Showing 63001 words to 66000 words out of 79064 words

Chapter 22 - MEKE FARUWA BOOK COMPLETE BY HALIMA K. MASHI.doc

hamsin ta iso.bayan gwaje-gwaje da %??ian tambayoyi ta gano cikin wata biyu da %??ian satittika, nan take ta sanar da Umma, murna gurinsu ba%??i magana,nan dai aka daura mata karin ruwa. mai martaba harda goron albishir ya hadama doctor Aisha dashi.ita dai Bily damuwarta daya,in Yarima ya samu labari yaya za%??i kwashe?A dare ko ya kirata sai tayi tunanin ta sanardashi kuma ta nuna masa ita bata so don in wani ya sanardashi to zasu kwashe ta babu dadi,yanzun ko ta siyasa zata bi.yace beauty yaya ne?Tace,um kai dai bari,muna cikin matsala fa,ya gyara zama tame kenan?Tace banga al%??ida ba gashi har na soma rashin lafia,Umma ta turomin doctor Aisha ta dubani bansan me tace ba naga dai gidan ya cika da murna,nidai gaskiya banason in haihu ka fada min me zanyi? Yarima ya kasa magana ma don takaici can yace gaskiya matsalar ma babbace, ko dai inzo ne acire shi? Gabanta ya fadi,amma sai ta daure tace kada kazo in akwai wata kwaya mai karfi ka min text dinta in aika asiyo min insha,yace yauwa kin kawo shawara, to amma wazaki aika?Tace Atika don batayi karatu ba kuma in gargadeta nasan zataje, yace shikenan zan turo inbai fita ba ki gaya min,tace to amma fa insu Umma sun kiraka sun maka murna kadaka nuna baka so don inmun cire kadasu gane ko su zarge mu. yace, haka ne beauty kada ki damu kin ji? Tace to sai na gani.
Hankalin Yarima ba karamin tashi yayi ba,shin wace kwaya zai ba wa beauty? Nan take ya shiga cikin asibiti gefen magunguna ya bincuko, nan take yazo ya turo mata su in ta samu kuma ga ka'i'dojin su, sannan ya kira ta yace ta gani? Tace, ta gani ta share ta ci gaba da sabgarta, shi ko kullum nacin tambaya ya ya fita? Tace Aa yace to zata iya ganinshi a kowane lokaci. Zai zo ya cire mata shi tace to gara haka din ma, ya ce ai su Umma sun kira ni har da mai martaba na dai nuna musu murnata tace to sai na ganka, ai suna gama waya ta kira magajin Malam a waya tace tana Neman shi yanzun nan, cike da far gaba ya zo don bata taba kiran shi ba.
Bilkisu ta sanar dashi Komai tace in yazo kasan dole ne ya cire cikin nan, ni yanzun ban san ya ya zan yi ba, kuma bana son in fada ma Umma, magajin Malam yace to lallai Yarima, amma kada ki damu ki barni dashi ni nasan yanda zan mishi in hana shi zuwa, nan take ya kira shi. Yarima ya soma mishi tsiya ango kasha kamshi, sai yau aka ga damar kiranmu? Magaji yace kai me ya hana ka kira ni? Yarima yace Aa bana son in takura maka ka samu gurin Hutu gashi kuma abun ya hada maka biyu, wato ga sabon shiga ga ka tuzuru yace ba komai, dama na kira ne in ce maka ina murna da samun baby, yaci gaba sai dai wani abu da bai min dadi ba, shi ne na shiga gaida bilkisu na same ta a galabaice, sai da aka dauko Doctor Aisha nan ta gano tasha wata kwaya ne don zubar da cikin, a tsorace Yarima yace yanzun ya ya ake ciki, su Umma sun sani? Magajin Malam ya kuma dagewa tamkar gaske yace yanzun dai da mun gama waya zan sanar dasu don na hana Doctor Aisha ta sanar dasu, musamman da na fahimci da saninka zata zubar da cikin, magana daya dai yanzun ko Ku janye ra'ayinku kai da matar ka ko kuma wlh zan sanar da su, musamman in har kazo don na sanka sosai zaka iya cewa zaka zo kayi aikin da kanka.
Jikin Yarima ya mutu, sannan yace amma dai magaji kasan haihuwa ba ra'ayina ba ne ko? Tsaki magaji yaja sannan yace, wannan sai ka gaya ma ubangijin da ya baka cikin, ya kashe wayar shi.ya dubi bilkisu bar shi kawai, ba zai zo ba, suka yi ta dariya ita da magaji tayi mashi godiya sannan ya tafi.
[8:38AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 81??}_

Ya kira bilkisu yana cewa, ya ya aka yi ta bari magaji ya sani? Tace ya shigo gaishe ni ne ya same ni cikin wani hali shi ne ya kira likita.... Ta soma kuka cikin kissa ni gaskiya ba zan iya ba, gashi yace zai gaya ma su Umma kuma kasan yanda su Umma suke murna za su dauki mummunnan mataki ne a kanmu, yanzu ya ya zan yi? Yace ya ya zaki yi kuwa in ban da hakuri? Kina nufin zan zabi bacin ran iyayena saboda ranki yayi fari? Ba ki kai wannan matsayin ba, ta soma sabon kuka wato danni baka kaunata in zan mutu ne in mutu ko shi kenan, ta kashe wayar sannan ta soma dariya tana cewa in kasan wata ai baka San wata ba, don ma kada ya dauka fushin wasa take yi sai ma ta kashe wayarta bayan ta kira Mansura ta mata bayanin komai, sannan ta ce zata kashe wayarta don kada ta nema ta ji shiru, Mansura ta kara ma ta wasu dabarun sannan suka yi sallama, hankalin ta kwance ta gode ma Allah tasan bata da matsala ta gefen Yarima, Allah yaga niyyarta Yarima da farko bayan ta kashe wayar cewa ya yi ke dai ki ka sani ko a jikina da bacin ran iyayena ai gara naki.

Amma kuma me?

Kunnuwanshi sun kasa daina jiyo mishi kukan da ta kashe waya tana yi yayin da zuciyar shi ta shiga cewa kamata ya yi ace ka lallashe ta ne, zugin zuciyar ya matsa mishi nuna mishi take yi bai yi mata adalci ba, haka dai ya daure yayi jarumta har zuwa washe gari inda abin ya ishe shi har ya nemi layinta cikin wayarshi amma a kashe, yayi ta kira shiru ya bata awa daya ya sake kira nan ma shiru, jikinshi ya yi sanyi, zuciyar shi ta dame shi yinin ranar babu kuzari duk wadanda suke tare dashi duk sun fahimci yana da damuwa, musamman Tina. Shi kanshi ya rasa dalilin damuwar tashi, akan matar da ya tabbatar ba sonta yake yi ba, wasa- wasa yau kwana hudu yana neman layinta babu dare babu rana, duk da ya kira magaji ya tambaye shi shin bilkisu tana nan? Magaji yace, ban sani ba sai dai ka kira wayarta, Yarima yace yau kwana hudu wayarta tana rufe, magaji yace to ka kira ta cikin gida mana? Yace bari ya yi hakan.

Umma ya kira bayan sun gaisa yace, Umma wai ya ya jikin bilkisu ne? Yaci gaba ina ta neman layinta amma shiru? Umma tace, jikinta da sauki babana, dazun nan ta shigo nan amma zan kirata in ji, yace to suka yi sallama.

Koda Umma tasa aka yi mata kiran bilkisu, ta tambaye ta ko lfy wayarta take ana ta nema ba a samu? Sai bilkisu tayi karya da cewa, batirin wayar tata ne ke da matsala, amma ta aika yanzu za siyo mata wani, Umma tace to dama maigidan ki ne yake ta nemanki, tace zan kira shi in nasa batir din.

Bayan taje daki sai ta kunna wayar ta cikin sa'a yana neman ta sai gashi ya samu wata irin ajiyar zuciya ya yi tun kafin ta dauka sai ya ji wani sanyi cikin zuciyar shi, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta daga. Da sauri yace, beauty, be??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????auty, kina jina? Ta soma shassshekar kuka,sai kurum ya samu kanshi da cewa innalillahi wa inna ilaihin raji'un, wai beauty me ke faruwa ne? Cikin kuka ta ce dole mana ka ce meke faruwa? Ka min ciki sannan ga wulakancin ka har da cewa baka damu da bacin raina ba to ni ba zan iya zama ba gidanmu zan tafi. Yana son yace ki tafi din mana, amma sai zuciyar shi ta ki furta haka,sai kurum ya ji bakinshi yana cewa, haba saurare ni ki ji.in ji wa ya ce ban damu da ke ba? Da kin tausaya min. Don Allah kiyi hakuri. Sai kuma yayi shiru yana mai jin haushin kanshi, yaushe ne yake baiwa mace hakuri amma zuciyarshi murna take yi musamman da taji bilkisu tana cewa shi kenan ba zan kara kashe maka waya ba, to kana son cikin? Yana tayi maganar cikin sigar shagawaba sai da tsigar jikinshi ta tashi, sannan nashi ra'ayin shi ne ya ce mata A'a amma ya kasa fadin hakan, sai ya samu kanshi da gudun bacin ranta, don haka sai yace ya ya zan yi ni dole in so shi tunda ni na diga shi, sannan shakuwarmu dake tasa ba zan guji duk abin da ke jikinki ba, tace kana nufin yanzun ka damu dani? Yace, ke baki damu dani ba? Tace na damu mana, sosai ma. Har fa tunanin ka nake fa zama in yi da baka nan.
[8:39AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 82??}_

Ta marairaice murya,kai fa kana tunanina? Yace inna ce miki banayi ai zaki musa ko ban tunoki don komai ba ai na tunoki ko don hutu beauty,ina bukatarki kusa dani,tace kilama ka samu wata,da sauri yace haba dai ni yanzun naki ne ke kadai taji dadi sosai sannan tace nima haka,yayi dan murmushi na sani beauty tun ranar farko dana soma kwanciya dake nasan cewa nayi dacen mata,Allah yayi min baiwa,bai duba halina ba,bai hadani da %??iar uwata ba wato mazinaciya, sai ya bani mai kofa a rufe nina budeta, tace ni ko kaga bana son in tuna wannan rana,yace don me?Dan wulakancin dakayi min, yayi %??iar dariya niko abubuwa da yawa sun tsaya min a rai ranar,zan gaya miki in nazo,tace shikenan sai anjima?Yace kin kosa muyi sallama ne?Tace a%??i nace kona tsare maka aiki ne,yace shikenan zamuyi waya da dare,tace sai naji ka kenan itace ta fara kashe wayar shi ko tsayawa yayi tamkar wawa,yana son tuno tabargazar da yayi shin me ma yace mata?Kasa tunowa yayi sai ma wata annashuwa da zuciyarsa keyi,hira tayi dadi tamkar acigaba sam ya manta me yakeyi ne,ya nutse cikin tunaninta.Tina ce ta dafa kafadunsa da sauri ya dubeta tare da fatan Allah yasa beauty ce ganin Tina sai yayi tsaki, jikinta babu kwari ta sakesa ta zauna tuni itama ta soma sabawa da halinsa,sai dai Allah ya jarabceta da sonsa,shiko duk sanda yake kan begen beauty yakan manta da komai da kowa baya son a matsa masa,wanda nasa ganin shakuwa ce duk ta kawo haka.Bily kuwa yanzun hankalinta kwance ga tattalin da surukanta suke mata, labarin cikinta ya yadu ko%??ina,don ko su Mamanmu da Mansu ta sanardasu sunyi murna, sannan gashi Yrm duk ya birkice kanta,don da taba Mansu labari Mansu cewa tayi Allah sonki yakeyi Bily tace a%??i duk hirar da mukeyi bai taba cewa yana sona ba,yadai nuna kulawarsa gareni,so kam ai na riga nayi rashinsa bazan taba samun wannan kalmar ba,Mansu tace shikenan za kuma ki gane nan gaba.

Yarima da Tina an sake dinkewa,a zuciyarsa yana kara shige matane da tsawonta da tsawon gashinta suna tuno masa da beauty, ita ma ta fahimci yana da wata a cikin zuciyarsa domin in suna kwance sunan beauty kawai yake kira.sannan inya shiga wanka takan dauki wayarsa ta masa bincike tana son sanin wacece beauty din nan?Yaya take ne don ta samu matsayi mai girma gurin wannan tsadaddan yaron.Kimanin wata hudu kenan da tafiar Yrm,cikinta kuwa yana wata biyar kenan tana zaune tana cin kwakwa da tasa aka siyo mata, Sumayya ce ta shigo tana sanye da leshi ja da kuma ratsin baki yaune zuwanta na uku gidan,ta zauna tare da cewa Maman biyu,Bily tayi %??iar dariya tace,Allah amin ya biya bakinki Sumayya tace amin.nan suka soma hira duk data hakura da Yarima amma duk sanda ta gansa ko taga hotonsa sai taji ma kanta haushin rashin samunsa, yanzun ma da take zaune kallon hotonsa takeyi tare da yaba kyansa, cikin zuciyarta. Bily tace,Sumayya kina kallon wuta ne fa,yakamata ace yanzun kin cire Yarima acikin rayuwarki,sannan ki godema Allah daya baki Magaji matsayin miji,tace ai tuni na hakura anty Bily, matsalata daya yanda zan cire shi daga zuciyata,ki dinga addu%??i inji Bily,ki rike mijinki Sumayya so da yawa abinda ka kwallafa rai kansa baka samesa ba to sai kiga alkairi ne rashin samun,ni kaina ban taba tunanin zan auri kamar Yarima sa%??ina ba,babu irin takaicin dabanyi ba game da auren amma yanzun sai ina ganin alkairai da dama acikin aurenmu.don haka ki kama mijinki ki samu ladan aure,Sumayya tace to nina rasa sam sai inga sam Yarima yafi Magaji komai, Bily ta hade fuska Sumayya lallai zaki daina zuwa gidana,domin babu wanda yafi wani gurin Allah face wanda yafi tsoronsa,in dai kina so mu shirya to ki kama mijinki. Sumayya tayi %??iar dariya ganin ran Bily ya baci,tace na daina anty Bily,shima Magaji cewa yake duk ranar dana zo nan gidan wai bana bata masa rai,shiyasa yake son inzo gurinki,ina aiki da shawararki,nan dai suka cigaba da hirarsu.Wani dare Bily tana bacci sai kawai tayi mafarki wai ga Yarma an kawosa ya rasu,nan take ta farka duk tayi sharkaf da zufa,ta kalli agogo sha biyu da %??ian mintuna duk da lokaci ba daya ba ne ji tayi bazata iya komawa bacci ba har sai taji muryarsa nan take ta kira layinsa daidai lokacin ya shiga wanka,Tina ce kwance rigingine a tsakiyar gadonsa,don haka wayar tana yin ringing ta dauka ta duba(beauty)taga an rubuta,da sauri ta daga wayar tare da cewa, wacece ke?Cikin harshen turanci. Bily ta tsorata, gabanta na faduwa tace,kiba mai wayar,Tina tace sai ta fada ko ita wacece,ran Bily ya baci dama Yarima yana nan yana harkarsa da matan banza,shine yace mata ya daina?Wani tukuki taji azuciyarta nan take ta kashe wayar cikin tane ya shiga murdawa,ji take tamkar zata haihu Yarima yana fitowa daga toilet din yaga phone dinsa ahannunta,nan take tayi saurin cewa an kiraka amsar wayar yayi ba tare da yace mata kalaba,koda ya duba yaga beauty ce ta kira kuma har ta daga nan da nan sai yaji hankalinsa ya tashi,da sauri ya soma kiran layinta,tamkar kada ta daga amma sai ta kasa tana dagawa sai ta saki kuka ya rasa me zaice,sai yace kiyi hakuri beauty na kasa controlling din kaina ne yau amma insha Allah bazan sake ba,na amsa laifina kiyi min addu%??i kinji?Cikin shesshekar kuka tace, Yarima baka min adalci ba,yaya na tsare kaina a gida kaika dinga bin wasu,ina tsoron kada Ayar Allah ta sauka akaina,domin Allah yace in har kabi matar wani sai anbi taka,in %??iar wani kabi kaima za%??i bi tak,haka kuma mazinaci baya aure face sai da mazinaciya %??iar uwarsa,ban kasance mazinaciya ba. Yarima ma jikinsa yayi sanyi yasan gaskiya ta fada ina ma gata gashi ne ya rungumeta tare da lallashinta, duk da haka sai yace na sani beauty ban kyauta miki ba,amma kada kiyi fushi dani zan shiga damuwa kinji?Tayi ajiyar zuciya,sannan tace bazaka daina ba Yarima ,yace ki daina fadin haka,insha Allah zan daina nidai kimin afuwa, tace Allah zaka roka donshi kayiwa laifi,da sauri yace zan rokesa,don Allah beauty kadaki kashe min waya kinji yanayin yanda yayi maganar sai taji dadi,tace bazan kashe ba
[8:40AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 83??}_

Zuciyarta tayi sanyi domin lokutan baya Yrm yana neman matansa a gabanta, zai iya kwanciya da mace a gabanta,amma yau gashi wayarta kawai mace ta daga duk ya birkice, ta san ko har yanzun Yrm yana neman mata to ta samu wani matsayi agurinsa tunda yake boye mata baya son ta sani,bugu da kari Yarima ne harda bata hakuri,tayi mamaki domin tasan sa sarai baya daga cikin mazan da suke bawa mace hakuri,baya lallashin mace amma ita sannu a hankali ya soma yi mata abubuwan da yake ikirarin bazai iya yiwa mace ba, zata dage da rokon Allah har Allah ya shirya mata shi. Shi kuwa Tina ya tsirama idanu cike da bacin rai irin wanda bata taba gani ba,don haka ta tsorata har ta shiga bashi hakuri,cewa yayi ta fita kawai.tana fita ya fada kan gado yana rubuta ma beauty dinsa text na ban hakuri, sai daya gama sannan yayi shiru yana mamakin kansa,shine Yrm kuwa?Shine mai ja ma mata aji? Shine wanda mata suke bi bashi ne ke binsu ba? To menene yasa shi rikicewa kan beauty?Yanda ya dade dasu Vicky bai dade da Bily haka ba me yasa zuciyarsa bata shaku dasu kamar yanda ya shaku da ita ba?Me yasa ita baya jin ta gunduresa?Me yasa baya son bata mata rai ne? Domin inya bata mata rai zuciyarsa sai ta ringa yi tamkar zata fashe,bai saba da damuwa ba,don haka baya son zama cikin damuwa,inya bata mata rai sam cikin damuwa zai zauna shiyasa yake kiyayewa.

A kwana atashi babu wuya agurin Allah, yau gashi Bily an shiga watan haihuwa.duk wani abu daya kamata mai jego da jariri %??ian gata su bukata, tuni Umma ta tanadeshi, can ma Zaria su Mama suna ta shirye-shiryensu na talakawa. Yrm ko hankalinsa ya kasa kwanciya ina ma a hannunsa beauty zata haihu baya son ya rasata,wayewar garin Alhamis ta tashi da ciwon haihuwa,tuni Umma tasa akayi asibiti da ita,inda take awo wato asibitin Doctor Aisha.har zuwa yamma shiru Modibbo ne yayi mata wasu addu%??i%??i ya tofa su cikin ruwa aka kai mata daidai lokacin Yrm ya kira wayarta har ya gaji,ya kirata cikin gida,Asabe ce ta dauka ya tambayeta Bily,nan take shaida masa tana asibiti zata haihu,yace tun yaushe? Tace tun jiya,nan take ya kira Magaji,Magaji yace duk suna asibitin ance nan da awa daya zata haihu,tsaki kawai yayi nesa bata maganin kusa,amma in yaga za%??i bata masa lokaci xai bar komai duk da suna tsaka da karatu,kasancewar sun kusa gama course din ya kira wannan ya kira wancan har awa dayan ta shige ya kara minti talatin duk yaji babu bayani,nan take sai ya soma shirin zuwa gida. nasa ganin likitar bata san aikinta ba,domin in shi zai amshi haihuwa ne yana ganin cikin awa daya mace zata haihu. sai washegari sannan ya samu tasowa, bai sanar da kowa cewa yana hanya ba kuma yana cigaba da kiran waya suna sanar dashi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login