Showing 42001 words to 45000 words out of 79064 words

Chapter 15 - MEKE FARUWA BOOK COMPLETE BY HALIMA K. MASHI.doc

falon gidan Yarima tana kallon tsarin falon irin dai gidajan da take gani cikin fina-finan turawa ko mujallarsu. Yarima ya nuna mata dakinta yana kusa dana sa ne,ta shiga gado ne madaidaici sai durowoyi wordrop da dai dan sauran abubuwa,ta kintsa daki duk da dai bashi da datti,ta shiga bayin karami ne ta tsaftacesa sannan tayi wanka da alwala wata tsohuwar baturiya ta shigo tana dauke da tire,tarkace ne ita jus din kawai tasha sam bata san wannan tarkacen ba,har wayewar gari bata fito ba,tunda tana da bayi kuma tazo da dambun nama dana kifi wanda Umma tasa akayi musu don haka bata da matsala,dama bata yi zaton Yarima zai nemeta ba,kuma hakance ta faru.Da safe ta lalubi kitchen taje shima ya tsaru,madam Dora tana ta %??ian aikace-aikacenta suka gaisa,Bily ta soma hakilon neman abin karyawa,tea ta hada ta soya kwai babu ko bread taci kayanta ta koshi anan kitchen din take suna hira da madam Dora inda madam din take shaida mata cewa tana da kyau,shin ita %??iar wace kasa ce?Tace mata %??iar Nigeria ce,sai tace oh,ta manta dama Prince ya gaya mata cewa ita kanwarsa ce.Bily batayi mamaki ba tace,eh hakane.Madam Dora tace dan uwanki yana da kirki sosai,tun farkon zuwansa nan kasar nake masa aiki ni da sauran ma%??iikatan yasan darajarmu yana mana adalci.Bily ta danyi yake tace ai hakane halinsa yake,tace koya sunanki? Bilkisu inji Bilyn ta shaida mata madam ta kasa sai dai Bikis haka ko taci gaba da kiranta.Da dare tana zaune afalo tana kallon wani fim,zuciyarta ko tana tunanin cewa tunda suka zo bata ko saka Yarima cikin idanunta ba,sai gashi ya shigo kamar ta share shi,sai dai ta daure tace masa sannu da zuwa tamkar baiji ba kuma tasan yaji don haka ta share shi kusan awa daya ya fito cikin %??iar T-shart fara da 3 kwatan wando ya nufi kitchen mai hade da dinning room.Can dai tana zaune sai taji wani abu yana kara,ashe intercom ne sai taga madam Dora tazo ta bude.Wata mace ce ta shigo tana sanye da siket da iyakar cinya,sai %??iar bes kana ganinta kaga chanis,suka gaisa da madam sannan ta nufo ciki tana tambayar madam ko prince na nan?Madam tace yana dining room can ta nufa,madam tazo tayi ma Bily sallama da cewa zata gidanta don basu da nisa,Bily tace to mu kwana lafia sai dai tanayi zancen ne kawai amma zuciyarta na gurin su Yarima,shin wacece wannan?Jim kadan suka jero ita da Yarima suna %??ian hirarrakinsu,suka zube nan falon.Tamkar a fim ko cikin mafarki sai ganin Yarima tayi yana wasanni da wannan macen,sam tamkar basu san da mutum agurin ba.Kasa jurewa tayi ta mike ta shige dakinta kan gado ta fada,har yanzun bakin Yarima take gani cikin na wannan matar, tasan bata son Yarima amma dole ne tayi kishin mijinta.Kai ko ba mijinta ba ba zata so taga wani musulmi yana kusanta kansa da zina ba,bare har ya aikata.Tasha kuka daga baya tayo alwala ta soma nafila tana kaima Allah kukanta.Washegari ko da safe misalin goma tayi yo kwalliyarta cikin super riga da zani tayi kyau,tana zaune kan dining tana karyawa ya shigo cikin shirin makaranta.Madam dora ta mika masa dan kofi da plate coffee ne aciki yana sha,suna gaisawa tana masa korafin sister shi tafi son tayi girki da kanta,yace eh ko gida ma haka take.Madam tayi %??iar dariya sannan tace kuma Bikis tana da kyau,sai ya fita daga kitchen din yana cewa,chelen tana jiransa bari yaje.Can hanyar fita ya nufa,sannan ya aje kofin da plate din ya tafi abin tsoro mata gidan Yarima wasu suna shigowa wasu suna fita,kuma karka ga yanda yake wani shassha musu kamshi,abinda kullum ke bata mamaki har yau da take satinta daya agidan bai taba mata koda magana ba kuma koda ta gaishe shi baya amsawa, haka nan baya damuwa ko agabanta ne yayi yanda yake so da %??ianmatansa hakan nan in sun nemi sanin ko ita wacece agabanta zaice kanwarsa ce.
[4:35AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 54??}_

Hankalin Bily bai gama tashi ba,sai daran ranar data cika kwana goma a kasar.Ta fito zata kitchen saboda tana son tashi da azumin alhamis,me zata gani?Yarima ne da mata guda biyu tamkar zasu cinyesa,kowace tana son nuna masa karshen soyayyarta,kuma tana son burgesa har ya juyo gurinta,cikin tsananin tsoro tace, A'uzubillahi minash shaidani rajim.Suka dubeta su biyun banda Yarima wanda ya rungumo su duk da ya ganta juyawa daki tayi ko ganin hanya batayi don tashin hankali cikin sanyin jiki ta zauna tama rasa wane tunanin zatayi ne?Kodai don bata kai kanta garesa ne yake kawo su gida don ya bata mata rai?Inko haka ne ai gara ta kai kanta gurin nasa koda zai riga mata fyaden ne in dai zai daina kawo wadannan matan masu kama da bebyn roba ta sani ba sun fita kyau bane ta sani ba wai tana son Yarima bane sai dai tasan in don rashin zuwa gurin Yarima ne yake zuwa ya kawo mata,to tabbas tana da kamashon zunubi,kila ma nata yafi nasa.Tabbas Yarima baiyi kuskure ba daya ce ta nemi maganin ciwon zuciya dana hawan jin,har gari ya waye tana tufkawa tana warwarewa.

Yaya batun su Mamanmu? Duk wanda ya auri boka da %??ian tsibbu lallai yana cikin dimuwa ba kuma zai gane ba,har sai ranar da karya ta kare,ga dai su Ladiyo nan anata fama yanzun ma da suke zaune gaba dayansu acikin dakin Karima suna tattaunawa ne akan duk malaman da suka je gurinsu,Salame tace abin kamar hadin baki malaman nan sunce mana inma an daura auren kwata-kwata ta dade tayi sati daya agidan mijin zai koro ta amma gashi yau mun shiga sati na uku.Ladiyo ta gyara zama ga kuma tsohon ciki tace yanzun ko bacci bana iyawa tunda akayi auren nan kullum ina raba idanu ne inga ta shigo gidan nan wutsiya zage,bani da buri sai na ganin bayan Bily.Karima tace kedai bari Ladiyo wallahi baki kaini ba,Ladiyo tace um um daina cewa ban kaiki ba,ni nan da kika ganni ko wannan cikin na jikina bana tunanin ranar haihuwarsa kamar yanda nake tunanin auren nan na Bily gashi kuma shiru. Salame tace mu koma mu sanar dasu aiki baiyi ba.Ni damuwata ma daya yanda mai adashen nan ke ta min sintiri naci na kasa zubi kudin da sune na bada muka kai gun malaman nan yaya tazo tana neman abin dauka, nace indai bani zaki dauka ba,ko yara ga sunan kwancar bani da wani abu dazan iya baki gaki dai ga dakin,in kinga abin dauka to dauki.Duk suka sa dariya,Ladiyo tace nima gado ne kurum yanzu ya rage min,Karima tace wa ma zai sayi wannan gadon naki,ko%??ina kudin cizo yayi kashi.Ladiyo tace eh,in zan saida ai dama wanke sa zanyi. Salame tace ai ko yaci klin din dari biyu dukkansu suka sa dariya,tace mu bar dariya mu fuskanci matsalarmu fa?Haka ko sukayi,washegarin ranar suka shiga mota suka nausa.kusan duk bokayan sunce musu kada su damu,aikin zaici ahankali. Shiko asalin bokan nasu cewa yayi yana zaton ma fa anyi sakin kila uwar yarinyar taki yarda su sani ne,sannan takai yarinyar gurin %??ian uwanta.Ya kara musu da cewa haba ku sai kace ba mata ba?Ku kanku ma fa sharri ne mai zaman kansa cikin irin siyasarku ta mata da kissa ai kwaji koda gurin mijinku ne.Kai ita kanta yanayin amsar da zata baku zaku iya ganewa, suka ce hakane.Ladiyo tace malam sai dai fa maigidanmu da kake cewa zamuji gurinsa wallahi yanzun ya juya mana baya tunda yarinyar ta samu dan sarauta shikenan duk ya birkice mana.Malam yace a%??i kuce akwai sabon aiki kenan,to kuna da kudi ko?Suka ce zamu nemo, amma don Allah ai mana aiki mai kyau,yace musu don wannan kada ku damu,an gama kuzo dai da dubu takwas,sannan da kaji biyu.Suka ce to sun gode,sannan suka muke suka dauki hanyar gida.Allah kasa mufi karfin zuciyarmu, amin. Suna shigowa gidan sun samu Mamanmu zaune tana yiwa auta tsifar kai,nan suka kyafta ma juna ido alamar su bigi cikinta,don haka sai suka hada baki gurin yin sallama.Mama ta dubesu ta amsa,sannunku da dawowa suka ce yauwa. Karima tace munje barka ne matar wan Salame,cike da fara%??i Mama tace,Allah sarki to Allah ya raya,ai da kun gaya min da munje. Salame tace umh ni ai gani nayi na gaya musu bikin Bily sunki zuwa, shiyasa nace bazan gaya miki ba tunda abinba tsoro bane,su basa son zuwa
[4:36AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 55??}_

Amma suna son aje musu.Mama tace,kai sai kace bin bashi?Ai lada ne in naje din,to Allah ya raya suka ce amin.Ladiyo tace,auta anata shan tsifa ne?Mama tace eh wallahi kin ganta nan kitson tunna bikin maigado taki tsefe sa,taje tasa anmata kitso yangu-yangu kuma sai da nace kar tayo kanana,amma da yake tana da kunnan kashi sai da tasa aka mata shi.Ladiyo tace ai duk haka suke,itama uwata gashi nan dama ita ba gashi ba yana nan kan duk yayi dugu-dugu ni dai ai bani da lokacin tsifa.Mama tace nifa tunda taki tsefewa ai tasan tawa tsifar sai na fece kai tas ta mun kuka in nade ta.Salame tace da kina can gidan amarya ai da kin huta.Asma%??i tace ba Mama ce tace adawo dani ba.Karima tace,ina ruwan amare,ana can dai.Duk suka kalli Mama suga yaya fuskartata zata nuna?Mama tace,um suna can,sun ma tafi ni wacce kasa ce inda mijin ke karatun likita.Gaba dayansu suka ce me?Cikin Ladiyo ya shiga juyawa,Mama ta kallesu saboda yanda taji sun hada baki,Karima ta wayance tace,a lallai Allah ya bada zaman lafiya. Asma%??i tace Mamanmu sunan kasar wai Malesia inji anty Mansu.Ai tuni suka sulale kowacce ta shige dakinta zuciyarta tana zogi tare da son tuno MEKE FARUWA ne?Abubuwan suke zo musu ahaka?

Sumayya taja tsaki sannan ta kashe wayarta,anty Salma ta dubeta ke kuma dawa kike tsaki? Sumayya tace,wannan Magajin Malam din mana ya dame ni wai ni yake so,ni ko gaskiya be min ba.Anty Salma ta harareta,sannan tace to menene aibun Magaji?Momy %??iar gidan anty Salma itace ta uku tana da kannai da kuma yayye guda biyu maza,tace Mama ita fa Sumayya wai uncle Yarima take so,lokacin bikinsa duk inda mukaje sai tayi kuka.Anty Salma tace ai da kina sonsa kika yi shiru?Sumayya tace, wallahi Ummanmu ce ta hanani magana.anty Salma tace,to ba gara ke ba,da wannan %??iar matsiyatan. Momy tace,ni ko ina sonta Mama tana da kyau.Anty Salma tace, ja can sakarya tayi ta kyannata mana,sannan ta dubi Sumayya tace,karki damu bari ya gama karatu ya dawo sai mun hadaku. Ai dama itama wannan ba wani sonta yakeyi ba hadinsu mai martaba ne da Modibbo. Murna Sumayya ta hauyi yayinda Momy ta shiga turo baki itama tsarar Sumayya ce Momyn.Tace to baga Magaji yana sonta ba,Sumayya tace to ni bana sonsa Momy ta taba baki sannan ta tashi ta basu guri.Umma ta kira lambobin gidan nasu Yarima na can Malesia ta hanyar land line har sau uku ana ukunne madam dora ce tazo tana buga ma Bily kofa domin Yarima ya fita,Bily taso taki daukar wayar don ita tun fitowar da tayi daren jiya datayi mugun gani koda ta daga wayar jin muryar Umman Yarima yasa tajin wani sanyi,tace sannu Umma ina yini? Suka gaisa tace ina baban nawa?Bily tace ya tafi makaranta,Umma tace ina fata dai kuna nan lafiya babu wata matsala ko?Ba komai Umma cewar Bily,to kiyi ta hakuri dai kinji ko?Tace to Umma. Umma tace yauwa %??iata ki kwantar da hankalinki, wata rana sai labari,nasan Yarima sarai ki ta hakuri tace to Umma,to na gaisheku in yazo kice masa na kira ina gaidasa, tace to mun gode,zan gaya masa.Ta lura yana shigowa ne karfe hudu, don haka kafin hudu ta shiga kitchen tayi %??ian girke-girkensu na hausawa,sannan tayi wanka,kwalliya tayi sosai irin wadda ake mata, sannan ta saka wani leshi mara nauyi kalar sararin samaniya,riga ne da siket tayi kyau ta saka gwala-gwalai kunne da wuya,da kuma yatsunta,tayi kyau sosai.Yau sai biyar ya shigo shida wani abokinsa dan Africa ne mai suna Saddik,tunda tazo sai yau ta gansa da musulmi,ta fito tace masa sannu da zuwa.Ya kalleta wani takaici ya cikasa aransa yace,har abada wannan ba zata waye ba,yace ai ke yafi dacewa ayi miki sannu, ko don wadannan kayan da kika lafta wa jikinki.Taji zafin maganar, amma sai ta daure tace Umma tana gaisheka, daxun tayi waya hanyar dakinsa yake tafiya amma sai ya dan tsaya ba tare da ya juyo ba yace me tace? Bily tace,ta gaishe mune kawai.Ya shige daki, ta dubi bakon sannu da zuwa ta masa cikin harshen turanci,sai taji ya amsa da hausa duk da hausar tasa batayi gargar ba,suka gaisa ta nufi daki.Bako Saddik ya bita da kallo,sanda tare da shiga daki gaban madubi ta tsaya bata ga aibun kwalliyarta ba,amma har yana wani cewa ta lafta ma jikinta kaya
[4:39AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 56??}_

Taja tsaki ai dama ita ba wai tana son sai ta burgesa bane kawai tana son ceto shine daga halakar daya shiga,amma akasan zuciyarta sai tana jin kamar ta canza shiga, amma sai wata zuciyar ta kwabe ta da cewa kinma damu sai kin burgesa kenan,don haka sai ta fasa ta fita zuwa kitchen dai dai lokacin ne taji bakon yana cewa,gaske kanwarka ce?Yarima yace,um hum! Bakon yace don Allah ina sonta she is very beautiful.Yarima ya mika masa littafin hannunsa tare da cewa amsa Saddik,kula min da littafina kasan ba%??i samunsa anan nima sai a England aka samo min duk da cewa muna dasu a library amma ba%??i son a fito dashi.Saddik yace, kada ka damu,yanzu muyi maganar sister dinka,I love her.Ga mamakin Bily, sai taji yace jeka gaya mata mana ni kazo ka dame ni kana sonta. Bily Sai data kusan faduwa don mamaki,shi wanan wato ko kishinta ma bayayi? Koda baya sonta ai ya dace yayi kishinta amatsayinsa na mijinta. Shin me hakan yake nufi? Guri ta samu acikin kitchen din ta zauna ta zabga tagumi,mijinta ne ke turo mata wani daya ce yana sonta,shin ko dai gaske ne Yarima bai san addini ba?Haka ta mike ta nufi daki bata ko ganin hanya sosai,dolenta ne tayi duk yanda zata ceto Yarima,amma duk da haka wata zuciyar tana ce mata Yarima ya wuce da tunaninta,amma sai tana karfafa ma kanta gwiwa da cewa,ai mata yake so kuma su yake nema,haka nan itama mace ce duk abinda wadancan matan suke dashi itama tana dashi,shin me zai hana itama ta bishi yanda sauran ke binsa?Ai itace ma ya dace ta bishi tunda mijinta ne,zata gwada irin nata salon,Allah yasa adace. Ta sani duk inda Yarima zaije baya wuce sha biyu.Wata rana ma baya kaiwa zaka ga ya shigo ko shi kadai ko shida %??ianmatansa,ko sai in yazo sannan su biyo shi,yayi ta ja musu aji.Don haka kafin ya shigo tayi wanka ta gyara jikinta da turaruka,don turare yana motsa sha%??iwa musamman irin masu sanyin kamshin nan,rigar bacci tasa kalar pink mai yala-yala,wato mai bin jiki tana da gidan nono kuma shi les ne mai shara-shara, ta gyara gashinta ta daure da ribon pink,ta kalli kanta a madubi tayi kyau ta zauna jiran Yarima Sha biyu saura ya shigo anci sa%??i shi kadai ne ya shigo,sai daya jima da shiga dakinsa sannan ta nufi dakin tana turawa kofar ta bude,ta shiga da sallama baya dakin amma da alamar yana wanka ne, ta kalli ko ina a dakin,lallai Yarima bashi da matsalar komai arayuwarsa,shiyasa yake yin yanda yaso.Zama tayi kan durowar gefen gadon tana cike da fargabar yanda zasu kwashe,kusan mintina goma sannan ya shigo dakin,waton ya fito daga bayin.Ya kalleta fuskarsa da alamar tambaya.Bily dai tana kallonsa bata ce kala ba,shima yaci gaba da harkokinsa.Shafa wannan matso wannan sa a hanci,sa a hammata, mamaki ma yake bata sai kace karuwan namiji,rigar bacci mai wando ya saka,sannan ya nufi wani dan fridge kwalbar jus ya ciro ya dauki kofi asaman fridge ya zauna gefen gado yana tsiyaya,ta gane nufinsa waton kala bazai ce mata ba,tasan zai iya abinda yafi haka ma,don haka sai tace,ina yini?Sai daya kurbi jus din sannan yace menene dalilin shigo min daki ba tare da izinina ba?Ta mike ta nufo shi yanda take tafiyar duk komai na jikinta girgiza yakeyi,kusa dashi ta duka,nazo ne in sauke nauyin da Allah ya dora min a matsayina na matarka.Ya dubi fuskarta idanunsa ya sauke akan lebunanta %??ian yala-yala masu laushi jajaye tamkar ta saka janbaki,sannan ya kauda kai wane irin nauyi?Tayi jim don nauyin kalmar da zata fada.Hakkinka dake kaina.Ya sake kallon saitin kirjinta,sannan ya kauda kai yace, bana bukata,in kina nufin bani kanki ne,wancan lokacin ma nayi ne domin in banbance miki tsakanin yaro da babba,wato aikin da namiji zai iya da kuma wanda mace ba zata iya ba koda %??iar shekara sittin ce shi kuma dan talatin duk da kince kashina baiyi kwari ba,nasan zaki shaida cewa ni ba raggo bane,don haka yanzun kama kanki bana bukatarki ko da zan ganki tsirara. Kash! Mu hadu a littafi na uku (3) don jin yadda zata kasance,shin yanayin hakurin ko ko,ita tana yin zuciya koko batayi.
[4:42AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_ MEKE FARUWA 57??}_

Jikinta yayi sanyi, zuciyarta ta
baci,duk da shakkarsa da takeji gami kuma da
yanda yake cika mata idanu,sai data ce kai ma
kasan baya ga aure mai hada namiji da mace
baka isa in zo ince maka gani ba,ka sani nima
bada son raina bane,don kawai na fita daga
hakkinka ne,kuma Allah ya sani na fita.Ta mike
tayi waje rai bace,da kallo ya bita tun daga sama
har kasa yake kallonta,har ta fita.Ya runtse
idanunsa yana kallon yanda jikinta yake
motsi,wata sha%??iwarta ce ta mugun tsirga
masa,ta baya ya fada kan gadon hannu ya kai ya
jawo filo ya saka akirjinsa ya matse gam,bakinsa
yana kwadayin lebunanta yana son jin kalar miyanta,nan zuciyarsa ta shiga tuno masa ni%??imarta duk da ya kusance ta ne cikin garari ba tare da wasu wasanni ba,amma abin ya tsaya masa a rai .Ya kuma shakar kamshin data tafi ta bar masa a dakin,ya sani bawai yana sonta bane
amma sha%??iwarta tun ranar daya soma ganinta
ta tsirga masa,ba kamar yau da yaga siffofinta
a fili,yace kai she is a beauty.Yayi tsaki tare da
cewa,ni gaskiya banyi ba,ta kawo kanta amma na tsaya, yayi shiru yana son

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login