Showing 57001 words to 60000 words out of 79064 words

Chapter 20 - Meke Faruwa Book Compelet

yasan %??iancin dan Adam, tace na gode sai da safe. Ya rigata kashewa ta kalli Mansu wadda itama taji duk abinda suke cewa saboda sun sata a handsfree.tace kin soma gano laifin ki ko?Yaron yasan abinda yakeyi don haka ki gyara takunki da safe ma sake kiransa ki gaishe shi.Bily tace,ni duk komai ina ganinsa banbarakwai ne,anya zan iya?Mansu tace,zaki iya sannan sai ma kinsha gyara zaki bar nan,da kin koma kada kiji kunya ki saki jiki ki jawosa ki mantar dashi matan banza ya zama kafin ma ya koma kin dasa kanki garesa,Bily tace,to Allah yasa zan iya,ni kunya ma nake ji inna tuna shekararmu daya dashi, nan gaba yazo yace yarinya yake so.Mansu tace ai sai kiyi,shin haramunne aurenku?To in baki sani ba bari in sanar dake,Manzon Allah (S.A.W)matarsa ta farko ta girmesa,kuma bazawara ce,shin in haramunne haka zata kasance?Bily tace,a%??i Mansu tace don haka saki jiki ki rike mijinki,Allah ne yasan dalilin zaba miki shi, kuma gata Ubangiji yayi miki sai nan gaba zaki gane,ga lada in kikayi sanadiyar shiriyarsa.Bily ta soma yarda da shawarar Mansu,don haka cikin kwanaki ukun da zatayi sun shirya duk yanda zatayi inta koma ga gyara tasha,ta shirya sosai kuma ta dauri aniyar ba sakaci daga yanzun cikin kwanakin sunyi rabon tsaraba,su Sakina ma sun koma gidajansu cike da tsarabobi masu yawa,su da %??iayansu har ma da abokan zama,Bily ko ranar da zasu tafi ta kara shiri sosai sauran batu zasuyi shi awaya, itama Mansu haka ta juya Kaduna cike da tsarabar da Bily dinta ta cikata dashi. Tun acikin mota tana kwance zuciyarta ta shiga kai kawon yanda zata jawo Yarima gareta. nan take ta ciro wayarta ta soma neman Yarima,sai ta samu kanta da karya muryarta,lokaci daya dauki wayar yana fadin,hello tace mijina ganinan ina dawowa yayi dan jim,don muryar ta dokeshi,sannan yace,to sai kun iso.Tace kana murna kuwa?Yace to murnar me zanyi,me kike min in kina gidan?Tace la,dama kana son inma wani abu shine baka sani?Yace,au,da sai na saki?Ina ce tun kafin kizo gurina an karanta miki zaman aure?Tai %??iar dariyar kissa,oh yes,na manta ne yace shikenan yanzun tunda kinje ai sai a tuna miki ko,yacigaba da cewa sai kin iso yanzun ina driving ne,ya kashe wayar.Sun iso daf da magariba ta shiga gurin su Umma suka gaggaisa ta kuma sanarda Umma iyayanta suna godiya kafin suzo an shigo da tsarabar zaria,su kuka ne,kubewa da dai sauransu,tunda kowa da sandar hannunsa yake kai duka.Data koma sasansu kuwa,lokacin an gama share mata ko%??ina an goge.tayi wanka ta shirya cikin wani material bulu da ja,tayi kyau bata daura dankwali ba,sai ta daure gashinta da dankwalin.ta nufi sasan Yrm gabanta na faduwa,ta samesa kuwa yana waya da Ashly ta danne zuciyarta har suka gama,ya dubeta fuskarsa kamar kullum, wato gim,ta zauna kusa dashi ta rike hannunsa tana murmushi tace,mun dawo.Ya dubi idanunta kun dawo lafia? Da idanu ta amsa masa tare da daga gira,wani iri yaji ajikinsa, har sai da yayi tsam.ta fito da harshe ta dan lashi lebenta kowa yana gaishe ka.muryarsa ta dan sarke ina amsawa. Ta mike kamar zata fita ya bita da kallo tamkar yace dawo,amma girman kai y hana,sai ta juyo nan take ya wani dauke kai ta dawo, kaci abinci?Kin damu inci ne? Tasa yatsanta daga goshinsa ta biyo dashi takan karan hancinsa har zuwa lebunansa,tana cewa sosai ma,me kake so?Shi kam tuni ya soma sakin layin da yake,don duk jikinsa ya motsu gani yake Bilyn daya sani ce %??iar kauyen nan mai boye kanta?Ya dai dake yace,na koshi.ta nufi fridge ta dauko jus din dayafi so tazo ta tsiyaya cikin kofi ta mika masa,to sha wannan.
[6:37AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 73??}_

Ya amsa babu gardama, ganin yanda Yarima bai gwaleta ba shine ya bata karfin gwiwar shige masa,shi kuma ya kasa gwaleta ne don yana cikin bukata sosai,kwanakin duk a matse yake.tace ni ina jin yinwa bari naje naci abinci, kamar yace zaki dawo ne?Amma sai ya share ta fita,koda ta gama cin abincin sai data sha kankana da rake tasha hadaddiyar zumarta, sannan tabi duk gabobinta tasa turare,bata sa komai ba sai rigar bacci shi ko lokacin yayi wanka ya saka rigar bacci ya kasa nutsuwa jinsa yake tamkar ya dauki waya ya kirata.nan take ya samu kansa da addu%??ir Allah ya kawota,yana ta kai kawo tsakanin bedroom zuwa falo,kamar daga sama sai ya soma jiyo kamshinta,sai daya shaka sannan ya dan juyo. itan ce cikin rigar bacci ja,yana iya kallon duk abubuwan kallon dake jikinta,wanda nan take ya shiga rudu,har ya kasa dauke idanunsa daga kanta,ganin haka yasa ta gane tarkonta ya hadu,don haka da taje kusa dashi sai ta sassauta murya tace,dama nazo ne in maka sai da safe.yayi ajiyar zuciya,sannan yace to sai da safe.Ta juya zata tafi ya wani dauke numfashinsa, zuciyarsa ta kasa daurewa,nan da nan yayi taku daya na biyu ya riko hannunta ya jawota zuwa kirjinsa,yasa hannu ya dago fuskarta nan take ta bude masa bakinta tare da miko masa harshenta. Cikin doki ya amsa,nan ta tuna Mansu da tace duk abinda yayi miki ki masa, ki nuna kin iya dama can baki son yi masa ne,nan take ta zage gurin son ta burgesa,sai ga Yarima ya kasa tsayiwa sunma kai ga zubewa,da zai yiwu in baku labarin wannan dare da kunsha mamaki,domin Yarima ya samu kansa ne cikin wata duniya mai nisa, ita kanta Bily sai ranar tasan da tayi wauta, duk da suna ikirarin basu son juna.koda suka samu nutsuwa sai Bily ta nemi ta koma dakinta,sai ya dubeta zuciyarsa tana masa fari yana wana sunsunar ta yace,ki kwana anan kinji Beautyna?Yana magana ne yana kallon fuskarta,gira kurum ta daga masa a ran ta tana mamaki lallai Yarima hada sabon suna na samu yau ke nan,don haka sai ya janyota zuwa jikinsa. Safiyar ranar sai gurin goma ta fito daga sasannasa, tana kuma mamakin yanda Yarima ke nan nan da ita,lallai gaskiyar Mansu ne,harda laifinta.Tana sasan su Umma ya shigo yana ta wani shan kamshi,kuyangi na gaisheshi,ita kuwa sai tayi murmushi ya dan saci kallonta,sannan ya zauna ya gaida Umma itama ta gaisheshi ya amsa yana wani daddakewa.Umma tace kunje kun gaida Modibbo kuwa?Yace,a%??i sai da dare,Bily tace inaso ma inje in gaishe da kakata, itama ta danyi fama da ciwon kafa, Umma tace shikenan ai saiku wuce gaba daya,ya mike ya fita.Yinin ranar jinsa yake tamkar wani sabon ango,ya dade yana son ganin ranar da Bily zata amsa gayyatarsa wato ya kusance ta tana so batayi masa tamkar gunki ba,sannan wani abu daya tsaya masa cikin rai shine,yana jin ta fiye da duk matan daya bi duk da kasancewarsu farar fata bai ma san yanda zai kwatanta ta ba.matsalar daya ba wai yana sonta bane,amma banda haka ko ta ina tayi fiye da zatonsa, yana jin zai iya zama da ita tunda shi so ba matsalarsa bane,nasa ganin ma inka dauke son Allah da Manzonsa da son abu tamkar kaga kaya kowani abincin haka kace ina son kaza ka siya to bai yarda da wai soyayya ba.nasa ganin mace da namiji ba wai suna son junansu don komai bane sai don sha%??iwar su biya ma kansu bukata,amma game da wancan son bai sansa ba,daren ranar ta shirya cikin atamfa super ta dora after dress ta nufi dakinsa yana sanye da shadda mairuwan siminti,tana ta sheki yayi kyau,tace kafi kyau cikin dogayen kaya,yace ni kuma damuna sukeyi ya dubi shigarta,nifa duk irin kayan nan basa birgeni, nafi son wadanda zaki fito a beauty dinki,amma zamu shiga kasuwa in saya miki,tayi murmushi ta dubi kanta kana nufin banyi kyau ba?Yace,a%??i ke kullum kina da kyau ai dan ke mai kyau ce muje ko? Cikin mota suna tafiya yana tuki jefi-jefi kuma idanunsa suna sha%??iwar kallonta,tace wash!Ya dubeta yaya ne?Tayi kasa da murya ina jin bacci ne,yace kwanta mana,ga mamakinsa sai kurum yajita acinyarsa,nan take kan motar yaso ya kufce masa domin ba kwanciyar kawai tayi ba,sai data kai hannunta wata jihar cikin salo,da sauri ya tsaya gefen titi ya dubeta,kina son mu f???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?adi ko? Tayi dariya,sannan suka dau hanya tace,haka zamuje babu tsaraba?Don haka suka shiga wani super market suka yi shopping Gurin Umma suka soma zuwa,haka kawai yaji tsohuwar ta masa, musamman yanda tayi ta yi ma Bily nasiha kan cewa tayi masa biyayya, shiko ga son girma sai kace gyambo,ya tsani Bily ta nuna ita sa%??irsa ce, daga karshe tayi ta shi musu albarka suka fita suka nufi gurin Modibbo ya samu sauki sai dai jikin girma,nan yaji dadin ganinsu. Ya musu nasiha sosai ya kuma jaddada ma Bily tayi hakuri da mijinta sannan tayi biyayya,don haka suna mota yake cewa,kin dai ji ko%??ina ana cewa kimin biyayya,amma ke sai ki dinga nuna kin ma girmeni, tace to da gaske dai ai kasan na girme ka fa yasa bayan hannu babu xato ya buge mata baki ta rike bakinta da hannunta shi kuma ya daure fuska har suka je gida bai kuma ce mata kala ba.Bayan sun isa gida ta dubesa yana sauri ya fita daga motar ta rike masa hannu,sorry nasan kai ne babba don Allah kada kayi fushi kaji mijina?Fita kawai yayi sannan itama ta fito,ta kofar da kai tsaye zata kaisu sasansu suka shiga gida,da kyar ta shawo kansa sannan ta nufi gurinsu Umma ta shaida musu sun dawo, tare da sanar dasu cewa duk suna gaishesu.Cikin satin banda soyewa basa komai,yanzu Yarima bashi da matsala game da mace, domin duk sanda yazo da bukata bata nuna ta gaji,duk kuwa da cewa tana karfin hali ne dan kuwa Yarima namiji ne ba kadan ba Koda sukayi waya da Mansu ta yiwa Mansu complain na cewa Yarima ya like mata tana daurewa ne kawai,Mansu tace ki cigaba har ki saba,sannan idan zamu zo bikinsu Magaji zan zo miki da wani magani in kina amfani dashi kema zaki daina saurin gajiya, yanzun amma baya waya da %??ianmatan nasa ko?Bily tace,tabdi!Yanayi,sai dai ina yin dabara ina kashe wayoyin nasa tun daga ranar da muna tare amma ya amsa wayar wata shegiyar muna kwance fa,wai danayi magana sai ya nuna yafi ni fushi da kyar ma na shawo kansa,tun daga nan dana kula hankalinsa ya soma nisa sai in kashesu.Mansu tace ki dai dage kuma ki daure zanzo miki da wasu sinadaran,Bily tace,to sai kinzo.
[6:37AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 74??}_

Yarima ya gama komai game da course din nasa,wanda zaiyi Beverly Hills ta kasar America zaiyi course din ne akan gyaran fata,wato(plastic surgery)don yaga cewa bamu da wadannan likitocin anan gida,sai dai ya saita tafiyar tasane bayan bikin amininsa wato Magaji. Zaman Yarima da Bily su kansu yana musu dadi,duk da hakuri kawai takeyi da halinsa na saurin fushi da isa da kuma jin kai,sai dai tana kokari taga ta kauce ma duk wani abu da zaisa suyi sabani,tun daga ranar da suka soma kwana guri daya har yau babu wanda ya kuma tunanin kwana shi kadai,domin hakan yana sasu farin ciki.Daren yau saura kwana shida bikinsu Magaji,Yarima babu zama yi nan yi can,yau ita kuma Bily duk bata jin dadi sai dai tana sharewa ne domin ta fahimci tana da shigar ciki,wanda shi kuma Yarima ba ra%??iyinsa kenan ba, in har ya sani zasu yi rigima ne.ta shigo falon Yarima yana zaune yana duba sauran katunan wadanda ba%??i kaisu ga masu su ba,tace sannu da hutawa abokin ango,ya dubeta sai ya ajiye katin, zo kiji,ta isa gurinsa kin kara kyau yau sai dai yaya naji dumin jikinki yafi na kullum?Tace,ko, ya kuma mannata ajikinsa ko kina zazzabi ne? Tace a%??i kalau nake,ya dubi fuskarta muje in sai miki kaya irin na gayu ko?Tace muje to.Wani katon Boutique suka shiga,sam Bily bata ga abinda ya burgeta ba cikin boutique din,shi ko Yarima sai jidar kayan yakeyi yana ayyana yanda zai gansu ajikinta,suka koma gefen takalma nan ma ya diba haka aka biyo su da kayan ledoji cikin mota,takaici ya cikata babu halin ta nuna yanzun nan ya hau fushi sai dai tana ganin an kusa jin kansu indai ita yake nufi tasa kayan nan.bayan sun iso gida da zumudinsa yace ta gwada kayan,duk wanda ta dago sai ta gansa bingil daga siket din har wandunan rigunan kuwa daga mai hannu daya sai mai hannun singileti,sai wadda sam bata ma da hannu Ta dubesa wai kana nufin ni sZan saka wadannan kayan?Ya murtuke fuska bansani ba,tunda ina da wata matar ne bayan ke?Don rainin wayo zakice ina nufin ke zaki sa?Tace tsaya kaji abin bana fada bane, bazan iya sa kayan nan ba,saboda ka duba gidannan gidane na jama%??i haushi ya turnuke sa yace me ya hana ki sanar dani tun a can,sai da nayi asarar kudina, dakin sani tunda mukaje sai kice kai nifa bazan sa ba, sai kika barni na siya sannan don kin raina min wayo yanzu kice bazaki sa ba,ta tausa murya baka fahimceni bane mijina,nifa saboda mutane ne? Yace to gurinmu da akwai mutane ne?Gaya min wanda yake shigowa nan gefen?Tace masu aiki zuwa su jakadiya,kaga bai dace ba,ransa ya sake baci afusace ya dubeta, shin wai ke harma kin isa mu tsaya ja-in-ja dake?To bari in sanar dake,nine wanda %??ianmata suke son in nuna ina son kaya su sa kudinsu su siya don in gani a jikinsu inji dadi.ya mike tsaye yaci gaba da cewa,amma ke ko baki da burin daya wuce kiga raina na baci,ban san bacin rai ba sai dana hadu dake,please kwashe kayan nan kibar min dakin tun kafin ranki ya kai ga baci,in ma zaki kona ne jeki kona,ke kin gama rainani kin maidani tsaranki,tunda mu sa%??innin junane koba haka kike cewa ba?Zata sake yin magana yace,fita nace banason jin muryarki. haka ta kwashe kayan ta fita jikinta a sanyaye,shi kuma ransa bace ganinsa ta maidashi mara tunani karamin yaro tunda bai aunaba ya sayi kayan.lokacin kwanciya yanayi tayi shiri ta nufi dakinsa tana zuwa cikin dar-dar baya falo ta shiga bedroom tana shiga yana fitowa daga wanka,wani kallo ya watso mata tareda daga murya gurin cewa me kuma ya kawoki dakina? Sai data zabura sannan tace,yi hakuri ta daure ta nufosa kawona goge maka jikink..fita nace,bana bukatarki babu wata mace data isa in saurareta matsawar bazata min yanda nake so ba,matan waje ma suna min biyayya ballatana matar aurena,wallahi nina sani mata da yawa da zasu samu in auresu ko tsirara nace ina son su min yawo cikin gidana sunsan yanda zasuyi,don haka fita kawai kin bata min rai sannan ynzu kin wani debo jiki dan gani jarababbe ko?
[6:39AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 75??}_

To ki sani kwanciyar hankali ce take sawa ayi komai,haka Bily ta koma daki ta fada kan gado lallai ta tsokano,shima Yarima koda ya kwanta sai yaji daban,cikin %??ian satukan sun shaku da juna musamman gurin kwanciya.Bily ta mirgina ta janyo filo ta dora akan kirjinta,kewar mijinta ce fal aranta,shima daidai wannan lokacin duk da ransa ya baci amma jikinsa yana maraicinta, hakan zuciyarsa zogi takeyi harma ya soma tunanin ko dai ya dauki waya ya kirata ne?Ya tashi ya zauna tsakiyar gado,ba wai sha%??iwar tace ta hana masa bacci ba,a%??i zuciyarsa ce daga can kasa take tsananin son ta ganta.ya janyo waya zai kirata sai wata zuciyar ta soma cewa,shin ka yarda ka zubar da ajinka ka kirata?Tayi ma laifi fa?Kuma kaine ka koreta in harka kirata gobe zata iya maka abinda yafi haka tunda tasan ba zaka jure ba zaka sake kiranta.tsaki yayi sannan ya jefar da wayar kan gado,itama duk ta damu sai tana ganin cewa in har biyayyar zatayi me zai hana tayin yanda Yarima ke so, wannan duk laifinta ne yau gata zata kwana ita daya,tana kewar kamshin Yarima ,ranar ko an tafka ruwan sama haka suka kwana jin sanyi duk da bargo da kowannansu ya shiga sannan babu wani bacci sai juye-juye.Oh! Allah shin me yasa suka damu da juna haka?Da safe bayan Bily tayi wanka,nan ta soma daddaga kayan taga wanne ne ya dan fi dama-dama,tasa dan taje bandaki,shi ko Yarima kosawa yayi lokacin zuwa gaida Umma yayi don yaje gaisheta ko zai ga Bilyn,don zuciyarsa ta daina zugi.Bily koda kyar ta samu wani siket gashi dai har kasa dogo sai dai tsagu tun daga kasa har cinya,sannan rigar bata rufe cibiya ba,kuma daga sama duk kirjinta waje,sannan kuma baya ma kusan rabi awaje ta sama,haka dai ta daure ta saka tare da sa takalmi daya daga ciki mara tudu sosai,hijabi ta dora sannan ta fito,amma kafin ta saka hijabin sai data kalli kanta a madubi tace oh,dubeni sai kace %??iar iska,ko irin %??ian good evening din nan Tana shigowa falonsa na kasa shi kuma yana sakkowa, zogin da zuciyarsa keyi sai ya tsaya cak,wani sanyi yaji yayinda ya ganta tamkar ya ruga ya rungumeta sai wata zuciyar tace masa yana sai ka nuna mata ka damu?Nan take ya dake sannan yayi nufin fita,da sauri tasha gabansa sannan ta cire hijabin,wani dadi ya rufesa amma sai yasha mur,tace me zaisa ka daure,kalli fa banyi kyau ba ne?Ya kalli kwayar idanunta masu hanasa yayi mata gaddama,yace Beauty kina son ki bani wahala me yasa ko yaushe burinki raina ya baci?In zaki min adalci nima fa dole aka min kamar yanda kema aka miki,amma bana son in matsa miki ke ko kinfi son ki ta bata min.ta dubi fuskarsa na daina duk abinda kake so shi zanyi,yayi ajiyar zuciya sannan yajata zuwa kirjinsa, sai yaji tamkar sun shekara basuga juna bane,harma baisan lokacin da yace I miss you ba,sai dai yaji tace me too Nan suka manne juna,ji suke tamkar su shige cikin juna,ko saboda menene?Oho!Bayaji su kansu sun san dalili.Nan suka nufi falonsa suna manne da juna,sai gashi ranar tare suka karya, har ma Yarima yana tunani aransa cewa dama cin abinci da mace haka yake da birgewa?Duk sanda zaisa abinci a baki sai ya kalli idanun nan nata masu narkar masa da zuciya,tana murmushinta dake kara mishi sanyi cikin zuciya,koda aka jima sai ma ya barcin abincin bai san ya zuba tagumi yana kallonta ba.a zuciyarsa son yake ya gano shinme yasa ita wannan ta fita daban cikin duk matan da yayi harka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0