Showing 48001 words to 51000 words out of 79064 words

Chapter 17 - Meke Faruwa Book Compelet

mata nuni da hannu,ma%??ina tayi yanda yace. Ta duba taga ba halin guduwa balle ta gudu
[4:47AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 61??}_

Duk suna zaune gaban asalin bokansu,Ladiyo ta gyara zama tace,gaskiya boka duk yanda kace muyi haka mukayi amma duk ba wanda yaci,yanzun da haka suna kasashen turawa ita da mijin. Salame tace sannan shima na maigidan munyi kuma yaci amma tamkar ma mun kara masa masifa ne, Karima tace ga %??iayanmu nan dake gidajan mazajansu suma mun amsar musu duk abinda ya soma tasiri sai kuma ya tsaya.Boka ya dubesu daya bayan-daya sannan yace,ance muku kullum ake kwana agado?Amma dai kun san ba yau muke tare daku ba ko?Sau nawa ina muku aikin yana ci?Duk sukayi shiru,Ladiyo tace to yanzun yaya za%??iyi? Yace yanda za%??iyi kenan kuje kuyi hakuri danni nan da kuka ganni da zaran mutum yayi min korafin aiki baici ba to aljanu sun daina masa aiki don haka yanzun ku tashi tun kafin su iso keme cikin nan su cire dan su saka miki kwado.ai da gudu suka tattara yanasu-yanasu suka tashi,suna tafe suna jimami har gidan wani malamin, a takaice ranar yini sukayi garari gidan malamai da bokaye.A hanyarsu ta dawowa suna cikin mota ciwon haihuwa ya kamo Ladiyo suka rasa yanda zasuyi,mai mota yayi parking gefen titi yayi ta masifa yana cewa ku karata can nidai ku saukar min daga motata,in banda bala%??in yawo mace kina da ciki wata tara in banda asibiti ina zaki? Amma ke kin fito shegen gantali ai gara ki haihu a titin kila zai zama darasi ga mata masu shegen yawo irinki,su Karima suna cewa,malam don Allah ka barta taji da damuwarta, shi dai ya sauke su yana cewa ku karata dai. Gyaluluwansu suka cire tare da taimakon wata Bayerabiya suka tare ta har ta haihu,saidai ga maza masu saide-saide a gefen titin ga kuma yara sun taru ta haihu da kyar uwar ta biya,sannan suka rufe jinin da kasa suka nado %??iar agyalan uwar suka nemi shatar mota duk da babu mai sisi cikinsu sai bayan magariba suka zo gida,lokacin malam mamman yana tsaye kofar gida ransa bace yana son yaga ta ina matannan zasu bullo ne? Karima ce da girki tun safe suka ce zasuje gaisuwar mutuwa har yanzun ga yaran duk yinwa ta ishesu,suna ta kuka,Mamanmu ce ma data gama girki ta zuba ma kananan ta soma sa musu su duka to amma bata yi da yawa ba,don bata san sun fita ba sai da bata ji duriyarsu ba,ta idar da sallar magariba kenan tana tasbihi sai kawai ta jiyo muryar maigidan yana ta zazzaga masifa,yana fadin dukku nemi hanyar gidajanku,badai gidana ba tun safe kuna ina?Yau gari ya waye?Da sauri Mama ta fito ko hijabin bata cire ba,sai taji ashe ma akofar gidane ake diramar,don haka sai tayi waje.Karima da Salame sunyi tsuru-tsuru,malam Mamman nata zabga bala%??i,Ladiyo ko tana cikin mota bai ma san ta haihun ba don suna tsayawa yaga sun fito yako hau ruwan bala%??i. Mama ta matso tana cewa,lafiya malam duk makota suna jin muryarka? Yace ba dole aji muryata ba,inna yi fada ace na cika masifa,Allah ya hadani da matsiyatan mata,ace macen arziki ta fita gida tun safe tana gantali ita ba ma%??iikaciya ba,ba %??iar kasuwa ba,yawo kawai shiga nan fita nan?To duk suyi gida dama nina gaji da halinku. Mama tace a%??i malam ka bari kaji uzurinsu mana. Yace basu da wani uzuri, Salame tace malam wallahi muna da uzuri,dai dai nan mai motan ya karaso gurinsu yana cewa,ku bani kudina ina sauri ne,Karima tace malam kaba mai motar nan dari hudu,wallahi Ladiyo ce ta haihu ahanya dalilin dadewarmu kenan,Allah ya tsareni ai ko kudi zasu kasheni bazan baku ba,ai yanzun don wulakanci a titi ta kware gaba ta haihu? Amma Allah ya isa tsakanina daku.Yayi ciki,Mama tace ina Ladiyon?Suka ce gata nan cikin mota,mai mota yace ku bani kudina sannan ku dauke ta na taimaka muku kuna ta bata min lokaci,gashi motata sai karnin jini Allah dana sani da ban taimaka muku ba.Mama tace to ku sallamesa a fito da ita mana.Salame tace,um babu mai ko taro cikinmu, gida Mamanmu ta koma ta dauko dari biyar taba mai motan,sannan aka fito da Ladiyo,suka taimaka mata zuwa cikin gida.Malam yace shifa su fita don yayi musu saki dai-dai,Mama tace haba malam,menene haka? Yace ba ruwanki,ki koma daki kada ki kuma min magana,su fitar min daga gida kawai.Mama ta wuce daki,Salame kuwa ta nufi sashen Gwoggo da kuka.Ta shaida mata cewa malam ya sakesu, gwoggo ta saki butar dake hannunta ta zabga salati saboda me?Inji Gwaggo amarya,saboda munje gaisuwa Ladiyo ta haihu can.Gwaggo tace muje gidan an kada an raya da malam yace dole ne su bar gidan nan yau,haka nan sai yayyansa suka ce to su dai je gidan asan yanda za%??iyi,Gwaggo tace ta sani ba haka kawai bane anje ne an kau mata da hankalin da daga kan matansa.Ita ko Mamanmu daya shigo dakinta magana ta shiga yi masa akan cewa ya dawo da matansa don ita bazata iya kula da yara kusan ashirin ba,yace sun cika masa ciki ne amma zai dawo dasu wasa-wasa sunfi sati sannan ya yarda suka dawo,maimakon ya zamar musu darasi,a%??i sai suka shiga tunanin yanda zasu dauki fansa acewarsu Mama ce tayi musu asirin da aka sakesu,don haka itama sai an mata sakin babu ma kamar Ladiyo tace ai gara ku nida na tara uban bashi ina lissafin inna haihu zan dan rage gashi yanzun babu batun suna tunda yace ba wani taron da za%??i masa yasa ma jaririnsa suna dole ne na hakura tunda yanzu an dusashe mana haskenmu daga idanunsa,Salame tace ai ko kun hakura ni sai naga bayan shegiyar matar nan da %??iayanta.

***************************
Umma ta dubi anty Salma tace,ke Yariman ne yace miki yana son Sumayya?Anty Salma tace,a%??i Umma Sumayya din ce wai ashe tana sonsa ta kasa fada ashe ma akansa ne taki sauraron samari.Umma tace,to yanzun ai sai ta sauraresu don kinsan Yarima da yaya ma aka samu yayi wannan auren?Don haka tama nemi mijinta inma da yana sonta baya sonta ba, ai daya yi magana, saboda haka kibar ma wannan zancan,ni na mafi son ya nemo matarsa can wani gurin kamar yanda yayi nan itama sai ta nemi mijinta bana son hadin nan su zo su bata mana zumunci,don Yarima bawai yana da dama bane.Anty Salma tace Umma bada wannan da ba asan asalinta ba ni wallahi matar nan ta Yarima bata min ba. Umma tace, karta miki ai badon ke aka aureta ba,don bata miki ba wata tsiyar ce? Bana ma son ta miki.
[4:48AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 60 ??}_

Ta rumtse idanu sannan ta soma balle masa botiran, shi ko fuskarta ya tsurama idanu,xuciyarsa tana fadin,she is beautiful kwadayin lebunanta ya kamashi ya kasa daurewa,hannu yasa ya kamo fuskarta cikin tsananin zumudi ya manna bakinsa cikin nata.Daga nan komai ya cigaba da wakana,Bily dai tamkar gunki ta zamar masa yayinda shi kuma yake duk yanda yaga dama da ita.Bily wanka takeyi tana kuka,ba wai tasha wuya bane kamar wancan karon,duk da dai taji jiki wannan din ma kukan bakin ciki ne ko na menene ita dai bata sani ba,amma wata zuciyar tana gaya mata cewa kukan rashin mai so ne,ita da dai tana son ta san me yasa maza basa sonta?Ta sani Yarima ba don yana sonta suke zaune ba, yama gaya mata kuma lokaci ya kure mata da jin wannan kalmar ta so daga bakin wani tunda tana da miji yanzun kila ita haka Allah yake son ya ganta ma%??ina bai kaddaro ta cikin wadanda zasu samu maza masoya ba.Yarima koda yake kwance cikin bahon wankansa, idanunsa lumshe yana tuno irin halin daya shiga ne lokacin da yake tare da Bily,me yasa yakan fita daga hayyacinsa harma yayi ta surutai,in yana tare da ita?Wanda ko chelen da suke shaye-shaye don nishadinsu shida ita baya samun kansa cikin wannan yanayin,kuma fa wai ma don bada son ran Bilyn bane,in da da son ranta ne zata masa duk abinda su chelen keyi masa yaya zai ji kenan?Tsigar jikinsa ta tashi yarr!A fili yace,kila sai na suma don haka yasa a ransa zaya yi kokari ya gwada yanda zai samu hakan.Ya jima yana tunani kafin daga baya yayi wanka ya fita,yayi mamakin ganin yanda lokaci ya tafi har haka daga yin mantuwa ya dawo dauka shine har kusan awa uku,yayi tsaki kowane lokaci ya bata lokacin sane kan yarinyar nan ce,bai san mutum ya zauna yana tunanin banza ba sai kanta,tun farkon haduwarsu har yau ita kadai ce din dai ke saka sa tunani me yasa?
[4:49AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 64??}_

Yana gaya mata cewa kada ma ta kama cewar yana da aure karta gayama kowa ma azata gaske ne. Chelen tace to yaya kake da ita? Yace kanwata ce bata son ta ganni da %??ianmata don kinsan addininmu bai yarda ba,tace ai ta yarda ba matarsa bace,tunda ta jima tana zuwa gidan inda matarsa ce tasan da tuntuni zata dauki mataki,yace kin gane ashe.Shi Yarima sam baya so chelen ta kai labarin yana da aure cikin school dinsu,shiyasa yayi haka sam baiyi don ya bata ma Bily rai ba,danne zuciyarsa yayi kawai,ita ko Bily bakin ciki ma ai ba%??i tonawa,ace mijinka ya nuna karuwa ta fika,ko baku son juna ai aure ya wuce wasa,da abin ya isheta da tukuki arai sai ta dauko maganin ciwon zuciya da hawan jini,kai da dukkan wata cuta ma,ta shiga karantawa,wato Alkur%??ini mai girma.Yanzun ta daina zaman dogon tunani,in ranta ya baci Alkur%??ini take dauka sai kaga nan take ta manta da duk wata damuwarta, don Allah kema ki gwada %??iar uwa,da zaran kin shiga damuwa ki dauko Alkur%??ini ko falaki da nasi kike ta karantawa,sai kinji sanyi aranki in baki manta ba dama shi waraka ne. Yarima ko bayan tafiyar chelen,ya shiga don ya dan watsa ruwa,lokacin sallah ya kusa hankalinsa yana tashe ne,can kasan zuciyarsa tana ta mintsininsa, me yasa zaima beauty haka?Jin damuwa tana son sasa dogon tunani yasashi yin maza ya watsa ruwan, sannan yayi alwala ya fito yana cewa bazai dinga zaman tunani ba,saboda ita amma me yasa kasan zuciyarsa yake mintsininsa? Me yasa zuciyarsa kullum burinta ta ringa kwadaita masa yarinyar?

Ladiyo ta dubi gefen da Mama take zaune,sannan ta kalli su Karima ta soma magana dubi matar can,sunan %??iarta na gidan sarauta amma kullum fate da rana.Salame tace ke da kike wannan zancan an san da zamansu ne?Har shi malam din da yayi hanyar auren,itama yarinyar tunda akayi auren shiru ko irin tazo din nan.Ladiyo tace ta samu dadi yaushe zata tuna da uwarta? Ai dai ba%??iyi dacen haihuwa ba wallahi. Duk Mama tana jin su,yi tayi tamkar bataji ba,aranta tace,oh yaushe rabon ta da faten ma,yau ma malam ne yace ta masa amma da sheri harda cewa kullum fate.
Tana mamakinsu gasu da abin zagi rututu amma sun danne suna zagin wani su da girkin ranar ma sai su debe shekara basuyi ba,ita bata da matsalar abinci,dan ko yaushe ne ma ko sati ba%??iyi ba da Mansu tazo ta kawo mata buhun shinkafa,katon din taliya,harda galan man gyada gashi su Sakina da Maryam suna mata aike daidai gwargwado,kuma zancan maigado su daba sa kasar kwana biyu ma basuyi waya ba,ko lafiya?Malam ya katse mata tunani da cewa,hakimi ne ya aiko inzo Fatima,bari inje in dawo.Tace lafiya dai ko?Yace nima ban sani ba,sai dai na dawo. Tace to,ya fita ba tare da musu magana ba,suka soma kwasa dariya suna cewa kila ma %??iar ce aka sako ta.Ladiyo tace,Allah yasa hakane,da sai na zuba ruwa akasa nasha don dadi.Karima tace,haba dani nan bari dai mu jira dawowarsa. Suka shiga %??ian wake-wake su adole burinsu ya cika.Shiko malam yana isa gurin hakimi ya samu %??ian aike daga Bauchi, mota ce guda shake da kayan abinci zuwa na masarufi,inji mai martaba sirikinsa,%??iarsa aka kawo ma mahaifin sirikarsa lokacin da ya iso gida murna dai ta kasa boyuwa,tun daga bakin kofa yake fadin ina Fatima,ga sako daga %??iarki.Nan aka soma shigo da kaya ana kimewa, Mama tace ikon Allah haihuwar %??ia mace mai dadi,yau ga uwar mata tana murna ni Fatima na gode Allah.Ai su Ladiyo sai aka shiga sirarewa ana shiga daki,zuciya fal bakin ciki,hassada ga mai rabo taki ce,haka abin yake. Mama ko cewa malam tayi,wannan kaya shi aka ba,don haka sai ya raba yaba kowace hakkinta, yace a%??i san musu za%??iyi,tace ai ba zai yiwu ba,a karshe dole ya amince ya raba musu,sai dai duk da haka sai daya kara mata,sannan ya ware mata wanda zata ba mutane,tayi rabo kam duk sauran sassan ta basu,haka kawayenta Umman Mansu ma takai mata da yawa su Ladiyo ko kunya aka amshe shinkafa har ki ga ana salo gurin dafawa ana ci ana zagin Mama da %??iarta, mutum kenan ba%??i iya masa.Umma tana ta zaton cewa Bily tana da ciki ne,don haka duk sanda sukayi waya da Bilyn sai ta rika ce mata don Allah kada ki biye ma babana da cin zakin nan da shan sanyin nan nasa kinji ko?Bily bata gane ba sai tace,to Umma shima Yarima sai ta riga cewa babana amma gida zata dawo nan gaba ko?Shima bai gane nufinta ba,sai yace dama fa kune kuka matsa sai nazo da ita,duk Umma ta damu har takai ga sanar da mai martaba damuwarta,tace ranka ya dade ina zaton matar Modibbo cikine da ita kuma daga shi har ita babu mai hankali cikinsu kada yaje yayi ta tura mata sanyi azo a haifi dan da sanyi ayi ta fama,mai martaba yace to yanda za%??iyi tunda ga azumi yana zuwa,in salla ta kusa sai mu tafi Ummara tare dasu daga can sai mu wuto da ita.Nan Umma taji dadin haka.Abinda yayi mugun bata ran Bily, harma da azumin nan Yarima bai daina kwana da mace ba,al%??imarin yayi mugun daga mata hankali, tasan cewa duk wani shaidani yakan aje shedancinsa a cikin wata mai alfarma,wata mai daraja,watan tuba,watan yafiya,watan da Allah yake %??ianta bayinsa,watan lada.Don haka tayi niyar zata yiwa Yarima nasiha koda zai dake tane, shiyasa ma yau tayi nufin zama a falo don yin buda baki.Ya fito dakinsa yana sanye da jallabiya fara tas,yaxo ya nufi dinning bayan ta gama mikewa taji zuciyarta tana karfafa mata gwiwa kan cewa taje ta masa magana,don haka ta isa gurin kallo daya yayi mata ya kauda kai tare da cigaba da buda bakinsa,ta zauna tana fuskantarsa.Nazo ne ina son yin magana da kai,ya dubeta sannan yace %?&nmhum. Taci gaba da cewa nazo ne in maka tuni kan wani abu dana san ka sani kila ka manta ne,matsayinka na musulmi bai dace ace cikin watan Ramadan kana aikata alfasha ba,kana zina ka sani duk wani musul.....ke!Ya katse ta da tsawa tare da buga teburin cin abinci har kofin glass ya fado kasa ya fashe,abincin gabansa ya tarwatse,ki shiga taitayinki dani,ni sa%??inki ne? Nace ni abokin wasanki ne?Itama tayi karfin hali ta mike tsaye danna gaya maka gaskiya?Yace bana son ji, ki fita daga idanuna,inba haka ba zan nuna miki waye ne Al%??imin.
[4:53AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 65??}_

Ya daga kyallen tebur din ya watsa mata a jiki ya fita daga gidanma.Tsaye Bily tayi tana tunanin dama Yarima ya iya ihu haka?Allah ya kyauta.Shi kuma tun daga ranar ya bude mata sabon daure fuska,wani bari na zuciyarsa yana zugasa kamar sa Yarima dan sarki wannan zatayi ma wa%??izi? Lallai ta samu sake,duk da cewa kasan zuciyar nan tasa tana masa zogi,tare da hura masa wutar sha%??iwarta, cikin wannan halin azumi ya kai ashirin mai martaba yace,lallai su zama cikin shiri,Magaji yana nan zuwa su wuce saudi tare,su gobe zasu wuce,don haka su samesu can.Bashi da amsar data wuce to duk da suna karatu,yasan tafiyar bazata shafi karatunsa ba,matsalarsa daya itace mata,zaije ibada ne.Ya tsaya neman mata? Sannan ma zuwan Magaji yau din nan zai sa dole ya hakura da kawo mata,shima gaskiya ba sansa bane kawo matan nan da yakeyi cikin wannan watan,amma da zarar yasha ruwa sai yaji su kurum yake bukata, daren ranar yayi niyyar hakura har sai sun dawo amma bazai iya ba,shida kansa yayi ma chelen waya tazo.Suna tare ne a falo sai ga vicky suna jin haushin juna amma ba sa gwadawa a gaban Yarima,domin sun san sa suna soma %??ian harare-harare zai sallamesu,kila kuma ya zama shine karshen alakarsu,kuma in har kikayi fushi kika tafi,to in zaki shekara nawa sai dai fa ke ki dawo.Shiyasa kullum yake ma kansa kirari baya bin mata sai dai su bi sa.Vicky ta zauna adayan gefen tare da dan tsikarinsa ya dubeta da guntun murmushi,sannan ya duketa a kirji,irin dai wasa na gogaggun matasa.Sun sashi a tsakiya kowace burinta taja ra%??iyinsa kanta,suna tayi masa wasanninsu na jan hankali,musamman da yake sun sansa yafi son wasannin fiya da ya kwanta da su don haka sai suka kuke dayi.Sha biyu da rabi Bily ta farka daidai lokacin da take tashi kenan,tunda aka shiga goman karshe tsayiwar dare takeyi har asubahi,in tayi sahur sai ta kwanta bayan tayi sallar asubahi kenan.Don haka inta tashi takan ajiye komanta na sahur ne akusa,kitchen ta fito don nufin dauko ruwan zafi tana fitowa falon sai me zata gani? Yarima ne da matan nan duk basa a hayyacinsu,batasan sanda tace,A%??izu billahi minash shaidanir rajim.Sannan tace haba don Allah haba Yarima,kaji tsoron Allah kana tuna mutuwa kuwa?Kana tuna kabari?Kana tuna ranar da zamu tsaya agaban Ubangijinmu?Watan Ramadan cikin goman karshe kuma karshen goman ma da duk wani musulmi yake rage bacci,don kwadayin daran nan na (Lailatul kadari)kuka ne yaci karfinta ta juyo da gudu ta koma ta fada kan gado,sai kuka a dhekarun baya ko watannin baya,tayi kuka tayi addu%??i tayi tsayuwar dare duk roko take Allah ya bata mijin aure.Yau ga miji yaro sharaf mai kyau ga ilmi da ake tunkaho dashi a yau ga kudi ga mulki gata cikin daula taci wanda take so tasha kuma wanda take so, amma hakan bai mata rana ba,hakan baisa ta farin ciki ba,zamanta ada gaban iyayanta yafi mata alkairi,zamanta cikin kunci da kiyayyar mahaifinta yafi mata auren Yarima shin dama haka matan da mazansu ke bin mata suke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0