Showing 39001 words to 42000 words out of 79064 words

Chapter 14 - Meke Faruwa Book Compelet

zo har da net din.Tana ciki tana wannan juyayin shi ko Yarima yana falo shaidan na tuno masa da sa%??in%??iar su shi da Bily,kalmar jahilci data tofa masa da kuma kiransa yaro sune suka dinga yawo cikin kansa nan take zuciyarsa ta shaida masa cewa ka nuna mata aikin jahilci dana yarinta zunbur ya mike ya nufi fridge din sa ya ciro wani jus na kwalba ire-iren wadanda yafi sha,ya dau kofi ya nufi dakin.Bily tana tsaye ta jingina bayanta da bango,bai ko kalleta ba ya nufi kujera ya zauna, sannan ya jawo dan tebur din gabansa ya jawo wata durowa ya ciro fakitin magani,ire-iren magungunan da suke sha da su Chelen in zasu aikata masha%??irsu,ya balle hancin kwalbar ya tsiyaya jus din cikin kofi ya afa kwayoyin ya bi da sassanyan jus din
[4:14AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 48??}_

Kan Bily yana kasa zuciyarta ta zurfafa da tunanin makomarta acikin wannan auren sam bata san bikin da Yarima yakeyi ba sai da wayarsa ta soma ringing ta dago idanu ta dubesa gabanta ya fadi kar dai giya ce wannan?Ta tambayi kanta zuciyarta ta yanke cewa lallai giya ce take taji ta kara tsanarsa gami da kyamarsa shi kam cike da isa ya soma hira da Chelen ba tare da shakkar ga amaryar tasa kusa ba,kuma abin takaicin hirar batsa ce tsagwaronta, da turanci suke maganar inda yake nuna mata damuwarsa game da kewarta da yayi acikin hirar tasu yana kara jaddada mata yana bukatarta sai dai inya tuna daren ranar da zaya dawo hutu yana jin saukin kewar a cewarsa tayi masa tanadi inya koma zata gurzu. A karshe ya kira sunan albarkatun kirjinta yace tasa masa wayarta akai shi kuma yayi kissing.Innalillahi wa%??inna ilaihir raji%??in,duk da Bily ba son Yarima takeyi ba hankalinta ya kai matuka atashi,ji tayi tamkar tayi waje da gudu.Da ace ba jakadiya ta kawo ta ba itace ta kawo kanta hakika data zunduma da gudu,sai dai bata san in ta fita ba me hakan yake nufi da sauri ta sulale kasa ta zauna domin sai taji jikinta ya kasa daukarta, kafafunta sunyi sanyi. Hawaye suka soma yi mata zarya kan kumatunta,shi ko Yarima ai suna sallama da Chelen sai ya kira Vicky itama hirar batsar ce dai,kai tir inji Bily cikin zuciya.Bayan Yarima yayi sallama da %??ian matan nasa sai ya mike da kofi ahannunsa ya fita falo jim kadan ya dawo ya aje kofin tare da cewa,in har kina bukata zaki iya sha.Da sauri ta dubesa tare da cewa,Allah ya tsare ni ya dubeta tare da daga kafadunsa gami kuma da taba baki alamun ko ajikina.Bayinsa ma ya shige ya watsa ruwa ya dubeta menene shirinki game da kwananki dakin yaro?Ta mike tare da yi masa wani kallo kafin tayi magana ya kuma cewa,amma ki rike acikin zuciyarki bana sonki kuma baki min ba sa%??irki daya kina da kyau kila in dinga kula ki don kyanki,amma ba don so ba,haka nan kema bana so ki so ni,ya zauna kan kujera yanzun ina son ki cire duk kayan jikinki ki kwanta kasa kan kafet kila inji sha%??iwarki.Tayi masa wani kallo sannan tace,ai kai abin kyama ne,domin ka kusanta kanka da zina,ka sani baka kai matsayin dani Bily zan cire maka kaya ba,don bana bukatar kayi sha%??iwata yanda kuma kake ikrarin baka sona to ka sani nima haka.Yace ashe ilimin da kike ikrarin kina dashi karya ne,don mace mai ilimi iyakacin sanina(koda dai kince ni jahili ne)bata gudun mijinta,matsawar yana matsayin mijinta dolenta ne tayi biyayya ba maganar so agurin,don haka kiyi yanda nace,in kinki zamu gwada kashi duk da kince(yaushe kashina yayi kwari?)domin dole ne na banbance miki tsakanin babba da yaro,ni dake yau dinnan ba sai gobe ba,duk da faduwar da gabanta keyi bata fasa cewa baza%??i cire kayan ba kaji ko,salon kaje ka goga min cuta,fasiki kawai ban cire kayan ba kuma bazan cire ba ban dama rashin kunya har ma ka dubeni kace in cire ka....saukar marin data ji babu zato tana ta masifa shine ya katseta,lokaci daya ya saka kafa ya kwashe ta,ta yunkura zata taso ya sake sa kafa ya maida ta tare da fincike hijabin jikinta.Sun sha kokawa amma ga mamakin Bily Yarima kyaleta yayi take kici-kicinta,don daya tashi lokaci guda ya murdeta sannan ya yaga rigarta haka nan bada soyayya ko lalama yake son maida ta mace ba irin yanda take karantawa cikin littattafai ba,a%??i fyade yake nufi don haka sai ta bar mutsu-mutsu domin ta samawa kanta sauki ta sadakar sai kukan zuci da kiran Allah.Shi ko Yarima duk da ya fahimci budurwace matar tasa sam cikin zuciyarsa babu nufin rangwame,haka nan gyaran da aka mata zuwa kamshinta sun kara taimako gurin fidda shi daga cikin hayyacinsa,har ma ya kasa tuna dawa yake tare illa sunayan %??ianmatansa da yake kira hakan ya kara ma Bily bakin ciki,ta shiga rera kuka.
[4:23AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 49??}_

Abin mamaki mintina suka shude bayan wucewar sakwanni har aka shiga awa itama ta shude kai har amarya ta kasa fahimtar shin aduniya take ko ko a lahira?Kuma bacci takeyi koko ta mutu ne?Ma%??ina ta sume gogan bai san ma me take ciki ba har zuwa uku da rabi inda ya samu sukuni na kyaleta ba tare daya ko kalleta ba ya shige toilet jikinsa ya gyara sannan yazo ya haye gadonsa ya barta nan yashe bacci mai nauyi ne yayi gaba dashi cike da nishadin da yake ji na daban wanda tunda yake harkarsa da matan banza bai taba jin hakan ba.Sanyin asubahi ne ya farkar da ita,dishi-dishi ta soma gani kafin daga bisani idanunta suka washe,daga inda take yashe tana hango Yarima tsaf cikin gadonsa yana sharar bacci fitilun tsakiyar gado sun haske masa fuska,bakin ciki ya cika zuciyarta tayi ta kokarin yunkurawa ta tashi ta kasa dole ta hakura jim kadan ya farka cikin mika da salati tana kallon bakinsa yana karanta addu%??ir tashi daga bacci,sannan ya sakko ya tsallaketa ya shige toilet.Ruwa ya watsa tare da alwala sannan ya fito ya saka fara kar din jallabiya ya fita duk abinda yakeyi yana yinsu ne akan idanunta amma ko kallo bata ishe shi ba.Ta tuna da Mansu kawarta daren Mansu na farko da Faruk,Mansu tace kwana yayi yana lallashina, sannan da sassafe jiki yana bari yazo ya daukar mata Bily yana ta faman tarairayarta haka nan cikin littafai inta karanta mazan kan rasa inda zasu sa kansu,amma ita dubi abinda nata mijin yayi mata,sam bata son tunawa da daren farkonta zuwa shida na safe ta danyi karfin hali ta mike zaune ta jawo rigarta wadda duk ya yaga mata gashi duk rigar ta baci da jini haka nan ta zura ta dafa bango da dafa bango ta fito falo yana zaune yana kallon aljazira ya ganta tana kokarin fita,ya mike da sauri.Ke kina hauka ne zaki fita ahaka?Ko kallonsa bata yi ba taci gaba da laluben hanya,da sauri ya kulle kofar sauka kasan,sannan ya zauna ya dauko waya ya soma kiran layin Umma,bayan sun gaisa yace ta turo masa jakadiya Kamar minti goma jakadiya ta soma kwankwasa kofa,ya bude sannan ya nufi kujera ya zauna tana shigowa taci karo da Bily daf da kofa cike da salati jakadiya tace %??iannan lafiya?Ta riketa tace,zomu koma ciki.Bily ta girgiza kai alamar a%??i,jakadiya tace yi hakuri ranki ya dade,ai ba kya fita haka ba.Ta rike ta suka juya tana cewa ikon Allah, a garin yaya akayi haka? Yarima dai volume din TV ya kara suka koma ciki. Haka jakadiya ta gargasawa Bily jiki,cikin katon bahon wankan na Yarima,kafin ta nufi sasan Bily don kawo ma Bily kayan da zata sa.Ita kuma Bily tayi wankan tsarki sannan ta daura tawul,jakadiya ta kawo mata kaya ta fita doguwar riga ce baka ta zura sannan ta fito duk jikinta babu karfi,jiri ma take gani.Jakadiya ta nado rigar baccin ta saka cikin leda sannan ta dan rike Bily suka fita kai tsaye dakin Bily suka nufa take cewa ikon Allah,wai gaddama kika masa ne har haka ta faru ni laraba?Bily dai shiru tayi.Jakadiya taci gaba da cewa,banda abinki yanzun wa ke yayin wannan?Yara kanana ma irin na kauye in an kaisu daki shiru kake ji tsakaninsu da miji bakaji ba ka gani balle ke da girmanki da iliinki kuma kinsan su maza ba kunya ce dasu ba,gashi ma shine ya kira azo a dubaki.Bily dai tana jinta,kala bata ce ba.Ta kwanta akan gadonta,sannan jakadiya ta fita,gurin Umma ta nufa tana zaune kan sallaya hannunta rike da carbi tana lazimi,jakadiya ta zauna gefe sannan tace ranki ya dade na dawo daga kiran na Yarima ta cira rigar baccin cikin leda tare da fadin Ubangidana yayi sa%??ir mace %??iar gidan tarbiya,ranki ya dade amarya ta kawo budurcinta gidan miji.Umma tace,kai to menene kuma Yarima bazai bar ma cikinsa sirrinsa ba?Ai yanzu an daina wannan abin ilimi ya ratsa ko%??ina.Jakadiya tace ranki ya dade abinne yazo da matsala,dole ya nemi taimako,yarinya ce tayi gardama ne nake ga shi kuma dan yau babu hakuri,wallahi karki ga yanda yarinyar nan tasha wuya jini kyace an yanka karamar kaza,tana can kwance babu yanda take Umma tace to yanzun bari inyi ma Doctor Aisha waya tazo ta dubata Ke kuma kije ki sanar da masu aiki su shirya mata farfesu na kaji dana kan sa ko ta danji dadin bakinta.Haka ko akayi,doctor Aisha ta samu Bily kudundune cikin bargo kuka kawai takeyi,ta duba ta likitar da kanta ta hada ma Bily tea tace tasha don za%??ii mata allura ne.Bily ta dan sha sannan ta mata allura tare da bata magunguna duk na gajiya ne,tare kuma da huce radadi,haka nan ma likitar tayi mata mita kan cewa mai yasa bata ci abinci ba kafin mijin nata ya kusanceta?Shiru Bily tayi,doctor Aisha tace rashin cin abincin ya taimaka gurin galabaitar dake sannan kinyi kokarin hanasa kanki,kin matse jikinki har ya kaiga ji miki rauni.Cikin kuka Bily ta kwanta tama tsani yanda suke cewa ta hanasa kanta,basa ma tunanin koda ace ta hanasa kantanne ya dace ya bita asannu,bacci yayi gaba da ita wanda dama bata same shi ba jiya.Biyu da rabi ta farka kamar acikin mafarki taga Mansu da dady da Asma%??i,suna ta shan farfesu,da sauri ta tashi zaune jikinta ya daina ciwon sai dai ta jita fayau babu kwarin jiki,ta sakko tana cewa Mansu yanzun kika zo?Mansu tace tun dazun,munzo kina bacci muka je gurin Umman Yarima,Bily tace zo nan dadyna yazo ta dorasa kan cinya tana cewa,ina Abbanka?Ita ko Mansu dariya take ta kunshewa har dai Bily ta gaji tace wai dariyar mecece haka?Mansu ta dubi Asma%??i tace,auta keda dady kuje falo kuyi kallon cartoon suna fita Mansu ta koma gefen gado kusa da Bily tace aminiyata Umma tace baki da lafiya duk rigimar kin bar Mamanmu ne ko?Bily ta soma hawaye ta kama hannun Mansu tace,wallahi ba kukan rabuwa da Mama nakeyi ba,dama yaushe rabona da Maman da aka kaini aka tsare kamar nai sata,tasa yatsunta ta matse idanunta,sannan taci gaba wannan mutumin ne yayi min wani mugun wulakanci,wallahi nayi dana sani sosai na sanin Yarima bama aurensa ba.Mansu tace wane mutumi?Bily tace Yarima nace miki.Mansu tace hala ya zazzageki ne?Bily tace ba gara ya min duka bama da fyaden daya min,wallahi har suma nayi kwana cur yana aikin abu daya, wallahi ni bazan iya wannan bala%??in ba.
[4:26AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 51??}_

Yarima yayi murmushi dama so yake ya kunna Magaji,kuma yayi nasara.Ya dubi Bily sannan ya wuce tare da cewa,wa ma sunanki? Biyo ni tace,Hum sannan tabisa ranta fal kunci gurin Umma suka soma shiga ta zauna gaban Umma kanta akasa tana gaida Umman,ita ko Umma Allah ya dora mata son Bily,don haka ta jawota jikinta tana cewa matso nan %??iata,yaya jikin?Cike da kunya Bily tace da sauki.Yarima ko cewa yayi da Allah malama taso in kaiki ni sauri nakeyi,Umma ta daure fuska ta dubesa,bai sake magana ba,Umma tace babu inda ke miki ciwo ko?Tace a%??i to kina bukatar wani abu?Nan ma tace a%??i,har ta mike zasu fita Umma tace,amm Bily babana dai baya miki wani abu ko?Da sauri ta dubesa ya ko banko mata harara ta kautar da kai sannan tace ba komai Umma,tace ki gaya min in dai da matsala,ba komai Umma cewar Bily,tace to zanba jakadiya sako ta kawo miki,tace to suka fita duk tausayin Bily ya cika ta don taga hararar da Yarima ya mata da alama tsoransa takeji.Sun zaga ko%??ina sannan Yarima yayi hanyar fita ta bishi ta zata nan ma wani sassan ne,ya dako mata tsawa ke!Dabba ina zaki bini?Ta ja ta tsaya,sannan ta juya azuciyarta ko fadi take,ina da aiki.Daki ta koma ta hau gado tana karanta addu%??ir yaye kuncin zuciya,nan take taji zuciyarta ta wanke tayi fes,kuma tun daga ranar kullum sai taje ta gaida su Umma,Umma tana nuna mata kauna sosai.Yarima zaune agaban mai martaba yana cewa ranka ya dade,gobe ne ya kamata in koma makaranta, domin tun wancan satin muka soma karatu.Mai martaba ya gyara zama sannan yace to madallah,sai ka sanar da iyalin naka ta shirya ko?Ko ka shaida matan?Yarima ya danne damuwarsa na zaci nan zata zauna?Saboda karatuna yana bukatar nutsuwa.Mai martaba yayi dan murmushi,sannan yace yaro,yaro ne yanzu kai dama baka fahimci don ka nutsun bane nace lallai ina bukatar kayi aure?Ya dafa dan nasa kada ka damu Modibbo, yanzun ne ma zaka samu nutsuwa yanda ya kamata kuma kayi karatunka cikin nasara,tashi kaje Allah yayi muku albarka maza ka sama mata biza kaji ko?Yace to na gode ranka ya dade,ya fita zuciyarsa fal kunci
[4:28AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FAR??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????UWA 52??}_

Haka ya shigo pallon umman shi rai bace Bily yana ta fadin shi gaskiya an takura mashi tare da nuna billy wai umma da wannan abun zan tafi ai kau umman ta hau shi da fada sosai ita ko billy kanta na kallon kasa tana ta sharar da hawaye, Yarima ya mike ya fita Bily ta daure ta dubi Umma tace Umma nima nafi son abarni anan.Umma tace a%??i Bily banaso kice komai kinji ko,ke dai kiyi ta hakuri sannan kici gaba da addu%??i,share hawayenki kinji ko?Nan take tace to Umma,Yarima ya rasa yanda zaiyi dole shi suka je shi da Magaji suka kammala mata komai,yana ta zafin rai,ai ko suna dawowa har daki ya same ta yayi mata tatas,yace in har kika bini dama kisan kin nemi maganin hawan jini dana ciwon zuciya,don kam kaken dana miki yanzun ne zaki gane dalili,sannan in har kika sake, kika tafi da wata kuyanga bana ji ana wani cewa ai musu biza ba tun cikin jirgin zan turo ki in huta,kinsan zan iya banza wawuya %??iar matsiyata ya fita,kukan da Bily tasha ranar babu iyaka daga karshe dai ta hakura ta kira Mansu ta gaya mata komai,Mansu ma hakuri dai ta bata,Bily cikin kuka tace,Mansu yaushe zanji dadi ne irin na kowa?Wai ni MEKE FARUWA dani ne?Haka zan dawwama Mansu,wallahi dana so aure saboda kuncin rayuwar gidanmu amma yanzu ga aure ga daula amma gara zamana na gidanmu gara ina gaban Mama su Gwoggo Ladiyo suyi ta min gorin yafi min yanzun.Mansu ma ta soma kuka tana cewa kiyi hakuri wata rana sai labari,haka suka yi sallama zukata abace.Sai da tayi kokari ta natsu sannan ta sake kiran Mansu tace mata ki kula min da Mamanmu.Mansu tace,kinsan wannan dole nane,ko baki ce ba,ni dai fatana ki kwantar da hankalinki duk me ya miki ki daure ki sama ranki cewa kina ibada ne,kinsan kuma bautar Allah sai da hakuri na sani kin sani no condition is permanent. Allah ma ya fada cikin Alkur%??ini kowane tsanani yana tare da sauki,lokaci yana zuwa da zakiyi dariya aminiyata cike da jin dadi Bily tace na gode Mansu,naji dadi insha Allah maganganunki zasu zamar min abin tunanina, duk lokacin dana shiga kunci,sukayi sallama katan guda biyu cike da begen juna. Yanda taga rana haka taga dare, tunani ne ya cika zuciyarta MEKE FARUWA da ita?Me yasa bata da sa%??i ne ita arayuwarta?Duk yanda Mamanta tasha wahala kanta ta kyautata rayuwarta taso kwarai ta samu mijin da zai kula da ita da mahaifiyarta,amma sai gashi wani can wanda bai san kimarta ba marar tausayi mara imani wanda in aka tsare sa koda bindiga ba zai nuna mahaifiyarta ba ya aureta ya kuma sameta abudurwa bai ko kula da hakan ba,wanda ada ita taci buri sosai akan budurcinta,domin tasan abin alfahari ne sai gashi amma shi ya keta ta ba tare da yako juya ba.Shin wane zama zasuyi a Malesia?Tasan sai tayi hakuri tasan zai bi mata,tasan sai dare zai dinga dawowa,tasan yana zuwa club,kila ma wata rana yazo mata a buge, tunani dai barkatai,lallai ta bakin nasa ta nemi maganin ciwon xuciya. Tun shigowarta gidan yau ce rana ta farko da taga ainahin gidan,mutane tankam an fitar musu da kaya,Umma dai tana ta nanata mata cewa,lallai in taji yaya ne ta kirata ta shaida mata,shi kuma taja masa kunne cewa ya kula da ita don ita din amana ce agaresa,kuma ta yabesa da cewa dama kai mai alheri ne,don haka ka lura da ita ka wadatata nan ya tuno da batun Modibbo jiya da yaje masa sallama,yace takwarana don Allah ka lura da matarka sosai,ka sani yanzu ka shiga wata rayuwa ce mai daraja kuma kaima ka zama cikakken mutum,yanzun ka kula da karatunka banda shirme.Yarima yace,insha Allah na kuma gode,an raka su zuwa filin jirgin sama inda Bily ta kara yarda Yarima dan gata ne,saboda %??ian rakiyazuwa jami%??in tsaro ne,suka shiga jirgi zuciyarta cike da addu%??ir hawa abin hawa,inda Yarima ya zauna kusa da wani tana ta hangen inda zata zauna kusa da mace %??iar uwarta tunda shi bai damu su zauna tare ba,don haka sai ta zauna ita daya akujerarta,wani kuwa yana shigowa ya zauna kusa da ita tare da gaishe ta,ta amsa tana satar kallon Yarima,don suna gabansa ne shi kam ko kallo bata isheshi ba,haka nan da jirgi ya tashi mutumin nan ya dameta da surutu har dai ta gaji ta soma baccin karya.
[4:31AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 53??}_

Kai jama%??i!Anya mutane ana cewa babu kudi babu kudi,shin gaske ne?Gidansu take kallo tana fadin haka cikin zuciyarta tana tsaye tsakiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0