Showing 33001 words to 36000 words out of 79064 words

Chapter 12 - MEKE FARUWA BOOK COMPLETE BY HALIMA K. MASHI.doc

yace,Allah dai yasa lafiya?Ya daga sun gaisa sannan Magaji yace,mai martaba ne yace a tambayeka yaushe zaku samu hutu?Yayi shiru,sannan yace,sai nan da sati kila bakwai,yace ok,zan gaya masa.Yarima yace,lafiya Magaji?I think so.Yarima yace,naso ma nayi hutuna anan.Magaji yace,ok,ka iya yin waya ka gaya masa.Kai fa,bazaka fada ba?Inji Yarima.Magaji yace,No.Ya kashe wayar tare da cewa kada ka fada din,ni zan masa waya.Chelen ta matso kusa tana lasar kirjinsa da yayi laf da suma,tace tana son ya koya mata Hausa tana son yaren,yace bashi da time,kuma shima ba iyata yayi sosai ba,don shima Hausa fulani ne.Idanu ta tsura masa tana gaya masa cewa bazata gaji da gaya masa cewa yana da kyau ba tace shiyasa take kara son sa harma takan kirasa da One in town.Shi ko ce mata yayi yana sonta ne kawai irin na sha%??iwa,yace shi fa bai ma gama yarda cewa akwai wata soyayya ta No one but you ba.Shiru tayi don tasan yana nufin abinda ya gaya mata ne,kuma ya jima yana gaya mata haka,tasan bazata taba tursasa zuciyarsa ta so taba,kuma tasha yin fushi dashi,sai ya share ta sai dai ta dawo da kanta don shi bai iya lallashin mace duk da yanda takai da ji da kanta.Shiyasa kawai ta hakura da yin fushi dashi. Sun iso zaria misalin sha biyu,kai tsaye gidansu Mansu suka nufa,sun iske Umma tana shirin fita.Abba kuma ya dan fita shima,tace su zauna tana zuwa,Bily tace bari ta leka gida Umma tace a%??i su dai jira gidansu Maman ta nufa,ta samu Mamman a dakin yace,yauwa Hajiya,shigo kinji fama nake da baiwar Allah nan za%??i kawo kayan nan dakin tayi wa %??ian uwanta waya suzo saboda mutanan nan zasu zo ne su kaita gidan ajiya,an jima kamar yanda nayi muku bayani jiya,duk taki ta bani hadin kai. Umma tace yanzu dai gata nan sun iso suna gidanmu,bari inyiwa Mansu waya ince suzo nan din ko dan tasan halin da ake ciki?Mama tace nima damuwata kenan,gaskiya in maigado bata son abin nan nima bazan so sa ba,dan fari ba mahaukaci bane,koda nake kauda kai kanta ba don bana sonta bane,ina dai kara ne,wulakancin dakayi ta mata cikin gidannan,ko tsinto ta akayi ba%??i mata haka ba,shikenan haka rayuwarta zata zama cikin bakin ciki.Nan bata huta ba kuma tayi auren kudi can ma taje taci gaba da fuskantar wulakanci?Sam bazan lamunta ba,yaja tsaki ai kinji ki da wani zance,ba%??i tuna abinda ya riga ya wuce,batun aji ra%??iyinta wannan ba dole bane tunda ko ashari%??i mune masu zaba mata miji.Mamanmu ta kalli Umman Mansu tace,kirasu dai muji zabinta shine nawa nina san wahalar da nasha kan %??iayana.Bily ta rasa dalilin dayasa suna nufowa gidansu taji gabanta yana ta faduwa,ta dubi Mansu tace,ko dai wani abu ne ya samu Mamanmu?Mansu tace,me kika gani?Ta kama hannu Mansu ta saka akirjinta tace kinji fa kirjina.Faruk yace,ba komai insha Allah.Suna shiga da sauri ta nufi dakinsu,ganin Mama zaune yasa tayi ajiyar zuciya har duk %??ian dakin suka dubeta,ganin Mama hankalinta ya kwanta,sai dai tasan da magana don banza Baba ba zaizo ya rashe haka ba.Ta shiga ta zauna kusa da Maman,tace Mamanmu har naji dadi dana ganki lafiya domin na zata wani abu ne ya sameki.Umma tayi %??iar dariya tace,%??iar Mama kenan Mama kuwa cewa tayi lafiya lau maigado.Su Mansu suka shigo,Bily ta kara shimfida wata tabarmar,sannan aka shiga gaisawa,ta gaida Baba wanda zuciyarsa ta tafi ga tunanin yanda %??iartasa ta nuna halin ko in kula dashi yau ne kurum abin ya fara masa ciwo,don da baya ma so ta nuna ta damu dashi Bayan gaishe-gaishe,Umman Mansu ta dubi Bily tace,kin san Yarima?Gaban Bily ya fadi,ko dai yasa anci ma iyayanta zarafi ne?Ta tambayi kanta,Umma ta katseta kin sansa nace?Bily ta girgixa kai alamun a%??i,tare da cewa ni sam bansansa ba.Yace nayi masa wani abu ne?Umma tace,a%??i sannan ta dubi Malam Mamman tace,malam bani kudin nan.Jiki yana rawa ya ciro ya miko mata,ta amsa sannan ta aje agabanta.Wannan sadakinki ne,Bily ta zaro idanu tare da dafa kirji,Umma taci gaba ga kaya can yanzun za%??i shigo dasu na zance,bikin bazai fi wata biyu da sati daya ba,me kika ce? A rude Bily ta juya ta kalli Mamanmu,sannan ta fada kan Maman tare da fashewa da kuka,tana cewa Mamanmu menene zabinki?Ki fada min zabinki shine nawa.Amma ina so ku sani Yarima zai aure ni ne ba domin yana sona ba,sai domin ya idar da wani nufi nasa na cin zarafina.Malam yace,ke dai kawai kice kinfi son kici gaba da zama agari babu aure,mutane suna zagina,amma ina kika san Yariman da har zaki wani ce yayi ne don yaci zarafinki mutumin da aka ce yana kasashen Turawa?Mama tace,tashi ki share hawayenki,in har ba kya son sa babu matsi,don ba akan kowa kike ba.Malam ya fita fuu yana cewa,ni dai ya rage naku.Uba ke bada aure kuma na bada ta.Sadaki kuma gashi nan a hannunku,in zaku ja da sarakuna ne bismillah.Ya sake lekowa,kada ku manta yau zasu zo su kaita su adana,sai ku shirya abin ce musu in sunzo ni kunga tafiyata,ya shuri takalmansa yayi waje.Umma ta dubi Bily dake kuka Mama nayi,ta waiga gurinsu Mansu inda sukayi shiru tamkar ruwa ya cinyesu,sai Mansu dake kuka,tace ku tashi kuje can gidanmu,ke Mansu har kai Faruk ku bata shawarar data dace,sai mu saurari hukuncin Ubangiji.Mansu ta kama Bily suka fita suna kuka,Faruk yana cewa suyi shiru kada su shiga cikin jama%??i da kuka waton awaje in sun fita.



[4:01AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 42??}_

Hakika mai martaba yayi murna da zuwan Yarima, fannin Umma kuwa sawa tayi aka shiga shirya ma autan nata gara kala-kala.Dan hutun sai da yayi wanka ya gama kyale-kyalen sannan ya fito gaban Umma yasa aka zube masa komai ya zauna tare da dararrashewa cike da shagwaba yake cin abincin suna shan hira,yace Umma taya naga duk zuwan da nake yi yau ne kuka fi murna da ganina?Ko dannayi zuwan bazata?Yace da haka kuma kazo ne akan gaba,wato kazo sanda ake son zuwan naka ma%??ina dama muna bukatar kazo din,ya dubeta saboda me?Tace saboda komai ma babana,kai dai gama zakaji komai gurin mai martaba.Gabansa ya fadi,amma sai ya daure ya jawo wata hirar.Umma kinyi kyau fa,kamar bake kika haifi su anty Salma ba.Umma tace,kai babana ko yaushe kazo zancanka kenan,wane kyau mun tsufa?Ai ba kyau ga tsoho,fatanmu dai mu ga jikokin kowa muga na auta,kasan %??iayanka sune asalin jikokin gidannan, kuma sune zasuyi gadon sarauta.Yayi murmushi insha Allah nima har nawa jikokin sai kin gani.Umma tace,a%??i babana bana fatan ganin wannan lokacin yace to mu sake labari bana so kina tunanin cewa wata rana zamu rabu,tace ai wannan ya zama dole,yau ina tawa uwar? Yace,shikenan dai Ummata,ina su anty Fulera? Ta dawo daga jiddan kuwa?Tayi murmushi tasan ya kauce wa zancanne.Tace,sun dawo tuni Abban ya samu sauki sosai,haka suka ci gaba da hirarsu cikin nishadi irin na da da uwa. Masu matukar son junansu,sannan Magaji ya shigo inda yayi masa rakiya zuwa sauran sassan don gaida kishiyoyin Maman tasa,daga nan suka isa fada don yiwa sarki gaisuwa.Bayan ya rusuna yayi gaisuwa,sannan ya karasa gefen mahaifin nasa ya dora kai kan kafar mai martaba,wannan abin tun yana yaro haka yakeyi, mai martaba kamar ko yaushe ya shafa kan Yarima tare da furta Allah yayi maka albarka.Sannan Yarima ya zauna yana kallon yanda fada ke tafiya har zuwa lokacin
Da dare suna cin abinci cikin wani shahararren falon mai martaba,falo ne na gargajiya,yasha kilisa da tim-tim,in yana nishadi yafi son yaci abinci cikin falon.Yanzu ma Umma ce take zuba musu kalolin abincin suna ci,shi ko Yarima fruit yake sha cike da nishadin gashi zaune gaban iyayansa.Mai martaba ya dubi Yarima cikin sigar wasa irin na iyayan da suka shaku da %??iayansu,yace Allah gafarta Modibbo dama ka samu labarin auren naka ne shiyasa kayi mana zuwan bazata?Nan take cikin Yarima ya kada, kamaninsa suka sauya yace,ranka ya dade dama da gaske ne za%??i min aure?Mai martaba yayi murmushi,sannan ya dubi Umma kinji wani shirme,dama ana wasa da zancan aure ne Modibbo?Umma tace,babana ai ka kusa angwancewa.Shiru Yarima yayi,sai dai duk kayan dake gurin sun fita ransa,duk da son cin dayake yi.Kofin ruwa ya dauka ya tsiyaya ya kai bakinsa yana sha,jin ruwan yake tamkar madaci,amma ya daure yana dan kurba don kada iyayansa su gane,sai dai ya makaro,domin tuni suka fahimci baiji dadin albishir din da suka masa ba sam.Mai marataba ya aje cokalin hannunsa sannan yace,mun maka laifi ko Al%??imin?Yarima ya kakaro murmushi yaya zaku min laifi?Ranka ya dade kunyi min gata dai.Ya sunkuyar da kai,na gode Allah ya rama muku.Ya dubi Ummansa banyi rashin kunya ba ko?Suka yi murmushin jin dadi,duk da sun sanya wayance ne.Yarima kam ya shiga rudu,lallai ya gamu da abinda yake tsoro,gashi bashi da mafita, bai saba musu da mahaifinsa ba,ba tarbiyar gidan sarauta bace,sai dai lallai da safe zai samu mahaifiyarsa yana son ya roke ta kan ta lallashi mahaifinnasa duk da yasan ba lallai bane hakan ya yiwu,bacci dai ranar kasawa yayi har nisan dare.Can ya dauki waya ya soma neman Magaji, magaji yana daga waya Yarima yace dan iska za%??i iya hada baki da kai akashe ni tunda har aka kulla min aure baka ce komai ba.Magaji yace,kai haba wace zaka aura?Amma fa nayi murna. Tsaki Yarima yaja sannan ya kashe wayar,ya kwanta badon yana saran bacci ba,sai don kawai yayi tunani,hakace kuwa ta faru domin sai daya dawo masallaci sallar asubahi. Sannan wani nannauyan bacci ya dauke sa.Tara da minti hamsin ya farka, zuciyarsa cike da damuwa haushin koma wacece amaryar yake ji,don ya tsani abinda zai daga masa hankali har ya fita lokacin wani abu ya shiga na wani.Da rigar bacci ajikinsa ya nufi dakin Umma,yana so ne ya dan lallashe ta kila ta goya masa baya duk da yasan babu tabbas.Tana karin kumallo ya sameta cike da fara%??i take dubansa, babana ka tashi?Ya dan turo baki irin na shagwababbun yara ya zauna ba tare da yace kala ba,Umma tayi dariya tare da cewa,auta yau shagwabar ta tashi kenan. Kafin yayi magana, jakadiya tayi sallama, Umma ta bata izinin ta shigo.Tayi gaisuwa gurin Umma,sannan tace,nazo ne in gaida uban dakina, tun jiya bamu hadu ba, naje yana bacci na koma aka ce kuna cin abinci,to yanzun dana je suka ce min ya shigo gurinki shine nace bari dai inzo na kosa inga uban dakina.Umma tace ga uban dakinki nan yana ta fushi.Jakadiya ta dubesa ran uban dakina ya dade,wa ya taba min kai?Yace dubi Umman shi Umma kinji?Tace naji me?Yace don Allah ki gaya ma mai martaba ajanye min zancan auren nan wallahi am too young shekaruna 24,amin aure,ku dubi karatuna mana yana bukatar natsuwa.Umma ta daure fuska,sannan tace kaga kada ka sake min maganar nan,magana an gama ta lokaci ya matso,sannan kazo da shirme?Yasa hannuwansa ya dafe kansa tare da cewa,Oh my God!Please Umma,I hope zaki iya shawo kan mai martaba,ni nafi son inna kai talatin sai inyi tunda kuna son nayi aure,amma yanzun fa 24 nake kafin talatin din ma ace ina da yaran?Bazan iya ba Umma.Ta mike sannan ta kallesa me yasa tun sanda ya sanar da kai baka musa masa ba,sai ni don ka raina ni zaka zo ka tasa ni agaba?To bari kaji bazai yiwu ba.Ta fita,jakadiya na cewa Allah ya huci zuciyarki ranki ya dade. Umma na fita jakadiya ta matso ta zauna kasa agabansa,ranka ya dade ai hakuri kawai zakayi.Ya dubi jakadiya idanunsa jajir yace,jakadiya na san kina taimaka min tun ina yaro,duk abinda nake so kina min kokari musamman agurin mai martaba.
[4:03AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 43 ??}_

Jakadiya tace,cikin sanyin murya da sigar lallashi ranka ya dade, wannan karon mai martaba bazai yi yanda kake so ba,in kuma mun tursasa shi yayi yanda kake so,to girmansa zai fadi,kimarsa zata ragu,me zai ce da sarkin zazzau wanda shine ma ya biya sadakin tare da kebe amaryar taka,wato ya killace ta?Shi kuma sarkin zazzau me zai ce da iyayan yarinya?Sannan kai kanka bakayi biyayya irinta %??iayan sarakuna ba,domin tarbiya gurinku ake koyo sai aji karfin iyayanka me jama%??ir Bauchi zasu ce?Ko kasan labarin aurenka ya shiga Bauchi da kewaye?Ka dawo tunaninka,ka kwantar da hankalinka tare dana Ummanka,gashi tayi fushi.Yayi ajiyar zuciya,ya sanin yanzun bashi da mafita,sai hakuri, ya dubi jakadiya yace, jakadiya yanzun to yaya zanyi?Tace yauwa uban dakina,ka samu Magaji ku shirya zuwa hira da amaryar taka wannan shine zaisa Ummanka ta sakko mai martaba yaji dadi su kuma yi alfahari da kai cewa zamanka a turai bai sa ka zubar da tarbiyarka ta Hausa fulani da addininka na musulunci ba.Yace shikenan,na hakura amma jakadiya Allah ya sani bana son matanmu na Nigeria,sam kauyawa ne basu ko iya kwalliya ba. Jakadiya tace,kai!Bari uban dakina,ba%??i fi %??ianmatanmu kyau ba da iya daurin dan kwali,asha jan baki da hoda.Yayi dariya,tare da cewa ai kauyancin kenan kullum jiki an rufe shi ruf,jakadiya tace ai wannan kuma haka addini ya tsara,inka aureta nan ne zaka ga kyanta kai kadai,ya taba baki sannan yace,ki sanar da mai martaba ashirya mana zuwa can ina ne ma kika ce?Tace zaria,yace %??iar masarautar ce?Tace a%??i,ba %??iar sarauta bace, shiyasa aka killaceta don dabi%??in sarauta ya shige ta.Ya fita yana cewa,bari inje in yima Magaji waya.A dakinsa kafin ya kira Magaji,sai daya zurfafa tunanin shi lallai dole ya hakura karya zubar da darajar masarautar mahaifinsa,in yaso ana yin auren sai ya koma makaranta ya barta anan in anyi hutu yaki dawowa yayi zamansa can inta gaji ta nemi su sahale mata, yin wannan tunanin shiyasa Yarima ya saki ransa ya kira Magaji yace ya shirya zuwa Motoci hudu ne cike da dogarawa ata gaban ta bayan %??ian sanda ne ta tsakiya kuwa Yarima ne shida Magaji, sai mai dauke da tsaraba zuwa kayan lashe-lashe wanda ango zai kaiwa amarya.Cikin bacci take jin gabanta ya tsananta da faduwa,ta farka da sauri ta tashi tana salati,ta kalli agogo biyu saura tace, a%??izubillahi mina shaidanir rajim.Har lokaci ya tafi haka?Sai da tayi sallah sannan ta shiga wanka tana zaune cikin bahon wankan tana saba jikinta sabulu tare da kara gode ma Allah yanda ya tsara mata surarta,ga fata mai laushi ita kanta tasan cewa ta keru ne samanta da kasanta,sai dai matsalarta daya ce,rashin dacen miji domin nata ganin me zai ce mata?Allah yasa ma yasan menene auren inma yasani ita kam ai ta masa girma sai dai ya nemi %??iar sha shida.Haka ta fito daga wankan tana tunane-tunane,ta gama shafa jikinta da mai ta zura doguwar riga mara hannu,tasan yanzu masu kula da kwalliyarta zasu shigo.Sai ko gasu sunyi sallama,ta amsa suka kama aikinsu cikin zuciyarta kuwa haushin wannan kwalliyar takeji,ba don komai ba sai don a iska ake yinta,tunda ba miji gareta da zaizo ya gani ba,ita kuma ba fita zatayi ba bare tace...Atika ta katse ta da cewa ranki ya dade Allah yasa bamu muka bata miki rai ba kike tsaki?Bily tace,ina tsakin wannan kwalliyar ne ta isheni.Suka ce ya kamata ace kin saba da wannan kwalliyar ranki ya dade.Su Yarima kam kai tsaye fadar sarkin zazzau suka zarce,suka kai gaisuwa, sunci sun huta tare da yin sallah sannan suka nufi gidan da amarya take. Yarima da Magaji sai dogarawa guda biyu dake biye dasu cikin wata mota,Magaji ya dubi Yarima cike da tsokana yace,nasan gabanka yana ta faduwa,kana tunanin fara ce? Baka ce?Mai kyau ce bata da kyau?Oho.Yarima ya dubesa kamar bazaiyi magana ba har ma Magaji ya sadakar bazai ce komai ba,sannan Yarima yace,ina ma sonta kenan?Yaja tsaki kada ka raina ma kanka hankali,ka zata sonta nakeyi,???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ko daya yanzu ma jaje nazo in mata.Da sauri Magaji ya dubesa %?naje? Yarima ya jingina da kujera tare da share Magaji har sanda suka iso gidan.
[4:04AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_ MEKE FARUWA 44??}_

A falon suka zauna,Magaji ya dubi kuyangin dake zube gabansu suna dibar gaisuwa yace,ina Gimbiyar take?Asabe tace,tana ciki ranka ya dade.Yace shaida mata isowarmu,tunda taji shigowar matoci ta kasa sukuni,ta mike tsaye tana ta kaiwa-da-komowa, sanye take da doguwar riga mai hade da hula. Asabe ta shigo ranki ya dade ki bani goron albishir,da sauri Bily tace,Mansu ce tazo ko Mamanmu?Asabe tace,ranki ya dade Yarima ne yazo.Ta dafa kirji cike da fargaba,tare da cewa,Yarima?Asabe tace,eh ranki ya dade.Bily ta soma zufa,koma kice ina bacci don bazan ganshi ba.Saroro Asabe tayi,amma dole taje ta fada,jiki babu kwari ta sanar dasu gimbiya tana bacci.Yarima kam ko juyowa baiyi ba,Magaji ko yace,to bari mu jirata.Ya dan saci kallon Yarima don ya fada ne kawai don yaji me Yariman zai ce,nan take kuwa Yarima ya dakawa Asabe tsawa da cewa,ki taso ta mana,ita wacece da har za%??ice tana bacci? Duk Bily tana ji,nan take ta tuno da maganganun da Yarima ya gaggaya mata,don haka Asabe tana shigowa kafin tayi magana,Bily ta fita.Yarima yana zaune ne saitin dakin nata,don haka tana fitowa tayi arba dashi,yayi kyau cikin kayan da %??iayan sarakuna suka fi sawa,sai hula mai gashi da kuma takalman sarakai.Sam Yarima bai ko kalli inda take ba,duk da yasan ta shigo yayi shiru yaji da wacce zata fara?Amma sai yaji shiru,sai Magaji ne yace,ranki ya dade karaso mana.Yarima ya juyo da nufin yaga wai shin wannan wacece ita?Zumbur ya mike yana nuna Bily da dan yatsa tare da fadin dama kece?Ya kalli Magaji ka gane ta?Bai jira amsa ba ya soma tafa hannunsa sai da yayi tafi so uku sannan ya taka a hankali ya isa gurinta.Ya dubeta sai yanzun na fahimci dama kina da wata manufa akaina,kuma kinyi Achieving shiyasa kika ce kin sanni tun randa kika fara ganina?So kinyi kokari,yanzun dama nazo miki da abu biyu ne,na farko in tayaki murna sannan in miki jaje,daga karshe kuma in baki shawara,to amma tunda kece ina nufin ba wata can da nake zato ba,wadda bata sanni ba aka tilasta ma aurena bace,to abu uku zan miki ke maimakon biyu zan fara jinjina miki sannan in miki murna in kuma miki jaje,sannan in baki shawara sai dai shawarar da zan baki tasha banban da wadda nazo da ita,taki ta dabance.Ya juya mata baya tare da harde hannuwansa a kirji, jinjinar da zan miki kuwa?Ita ce na yaba da kokarinki yanda kika shiga kika fita tun daga kakana Modibbo zuwa mahaifina kika

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login