Showing 36001 words to 39000 words out of 79064 words

Chapter 13 - MEKE FARUWA BOOK COMPLETE BY HALIMA K. MASHI.doc

kuma hado da sarkin zazzau kinyi kokari har zuwacin nasararki na aurena.Sannan ina miki murnar samun miji kamar ni,hakika kinyi sa%??ir samun wanda mata ke so,kuma mai burin zama da mace daya rak karin sa%??irki kuwa?Itace gidan sarauta ba%??i saki mutu ka raba matsawar ba kin zo da wata alfasha bayyyananniya ba Sai shawara da farko nazo in ba wadda za%??i aura min shawara ne akan kada ta yarda ta shigo hurumina, wato ta bijire ma aurena kafin zuwan ranar auren. Amma yanzun ke ya juyo ya nunata,bazan baki shawarar karki aureni ba,domin kece kika nema,kuma nima naso hakan don in banbance miki tsakanin aya da tsakuwa,sannan shawara sai kinyi hakuri da zama da karamin yaro kuma bugu da kari yaron jahili da kakkausar murya ya fada.Magaji ya taso yana cewa a%??i Yarima what are you thinking? Yarima ya daga masa hannu don%??i say anything baka san komai ba akan wannan yarinyar.Bily tace,kaini daina ce min yarinya domin ba sa%??irka bace ni,sannan ka daina babatun na shiga nafita don na sameka wallahi kayi kuskure,yanda kake jin an matsa maka haka ma nima har ma gara kai,nida aka tuge ni kan aikina sannan duk zaman da kake bukata na shirya sai ka sani ni ina da ilmi kuma bana fata nabar tafarkin da musulunci ya shinfida min,don haka zan bika in Allah ya sa kai ne mijin nawa(hawaye ya soma zubo mata)sai dai na cutu don ba irin ka naso in aura ba.Ta juya zata tafi Yarima ya fizgota,kinsan zaman da zamuyi?Ya zuba mata manyan idanunsa cikin nata idanun masu tsananin haske da matsakaicin girma,yace ina tambayarki?Tace sai ka fada.Mace mai shekaru da ilimi mijinta karamin yaro jahili,kuma mai tsattsauran ra%??iyi sannan miskili in kin shirya you are welcome ya saketa da karfi ya fita. Magaji ya taso kusa da ita yace kiyi hakuri insha Allah komai zaiyi daidai, murmushin bakin ciki tayi ga hawaye yana zuba ita kam yaya zatayi?Daki ta shiga ta hau gado tana kuka zuciyarta kuwa tana tambayarta sai yaushe zatayi farin ciki?A baki ta furto babu rana,don yanzun zaka shiga sabon babin bakin ciki ne gidan Yarima gashi babu saki MEKE FARUWA dani ne? Lokaci baya jira sai dai ajira sa inji %??ian magana,wannan haka ne domin yanzun dai saura sati daya bikin Yarima da Bily,gefensu Mamanmu babu zama,duk da ance ba%??i son azo da komai Mamanmu ta dage lallai abada koda daki daya ne don azuba ma maigado kayanta,Mansu kuwa dubu dari ta zube ma Mama tana bada hakuri babu yawa,ban dana Faruk,su Sakina kowa yayi kokari sai dai su Gwaggo Ladiyo su hana kansu sukuni,sunata faman shige-shige %??ian tsibbu suma sunyi nasu shirin.Gefen ango kuwa sam ba wanda ya zaci baya so,nan ya sake aka shiga shirya yanda biki zai kasance dangi kowa ya kosa.%??ian kawo lefe gidan Umman Mansu aka saukesu,suna dauke da akwati doxin biyu tare da key din henesy su anty Salma sun raina ma gidan da aka nemo ma Modibbo aure duk da tsarin gidansu Umma Mansu ina to ace gidansu Bilyn ne kila ko zama bazasuyi ba.Sai dai sun dan yaba da tarbar da aka musu,na kayan lashe-lashe da kuma ciye-ciye, sannan tukuicin dubu dari sun ansa a raine don bai wuce kudin shan sweet din yaransu ba,haka suka tafi suna ta surutu.Koda suka je suka gayama Umma,cewa tayi bata son surutu,in ma ba%??i basu tukuicin ba ai ba addini bane.Ana saura kwana uku biki aka dauko Bily,wadda tasha gyara gurin tsohuwar da jakadiya ta tura,ga kuma Mansun ta tazo mata da tata tsarabar,sannan ga mai lalle tare da dilke.Nan fa Bily tayi kyau kamar aljana.Suna sa kai dakin Mamanmu dangin Mama suka kama fadin tubarkalla masha Allah, Allah yanda mutane suke ta cewa kai Bily kece kuwa?Kinyi kyau kaza- kaza,sai kawai ta boye gidansu Mansu,walima kawai suka shirya inda aka sha wa%??izi da kuma nasihohi,bayan daurin aure kenan.
[4:07AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 45??}_


Amarya hijabi har kasa da nikabi tasa ta rufe fuskarta don tunda ta fito daga inda aka killaceta sai ta ringa ganin haske yana haske mata idanu,don ta jima bata ga rana ba.Motocin daukar amarya sun kai ishirin zuwa gidan sarkin zazzau,sauran dangi sun wuce Bauchi a mota amarya ko jirgi zasu biyo su Ladiyo dasu Karime suma sun taho don su danyi %??ian binne-binne nan da bokayensu suka basu. Haka nan yanda Mansu ta tubure sai da Faruk yayi ma Bily kaya haka Bily itama ta tubure sai an raba musu nata.Lallabata akayi Mansu ta diba,don Umma cewa tayi baza%??i raba ba tunda tsadar kayan ma ba daya bane, tunda babu kasa da aura duk cikin kayan Mamanmu ma cewa tayi sai sun raba Mansu taki.Amarya ta isa gidan iyayan mijinta daf da magariba nan zasu fara zama agefensa tunda Malesia zasu wuce,gefen yasha gyara da kayan alatu,sannan ga dakin da aka basu suma su Mama sunyi kokari,sannan ga kuma gara shake da mota,duk fa hidimar nan malam Mamman ba ko taronsa,sai dai fa diyarsa ta auri dan sarkin Bauchi.Dinner daya da daya aka shirya a kayataccen Hotel kusan mutum shida ne akan amarya suna shiryata.Ni kaina muna hada ido nace subhanallahi,to ina ga ango.Yana zaune cikin shiga ta alfarma,wata alkyabba ce karshen tsada cikin motarsa limousine Ya kashingida yana kallon TV kuyangi da sauran dangi suka rakota har gurin motar suka bude mata ta shiga kamshin turarenta ne wanda tun tsawon zamanta agidan da aka killaceta tsohuwar take turareta dashi ya bugesa ga kuma na musamman domin shi Mansu tayi mata wanka dashi,ta shigo ta zauna tayi sallama,ba tare da ya kalleta ba ya amsa,sai dai yana kallonta da wutsiyar manyan idanunsa kyan da tayi tare da kamshin turarukan jikinta sun rikita sa kuma take sha%??iwarta daya jima yanayi ta motsa masa,sai dai ya dake ya kuma shareta, amma zuciyarsa tana ta fadin she is beautiful.Ita ko Bily kasa kurum take kallo tare da yin wasa da yatsunta, xuciyarta kuwa tana kambama kyan halitta irinta Yarima. Guri yayi guri,dama ango da amarya ake jira shigowarsu cikin hall din zuka tana jama%??i sun tsumu %??iayan Gwamnonin da %??iayan sarakuna sun jinjina ma zaban Yarima.Kai wani dan sarki daya kasa daurewa sai daya iska Yarima har mazauninsa ya bashi hannu,bayan sun gaisa sannan yace Prince Al%??imin ka dauki ta karshe acikin mata,Yarima yayi dan yake tare da godiya. Mansu ta dafa Bily sannan ta rusuno bayanta tace aminiyata kunyi kyau da yawa kun dace sosai tsaki Bily tayi tare da cewa ni duk kunya ma ta isheni, don abin kunya ne in auri dan wannan yaron.Mansu tace yanzun dai ya zama miji sai adaina ce masa yaro,Bily ta dan dubesa %??ian jarida suna ta hira dashi tace bazan daina kiransa yaro ba,tunda ba girmata yayi ba.Dinner tayi kyau,gurin ya tara duk wani mai ji da kansa,%??? yanmata da yawa sun kira Bily da mai tsananin sa%??i,domin cewarsu samun Yarima sai an tona.Bily takai kunnanta lokacin da wani dan jarida yake tana bayan Yarima wane irin farin ciki yake ciki yau kasancewar yayi aure da abar sonsa kuma mai tsananin kyau budar bakin Yarima sai cewa yayi shi wannan rana itace rana mafi muni cikin ranakun da yayi aduniya saboda me?Inji dan jarida cikin mamaki nan take Magaji ya katse dan jaridan da cewa tsabar murna ce tasasa baya iya saita maganarsa please ka tafi sannan na roke ka daka goge wannan bayanin da yayi.Bily bata ji komai ba don yace haka, dama tana tsammanin zance abinda yafi haka ma.Magaji da Faruk sunyi kokarin ganin Yarima baiyi wata tabargaza gaban jama'a ba gurin yanka cake nan ne suka danyi fama dashi yace bazai tashi zuwa ko ina ba don haka suka dauko cake din zuwa gabansa tare da baiwa jama%??i uzurin cewa kunsan Yarima namu dan gata ne sannan shaukin mulki yana dibansa don haka bazai iya zuwa gaban cake ba sai dai mu kawo masa,haka an sha fama kafin yayanka sannan yasa mata abaki itama bayan Mansu tasha fama gurin lallashinta dan haka hoton ba da cake din nasu duk ransu bace yake,sai dai haka ni bai hanasu yin kyauba,haka dangi sukayi ta rawa suna zuwa suna zuba ma ango da amarya kudi, kasancewa duk sunki rawa Bily kam abin bai birgeta ba,ta tuna %??ian watannin baya kafin ta gamu da Yarima bata da wani buri daya wuce ta samu miji,burinta shine aure farin cikinta taga wanda zai ce wance ina sonki,amma hakan ya gagara,har zuwa wannan lokacin da take aure.Ta dubi Yarima cikin zuciyarta tace,gadai mijin kuma mijin nunawa tsara,ta kalli dinbin mutanen dake gurin wadanda ada sai dai ta gansu cikin TV ko jarida ta dubi kayan jikinta zuwa gwala-gwalan hannunta duk wadannan abubuwan sun kasa sakata cikin farin ciki saboda rasa wannan kalmar ta so.To wai ita MEKE FARUWA da ita ne maza basa sonta?Sai ko ga hawaye shar daidai sanda wani dan jarida yake cewa,wane irin farin ciki kike ciki yau ranar aurenki?Ta bude baki zata ce tana bakin ciki ne ita aranar yau sai muryarta ta hau rawa,nan da nan Mansu tace da %??ian jaridan bazata iya cewa komai ba farin ciki yayi mata yawa gashi har kuka ma takeyi.Bily tanaji bata tanka ba,ita damuwarta tasha mata kai,haka akayi ta shagali dangi suna ta bada kyautukan zannuwa, agoguna,masu dauke da hotunansu,wani iya shege da Magaji yayi shine,duk maroki ko mawaki daya zo gabansu Yarima yayi roko sai Magaji yace, yarima ya baka kujerar makka,ko mota kamar sau hudu ana haka,Yarima yana jinsa da yaga Magaji watan bai san zuri ba,kuma kyautar gidan sarauta babu karya ta bada,don haka sai yace Magaji ya isheka haka, inko ba haka ba duk wanda ka sake yiwa kyauta kaine zaka basa,don ni ban dauki yau ranar farin ciki bare har nayi wata kyauta,dariya kawai Magaji yayi yasan dai ya kunna Yarima. Bayan tashi daga gurin dinner haka akayi jerin gwano zuwa gidan mai martaba inda su Bily suka shige gefensu,sai da tayi wanka sannan tazo tayi alwala ta samu su Sakina duk sun kwanta da sauran jama%??i.Bily ce kawai take sallah,nan itama tayi sallarta sannan suka soma hira gurin dinner.Bily dai korafi takeyi akan yanda Mansu ta ringa bada ita gurin %??ian jarida ita ko Mansu zakewa tayi tana ta fadin yanda sukayi yau cewarta bata taba ganin mata da miji da suka dace kamar ita da Yarima ba.
[4:09AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 46 ??}_

Sannan ta koma yiwa Bily hirar kayan gyaran jiki,Bily tace don Allah ki kyale ni kina yi kamar baki san wanda na aura ba,wannan yaron ne zan tsaya ina damun kaina saboda shi?Ta dan ja tsaki kinsan Allah koda ina son shine wallahi bazan bata kudina ba gurin wani gyara jiki saboda me ma ya sani game da auren?Ballantana ma ni bai min ba,ba sonsa nake ba shima haka. Mansu tayi dariya har da kwanciya, sannan tace,Bily baki san matasan yanzun ba kenan?Bily ta kwanta tana fadin barni da zancan nan kinji in huta,bacci nakeji. Mansu tace gobe ai ba kya yi shi ba,in mun watse, Bily tace sai ki hanani.Mansu ta kwanta tana cewa,in ban hanaki ba ai Yarima ya hanaki. Cike da tsokana tayi maganar,irinta kawaye. Banza Bily tayi mata taci gaba da addu%??i%??inta na bacci,ta rumtse idanunta duk da cewa bata da tabbacin cewa baccin zai dauketa ko a%??i.Washegari sabon biki ne ya tashi gidan sarki dama su Umman Mansu suna can gefen Umman Yarima tare da su Gwaggo Ladiyo duk dai iyayen suna can matasan ne kurum anan gun amarya.Misalin sha biyu %??ian yiwa amarya kwalliya suka shigo,sai da sukayi mata turare kusan kala goma daga ita sai vest da skirt,hatta gashin kanta yasha turare iri-iri,sannan ta saka wani leshi marar nauyi aka nade ta da laffaya,zobuna sarkar kafa,%??ian kunne,abin hannu. Subhanallah,haka mutane suketa fadi aka fito da ita zuwa falo ana jiran Yarima zasu je gurin sarki yasa musu albarka,sannan azo ayi budar kai.Shi ko gogan yana can ana fama dashi, jakadiya da Magaji sun tasasa da lallashi suka koma masifa.Magaji yayi zuciya ya fita,jakadiya cewa tayi bari taje ta sanar da Umman shi har takai bakin kofa yace jakadiya ta juyo yace yanzun me kike son inyi?Ta dawo cike da fara%??i da kirari,sannan tace ranka ya dade da guda tamkar da dubu wanka zaka soma yi kayi shiga ta alfarma,gimbiya fa na jiranka a falo,na gode ranka ya dade sai ka fito.Ya bita da kallo har ta fita,sannan yaja tsaki ya shige toilet kusan awa biyu ya dauka sannan ya fito yana shigowa falo kuyangi suka mike jakadiya ta tasasu lallai ga zara ga wata, Suka ratsa jama%??i har fada inda sarki yake zaune tare da fadawa da kuma manyan baki %??ian taya sarki murna.Sun zube sunyi gaisuwa suna zaune gaban sarki yayi musu addu%??i sannan yasa musu albarka ya umarci waziri da a miko masa alkyabba ta musamman ce ya tanade ta don yau,nan take yasa ma Bily.Wayaga gimbiya Bily,sarki da kansa yasan dan nasa yayi dace,nan malamai sukayi addu%??i%??i,sannan marokan sarki suka dora busa da kirari,su Bily suka fito mata suka dau guda ga kuyangi cikin ado suna biye dasu,sai gurin da aka gyara don budar kai,wani katon fili ne nan cikin gidan yasha decoration nan akayi budan kai.Ango da amarya sun samu kudi babu ma kamar ango inda matan sarakai kawan Ummansa da matan Gwamnoni zuwa masu fada aji,banda kyautar kuyangi daya samu daga sakkwato.Ana gamawa dama kamar yana kan kaya ne,suka nufi masallaci da suka dawo wanka yayi sannan ya saci jiki ya fita,wani guest house ya nufa ya kama daki yayi kwanciyarsa da nufin hutu.Su ko can gidan anci gaba da %??ian bukukuwa,yayinda wasu bakin suka soma nade kayansu don tafiya gida.Ciki har da dangin Bily wadda hakan yayi mugun daga hankalita, musamman da taga Mansu ma tana hada kaya,ta zuba ma Mansu idanu tace,Mansu me kike nufi ne? Tace Gombe zanbi mijina,Bily tace ki daina min wannan magana,gaskiya bazaki tafi ba,kuna nufin ni kadai za%??i bari bansan kowa anan ba?Mansu tana dariya tace,ba auren kenan ba?Bily tace amma ke ai na zauna miki. Mansu tace a ina? Tuna dai haka kuka kai ni Gombe kuka baroni,nan take Bily ta soma kuka tun Mansu tana tsokanarta har tazo tana bata magana,itama tana hawaye yanda Bily take kuka duk su Umma Mansu babu wanda baiyi hawaye ba,amma suka ki su kara kwana.Amma Faruk yace kafin su koma Kaduna zasu biyo su Sakina da Maryam suna kuka suka tafi,amma an bar mata auta kafin hutunta na makaranta ya kare,duk daba azo mata da kaya ba tunda ba%??i shirya za%??i barta tun daga gida ba,Umman Mansu ce tace abarta kafin Magariba duk an gama tafiya sai Bily kwance kan gadonta tana ta kuka,auta ko tana falo tana ta kallonta.
[4:12AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 47??}_

Can dai taga bata da nayi sai hakuri,don haka ta tashi ta shiga toilet ta dauro alwala tazo ta tada sallah,Asma%??i itama tazo ta tada tana zaune har isha%??i tayi,tana idar da sallah kuyangi suka shigo suna shaida mata batun cin abinci,tace ita kam alhamdulillah,sai dai ga kanwarta nan su bata. Yinin ranar ma ita banda ruwa babu abinda tasha, balle abinci,haka nan suna kwance ita da Asma%??i bacci ma yayi gaba da ita ko kayan jikinta bata cire ba,duk ta gaji take jin jikinta tana cikin baccin taji muryar jakadiya tana cewa,ranki ya dade har kin soma bacci ne?Bily ta tashi zaune,jakadiya tace wanka zakiyi yanzun.Bily kamar tace ki barni inyi baccina,amma sai ta daure tace to ta mike taje tayo wanka sannan tazo zata sa kayan bacci kenan sai ga jakadiya,tare da wasu kuyangin suna dauke da wasu kaya cikin kwalaye,nan take suka shiga yi mata kwalliya, shafa wannan goga wancan fesa wannan gashi kai ma yasha turare yafi kala goma.Jakadiya tana gefe sai data bada izinin su bari sannan ta mika mata wani kwali,kisa wannan ina dawowa.Ba musu ta amsa,jakadiya ta tasa su suka fita,Bily ta bude kwalin nan ko ta dago wata shegiyar rigar bacci bata taba ganin irinsu ba,koda yake yaushe ma ta shigo garin?Cewarta nan take ta saka har da takalmi,jim kadan jakadiya tayi sallama tare da neman izini.Bily tace shigo bayan ta shigo tace ranki ya dade kinyi kyau yanzun sai ki zo muje gurin Yarima.Ita kuma %??iar uwar taki zanje da ita can gurin Umma mai babban daki.Kamar ta gaddame amma sai ta tuna da maganarsu Umman Mansu,inda suke cewa,ki zama mai biyayya musamman kasancewarki acikin gidan sarauta su ba%??i gaddama don gidan ilmi ne da tarbiya,don haka sai ta mike tabi jakadiya.Suka fita ta cikin falonta suka shiga wata kofa nan ma wani dan madaidaicin falone sannan suka kara shiga kofa,nan ma karamin gurin hutawane ko yin karatu,sai kuma ga kafar bene tayi sama.Bily dai tana biye da jakadiya suka hau sama nan ko wani hamshakin tafkeken falo ne mai tsari.Jakadiya tayi sallama shiru ta nufi wata kofa daga cikin kofofi ukun dake falon ta kwankwasa. jim kadan aka bude,Yarima yana sanye da jallabiya,ya dubi jakadiya kafin yayi magana tace,ran Yarima ya dade,amarya na kawo maka.Ta juyo ta yafito Bily da hannu,Bily tazo ta tsaya kusa da jakadiya. Jakadiya ta nuna mata dakin tare da cewa,mu kwana lafiya.Yarima dake bakin kofar ya hana hanya tare da cewa,haba jakadiya, kuna tirsasani da yawa,shin bata da daki ne?Tana dashi ranka ya dade,amma addini yana tafiya daidai da al%??idar gidan nan,ga al%??idar wannan masarautar gimbiya Bily bata da gurin kwana sai dakinka,kuma saba ma hakan laifine babba.Jakadiya ta dubesa in kaji zafi Allah ya huci zuciyarka,mu kwana lafiya,ta fita.Yarima kam falo ya fito,Bily ta shige ciki.Subhanallahi!!Ta furta afili tare da hangame baki tana kallon dakin,afili tace jama%??i kamar baza%??i mutu ba? Gado ne gashi nan kamar na zinare,in ma ba gold bane to kalar ce asaman gadon.Akwai wasu fitilu kusan guda sha biyu kaloli daban-daban,gadon kawai suke haskawa sannan ga wani net mai ruwan madara ya rufe gadon ruf.Ta tsakiyar net din fitilun suke,ta kai duba kan gadon yana liliye da shimfidu na alfarma ga fuloli da yawa kanana da kuma manya.Kujera daya ce adakin katuwa,sai madubi suk seti suke da gadon,kafet zuwa labule masu kalar madara ne kila ma tare suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login