafe tana masa bayani shiko saurarenta baiyi ba shi dai burinsa shine ya isa gurin matarsa.yana shiga ya ganta tana ta fama ga Nurse kanta a tsaye ya isa gurin da sauri ya kamota lokacin abun ya kan kama sosai,nan ya shiga aikinsa cikin minti tara dan ya sawo kai,nan Yrm ya jawosa ya mika ma Nurse bayan ya yanke cibi.bai ko tsaya kallon yaron ba shita matarsa yake,duk abinda ya dace shine yayi mata,sannan yayi mata allurar hutu. Koda ya fito ana ta kallon jariri wannan yaba wannan, wannan yaba wancan duk sai yaji sun bashi haushi,su ta yaro sukeyi ma ga matarsa can a galabaice.shi kam me zaija masa kara haihuwa?Gida kawai ya nufa,ya watso ruwa,yana dawowa tana farkawa. Ta dubesa da dan murmushi,me muka haifa?Ya dan daure fuska bakiyi murna da ganina ba sai abinda kika haifa ko?Ta yunkura ta tashi,yayi saurin riketa kada ki tashi tace naji karfi fa ya zauna kusa da ita,tace naji dadin zuwanka sosai mana.
[8:40AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 84??}_

Kallon fuskarta yakeyi,ji yake tamkar ya bude kirjinsa ya sakata ciki,yace beauty kinji jiki,hankalina ya tashi sai zuciyata take sanar dani kamar zaki mutu ne tunda naga Allah ya kawo mana da sauki kila gobe na juya dama ina tsakiyar ayyuka,nan da wata uku zan gama in dawo mu zauna tare.tace yanzun ba zaka tsaya ayi suna ba?Sallamar su anty Salma ce ta katsesu,suka shigo suna faman taba baki,anty Fulera tana dauke da yaro,anty Fatima ce ta soma cewa,maijego kin tashi?Ai nazata bazaki iya tashi yanzun ba, saboda tsabar ragwanta. anty Salma tace gaskiya raguwa ce. Yrm yace kinfa san tun shekaran jiya take aikin abu daya,gaskiya tayi kokari,ni likitar cema naga alamar kamar bata san aikinta ba.suka ce ba wani nan ragwanta ne,Bily ta nuna ita dai tana jinsu yace to shikenan ku barta ta huta,suka mika masa yaron ya amsa yana kallon fuskarsa,sai yaji yaron ya burgesa,tunda ya amshi yaron shi take kallo ta gani shin yaya fuskarsa zata nuna,ga mamakinta sai taga yayi murmushi tare da cewa,yana da kyau bebyn,ta kalli su anty Fulera ta sunkuyar da kai,har suna hada baki gurin cewa munafunci in zakiyi magana yi mu kinga fitarmu,abinda haihuwarma kinyi kikayi kin tsaya sai yazo suka fita.Yrm yace,sun cika hayaniya,ya mika mata yaron yayi gashi ki ganshi ta girgiza kai,yayi dan murmushi yace,baki sonsa ne?Ta kallesa tana dan murmushi,sannan ta kalli yaron tace kai kana sonsa?Ya dago yaron zuwa bakinsa ya sumbacesa agoshi ina sonsa yanzun yana da kyau,tace kama da kai yayi?Yasa matashi a cinya kallesa ki gani,ta zata axuciya tace hasbunallahu wani'imal wakil,ya dubeta tace tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya bamu wannan yaron,%??iar dariya yayi kin rude ko?Likitar ce ta shigo ta dubata sannan tabasu sallama tana tsokanar Yrm.yaso tafiya washegari, amma beauty da yaronta suna daukar hankalinsa har ya kara kwana,dazai tafi hadasu yayi ya rungume wayarsa ya fito da ita abin mamaki yana ta daukar hoton Bily da bebyn ta Lallai abin mamaki ne domin in kaga Yrm yana daukar hoto cikin waya to wani abu ne mai mahimmanci daya danganci aikinsa bazaka samu hotunan banza cikin wayarsa ba,domin bashi da lokacin zaman kallon hoto,tsiraici a hoto baya burgesa,yafi son ya gansa muraran.bayan ya gama yana bakin gadonsa itama ta zauna,idanunsa suna kan jaririn yace beauty ji nake tamkar kada na tafi, ya juyo da dubansa gareta yana kallon tsakiyar idanunta,nazo da sha%??iwarki zan koma da abuna.ta matso ta kama tafukan hannunsa ta matsa,abin ya ratsasa har ya lumshe idanu tare da jn numfashi,tace daba don ina cikin biki ba,ko ban warke ba zan baka kaina har sai ka gaji,amma kada ka damu zan dinga zuwa maka cikin mafarki.ya tallabo fuskarta ya soma kissing dinta baki cikin baki,kukan yaron ne ya dawo dasu,shine ya rigata dauko yaron ya mika mata tasa shi a kafada yace no bashi nono in gani zama kiyi kyau da shayarwa?Tayi dan murmushi,ta soma kici- kicin ciro nono yana taimaka mata,yaron ya kama yana sha,Yrm ya tsura ma nonon idanu,sun cika sun kara girma, sannan basu kwanta ba,ya lura da kasan nonon yana da fadi,lallai ya taka sa%??i wannan baya faduwa komai tsufa,domin da irin masu faduwan ne ma gareta da sai yayi mata gyaransu sun mike.ya matso ya rataya hannunsa akafadarta ya saita wayarsa ya daukesu hoto su biyu ne suka fito don yaron yana cinyarta yana shan nono. Kwankwasa kofar ce ta dawo dasu daga shirman hotunan da sukeyi,Yrm ya bude kofar anty Saliha ce tace ina maijegon tun dazun nazo da baki %??ian barka suna can a zaune tazo nan ta nane inba zata samu zuwa su gaisa ba to ta bani yaron.cikin fushi take maganar,yace haba anty tana zuwa muna sallama ne, ta juya fuu, yace taso kina da baki ni dai saura minti kalilan jirgin Lagos ya tashi,suka kalli juna tace sai munyi waya,yace to,sannan ya shafa kan yaron tare da sumbatar lebunanta sannan ta fita.yana rike da kofarsa yana kallonsu har ta sauka daga falon,yayi ajiyar zuciya ya koma yana hada shirginsa.Koda ta isa dakinta haka anty Saliha tayi ta mata masifa agaban dangin mijinta,wai ita %??iar dadi miji,tabi ta like masa menene-menene, dhiru kawai tayi mata hardai suka fita haka akaci gaba da shagalin har zuwa ranar suna,inda yaro yaci sunan mai martaba,tun ana gobe suna %??ian Zaria suka iso,Mansu kuwa tun kwana hudu da haihuwa ta iso.anyi suna irin na %??ian gata,kyautuka dai maijego ta samu,kaya kuwa tasa har ta gaji,har washegarin suna jama%??i ce.sai da gari ya kara wayewa sannan Mansu ta tafi,bayan sun kammala komai ta bata kudade tasa mata cikin account dinta,don ita bazata samu fita zuwa banki ba.mai martaba doki yava takwaransa,Yrm yana kwance yana kallon hotunansu baya gajiya da kallon hotunan,wasu abokan course dinsa sunsha mamakin ganinsa yana kallon hoto harma suka tayasa kallo,sai gashi Yrm mai boye cewa yana da mata shine mai fadin matarsa ce da dansa,sun rude wanda har yaji haushin kansa me yasa ya nuna matarsa?Murna suka tayasa kan cewa yayi matukar dacen family koda yaushe Yrm yana nane da wayarsa,jira yake ya samu dan sarari zai kira beautynsa,waya ga ba sabon ba,su Yrm an shiga tarkon so sai dai shifa har yanzu bai san wai son matarsa yake ba kuma bai samu wanda zai sanar dashi ba.nata bangaren kuwa ba don har yau Yrm baice mata I love you ba data ce sonta yakeyi,koda bata san yaya so yake ba ai tana kallon fina-finai tana kuma karance-karance yanda Yrm ke nuna mata yasa ta bashi wata daraja cikin ranta.ita da Yrm yanzun kullum suna cikin lissafin kwanakin da suka rage masa,sannan anan gefen tana shirya masa kanta tana son ta tare shine yanda zai san tana da banbanci,sannan yasan har yanzu itace din dai,shiko nasa gefen tsaraba ce yake ta jibgo mata ita da danta,duk abinda ya gani sai zuciyarsa tace beauty zata so wannan,sai kawai ya loda in ma na yara ne sai yace kai bari in sai ma son,haka yake kiran yaron (son)wata rana kuma yace(my friend)wai yaron abokinsa ne tunda wai kwata-kwata da shekara nawa ya girmesa?Sai Bily tayi dariya.
[8:41AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 85??}_

Tunda Yarima yace ma Bily beauty cikin satin nan zan diro,amma ba zance miki ga rana ba,ta kasa zaune ta kasa tsaye, harma su Umma sukai ta mata dariya.yau ta shirya wannan tayi wancan da kanta take shiga kitchen amma shiru sai kiga har dare babu labari,yau kam tasha alwashin ba zatayi komai ba,tana falon Umma bayan sallar la%??isar, Umma tana zaune kan kujera yayinda ta dora kafafuwanta kan tuf-tuf.yallabai wato jaririnsu Bily yana kan cinyarta,Bily tana zaune kasa kusa da kafafun Umma tana shafa mata maganin ciwon kafa,tare da dan mammatsa mata kafar Umma tace,%??iata yau baza%??iyi wa ubannawa girkin ba?Cike da tsokana tayi maganar,Bily tace,na gaji Umma,babankin nan ja min rai kurum yakeyi bawani zuwan da zaiyi.Umma tace,muma kinga ai munci girki kwana biyu, dama haka kika iya girki?Kafin Bily tace wani abu sai sukaji sallamar Yarima da wannan muryar tasa ta kasaita. Zaraf Bily ta mike tsaye tare da cewa, dama kana hanya? Shiko kallonsu yakeyi ransa yayi fari kar yanda ya samesu yaji dadi,Bily ji tayi tamkar ta rungumesa,shiko ita ya nufo sai tayi maza ta zauna ya kalli Umma yana dariya,sannan yasa hannu ya dauki dansa yana cewa, Umma son yayi girma fa,kuma ya kara kyau, gaskiya beauty ta iya haihuwa.Umma tayi dariya sannan tace, shirmen kan nan yana nan dai babana?To kaki sanar damu ranar dawowarka, kullum sai Bily tayi maka shiri na musamman in baka dawo ba mu da %??ian gida kakarmu ta yanke saka sai mu kwashi gara, yace Allah sarki beauty yau dai gani ta dan harare sa cikin wasa tace,yau kam sai dai aci na gida nan ya gaida Umma sannan ya nufi sasansu Bily ta zauna zata cigaba da shafa ma Umma kafa tace a%??i-a%??i na yafe jeki gurin mijinki,haka ta bishi. Ai suna shiga falon farko ya ajiye(son)kan kujera ya jawota zuwa kirjinsa,wata irin ajiyar zuciya ya saki, jinsa yake tamkar an masa gafara,yace I miss you beauty,sannan ya lalubi bakinta.sun jima sannan suka dauki dansu zuwa sasansu. Nan ma da suka shiga ya kara jawo ta jikinshi ya tura hannuwan shi cikin rigar ta yana wani sansanar kamshin ta ta dan ture shi abban son kaki bari nayi maka sannu da zuwa ma ya dan tsotsi bakin ta toh ai beauty wannan ita ce sannu da zuwan ko? Ko akwai wanda yafi wannan ya kara shige mata dole ta hakura saida ya ja ta suka lula duniyar da suka kwana biyu basu je ba sannan suka yi wanka ta kawo mashi abinci yana ci yana kallonta yana jin nishadi da farin cikin dawowarsa wurin kyawawan iyalansa.

Da dare sun gama shirin kwanciya tana jikin Yarima son na gefen su sai kawai wayar Yarima ta fara ringing kuma tafi kusa da ita sai ta dauko Wayan kan screen din taga an rubuta T.girl ta mika masa sai ya kasa dauka tun a nan ta gane bashi da gaskiya sai ga call din ya kara shigowa sai ya dake dan kar ta zaci wani abu ya dauka duk da haka tana kwance jikinshi kuma tana jiyo muryar ta kadan kadan tana lura da a darare Yarima ke amsa mata har ya kashe tace kai da wa kake waya ya dake yace abokiyar karatun sa ce tace iya matsayin ta ke nan? Yarima yace ban gane ba tace kasan abunda nake nufi ai ko ita ce wadda ka maye gurbi na da ita da ka tafi sai ya hau fada shi baya son zargi kaza kaza ba dama yayi wata hulda da mace sai kice ina neman ta sai kawai ta tsura mashi ido kawai har ya gama tace masa Yarima da duk abun da kake ba wani damuna yake ba amma yanzu kasan wannan ta canza kuma da baka boye gaskiyarka amma yanzu ka koyi karya ta tashi ta dauki dan ta ta bar masa dakin ya bita da kallo tamkar ya bita sai kuma ya fasa,ransa ya sosu, yace tayi ta tafiyarta mana don taga na damu da ita shiyasa take yi min abinda take so,ya koma yayi kwanciyarsa,duk da bawai yaji dadin kwanciyar tasa bane, kuma yana zargin kansa da cewa shine bai mata adalci ba,ita kuma data kwanta sai ta soma tunanin cewa fushinta ba mafita bane,shin dama fushin tane ya dawo mata dashi kanta?Lallai fa ba fushinta bane,hakurinta ne da kuma addu%??i dole ne taci gaba da hakuri tare da addu%??i,amma bari ta barsa sai da safe ta koma gurinsa. Da safe tayi wankanta tana sanye da riga da siket na blue jeans kanta babu dan kwali ta tufke gashinta da ribbon blue,tana zaune tsakiyar gado tana yiwa son shafa, tafi son ta shirya yaronta da kanta. Yarima ya rasa sukuni dole ya nufo dakin beauty ya iske ta tana kici-kicin saka masa pampers. tsayawa yayi ya harde hannu daga bakin kofa yana kallonsu, cikin tsananin sha%??iwa, ajikinta taji da akwai mutum a bakin kofa,da sauri ta juyo tana kallonsa,murmushi ta sake tare da cewa, abban son muna sauri muzo mu kwashi gaisuwa shine ka rigamu zuwa?Ya shigo cikin jin dadin yadda ta tarbe shi,shima gadon ya hau ya zauna kallonta yakeyi sannan yace,ni da kuke fushi dani?Ta dora masa son akan cinya, kafafunsa kuma suna kan gado tana kokarin sa masa wando,tace haba nawa, wazai fushi da aljannarsa?Yasa hannu ya shafi kumatunta,dama matan duniya suyi koyi da kyawawan halayanki na hakuri da saurin yafiya,ga mazajansu,saboda ladabin da kike min yanzun ina jin kunya ki kamani da wani laifi tace ni dama ina jin kishinka bana son ka dinga rabar mata abin yana soya raina,ta zuba masa idanu gami da tagumi ya jawota zuwa jikinsa,insha Allah ba zan kuma ba,kinji?Tace to ka yafe min jiya na barka kai daya amma kasan banyi wani bacci ba,yace na yafe miki beautyna, inda kana gurin kai ko baka san so ba zaka fahimci wadannan suna cikin mayen so amma su basu gane ba.

Ranar da Yarima zai fara halartar asibiti don fara aiki a matsayin babban likitan mata,duk hankalin Bily ya dagu,gani takeyi matan zasu kwace mata miji,ya gama shirinsa tsaf cikin suit,takwas saura kwata ya kalli beauty yace duk wannan damuwar ta mecece?Tace to doctor ba ka fa karya ba zaka fita,ya tura mata kofi zuba min lipton kinsan bazan iya karyawa 8:00 ba,tace to in ten din tayi in kawo maka office?Ya girgiza kai,bance ki fita ba,tace to ni don Allah kada fa ka kalli mata,cikin sigar shagwaba tayi maganar, yace cikin dariya kema kinsan dole na kallesu tunda sana%??ita ce kallon nasu,ina nufin aiki nane duba lafiyarsu, in ta kama ma har taba jikinsu zanyi,t tace daina gaya min abin haushi,ya dubi agogo beauty barni in tafi,kinsan cikin tsarina babu African time 8 nayi alkawarin halattar office kinga saura mintuna,ta dauki jakar muje in raka ka Umma tayi maka addu%??i.yace ta min tun asubahi zan dai musu sallama a tsaitsaye, suka fita tare.goma daidai ta kirasa cikin hanzari ya daga wayar tace yaya aiki nawa?Ya lumshe idanu ya bude,aiki kam gashi nan inayi,kamar ni aikin ke jira,dama kinsan Allah beauty?Yacigaba tunda na zauna kan wannan kujerar marasa lafia suke shigowa ga kuma katunan wasu nan jibge,so ki tayani da addu%??i,tace zanyi amma break fa?Yace babu time tace haba don Allah shikenan nima bazanci komai ba,yace no,no kada kiyi min haka, me son zai sha yau?Tace duk mu hakura har dashi yace,a%??i zanci to nan da sha biyu kinji beautyna. tace zan kira sha biyun dai,ta kashe wayar.

**************************
Haka suke rayuwa mai ban sha%??iwa,sai dai a boye Yarima yana amfani da wani cream lokacin saduwarsu wanda a lokacin tarayyarsa da Tina yasan wannan in ya shafa shi yana tsinka spam ba zaiyi da ba sam bata sani ba ta dai gaya daina mata zancan tsarin iyali.
[8:41AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 86??}_

Duk wannan satin Bily rigima takeyi ita tana son taje Zaria,ta jima tana naci yana cewa son bai saba da iska ba,baya so a debo masa sanyi,ta hakura amma yau ta tada daru. kallonta kawai yakeyi duk taki cin abinci yanzun ma da zasu kwanta sai ta saka kanta gurin kafafunsa komai tayi sai yaji birgesa takeyi,ya tashi zaune yanzu beauty ba zaki ci abinci ba?Ta tashi zaune tana shasshekar kuka,don Allah yaya zanyi in iya cin abinci?Ni dai in kana son inci ne sai dai inka yarda inje inga mahaifana. sun jima suna son ganina kuma su suna min kara ne irin na %??iar fari bazasu iya zuwa gidana ba,sai yaji tausayinta yace to naji zakije,amma shine kika juya min baya,alhalin kin san na tsani hakan ko?Ta fada jikinsa to yi hakuri yaushe zan je?Yace jibi amma kwana nawa zakiyi?Tace sati ya zaro idanu,to wallahi a fasa tafiyar,ta kankamesa sorry,to kwana nawa zanyi?Yace zan daure kiyi daya,tace haba dai yaushe muka gaisa?Ta turbune fuska ta ja baya,indai daya ne na hakura,yace to naji biyu,tace ina laifin uku don Allah,shima a maneji, yace to naji amma gida nawa zaki bana sonki yawaita fita ana kallonki, tace to ina zanje ma daga fa gidanmu sai gidansu Umman Mansu,sai ko makota sai gidan Mansu din,ya zaro idanu Kaduna?Tace eh,ya girgiza kai ina hauka nike in barki kije Kaduna mutanan da aka ce suna kwace matan aure?Yanayin yanda yayi maganar sai data yi dariya, tace duk ba gaske bane fa ni dai iyakata gidan Mansu,sai kasuw... ya katseta da cewa kasuwa? Tabdijam, ki fasa zuwan ke nan salon kije maza suyi ta kallonki bazan iya ba,tace to shikenan na fasa zuwa kasuwan kaji?Amma fa gobe zanje gidan Umma muyi sallama da kuma Modibbo,yace goben sai da daddare na kaiki.ta shirgi tsaraba ga kudi da Yarima ya jibge mata, sirikanta ma sun hada mata tasu. su Mama sunyi murna da zuwanta, wannan karon ranar data zo tasa babansu ya kira masu aikin gini sukayi mata lissafin kudin da gidan nasu zai ci,fulastan bangon tsakar gida da kuma yin barandar waje tare da siminte bangon waje,Nan ta cire kudin ta bada ga abinci lodi-lodi sannan tabawa Umman Mansu kudi in an gama gyaran ta siyawa Mama kayan daki.itama ta bata nata.su Ladiyo duk sun zama ababen tausayi, suma ta basu kudi dama kowace bashi yayi mata kanta,nan sukayi ta godiya,da dare tana kwance Umma tana shafa%??i da wuturi,Yarima ya kirata yace waton yau an sami Mama an manta dani ko?Ta dan dubi gefen Mama,sannan ahankali tace,haba nawa komai na keyi kana raina,ban manta da kai ba,shine kaima kaki ka kirani yace ina sane na zata zaki kirani ne,tace to ya aiki? Yace lafia ina son dina?Tace gashi nan kusa dani yana bacci yace Mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login