Showing 51001 words to 54000 words out of 79064 words

Chapter 18 - Meke Faruwa Book Compelet

ji?Lallai ta jinjina musu don suna cikin ukuba,jin zuciyarta take tamkar ta fashe don bakin ciki.Shiko Yarima jikinsa ne yayi sanyi,nan take kwadayinsa ya kwanta sannan ya dubi su chelen yace,su tafi cikin daurewar kai suke tambayarsa dalili, tsawa yayi musu tare da cewa su fita mana?Vicky ta mike ta fita abinta, chelen ce ta tsaya son jin me kanwarsa ta gaya masa? Yace ta fita kafin ransa ya baci da ita,haka itama ta figi rigarta ta fita tana gungunai,shiru Yarima yayi azaune tunani ne fal zuciyarsa yasan tuni ta masa amma anasa girman kai yana nufin ita bata isa ta gaya masa ba,nasa ganin ba girmansa bane tayi masa wannan abin ba.Ya mike ya nufi dakinta har lokacin kuka takeyi,kausasa murya yayi yace,ke!Da sauri ta dago tana dubansa,fuskarsa adaure yace,ban hanaki shiga harkata ba?Bance bana son sa ido ba?Ke kin isa ne ki sani nayi abinda banyi niyya ba?To bari kiji karki kuma shiga harkata, nima kaddara ce Allah ya dora min,bata san lokacin da tace daina gaya min kaddara,Allah baya dorama wata rai abinda ba zata iya dauka ba, wannan wani abune daka dorama kanka.
A yau in kaga dama.... saukar marin data ji ne yasa ta dafe kunne,yace ni kike ma ihu?Ni kike gayama magana?Tace bazan gaya maka ba? Kullum ina dana sanin aurenka bazan gushe ba, gara min auren talaka lis wanda sai ya fita yasha wahala ya nemo sannan muci,matsawar ya tsare kansa daga zina nan ya kuma gabza mata wani sabon marin wanda yasa sai da network dinta ya dauke na wucin gadi.Ya nunata in har kina neman zaman lafiyarki to ki cire idanunki daga kaina iyayena ma basu takura min ba balle ke banza wofi kuma yanda kike dana sanin aurena haka nima nake dana sanin ganinki tun farkon ganina dake,kece mutum ta farko data ke min katsalandan arayuwa,bansan tunani ba bansan mugunta ba duk kece sanadi,ban taba marin wani ba ko zagi ke duk kin sani na iya,don haka in kina neman zaman lafiya dani to ki cire idanunki akaina.Kin taba zagina jahili yau kuma kina cemin mazinaci,kece mutum ta farko da kika taba zagina,ko mahaifina lallabani sukeyi,don haka ina gargadinki da babban murya ki fita harakata,in kin manta wanene ni Yarima Al%??imin nake,ni daya ne tamkar da dubu agidanmu, dan haka maida hankalinki ya fita.Kai ta kifa taci gaba da kuka wato yanzu duniya babu gaskiya don kawai ta sanar dashi abinda zai amfane sa, shine harda dukanta?Ranar dai kwana tayi tana kuka ko sahur batayi ba.Wayewar ranar ne Magaji yazo shi kansa yayi mamakin ganin yanda fuskar Bily ta kumbura,idanun suma sunyi luhu-luhu ya nemi jin ba%??isi tace,ba komai aranar suka gama abubuwansu na tafiya.Ana jibi sallah suka tafi,ko cikin jirgi %??iar shariya akayi.Magaji da suka zauna guri daya da Yarima yake cewa,kai dama bakaje ba,Yarima yace wai saboda kurewar lokaci? Magaji yace,a%??i bama don haka ba,na gane kana gaba da iyalinka kuma zaka gari mai tsarki.Yarima yace ka barni da yarinyar can %??iar rainin hankali ce ita,tsaki Magaji yayi tare da cewa Allah dai ya shiryi halinka. Sun hadu dasu Umma da mai martaba gidan da mai martaba ya kama musu nan suka same su.
[4:54AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 66??}_

Bily ta yarda da zancan Yarima,da yace shi da daya ne tamkar da dubu,domin yanda taga iyayan suka nuna karara son dan nasu suke,haka nan manyan mutane abokan nasa da wasu da suka samu zuwa daga cikin danginsu sai ina ka saka ake dashi.Umma ko sororo tayi lokacin da suka hada idanu da Bily, tasa rai ta ganta tana daga kafa da kyar sai gata tangaran to ko dai karami ne ko kuma yabi jiki?Duk wannan tunanin Umma ne amma tasha alwashin zata tambaye su taji kar dai suna shan kwayoyi ne?Yin wannan tunanin sai da gaban Umma ya fadi tace,inko haka ne sun cucemu.Bayan shan ruwa sunci sun sha ana zaune ana hira kafin lokacin zuwa masallaci,Umma ta dubi Yarima tace,ubana na zaci zanga matar taka da tsohon ciki?Yarima yace,haba dai Umma tun yanzu?Tace kaji shashanci da sai yaushe mu da kullum addu%??irmu muga %??iayanka,yace dazun ma mai martaba fa cemin yayi wai to kai Modibbo in zamu tafi da matarka zamu wuce inta haihu sai ta dawo,abin ya daure min kai nace ranka ya dade tana da ciki ne?Sai cemin yayi kuji zancan banza, ni zaka tambaya?Suka kwashe da dariya, Umma da Magaji.Yarima murmushi yayi don shi baya kyalkyala dariya.Bily kam sai tayi kasa da kai, Magaji ya mike tare da cewa zo muje masallaci. Yarima yace kwarai muda bamu zo da wuri ba.Suna fita Umma ta dubi Bily wai da gaske ne %??iar nan baki da komai?Kunya ta rufe Bily,kanta na cikin cinyarta tace,wallahi Umma ba komai,tace ko dai kwaya kike sha ne?Tace Allah bana shan komai,tace ko shine dai ke baki,yace kada ki fada?Don fa karki yarda ki dinga shan kwaya nan gaba ta miki illa,kinga shi namiji ne da zarar yaso %??iaya zai iya karo aure,ke kuma an cuceki. Bily tace,wallahi Umma bama shan komai,to kun taba ganin likita?Cewar Umma,a%??i inji Bily,bamu taba gani ba,tace to wannan ai shirme ne,kafin mubar garinnan sai munje kunga likita. Gurin kwanciya, Bily ta shige gurin Umma dama su Yarima suna can masallaci suma zuwa sha biyu suka nufi masallacin, haka sukayi ta ibada har ranar sallah.
Bily kam ranar data ganta gata ga Ka%??iba,ai addu%??i sai wadda ta manta. Murna kuwa harda hawaye, domin arayuwarta bata taba tunanin yau rana zata zo da zata ganta agaban Ka%??iba ba.A cikin addu%??i%??in da Bily tayi ta roki Allah game da aurenta da Yarima,kan cewa in mai shiryiwa ne Allah ya shirya shi sannan ya daidaita tsakaninsu in kuma babu daidaitawa,to Allah ya watsa abin ya kawo mata karshen wahalarta,sannan ta roki Allah ya sassauta ma mahaifiyarta,game da abokan zamanta ya kuma sa mahaifinta ya dawo kan hanya.Ranar sallah mai martaba ya nufo gida,Umma dai ta tsaya sai sunga likita.Daran ranar Yarima ya kasa hakuri da jarabarsa ta motsa,dakin Umma ya shigo Ummar tana toilet sai Bily dake zaune,tana neman layin Mamanmu sun gaisa da kowa amma ta kasa samun Mamanmu ya dubeta ransa ya sake biyawa,amma girman kai ya hanasa yayi mata magana.Har zuwa sanda Umma ta fito,tace yaya ne babana?Ya danyi murmushi sannan ya dubi inda Bily take zaune yace ba komai dama nazo ne nace miki sai da safe. Abinka da manya,nan Umma ta gano nufin dan nata,don haka tace,Bily tashi kije gurin mijinki mana, ni sai naga ma kamar gudunsa kike tunda muka zo banga kina bashi wata kulawa ba.Tana wannan maganar ne bayan fitar Yarima,taci gaba da cewa kin san fa su maza %??ian lallashi ne,suna san kulawa bare irinsu Yarima.Bily tace Umma ba kirana yakeyi ba,Umma tace kaji sokuwa, yanzun yaushe ake jiran kiran miji?Har dai Yarima dan jin kai?To maza tashi ki bishi dama zaman da kukeyi kenan sai yace zo? Tashi-tashi maza-maza kar in sake jin haka.Bily ta mike ranta bace zata tafi,Umma tace,haka zaki je ba ko dan saka turare?Bily kam ta cika ne da mamaki,da bata zata haka Umma take ba,kuma sai tana ganin kamar ko san kai ne Umma take nunawa,don dai Yarima danta ne,duk da ta sani Umma tana sonta.Hoda ta murza sannan tasa turare ta saka kayan bacci sannan tasa hijabi ta fita,yana zaune bakin gado ya rasa me ke masa dadi,kamar ya zama kuda ya dauko Bily yake ji. Ta shigo da sallama fuskarta daure, tamkar an jefa shi cikin gidan aljanna haka yaji,harda yin wata ajiyar zuciya,amma don jan aji irin na Yarima sai ya wani daure fuska tare da cewa, lafiya ?Bata yi magana ba,ta zauna can gefe kan kafet,kin shigo min daki kina ta wani daure-dauren fuska bayan ban kira ki ba.Shiru dai ta masa,yace ok,in baki da magana tashi ki kama gabanki.Ga mamamkinsa sai yaga ta mike zata fita,yasha gabanta, ai bazaki fita ba har sai naji dalilin zuwanki. Bily ta dubesa, Umma tace inzo,oh shine dan kin raina Ummar zaki koma can ko?Tan ki koma din,ya koma gefen gadonsa ya zauna sannan ya dauko laptop dinsa ya soma kunnawa tana dai tsaye.Ta dawo ta zauna inda ta tashi yaci gaba da tura wani assigment ya jima yana turawa har ya gama,lokacin ta soma gyangyadi yace,ke ta farka idanunta fal bacci yace zo ki kwanta ba don halinki ba,tace nan ma ya isa, yace ke komai sai kin min gaddama,harda kice nan ya isa ance miki ina kalanki ne?Kema gulma ta kawo ki ko da Umma tace ki zo nasan kina son zuwan ko don a sosa miki abinda ke miki kaikayi, bani da yanda zanyi tunda an makala min ke.Mikewa kawai tayi taje ta kwanta, sai daya gama mata wulakanci kala-kala sannan ya shiga yin abinda ransa ke so da ita,jikinsa har bari yakeyi duk da dai yau ma kamar kullum,gim ta masa kamar kullum,haka ma da safe gari yayi haske amma ya fake da cewa kada ta kuma dawo masa yau bari ya sallameta gaba daya,bashi ya barta ba sai da Umma ta kwankwasa musu ita dai ta sani arashin %??ianmatansa ne ya kula ta shiyasa bata jin itama zata sakar masa kanta yanda ta kula yafi bukata, ta aje aranta yanda ta rasa wanda zaice Bily ina sonki,haka ta hakura da jin wannan dadin don a duk lokacin da Yarima yake kusantar ta zuciyarta tana gaya mata cewa makiynki ne ke son hutawa da ni%??imarki,don haka sai taji duk mugayan maganganun da yake gaya mata suna dawo mata,kuma sai taji tana kyamarsa saboda matan da yake hulda dasu, sannan burinsa na taji dashi dadi ba zata ji dashi ba har abada,sai dai yanda suka saba.
[6:28AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 67??}_

Suna zaune gaban likita sun masa dukkan bayanin daya dace,sannan ya shiga dubasu.likitan ya tabbatar da cewa lafiayarsu lau,sannan ya basu wadansu kwayoyi wai su sha bayan sun dawo gida Umma tace,to su zo suje suyi tsaraba don ita gobe jirginsu zai tashi zuwa Nigeria su kuma sai gobe sannan zasu wuce Malesia tace wallahi Umma naso in biku gida nayi missing din Mamana.Umma tace,me zaki je Nigeria kiyi mijinki yana?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? wata duniyar?Ke dai kiyi hakuri ba shekara mai zuwa bace zai gama ko ta sama ce? Kamar yau ne gurin Allah Mamanki ba kuna waya ba?Tace mu kanyi saboda yawanci sai sanda Mansu taje gidan sannan ta kira ni,Umma tace a%??i bata da waya ne?Tana da shi,inji Bily to ni yaushe rabona da wayata taga kati sai zuwanmu nan da Magaji yasa min,Umma ta kalli Yarima, me kenan babana?Yace to Umma yaya zan mata,ita fa tunda taje tafi karfin tace min tana son kaza,ko na ci ko a na sha bare kati, Umma tace to ke kuma ai wannan hauka ne, keda mijinki?Kusan shekara kin kasa sakin jiki dashi to dawa zaki saki jiki?Ki daina haka kinji ko, gaki kamar kanki a waye?Duk abinda kike so ki masa magana tace,to Umma yace kuma da kanta take abinci amma bazata ce tana son abu kaza ba,madam dora ce ma take gaya min cewa, tana cin taliya shine in sun zo shi cefane sai nace ya siyo mata,Umma tace ta daina haka Bily tace to insha Allahu bazata kara ba, azuciyarta sai mamaki takeyi shin Yarima da gaske ne da zata tambayesa abu zai mata?Tasan kila bazai ba don dai yaga mahaifiyarsa ne kurum.Sun shiga siyayya shagunan larabawa,nan taga mamaki Umma cewa tayi duk me take so ta diba na tsaraba nasu Mamanta ma ta dauka sai ta wuce dasu ta bada akai musu,amma ta kasa daukar komai sai Umma ce ke cewa, dau wannan dau wancan daga karshe ta daukar ma Asma%??i auta dankunne da sarka na gold ita da yarinyar Mansu,sannan ta yiwa Dady tasa haka suka yi ta shiga shaguna suna kashe kudi,Yarima dai ya jidi kananan kaya harda %??ianmatansa yayi ma tsaraba,da Umma tace na Bily ne kai tsaye yace a%??i ya sayawa abokan karatunsa ne,kuma ga mamakin Bily Umma ba tace komai ba.
[6:30AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 68??}_

Komai me lokaci yana da iyaka,su Yarima anyi jarabawa cikin nasara an gamata a sa%??i,ya zama cikakken likitan mata gwani,Doctor.Ana gobe za%??i tabbatar musu da zamansu likitoci,su Magaji suka iso tare da mai martaba,da kuma wasu daga cikin yayyansa,tunda Umma ta sanarda Bily zuwan bakin nasu,suka je kasuwa don shirin tarbar bakin,sun kammala komai,sannan bakin suka iso.Su anty Fulera sai %??ian harare-harare akeyi,Bily dai ta kula da take-takensu amma ta share ita farin cikinta daya, kammala karatun Yarima zata gida taga Mamanta da %??ian uwanta,ranar rantsar da likitocin rana ce mai mahimmanci gurin Yarima da mahaifinsa guri yayi guri,manyan mutane daga nahiyoyi sun halarta. Yarima shine dalibi mafi kwazo cikin daliban da suka hattama karatun,don haka hukumar ilmi ta kasar ta bashi lamba ta farko data yabo sannan ta bashi dama ya zabi duk kasar da yake so cikin jerin kasashe goma don yin wani course na daban har na tsawon shekara daya ko biyu,wannan nasara da Yarima ya samu tasa shi farin ciki shida masoyansa,sun shirya %??iar kwarya-kwaryar party shi da abokansa. Can gida kuma suma suna tasu walimar.Mai martaba dai yana can masaukinsa,tun ranar suka so,a nade kaya farin ciki gurin Bily ba%??i magana, a daren ana gobe zasu dawo gida Yarima an samu nutsuwa,tunanin shi daya inya koma gida babu mata kenan, Allah sarki,Ashly yarinyar da suka hadu babu dadewa tana masifar ji dashi, shiyasa ma yake matukar sonta don shi yana son akula dashi,ko bai sallama da kowa ba dole ne yayi sallama da ita,suna hira ne da %??ian uwansa amma ya mike can gefe ya kirata ya kuma sanar da ita cewa su hadu guri kaza. Ashly irin black american din nan ce,tana da tsawo da kiba,amma kibar ta a mazaunai ne da kuma kirjinta,tana son Yarima musamman data fahimci shi mai sha%??iwa ne,tana matsa shi sosai kuma ba tsararsa bace,zata girmesa,kafin yaje gurin ta rigasa,sun lalace son ransu sannan ya tile mata kudi sukayi sallama,kuma ya mata alkawarin indai ya ga da sarari zai mata kwatance tazo Nigeria itama harda kuka,nan Yarima ya kara susucewa danshi yana so yaga mace ta mutu kansa. Sanda ya dawo suna ta hira da Bily,yana shigowa ta kallesa ta kauda kai tasan me yaje yay,haka nan Magaji.Washegari suka hau jirgi sai gida. Abuja suka sauka,Bily tana shakar iskar kasarta sai taji tamkar an sakata cikin gidan aljanna,nan suka hau wani jirgin zuwa Kaduna,Bily taji tamkar ta sauka zaria lokacin da suka dauki hanyar Bauchi. Lifaya sosai aka shirya musu,sunci sun sha ana ta hira ita dai Umma damuwarta rashin ganin Bily da tsini agaba,haka sauran kishiyoyin Umma sai da sukace amare har yau anata amarcin tukunna?Anty Fatima tace,mu bama son wani amarci,%??iaya muke bukata,mun gaji da sai dai aci ayi kashi.Umma tace kadaku matsa mata, haihuwa aita Allah ce,ni damuwata ma ko kiba banga ta kara ba %??iar tawa. Anty Saliha tace, amma Umma aita murje,dibi yanda fatarta ke sheki,sai kace tarwada?Bily dai tana jinsu,ita dai matsalarta daya tana son ganin Mamanta,zata gwada tambayar Yarima ta gani ko zai barta?Da safe ta shiga gurinsa ta samesa zaune yana kallon(BBC)ta zauna dan kusa dashi tace ina kwana?Ya dubeta dama kin iya gaisuwa?Tace to inna gaishe kane baka amsawa,ya dan taba baki tare da cewa,kina bukatar wani taimako ne?Tace,em dama ina wannan ne ya dubeta kiyi magana bana son kwana-kwana,tace ina son naje naga mahaifiyata ne,yace yaushe?Tace duk sanda kace,yace shikenan kije sai sanda nace din,tace to yaushe? Yace bana son naci ki jirani tukunna,tace shikenan ta mike ta fita.Satin duk bata da sukuni ba ta zuwa sasan shi shima baya nemanta duk da yana bukatarta,jin shiru ne yasa ta sake nemansa taje da dare baya nan da safe zata shiga kenan tazo falonsa na kasa sai gashi ya sauko tayi sauri tace,ina kwana?Ya amsa da lafiya, zai wuce tace gurinka fa nazo,ya tsaya sannan ya juyo yana kallon lebunanta da matsala ne?Maganar zuwa gida kaga tunda nazo ban taba zuwa ba ka dubi tsawon lokacin?Ya soma tafiya da cewa duk sanda kikaga ya dace sai ki sanar dani,tasha gabansa da sauri yau ko gobe,yace fine ya fita ta tsaya shiru ko dai gatse yake mata?Kai takan rasa gane hali irinna Yrm,shi kullum ana tarasa nan yana botsewa data shiga gurin Umma suka gaisa ta sanar da Umma cewa tana son zataje gida don taga mahaifiyarta,kuma ta sanarda Yrm yace ko yau ko gobe,Umma tace sai dai goben don sai an sanarda mai martaba,tace to data shiga dakinta murna harda tsalle,sai kace karamar yarinya.Ta kira Mansu ta shaida mata cewa gobe tana zuwa,ta kira su Maryam da Sakina duk ta sanar dasu,ta kira Mama tace gobe tana hanya,Mama tafi kowa murnar zuwan Bily,saboda gorin da kishiyoyinta suke mata cewa sukeyi tir da wannan %??iar ta samu daula ta mant da uwarta,gori harda surukarsu Gwoggo amarya,tace inda kwadayi to da wulakanci,an tura yarinya gidan miji gidan sarauta don kwadayi gashi nan kila ma tana can tana wahala,inba haka ba shekara nawa bata zo ba,kamar an saida ita.haka nan %??ian unguwar akayi ta surutu,wasu ma sai sun hadu a sha%??ini sai kaji sun ce ina amare?Ana can dai,Mama kance um tana can da an dameni batayi aure ba batayi aure ba,yanzun kuma tayi an koma kan bata zuwa indai tana zaune lafiya acikin dakinta ai alhamdulillah, sai kaji mutane ana cewa hakane fa,Mama tana sa tare da cewa insha Allah maigado tazo garin nan sai nace ta shiga duk makotan nan ta gaidasu. Malam ya shigo tace, Malam gobe fa maigado tace tana hanyar zuwa,murmushi ne ya subuce masa cike da fara%??i yace ikon Allah,nidai dama kullum yarinyarnan tana raina,lallai muna da babbar bakuwa,Allah yasa ta iso lafiya,Mama tace amin.Bily daren ranar batayi baccin kirki ba, saboda tsabar murna,tunda duku-duku ta shiga gurin Umma, umman lazimi takeyi don haka gefe ta samu ta zauna bayanta gama suka gaisa,Umma tana murmushi tace,Bily kin kosa kije gida ko? Tayi dariya tare kuma da sunkuyar da kai,Umma tace to kinyi tsaraba ko?Bily tace,sai dai wadda muka yo daga malesia, tace a%??i wannan tayi kadan tunda kila wasu kika gayyade kika sai musu wannan ko ganin gida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0