Showing 75001 words to 78000 words out of 79064 words

Chapter 26 - MEKE FARUWA BOOK COMPLETE BY HALIMA K. MASHI.doc

tace ni ban sani ba bata nan ne?Yace a'a na zaci tazo ne ya fita,gidan Umma ya nufa yana tafe yana neman layinta amma a kashe,bayan sun gaisa sai yace shin ko Bily ta iso?Umma tace ta nufo nan ne?Yace dana ce tazo ne ina zuwa kila tana gida ya fita duk inda yasan Bily tasansu sai da yaje har magariba ta shigo ya dawo gida ta gurinsu Umma ya shigo tana sallah son ma yana ta binta sallar.ya fita ya nufi sasansu,ya daure ya watsa ruwa sannan yayi sallah ya ci gaba da neman layinta shiru sannan ya kira Magaji bai boye ma Magaji komai ba,Magaji yace shikenan gaskiyarta ne tunda ta tafi ba sai ka huta ba? Haushi ya kama sa yace haba Magaji na kiraka ne fa don ka taimaka min yanda zan bulloma al%??imarin ka kuma dauko wata caftar, Magaji yace to in ba haka ba me zance?Yarima yayi shiru can yace da zan iya dana ce tayi tafiyarta amma na kasa ba zan iya ba, cewa fa tayi wai in sake ta? Magaji yace ka saketan mana to yaja tsaki,sannan ya nuna ma Magaji kofar fita,fita baka da amfani,Magaji ya mike ya fita Yarima yabi shi da kallo. Bacci ranar sai dai barawo amma kasa bacci Yarima yayi,baya son su Umma susani amma dole ne suji,sai dai zai ce musu taje gaida iyayenta ne,to kuma zasu ce babu ko sallama?Haka yayi tayi ya saka ya kwance,har gari ya waye.Magaji daya koma gida sai ya kira layinta yaji sa akashe, washegari ya fito ya shiga gidan sasan Yarima ya shiga lokacin Yarima shima ya gama tunanin cewa dole ya koma gurin Magaji,domin shine yasan zaria, kai shi abin kunyar nasa ma yana da yawa shekara nawa shida matarsa bai san kowa nata ba sai wanda ya kawo kansa yanzu gashi zai je dalilin yana bukatar ta dawo?Magaji ne ya katse sa da cewa abokina yaya ne? Yarima ya dubesa mun tashi lafia?Lafia lau inji Magaji sukayi shiru can Yrm yace ko can gidan iyayanta zamuje? Magaji yace to sai muje,kaga kaima tunda yanzun tayi dalili sun san kai Yarima yace to sarkin sheri naji yanzun yaushe zamu tafi?Magaji yace ko yaushe,Yarima ya mike yace jeka shirya mu tafi.sun iso zaria misalin karfe biyun rana,unguwar suka shiga kai tsaye, kallon unguwar yakeyi yana mamakin dama beauty a irin wannan unguwar take?Duk da an ce iyayanta talakawa ne da za%??ibarsa inya iso(G.R.A)zai nufa nemanta,bai kara tsinkewa ba sai da suka tsaya akofar gidan,yace Magaji don Allah nan ne gidan iyayan beauty?Magaji yace tabbas Yarima yace,amma baka kyauta min ba da ka kasa sanar dani kamar ni ace surukaina suna cikin wannan gidan, ai samuna yazama na banza.Magaji yace lokacin gyaran ne baiyi ba shiyasa Allah bai horeni da sanar dakai ba amma yanzu ai kaga lokacin yayi tunda ance gani ya kori ji.suna fitowa daga mota Asma%??i tana fitowa daga gida,tace a%??i yaya Yrm sannunku da zuwa,Yrm cikin zumudi yace Asma%??i beauty tana ciki ko?Asma%??i tace wace antynmu?Yace eh,tace bata zo ba.Magaji yace babanku yana nan?Tace yana ciki,yace to shaida masa ga baki. Da sauri ta koma tace Mama ga yaya Yrm mijin anty,ta mike da sauri tace,to ina malam kirasa dakin Salame ta sanar dashi da sauri ya fito sai daya canza %??iar riga mai haske sannan ya fita wajen yayinda Umma ta shiga gyara gurin. malam ya shigo dasu Asma%??i ta fita siyo musu lemu mai sanyi.Yrm cikin tausayi yake kallon gidan hakama dakin,bayan sun gaisa Asma%??i ta kawo musu swan water mai sanyi da lemu,Yrm dai ruwan kawai yasha.Magaji ne ya gabatar da Yrm, sannan yace sun zo ne su duba ko Bily tazo gida,s saboda wata %??iar matsala da suka samu.Mama ta kalli malam shima ya kalleta sannan yace ikon Allah,amma ko daya ban zaci haka daga gurin Bily ba,domin yarinya ce mai hakuri,amma kunga bata zo nan ba,tun yaushe ne?Magaji yace jiya ne. Yarima ya cire hula saboda wata zufa data feso masa,a hankali ya furzar da wani huci mai zafi.sannan yace,ni babbar damuwata bata da isasshiyar lafia,to amma baba ba kuji anan din akwai inda zata?Malam yace kun duba cikin gidan Umman Bauchin kakarta?Magaji yace duk bata can,Mama ta nisa tace kun tuntubi Mansura?Duk da dai Mansu ma tana nan zaria,kila gidan Mansu taje.tunda kunce jiya ne ni kuma shekaranjiya Mansu tazo nan,nan aka hada su da Asma%??i zuwa gidan Mansu,sun samesu har Faruk dinma yasha mamakin ganin Yarima a gidansa.Mansu ta musu kyakkyawar tarba sai dai Yrm ya kasa cin komai domin baiga beautynsa a gidan ba,sannan bai tsaya kwauron baki ba ya shaida ma Faruk dalilin zuwansu.cikin mamaki Mansu tace,Bily tabar gidanka?Yace wallahi tun jiya babu inda banje ba,Mansu tace shiyasa na dinga neman layinta shiru?To ina Bily zata?Wai ma meya faru haka da zafi ne har ta saka kafa ta fita?Yrm yace gaskia laifina ne,na sani kedai kawai abar zancan sai in Allah yasa anganta.wasa-wasa har kwana uku,su Yarima sun koma gida,Magaji shine ya sanarda Umma komai, amma ya boye kama shi da wata ?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????da Bily tayi, ya dai ce Yarima ne ke cire mata ciki shine ta gaji ta gudu gashi kuma su anty Salma suna ganin laifinta. Hankalin Umma ya tashi ta shiga cewa dama nayi tunanin yarinyar nan bazata aikata wannan aikin ba.
[8:43AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 91??}_

Hankula sun tashi ana ta nemanta,ita ko tana can tana zamanta gidan Mansu na Kaduna,ta kashe wayarta,bata bukatar ji daga kowa kuma ba wanda hankalin sa yaje gurin.mai martaba daya samu labari ranar Yarima yaga bacin rai irin wanda bai taba gani ba,sannan mai martaba ya bashi kwana uku rak mazamaza ya nemo inda Bily ta shiga inko ba haka ba zaisa a tsare sa har sai an ganta.al%??imarin ya wuce duk yanda Yrm ya zata,domin wai don ma basu ji dayan ba.Waziri da Magaji sune suka roki mai martaba kan batun tsare Yarima,amma fa yayi fushi dashi sosai daidai da magana ta daina hadasu, ko Yrm ya gaisheshi baya amsawa.ranar data cika kwana goma cikin dare ta kunna wayarta,sakwanni tayi ta gani suna shigowa na Yrm ne,tayi ta delete bata karanta ba,amma nasu Mansu,Magaji,su Sakina da Maryam harda auta,kowa dai rokonta yakeyi ta dawo,hankula sun tashi Magaji har abinda mai martaba da Umma suke ma Yrm sai daya shaida mata sai taji dan sanyi cikin ranta damuwarta iyayanta,don haka sai ta tura ma Mansu text cewa tace suma su kwantar da hankalinsu tana nan lafia,sai dai bata Kaduna in lokaci yayi wato in Yrm ya saketa zata dawo ta tura sannan ta tura ma Yrm cewa,tana fa jiran sakon sakinta,tana tura masa ta kashe wayar. Lokacin da sakon ya shigo yana zaune kan sallaya ya idar da nafilfilun da suka zamar masa a madadin bacci yanzu,yana ta addu%??i%??i gani yake tunda iyayansa suna fushi dashi bama zai ganta ba,shi dama zasu barshi da zafi gami da radadin rashin ganinta domin yanzun da baya ganinta dinnan yafi kowa tashin hankali,ya yarda sonta ne ya kamashi tuntuni bai gane ba sai yanzun.ganin sako ya shigo da sauri ya dauki wayar yana dubawa,jiki na bari ya soma kiran layin a kashe.haka yayi ta kira har ya gaji,yanzun yama daina zuwa asibiti,kuma sai yanzun yayi kukan rashin Modibbo,yasan da yana nan da iyayansa ba zasuyi fushi dashi ba,yaji da batan masoyiyar tasa. Mansu sun wuce Gombe bayan Bily ta shaida mata cewa tana nan lafia lau,sai dai bazata sanarda ita inda take ba,wasa-wasa shiru har sai da aka kai dasa rokon Allah ko ta wane gefen,gurinsu Umma ne gurinsu Mamanmu ne Allah ya bayyanata,su Umma yanzun sun sassauta ma Yrm saboda ganin halin da yake ciki,duk ya sukurkuce jin cewa su Mansu sunzo Gombe ya nufi Gombe ko zai samu wani labari.Yrm da kansa ya zauna gaban Mansu yana shaida mata cewa alhakin Bily ne yake binsa,Allah ya jarabce sa da sonta,yace kalleni kiga yanda na dawo shin baki sami wani labari daga beauty ba? Tausayinsa ya cika Mansu,tace tayi min text cewa tana nan lafia,yace to ni dazan san inda take wallahi ko ina ne zanje kome zata min indai zata huce zan yarda,tana da hakuri,Mansu tace,ai tasha a nonon hakuri ne haka mahaifiyarta take ya gyara zama don Allah bani labarin beauty mana? Nan ko Mansu ta zauna ta zayyane masa komai,sai kawai taga hawaye yana bin kumatunsa,dama cikin mafarki Bily ta soma saninsa?Lallai aurensu hadin Allah ne,dama tasha wuya agidansu?Yanzunne ya gane taki zuwa gida ne saboda kada kishiyoyin Mamanta suyi mata dariya.lallai bai dace ya wulakanta Bily ba tun farko lallai ya mata laifi dayawa.Mansu tasha mamakin ganin Yrm yana kuka,mai saka mata kuka yau gashi yanayin kuka don mace lallai gara da Bily ta tafi gashi sanadin haka ansamu cigaba, domin su anty Salma ma mai martaba ya saba musu yace dasa hannunsu Bily ta bace,kuma yana fushi dasu bazai gushe ba sai sun roketa gafara.Faruk yazo kuma sun lallashi Yrm, daya dawo hankalinsa yace yana so ya taimaki iyayan Bily amma kada suce sai da %??iarsu ta bata,Mansu tace bazasu ce ba,shida Faruk da Magaji suka je zaria inda suka samu shahararren mai gini ya tsara musu yanda za%??i maida kafdin gidan kirar zamani ba tare da an shiga hakkin kowa ba,nan ya yarda da aikin yace kuma yana bukata cikin gaggawa Abu indai da kudi yanzun ne sai gashi cikin sati biyu an tsara guri,matan gida kuma duk sai kowa ta koma neman shiga gurin Mama,gefen su Mama yafi kyau ga kayan alatu daya zuba musu,ya saiwa malam wanda yanzun ya koma Alhaji Mamman tun shekarar da suka je makkah,katon shago yasa akayi daga waje ya cika masa da kayan masarufi na saidawa,sito kuma cike da abinci,lokacin Yrm gani yake koda zai karar da dukiyarsa bazaiji komai ba.su Ladiyo anga babu sarki sai Allah an hakura, domin dai nagaba yayi gaba wadda suka tsana yanzun arzikinta suke ci.hassadar da sukeyi baya suke ci ba gaba ba.Yau watansu Mansu guda da kwana goma tuni sun soma shirin komawa gida,don ma sun tsaya ne sunsha sunan Sumayya,ta haifi %??iarta mace,inda Yrm ya rada mata Bilkisu.sai da suka bita zaria sannan suka wuce,abinda Mansu ta rinka tunawa tana dariya a mota,lokacin da suka je yiwa Mama sallama,sai ta samu su Goggo amarya(kakarsu Bily)zaune a falon Mamanmu suna kallon TV.Ladiyo kuma an leko cikin falon tana cewa yaya gashi na fere miki doyar ai Goggo kuna kallo ne?Nima bari inzo in kallata. shima Faruk sai daya dara da Mansu ke bashi labari.abin al%??ijabi suna shiga farfajiyar gidansu sai taga motar Bily ta fito da sauri tana cewa abban dady ko dai nan gidan Bily tazo?San da suka shiga tana bacci kan kujera, gabanta kwalbar maltina ce da plate din farfesun kaji.duka Mansu ta dada mata tare da cewa,%??iar iskar nan dama kina nan?Bily ta tashi tana dariya tace,kash!Da nasan yau zaku dawo dana cigaba kafin kuzo,Mansu tace wannan %??iar duniya ce dama nan kike?Kin shammace mu kina nan kici goma ki tsoma biyar,lallai %??iar duniya kin wahalar da Yarima kuma sai Allah ya saka masa.ta daure fuska wane abu ne kuma Yarima ?Don Allah kadaki sani nayi amai, Faruk kuwa mamaki ne ya hanasa magana,sai dai kallon Bily yakeyi,Mansu tace dole ka rasa bakin magana.Mansu tana shiga daki ta kira Yrm tace yazo ga Bily agidansu, sannan ta sanar dasu Mama.yarima jin abin yayi tamkar mafarki,a gurguje ya nufi toilet yayo wanka yana fitowa ya kira Magaji awaya cewa ya shirya suje Kaduna anga Bily,suna mota ne Magaji ke cewa da munje kayi aski gami da gyaran fuska,yace muje zanyi acan.cikin dare suka iso,Mansu lokacin ta soma bacci,Bily kuma tuni tayi baccinta,suna shiga Mansu ta nufi kiran Bily,tace wallahi bazata fito ba dole aka kyaleta Faruk yakaisu masauki.b bacci ranar Yarima baiyi ba gani yake inya kwanta zai farka yaga cewa cikin mafarki ne.babu yanda Mansu batayi ba ta fito su hada abin karyawa takai musu,tace Allah ya tsareta. Koda Mansu ta gabatar musu da kari,sai Yarima ya debe tsammanin ganin Bily,harma yace Mansu ban taba zaton zaki tsokane niba,zolayata kikeyi ashe.tace kai dai kugama tana zuwa,sam ko sha%??iwar karyawar baiyi ba,ya koma ya zauna can kuma harda kuka Bily wai ita bata ko son ganin Yrm.Faruk shida kansa ya shigo yace dan Allah tazo,tana kuka tace kayi hakuri baban dady bazan iya kaffara ba kan cewa bazanje ba.ya mike ya fita kai tsaye gefen bakin ya nufa yace suzo ta hada kai da gwiwa suka shigo da tasan zasu shigo data shige toilet,Yrm yana yin arba da ita da sauri ya nufi gurinta kusa da ita ya zauna tare da cewa, beauty!Da sauri ta dago idanu jajir ta zabga masa harara.yayi murmushi tare da yin ajiyar zuciya, sannan ya mike ya kalli gabas ya tsugunna yayi sujjada,yana daga zaune agabanta yana kallonta shi duk tausayinta yake ji tunda yaji tarihinta agurin Mansu.yace beauty ki min duk abinda kike so nidai bukatata ki yafeni bazan kara ba,na dauki alkawari tsakanina da Allah.ta dubesa kabani takardata cikin mutunci kafin mukaiga kotu,yace kin manta ne beauty aure gidanmu ba%??i saki,har sai mace tazo da alfasha, keko saliha ce.ya dubi Magaji sa baki abokina, Magaji yayi gyaran murya sannan yace kiyi hakuri Bily kiyafe masa komai ya wuce,tace Magaji ina ganin mutuncinka kayi shiru kawai cikin wannan maganar,yace to nayi shiru Allah ya huci zuciyarki.
[8:43AM, 12/28/2016] %???+234 814 912 1821%???: ??}_MEKE FARUWA 92??}_

Ya tashi ya fita Yrm ko sai gashi y zube gwiwa biyu gaban mace,macen ma %??iar Nigeria %??iar Arewa wadanda ada yake kira kauyawa.yana cewa ta yafe masa ki yarda dani wallahi ina sonki da sauri ta dubesa gami da bude idanuwanta sosai,ina tsananin sonki beauty ban farga da tsananin sonki daya kamani ba sai da baki tare dani,na azabtu na wahalu,kalli yanda sonki ya maidani.hawaye ya soma gangaro mata tace yaya ka gane cewa kana sona?Ban yarda ba zaka yaudareni ne zaka cuceni ne,ya matso ya rungumeta duk da ta game jikinta guri guda, yana cewa I love you my beauty,I love u so much,I miss u a lot.turesa tayi tare da cewa ni bana sonka don Allah kabarni a takaice duk yanda suka zaci shawo kan Bily cikin sauki sai abin ya faskara, har Umman Mansu ta shigo ciki amma Bily ta kekashe nan ta tasa ta suka nufi zaria tace da Yarima yaje yayi hakuri zasu kawo ta ya dubi Umma yace don Allah kada ku mata fada laifina ne.bari in sanar dake laifukan dana mata.Bily ta dubesa da sauri an tambayeka ne?Yace a%??i zan dai fada musu ne don kada suyi miki fada suga laifinki bada hakkinki ba,tace suma kasheni ina ruwanka ba%??ice dai kafada ba,harma abin yaba Umma dariya tace to kai tunda bata son aji laifin naka ba sai ka barsa ba?Ku koma zamu maida ta insha Allah. A zaria idanu Bily ta zare tana kallon yanda aka fitar da titi cikin layinsu ga kwalbati layin yayi kyau bata gama tsinkewa ba sai data ga gidansu taga gefen mahaifyarta nan tayi sororo,Umma tace duk aikin Yrm ne,kuma yace shi don Allah yayi bawai saboda yana aurenki ba,ni kaina mota ya sai min wai in dinga zuwa aiki,baki kurum Bily ta taba ita abin bai burgeta ba.washegari sai gasu anty Saliha dasu Salma mai martaba yace suje su bada hakuri harda son suka zo yayi lakur jikin mamansa suka ce ta yafesu,tace insha Allah ya wuce.amma ita sai jibi zata dawo,Yrm yana samun labari sai yahau gyaran gidan aka sake fenti ya kwashe komai ya zuba sababbi don da tuni ya kammala nasu to hankalinsa ba kwance ba. Kafin ta dawo sai da Mansu tazo sukaje aka yimata gyaran gashi da lalle sai kace sabuwar amarya,ga kuma ainahin gyaran duk anyi suka nufi Bauchi.hutawa kawai Umma da Goggon sasa suka yi mata nasiha suka tafi.tana kwance kan sabon gadonta tana kallon kudin da Yarima ya kashe acikin dakin kawai sai kace baza%??i mutu ba,son yana bacci a gefenta,Yrm ya shigo cikin kayan bacci,zo muje mu kwanta beauty ko nan zamu kwana?Tayi masa shiru,ya matsa jikin gadon daidai fuskarta ya tsugunna cikin kunnenta yace baki huce bane?Tace,subhanallah don girman Allah ka barni nace ya mike na barki sai da safe.komawa Bily tayi tamkar bakuwa agidan, kowa na gidan tana dari-dari dashi har Umma sai datayi mata magana tace wai shin %??iar nan kin kasa sakewa kodai baki yafe bane? Tace,a%??i Umma aini dama ban riki kowa cikin zuciyata ba,ko Yrm da yayi sanadin komai tun kafin ya ganni ma na yafe masa,Umma tace Allah sarki,ai haka ake son bawa na kwarai,me saurin yafiya.Ubangiji yana yafe ma mai yafe laifin dan uwansa,Allah ka yafe mana zunubanmu wanda muka sani da kuma wanda bamu sani ba.Bily sai da ta dan kara gyara Yrm na sati daya sannan ta dauri aniyar karbarsa ranar juma%??i ta shiga cikin kitchen ta tsara girki sai ranar ta shiga gefensa tunda ta dawo,yanda ya tsara gurin ya burgeta sosai ta jere masa abinci,sannan taje tayo gayunta cikin riga da wando na yan ubansun gurin Umma ta tura son ita kanta data dubi madubi tasan tayi ne.Yrm suka shigo da Dr. Salihu duk da yana dar-dar din kada ta bada shi ga mamakin Yarima sai ya ganta cikin gayun da yaji dama bai shigo da Dr. Salihu ba,domin zai kalle masa ado.tace abinci yana samansa,ai fa Yrm sai doki nan suka hau ta zuba musu,Dr. Salihu yace yana son abincin gargajiya ita matarsa tafi son na nasara,zai kawota su saba ta koya don ta rika masa,Bily tace sai sunzo.Yrm ya rakasa ya dawo. Ya zauna yana dubanta gaskia kinyi kyau,ta dubesa da fara%??i ko?Yace sosai ma,har fa sai naji haushin shigowa da Salihu,tayi %??iar dariya ka kara abincin naga kamar baka koshi ba,yace ai kallonki ya kosar dani beauty,dan dawo kusa dani in dan ji kamshinki,da dan dumin jikinki.ba musu ta dawo,wayyo yau Yarima jinsa yake tamkar yau ne ya cire beauty dinsa daga leda,surkulle dai kala- kala ta jisa har sai daya bata tausayi kalaman so kuwa har sai da tayi hawaye don dadi ashe za%??i gaya mata wannan kalmar a rayuwarta? Fahimtar da Yarima yayi beauty tana son a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login