Showing 30001 words to 33000 words out of 79064 words

Chapter 11 - Meke Faruwa Book Compelet

martaba ya noke hannunsa suka gaisa.Modibbo yace,kai da nace zanzo?Mai martaba yace,Allah gafarta nine yakamata nazo donni danka ne.Modibbo yace,to amma kuma ai kai shugaba ne.Mai martaba yayi murmushi yace,amma Allah gafarta Malam,maganarmu bata shafi mulki ba,don haka in an bar batun mulki an dawo gida ni da ne,kuma duk da nagari dole ne yabi iyayensa Murmushi Modibbo yayi,yasan gaskiya ce mai martaba ya fada.Don haka kai tsaye yaje da fadin dalilin son haduwar tasu game da zancen takwarana ne yace Malam Shehu yazo min da sakamakon binciken dana sa shi.Yaci gaba,Malam Shehu Almajirina ne tunda dadewa,shi dan Zaria ne musamman nasa aka kira minshi awaya na sakasa yayo min bincike menene asalin Bilkisu?Kuma naji komai game da duk wani abu da shari%??i ta nema asali ga mace,sai dai yarinyar ba masu hali bane yace sai muce Alhamdulillah ,don haka sai atashi %??ian neman aure su tafi.Mai martaba yace,to Alhamdulillah, talauci kam sam ba abu bane da zai hana aure ina son zan tura Fadawa zuwa ga mai martaba sarkin Zaria,daga nan sai su nemi dagacin ko hakimin unguwarsu sannan kuma shi sai ya nemi mahaifinta.Modibbo yace,to,Allah ya shige mana gaba,zamu taya ku da addu%??i.Kwana uku da wannan magana,mai martaba ya tashi Fadawa da sako zuwa Zaria.Sun samu tarba ta karamci irin na Zage-zagin asali.Sannan suka sanar da sakon mai martaba nan mai martaba yaji dadin wannan batu,sannan yasa aka nemo masa dagacin yankin,ya umarcesa daya nemi mai unguwar Ojo suzo fada gobe.Washegari suka amsa kiran sarki,nan yayi musu bayani,sannan akace su nemo Malam Mamman mai rini,suna dawowa mai unguwa yasa akira masa Malam Mamman.Sakon ya samesa lokacin yana zugama Mamanmu rashin mutuncin nasa,yana cewa karuwancin ya isheshi haka,dole yana son Bily ta dawo gida ya gaji,kilama shi yana tafiya mutane suna nunasa bai sani ba.Shiru ta masa yayinda su Kariman da suka zugosa,suka hada dan dandali suna shewar dariya.Cikin haka ne aka kwada sallama,baiji ba yana sababi sai da aka sake sannan ya shuri takalminsa ya nufi hanyar waje,yana cewa ai wannan yarinyar da haihuwarta gara barinta.Yarinya ta balaga ta balage min agida ta zamar min kaya?Daidai nan ya isa kofar gida,ya mika ma dan sakon me unguwa hannu suka gaisa,dan sakon ya shaida masa cewa mai unguwa yana nemansa.Malam Mamman yace,lafiya dai ko?Lafiya lau,yace dai muzo tare.Suka rankaya gidan mai unguwa.Gefen tabarma suka zauna yayi gaisuwa,mai unguwa yace,Malam Mamman ka samu sakona ko? Mamman yace,kwarai,shine ma dalilin zuwana
[8:48AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 34??}_

20-Mai unguwa yace,to nima hakimi ne yayo min aike naje,shine yace lallai muzo tare da kai.Idanun Malam Mamman ya shiga zarewa tare da cewa mai girma hakimi kuma ranka ya dade?Mai unguwa yace ,shi don haka yanzu sai kaje ka shirya mu tafi.Jikin Malam Mamman yayi sanyi,yace cikin in-ina,badai wani abu nayi ba ko?Ranka ya dade nifa ko hakimi ma ban sansa ba.Mai unguwa yace,to ina zaton dai kan %??iar wajenka ce ko Bilkisu ne sunanta?Sai dai munje kaji saboda shima hakimi ina zaton sakon daga samane,can gurin mai martaba sarki,don haka kaje ka canza tufafi.Jiki yana rawa ya nufo gida,yana tafe yana surutai ni wannan yarinya ta zame min bala%??i,ni in za%??i kasheni banace ga kamannin dagaci ba,amma yau sanadin wannan %??iar iskar yarinyar gani wai har gaban sarki zanje,ko wane bala%??in ta jono min?Oho!,yanzu haka labarin karuwancin nata ne yaje kunnansu.Daidai nan ya shiga gida yana tsaki,matan suna gindin murhu suka dubesa har suna hada baki,lafiya malam?Yace ina fa lafiya,waccan %??iar iskar taja min wai yanzun gidan sarki ake nemana.Suka ce,wace?Yace,Bilkisu mana.Mamanmu dake daki ta jiyo,don haka da sauri tayo waje don jin me Bily taja masa?Ta fito daidai sanda yake cewa kurum zataja min fitina,yanzu haka ma sunji labarin gantalin da takeyi ne shine aka kirani ahukunta ni.Ladiyo tace,a%??i karka yarda malam,ai ba kaine ke karuwancin ba itace ko kaje karka yarda acutar dakai.Salame tace,ko ko sunji har yau ba a mata aure ba ba.Karima ko cewa tayi,nidai da zakaji tawa,da ka ki zuwa saboda ina tsoron kadasu daure ka ba da hakkinka ba,in haka ta faru mu aka cuta masu kananan yara.Ladiyo tace hakane,ya shiga dakin Salame yanasa kaya,yana cewa, wa zaiki zuwa kiran sarakai?Ai sai azo da dogarawa akamaka.Daya fito ya kalli gurin da Mamanmu take,ki shirya kayanki,domin inna dawo da wani cin zarafin kema zaki samu naki rabon.Ya fita nan Salame ta yafa mayafi ta shiga sashen Gwoggo tana hawayen gulma,wai anzo daga gidan sarki an tafi da malam saboda Bily,yawon banzan da take yi yaje kunnansu.Budar bakin Gwaggo sai tace,babu kaico,na mayi murna ga bokon nan,ni nasan dama haka za%??iyi.Ta soma masifa da cewa,ni dai abar min dana suzo su kama uwarta don itace ta tsaya mata.Kafin kice haka,labari duk ya kaima sauran sassan,nan da nan gidan ya cika,sassansu Mamanmu suka dungumo inda take zaune bakin gado cikin daki,ta hada kai da gwiwa.Hankalinta atashe,tasan wani sabon sharrinne za%??i kagawa Bily.Masifar Gwaggo ce ta sakata kuka,tana dai ciki bata fito ba,kowa yana ta fadin albarkacin bakinsa,sai tsinuwa tareda zagi suke yiwa Bily wadda bata san hawa ba bata kuma san sauka ba.Suna isa gidan hakimi,babu bata lokaci suka tafi gidan sarki cikin motar hakimin,anyi musu iso suka shiga duk jikin Mamman yayi sanyi,yana dai binsu ne.A zuciyarsa yana Allah ya isa tsakaninsa da Bily.Suka zube sukayi gaisuwa cikin magana irinta manya sarki ya soma bayani,da farko yace ina mahaifin yarinyar?Hakimi ya nuna shi tare da cewa,gashi nan ranka ya dade.Mamman kamar yace bashi bane,sai dai yasan ba%??i katsalandan afada,don haka yayi shiru,sarki ya gabatar da maneman auren Bily,daga masarautar Bauchi.Idanu ya zaro yana kallonsu,nan suka gabatarda bukatarsu,jiki yana rawa Mamman yace,a-an baku.To hakane ai ba komai,hakimi yace,ka nutsu Mamman.Suka bukaci afadi sadaki,Mamman yace,ni dai na bar komai gurinka hakimi,duk yanda kukayi ni me biyayyane,ko sadaka ne ai zan bada ita kunfi karfin wannan ranka shi dade.Nan dai hakimi yace su bada dubu dari,Allah ya sakama abin albarka.Sarki ne ya bada sadakin,yace tasa gudunmuwar.Sun gabatarda kayan na gani ina so,akwati biyar,ga na uwa dana uba,uku-uku ga kuma wani seti can guda hudu,suka soma bayani kansu,wannan sune kayan da zata koma sawa yayin tsareta ga al%??idar gidan sarauta in dan sarki zai auri yarda bata shafi sarauta ba.Ana boye ta na tsawon wata biyu,babu wanda zai ganta sai Yarima,sai ko shakikanta.Sannan zata daina amfani da duk kayanta sai wannan,wayar hannunta za%??i karba abata wannan Yarima ne kawai zai dinga kiranta,sannan tunda an bada sadakinta,ynzu mune ci da shanta.
yanzun mune ci da shanta har ayi auren. Don haka a kiyaye, kuna da gurin boyeta ne ko mu bada gida! Mai martba yace, ni zan bada guri tare da masu mata hidima har zuwa auren. Hakimi ya matso kusa da mallam mamman yace,to sai zancan tukuici, ana fa badawa. Mlm mamman yace. To.To!Ni me zan ba su? Sai dai sadakin. Hakimi yace Aa,sadaki hakkin yarinya ne.kawai sai suka ji sarkin mai adalci yana cewa a rubuta musu check na dubu dari biyu a buga sterm suje su amsa. in takaita,nan dai suka shirga kaya cike da mota sannan aka kwaso da sharadin cewa gobe za azo a tafi da Bilkisu, ko in ce anuna musu gidan Bilki. Kuji wani lamari.suna isa gidan har yanzu cike yake da yan jaje,don bayan yan sassa har makota sun shigo.
sai dai suka ji tsayiwar motoci, sannan sai ga Dogarawa suna shiga da akwatuna, jiki yana bari yasa aka shimfida katuwar tabarma aka soma Jere kaya seti- seti, nan mutane suka shiga kallon- kallo kowa yana son jin Karin bayani. Mlm mamman babu baka sai yake yi. Ya Ciro kudi ya ba Dogarai yana godiya suka tafi suna mishi murna, lallai ya iya haihuwa, sun so suga wannan yar tashi suga ya ya take?

Shi ko nan jama'a suka yo kanshi, uwarshi ta soma da cewa mamman me ka je yi gidan sarki, wannan kayan fa? Cike da doki yace, Goggo ai arziki ne ya kira ni. Ya shiga raba idon ina zai gano Mamanmu cikin matan dake gurin amma bai ganta ba, sai yace INA Fatima ne? Fatima ki zo ga ikon Allah. Tana tsaye daga kofar dakinta amma bata ko kalle shi ba. Ya ce Goggo daga Masarautar Bauchi ake son Bilkisu. Yasa hannu cikin aljihu,ga sadakinta dubu Dari cif haka ya dinga nuna komai yana washe baki jiki yana rawa sai kace a wasan kwaikwayo,

Makota suna ta sambarka yayinda matan gidan suka shiga zare idanu.gwaggo kuwa ko kunya, murna ta shiga yi tana cewa lallai mun haye, sai godiya. Karima tace, ka ko ji da kyau? Salame tace shi ne dai anya ma kuwa zancan nan gaskiya ne? Ladiyo kam kasa magana tayi.
[8:48AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 35??}_

Mamanmu cewa tayi.
Mlm gaskiya ban yarda da wannan zancan ba,in dai ka saida ita ne ka sanar dani, don nasan dama neman yanda zaka rabu da ita ka ke yi, don haka ni bana neman kai da ita,haka kawai bata ga mutum ba bai ganta ba ace an biya sadakin ta naira dubu dari? To ban yarda ba ka ji na ma gaya maka tun wuri ka maida musu kudinsu.

Ya zaburo ke Fatima ahir dinki, 'yarki CE ko ko 'yata? Dama ina neman wanda zan ba na rasa sai kuma gashi an zo nema har gida? Daina wannan zance, to ni ina ruwana da wani suga juna? In anyi auren sun ga junan. Gwaggo tace, kai barta me kashin tsiya,in bata yarda ba fasawa za'ayi? Kwaso kayan ina yara kai Ku kira almajirai,. Sukai can sassan gwaggo amarya, ita kuwa gwaggon sasa cewa tayi, haba Amarya komai fa yana son bincike, Ku bari a bincika a ga wanene duniya fa ta lalace, da masifa gwaggo Amarya tace, ke rufe min baki bana son bakin ciki, idan jikarki ce ai ba za ki ce ayi bincike ba, binciken banza? Allah ma ya hana bincike. Gwaggo sasa tace Allah sarki, ni na San in dai mutumin kirki ne ni na ma fiki murna, kema ganin kudi ne ya gama zagin yar da uwarta? Tasa kai ta fita a sasan,
Mamanmu tace, lallai yanzu ne kasan yarka ko?Ni dai naga yanda za ayi wannan aure.Yace,Oho kya ja da sarakai,danni na riga na amshi sadaki,gara ma kiyi mata waya tazo don gobe zasu zo su tafi da ita.Salame tace,to ko dai har an daura auren ne?Ya fita yana cewa,ke kuma ina ruwanki? Sarakan bakin ciki! Salame tace,ai yau kuma mune yan bakin ciki.?Yace,eh ku ne mana.tamkar wani zautacce ya fita yana cewa,bari in kira yara su kwashe kayan sukai sasanki gwaggo,kada cikin dare a kunna musu wuta.mutane duk suka tafi suna cewa,ko dai mutumin nan ya saida yarsa ne,tunda dama ba sonta yake yi ba?Wasu kuma suna cewa,Aa gaske ne zai aurar da ita ne ga sarakuna don yaga kudi,kilan dai tsoho ne mijin su ko su gwaggo karima da salame da ladiyo dakin ladiyo suka shige suna jajanta ma juna tare da neman mafita. Ladiyo tace,ni duk ji nake yi ma duk zazzabi ya rufe ni, wato mlman nan kudinmu suka yi taci basa komai?Karima tace A'a dan yifa aiki yayi, tunda ai babu saurayin da ke kula tan kamar yanda muka bukata Amma sai dai muce yanzu dai aikin ya baci an samu akasi,ai bamu makaraba,sai muje a wargaza al'amarin.Salame tace. To ko cikon kudin nan ne da bamu bashi ba yaki mana aikin?Nan take suka yarda cewa haka ne,kuma suka yanke shawarar cewa zasu je goben nan. Dan ma kada su fita yau nd a gane dama gashi lokaci daya mlm ya canza har dayi musu habaici.ta ajiye hijabin sannan ta koma ta zauna tunani yasha kanta.Ta rasa wa zata tunkara.Zaraf ta mike tace bari naje gidan Umman mansura. Mamanmu tayi sallama a gidan,ta shigo daidai sanda umman mansura ta ajiye hijabinta tare da amsawa.ta fito taga mamanmu,tace,Aa dama ke ce?Shigo nima yanzun nan nake cewa kwana biyu ba mu gaisa ba,da safe in zan je aiki zan biya.Mamanmu tace,uhum!Ke dai bari, nima yanzun zuwa nayi ki kira min maigado,kira min lambarta.Umman mansura tace,lafiya? Mama tace,ina fa lfy, babansu ne da rikicinshi kin dai san halinshi, wannan karon kuma dazun fa ina zaune da rana ya same ni cikin daki,wai shi ya gaji da ganin maigado tana yawon karuwanci Yarinya ta zama annoba,menene wanene?Ta inda yake shiga bata nan yake fita ba.Can aka yi sallama dashi yana dawowa kuma sai cewa yayi in hada kayana,gashi nan an aiko nemanshi daga gidan sarki,wai suma sun ji labarin gantalin da maigado take yi. Yana dawowa zanga cin zarafi.to in dai takaita miki umman mansura, yana dawowa sai gashi da kaya niki-niki da kudin masu yawa wai sadakin maigado ne, akwatuna kashi-kashi, wlh ni sai ma tsoro ya kama ni,na soma tunanin ko dai ya saida ta ne tunda nasan baya kaunarta?Umman mansura tace,ikon Allah to a ina ya samo mata mijin?Mamanmu tace. Oho,ni ko sauraron shi ma ban yi ba,kila ma sun daura auren ne don naji yana cewa wai gobe zasu zo su tafi da ita. Umma tace,Ikon Allah. Ina zuwa bari in kira Abban su mansura muje mu same shi a ji kan zancen.amma ai ba akira Bilkisu yanzun ba a ruda ta,gashi kin san ta bata iya rudewa ba.yana gida ko?Mamanmu tace, yana nan kofar gida ya tara makota da yan uwansa mazan sai lbrin yake basu,sai ka ce wani zararre.. Umma tace,kije gida in anyi sallar isha'i zamu zo yanzun insha Allah. Mlm Mamman ko ana idar da sallar isha'i ya shigo dakin mamanmu tana zaune kan abin sallah,tayi tagumi ya zauna yana 'yar dariya. Abin al'ajabi wai yau malam ne yake min fara'a cikin zuciyar mama kenan take sakawa.yace fatima cire tagumi ai kin daina tagumi,ki kwantar da hankalinki muyi magana,sallamar umman mansura ne ya tsaida shi ya amsa tare da cewa,ku shigo.Tace yauwa kana ciki ba? Nima ni da maigidan ne dama gurinka muka zo, yace bismillah ku shigo, shimfida tabarma fatima. Umma tace bari in kira shi to. Sun zauna bayan gaishe-gaishe,sannan Abbansu mansura ya soma da cewa,mlm mamman,mai dakinka ce tazo mana da wani batu na game da yarinyar nan Bilkisu,shin me yake faruwa ne?Mlm mamman ya gyara zama,ya shiga rattafo musu yanda abin ya faru,daki-daki.cikin jin dadin shi gashi lbrin baya gundirar shi,hakan baya gajiya daba lbrn. Babu wanda ya katse shi sai da ya kai aya. Abban su mansura yayi gyaran murya sannan yace Maman Bilkisu in dai abin da ya fada haka ne, to wannan abin farin ciki ne da murna, ki kwantar da hankalinki, zan yi waya gidan su mansura yanzu, kuma zan sa a darennan shi mijin mansuran ya bincika min ta hanyar buga waya mu ji gaskiya lamarin, tunda ai Yariman da ake magana kani ne a gurinsa, dole zai San komai, mlm mamman yace, ita dai ta sani ni fa na riga na bada 'ya, ke ko dan wa'yancan sakarkarun matan masu nuna bakin ciki ba kya ware asha daula ba. Mamanmu ta ce, kai dai ka sani kun fi kusa da su. A yau ne kasan sakarkaru ne? Umman mansura dariya ma ya bata,a ranta tace, namiji kenan.

Lalubawar farko Abba ya samu farooq, lokacin yana kwance ya dora 'yar bebynsu sa'adatu a kirji, Mansura ta saka kanta a cinyoyinshi, ya dauki wayar ya duba.yace, kai Abba ne ya tashi zaune tare da dora babyn akan katifa, yace salamu alaikum, Abba ina yini? Suka gaisa. Abba yace, kana da lbrin Yarima dan uwanka zai yi aure? Farooq yace Aa ai baya nan ma.Abba yace, to yi waya ka min bincike yanzu-yanzu, farooq yace, to Mansura da ta tsura mishi idanu tace, meyace? Ya daga mata hannu, inda zuwa, layin magajin Malam ya nema yasan shi ne zai San komai, bayan sun gaisa ya ce magaji shin gaske ne Yarima zai yi aure? Magajin Malam yace, haka ne, har ma an bashi matar a Zaria, kawar matar ka ko? Cike da mamaki yace, Oh dama Bilkisu CE? Magajin Malam yace ita CE mana, yanzu haka an biya sadaki farooq yace, Yarima ya sani? Aa in ji magaji, bai ma san za ai masa aure ba, kuma mai martaba yace kada a sanar dashi. Farooq yace shi kenan, mun gode. Ya kira Abban Mansura yace eh Abba zai yi aure wai Bilkisu ce ma, Abba yace, to shikenan, ina so tunda gobe Sunday kana gida ka zo min da Bilkisun, amma kada kace mata komai ko ta sani? Farooq yace Aa yace kar ka sanar da ita sai kun zo. Ya kashe wayar.....
[8:48AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 36??}_

Cike da mamaki farooq ya zuba ma waya idanu, Mansura a tsorace ta zaro idanu itama, tana kallon shi tare da cewa, wai menene Baban dady? Ya yi ajiyar zuciya sannan ya ce wai Yarima ne zai yi aure. Ta dan ja tsaki, to in Yarima zai yi aure me ya kawo Abba ciki? Ni wlh har na tsorata, zatona babu lfy ne,.Yace. Aa to kin San wadda Yariman zai aura ne? Ta sake zaro idanu tace wa? Yace Bilkisunki ta nan gidan.. Mansura ta mike Bil..... Wa? Yace, Bilkisu. Ta kuma dafa kirji in ji wa? Yace, gashi yanzun na kira magajin Malam ya tabbatar min har an biya sadaki! Sai dai wata tsiyar, shima Yariman bai sani ba, yanzun haka bai ma San za ai masa aure ba, itama nan gashi bata sani ba. Amma Abbanku yace gobe muje kada ki nuna mata kin San komai. Mansura taja tsaki, gaskiya ban so mata Auren Yariman nan mai zafin kai ba, farooq yace, ni ko na mata murna, domin Yarima yana da halin girma irin na gadon gidan su abin da ya faru tsakaninsu wannan shedanne . da zaran sun zauna zama na Auren sunna za su sasanta Kansu, kuma za ya kula da ita. Mansu tace, Allah yasa.

Su ko a nan zariya, Abba ya tabbatar ma da Mamanmu cewa batun aure gaskiya ne haka ne. Ya kara kwantar mata da hankali su da Umman mansura. Sun tafi kan cewa sai gobe in Bilkisu tazo zai zo a fito da kaya a duba.

***************************
Wayarsa ta soma ruri,Chelen ta mike ta dauko masa wayar,yana ganin number Magaji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0