Showing 1 words to 3000 words out of 56554 words

Chapter 1 - JIddah Book Compelet Naima Suleiman

[12/9, 5:39 PM] +227 99 46 01 51: 💞 ```HEARTBEAT``` 💞
*JIDDAH*


MALLAKIN😘
```ANTY NI'EEMERH
Nimcyluv```


CHAPTER 1
RELESED FROM JAIL


Wattpad@nimcyluv


*🌈KAINUWA WRITER'S*

```If you are looking for story that will touch your heart and soul this is it```

DEDICATED TO
*~My shera family all u soo much my family so much ƙauna in my heart~*

*i seek for Allah's guidance in writing this book,Allah yasa ya amfani Al'ummar musulmi baki
ɗaya,wannan labarin ƙaƙƙyan labari ne (fiction)hannunane ya rubuta shi basira tace tayi aiki
akansa,tunanina yasa na kawo littafin na (JIDDAH) ni Anty Ni'eemerh nimcyluv ban yarda wani
ko wata ya juyamin wannan labarinba ta ko wacce siga ok🤗wannan littafin free ne zaizo maku
domin jin daɗin readers�*

_just follow my pen for i assure you,you are going to fall from Relesed in jail_



_Bisimillahir Rahamanir Rahim_

Chapter 1


A zaune yake aƙasan wata tabarma an rufesa cikin wani ɗan kurkoku irin wanda ake ajjiye
masu manyan laifin gidan yari,wani ma'aikacin gidanne yazu ɗan ƙaramin wajan da aka rufesa
hannu yasa cikin aljihunsa ya ɗauko tulin keys,wani babba ya ciro sannan yasa ya buɗe ƙofar
kallon mutumin ciki yay sannan yace"sir you are free now congrat"ya faɗa yana kallonsa, ko
inda yake bai kalla ba bare yasa ran zai bashi feedback na tayashi murnar fita daga gidan

yarin,lumshe gajiyayyun idonsa yay tare daya mutsa fuska kamar zaiyi kuka,a hankali ya miƙe
tsaye tare da kakkaɓe jikinsa tare da fituwa daga cikin ɗan ƙaramin ɗakin,babu wanda ya kula
harya gama fita ya nufi babban get ɗin gidan yarin tsayawa yay tare lumshe ido yana shaƙar
iskar gari wacce ya daɗe bai shaƙa ba,ci gaba yay da tafiya har yazu bakin get ɗin kwaɓe fuska
yay jin hayaniya tayi yawa hannu yasa ya dafe forehead ɗinsa wanda yake bara zanar
tarwatsewa ci gaba yay da tafiya harya zu bakin get.

Wata ƴar jaridace ta zaro ido waje ganin shigar dake jikinsa,daga shi sai three guater da kuma
farar t.shirt mai ƙaramin hannu wacce ta haska black skin ɗinsa,gaba ɗaya ɓarin jikin ayi masa
zanen TATU irin na arna duk kasan cewarsa baƙin mutum amma sosai zanen TATU ɗin ya fitu
raɗau a faffaɗan ƙirjinsa da kuma gefen wuyasa,sumar kansa baƙace sosai wacce ta sakko har
wuyansa sai kuma manyan idonsa wanda ya dace da siririn hancinsa,kwayar idonsa data
kasance blue mai ɗaukan hankali kuma mai bara zana wa ƴan mata ita ya saukewa ƴar jaridar
wacce ta tsura masa ido,numfashi taja sannan tace.

"i'm FEEYA can you tall us how fell from Reseled in jail?"

Ya mutsa fuska yay kafin ya mutsa ƙaramin bakinsa wanda yake ɗauke da red lips masu kauri
yace.

"fuck you" yana faɗin hakan ya nufi wata babbar mota baƙa mai kyan gaske number motar an
rubuta IRFAN MAI FATA 2 yana zuwa wajan motar ARYAN ya faɗa jikinsa tare da rungomesa
yace" congratulations from relesed from jail boddy"ya faɗa yana share ƴar ƙwallar dafa zubu
masa,motar ya buɗe masa sannan ya faɗa gidan baga yayinda ARYAN ya koma wajan drever
yaywa motar key sunajin jama'ar wajan na faɗin"sir IRFAN congrat"kota gansu baibi ba suka ja
motar a guje sukabar cikin gidan yarin.



*Jidda pov*

A tsaye take tayi shirinta tsaf domin tafiya wajan aiki,sanye take da Atamfa ɗinkin riga da siket
sosai ya kama ɗan kyakkyawan jikinta,fararan idonta ta ɗaga ta kalli cikin madubi ɗan murmushi
tayi tare da rolling lulu eyes ɗinta.
Ƙofar ɗakin aka tura mamaki fal fuskarta tace"JIDDAH you're still here?"ta faɗa tana ƙara
duban fukar Jidda wacce sam shigar da tayi bata yi mata ba,Jidda banda turo baki babu abinda
take,kallonta MaMa ta ƙarayi kafin tace.

"hurry up dear they will be here any minute"

gwalo ido Jidda tayi ita sam ta manta za'azu maganar aurenta,gyaɗa kai kawai tayi sannan ta
juya taci gaba da kallon madubi zaman glass ɗinta ta gyara sannan taɗan kwaikwayi muryar
maza tace.

"Daddy i can't marry this girl and i don't like her any more she is blind"

Ta faɗa tana dariya ƙasa² ƙara gyara farin glass ɗinta tayi kafin taja numfashi tace"ABBI da
zaka gane daka haƙura da maganar auren nan babu wanda zai auri makauniyar ƴarka.


*IRFAN POV*

A gaban wani kata faran gida suka tsaya horn Aryan yayi mai gadin gidan yazu ya buɗe masu
get ɗin,hancin motar ya cinna cikin kata faren Compond na gidan bai tsaya ko inaba sai rumfar
ajjiye motucin gidan,parking yay sannan ya buɗe ƙofar motar ya fitu hannu yasa ya buɗe side
ɗin baya,a hankali ya fitu da ƙafafunsa daga cikin motar yana ƙara lumshe manyan idonsa,ɗan
dariya Aryan yay yace"wlcm to ur hause IRFAN"cije lips yay sannan yay gaba zuwa ƙofar da
zata sa dashi da cikin gidan,ɗan matswa yay gefe Aryan ya fitu da wani ƙaramin remote daga
Aljihunsa dannawa yay nan ƙofar glass ɗin ta wangale shiga sukayi a tare suna zuwa ya nufi
wajan ƙaton frige ran Aryan ne ya ɓaci amma baice komai ba,buɗe frige ɗin yay dai lokacin
daya lumshe idonsa tare fitar da numfashi cikin gajiyayyiyar muryarsa yace.

"how my Diables?" ya faɗa yana jan numfashi dai² lokacin da yake ɗauko ƙwalabar
alchol(GIYA) kallonsa Aryan yayi sannan yace"they're all fine" ɓalle murfin yay zai kafa a
bakinsa akai saurin riƙe ƙwalbar,runtsa idonsa yay dan aduniya ya tsani Interupt.

"Ifran think about ur father he did like ur habit"cewar Aryan yay,da kallo Irfan yabi Aryan ba tare
da yace komai"ur father need u"da sauri ya ƙara kallon Aryan lokacin idonsa harya fara
sauyawa jinjina kai Aryan yay sannan ya ƙara cewa"yes boddy ur Daddy need ur love notin
else".
Kwace hannunsa yay daga hannun Aryan rai ɓace yace"don't ever call dat name,how is my
father?i don't have any father i'm single father is already die"

Ya faɗa yana ƙoƙarin kafa ƙwalbar giyar a bakinsa Aryan ya ƙara riƙesa yana faɗin.

"no Irfan don say dat pls"

Hannu Irfan yasa da dukkan ƙarfinsa ya hankaɗe Aryan,nufar step ɗin bene yayi tare da kafa
giyar a bakinsa ya shiga kwankwaɗa saida ya shanye tas sannan ya cillo kwalbar giyar ƙasan
bene ji kake tasss. *~ta hanyar Comments da kuma share zan tabbatar da ƙaunar da
kukemin�idan naji daɗin haɗin kanku kuma naga Comments tare da share ɗin wannan book
ɗin zan ƙara readmore kuma update kullum pls kada a aban kunya�Nimcy luv ta kuce nima
ina sonku😘~*

08119237616
20/Oct/2020
[12/9, 5:39 PM] +227 99 46 01 51: ```💞HEARTBEAT💞```
*JIDDAH*

```MALLAKIN😘
ANTY NI'EEMERH
Nimcyluv```

CHAPTER 2
CANCELLED THE VISIT

```Wattpad@nimcyluv```
*🌈KAINUWA WRITER'S*


*Dedicated to*
```Anty Hafsat A Garkuwa i luv u with all my heart tnx for care kinji daɗinki�```

*Sadaukarwa* ~ga Fadar nimcy da Nimcy hausa novel da Real nimcy fans�hakiƙa naji daɗi
comments ɗinku wlh kunban mamaki kamar yadda maryama ta faɗa ina fatan comments ɗinku
na yau yafi na jiya wlh kuna raina gaba ɗaya�bari na gani tsakanin groups ɗinan guda 3
wanne za sufi comments the gam is begin now~
*YA HAYYU YA ƘAYYUMUí ½í±�🏻*


_Bisimillahir Rahamanir Rahim_

Chapter 2

Lumshe gajiyayyun idonsa yay jin saukar kwalabar a ƙasa gaba ɗaya baya son haniya,ci gaba
da taka steps ɗin benen yay yana tafe yana tangaɗi domin giyar fa fara ɗibansa,babban parlour
ya huce sannan ya nufi wata hanya yana zuwa naga ƙofar da buɗe wani haɗaɗɗan bedroom ne
wanda yaji kaya na mure rayuwa,yana zuwa ya faɗa kan bed ɗin yana ƙara lumshe idonsa
kamar mejin bacci,hannu yasa ya shafi mararsa a hankali yaja numfashi tare da buɗe ƙaramin
bakinsa cikin muryarsa mai sanyi da kuma daɗi yace"i don't have any father..idan ina dashi
yana ina?..ko uban daya ɗaukeni da kansa yakai gidan yari gidan kangararru shi ake nufi zan
kirasa ubana kuma mahaifina..no i can't"ya faɗa muryarsa a hararrabe kamar zai kuka surutu ya
fara lokacin da giyar ta gama kwasarsa a haka bacci yay gaba dashi idonsa ɗauke da wasu
siraran hawaye.

Ajjiyar zuciya Aryan ya sauke ganin bacci ya ɗauki Irfan hannu yasa ya ƙashe masa wutar

ɗakin sannan yaja ƙofar ya rufe,juyawa yay tare da fata taga steps ɗin benen cikin sauri ya
gama sauka daga benen zuwa ƙasa,safa da marwa ya shigayi daga parlour'n yana tunanin
mafita.
Wayarsa ya ɗauka ya shiga dailing wata number buga ɗaya aka ɗauki kiran cikin rusunasa ya
shiga gaisarda mutumin daya kira kafin ya zauna kan sofa yace.

"Anty Amrah nasan kinsan yau boddy relesed from jail duk tsayin shekarun da yay mun ɗauka
zai sauya hali amma ina,ni nama rasa mezance maki wai yau Irfan da kansa yake cewa bashi
da uba mahaifinsa ya rasu"

Shuru yay yana sauraran abinda take cewa son ɗauki tsahun wasu mintuna kafin ya ƙara
faɗin"ok Anty sai kimzu"yana gama faɗin hakan ya kashe wayar tasa lapton ya ɗauka ya shiga
danne² wani muhimman messages yake turawa zuwa *Irfan Petroleum and gass* sabida ɓarar
da ma'aikatan wajan suke ta kuɗi tayi yawa yana tunanin gwara a rufeshi zuwa wani lokacin,ya
daɗe a wajan kafin yaji wayarsa ta fara ƙara ɗauka yay tare da mannawa tunkafin tayi magana
yay waje"Anty kin ƙara sune?ok ganinan fita yay tare da ɗaukan remote ɗin ƙofar yana zuwa ya
danna ya buɗe fita yay ya nufi wata mota wacce yake tunanin tana ciki.

Murmushi tayi daga cikin sannan ta buɗe ta fitu wata matashiyar matace wacce ba zata huce
irin 30 years ɗinan ba,farace sosai saɓanin Irfan da yace ɓaki amma kana ganinta za kaga
zallar kamar da suke idon sune kawai ya banbanta nata fari ne na Irfan kuma blue ne tamkar na
mage"ur wlcm Anty"murmushi tayi wanda ya ƙara fitu da zallar kyanta tace"tnx u Aryan ya
hakuri da abokinka?"faɗaɗa fuskarsa kawai yay baice komai ba harya buɗe ƙofar suka shiga
cikin gidan,a parlour ta zauna tace Aryan yaje ya ganu mata koya tashi,second kaɗan ya dawo
ya zauna akan kujera nesa da ita yace"ina tunanin wanka yake"kai ta jinjina dan itama magana
bata dameta ba"zuba mata ido kawai Aryan yay ko kiftawa baya yayi sabida wani mugun kyau
da tayi masa ta haɗu sosai wata zuciyarce tace"a'a Aryan wannan sister ɗin Irfance than matar
aurece hadda yaranta" wajan 30minute suna zaune a parlour kafin suji ƙamshin turarensa
wanda ya cika parlour'n da ƙamshi cikin sauri yake taka steps ɗin benen mamaki fal fuskar
Aryan yake kallon ikon Allah ganin shigar da dake jikin Irfan sanye yake da milk ɗin boyal mai
manyan zane yadin mai shara² ne hakan tasa ake ganin ƴar t.shirt ɗin da take ciki,gaba ɗaya
yadin ya ɓuye TATU ɗin jikinsa,ƙafarsa ɗauke da baƙin takalmi sai agogwan apple daya ɗaura a
tsintsiyar hannunsa,sumar kansa sai ƙyalli take yayi fresh baƙar fatarsa ta ƙara fituwa wanda
blue ɗin idonsa ya haska fuskarsa wacce take ɗauke da red lips masu kauri yay kyau sosai.

Tun daga nesa yay masu kallo ɗaya ya ɗauke kansa,inda yake ajjiye key ɗin motarsa ya nufa
yana zuwa yasa hannu ya cire guda ɗaya kansa tsaye ya nufi hanyar fita daga parlour'n"wato
Irfan ni kake kallo kake ɗauke kai ko,bayanni baka da kowa sai mahaifinka wanda ka ɗauka a
matsayin ma ƙiyinka sai kuma abokinka Irfan wanda ya zama ɗan uwa a gareka shin bayanmu
kana da wasu ne?"ta faɗa cikin muryar mai rauni tare da zuba masa ido yayinda shi kuma
Aryan yake kallonta.

*Jidda pov*

Ta ɗauki lokaci tsaye a gaban madubin tana kallon kanta,kasan cewar farin glass ɗin yana
taimaka mata wajan gani kaɗan.

Juyawa tayi ta ɗauki ƙatun hijib ta sakama jikinta nan hijib ɗinan ya saukko mata har
kafarta,fita tayi a ɗakin zuwa ɗan ƙaramin parlour'n gidan a zaune ta tadda ABU (mahaifinta)sai
kuma MIMI ƙanwarta ta sha ado cikin wata abaya ash colour,kusanta taje ta zauna kafin ta ɗaga
kai ta kalli mahainta nata cikin muryarta mai sanyi da kuma nutsuwa tace.
"barka da hutawa Abu"murmushi yay mata tare da faɗin"Jidda kin fitu"murmushi kawai tayi ba
tace komai ba"yaya jidda sannu da zaman ɗaki"cewar Mimi,turo baki tayi tare langwaɓar dakai
ba tare data amsa Mimi ma.
Mimi ce ta kalli ABU tace"Abu kana ganin baƙin nan za suci abincin gidanan kowa" kallonta
yay yace"why Aminatu"gyara zama tayi tace"daga u.s zasu zo kaga ba lallai suci abincinmu
ba"murmushi kawai yay kafin yay magana Mama ta shigo ɗakin ɗauke da wayar Abu tace"gashi
ana kiranka"karɓar wayar yay tare da barin wajan.
Tashi tayi daga inda take ta dawo kusa da Mama zama tayi tare shigewa jikin maman tana
suke numfashi can ƙasan ƙasan maƙoshinta tace.

"meyasa kukeson aurar da nine bayan kunsan ina da wanda nakeso meyasa kuka manta da
Sameer Mama?"

Shafa kanta tayi tace"no Jidda kinsan mahaifinku ba'a sauya masa ra'ayi nayi ƙoƙarin fahimtar
dashi amma yaƙi,kuma kinga ƙanwarki tana da wanda take so da ace anbashi dama da tuni
anyi bikinshi da Mimi to kinsan ra'ayin mahaifinku bazai taɓa aurar da Mimi ace ke kuma kina
gabanmu dole suyi hakuri sai kinyi aure"
Mimi ta zabgawa Jidda harara cike da baƙin ciki ƙila tana sani taƙi nemu mijin aure tsabar baƙin
cikin da take mata,wannan ai mugun tace haba.

Babu wanda ya ƙara magana sai Abu daya dawo daga wayar fuskarsa babu yabu babu
fallasa,mama ce tace"lafiya?"shuru yay mata banda kallon Jidda da take kwance jikin mama
babu abinda yake numfasawa yay yace.

"they've cancelled the visit"

A kiɗime mimi ta tashi duka jikinta rawa yake wasu hawayen baƙin cikine suka fara zubu mata
wai meyasa yaya jidda ke mata hakane kilama ita tace masu bata sonsa wallahi ba zan iyaba ni
aure na keso.

Mama ce ta kallesa tace"but why?"juyawa yay jin masallacin *Abuyazeed* sun fara kiran

sallah,yana tafiya yana faɗin.

"his mother made a list of 10 girls since the boy was in the u.s,so he liked the first one he met"

Murmushin jin daɗi jidda tayi tare da faɗin"daman na sani nifa Sameer shine rayuwata kuma
shine kawai zan iya aure na pls my luv come back soon"


*Irfan pov*

Duk maganar da take baice mata komai ba saima ƙara tsaiwarsa da yay,sosai ya kula ran ƴar
uwarss ya ɓaci amma dole itama ranta ya ɓaci indai zata ci gaba dayi masa maganar wani can
da baisani ba.

Ƙara rage murya tayi dan aduniya babu abinda yake ɗaga mata hankali irin taga Itfan yay fushi
da ita ko yaƙi kallonta,tashi tayi tazu inda yake ta dafa shoulder ɗinsa ajjiyar zuciya ya sauke
yana jin kamar ya faɗa jikin ƴar uwar tasa yay ta kuka ko zai samu nutsusa,sunkuyar dakai yay
dan bai yarda sun haɗa ido da ita ba.
A sanyaye tace"yanzu bro ni kake fushi dani akan ina faɗa maka gasky ko?to meye laifina ni
idan kai kace shiba mahaifinka bane ai ba zaka hana duniya kiranka da suna *Irfan Imran mai
fata* ba"

A haukace ya ture hannunta daga jikinsa ya nufi wajan frige yana zuwa ya buɗe tare da ɗauko
wata ƙatuwar kwalaɓar alchol cikin sauri ya buɗe murfin giyar yana shirin kaiwa bakinsa yaji
masallacin *Abuyazeed* sun fara kiran sallah,cike da baƙin ciki yay jifa da kwalbar da taji T.v
wacce take manne da bango jikake tass.
Kallon Aryan Amrah tayi nan idonsu ya mannu cikin na juna"zuka kwashe wannan tarkacan na
cikin frige kayi waje dasu"

Sai lokaci ya ɗaga ido ya kalleta cikin muryarsa wacce ta gamayin rauni yace"stop" ok Aryan
basshi ni bari na kwashe da kaina"tana faɗin hakan ta buɗe frige ɗin ta fara kwashewa cikin
tsananin ɓacin rai wanda ya daɗe bai shigesa ba yasa hannu ya hankaɗe Amra,ƙara ta fasa
tare dayin baya zata faɗi ajjiyar zuciya ta sauke jin ta sauka akan wani abu ɗaga kanta tayi nan
jikinta ya ɗauki rawa ga kuma wani abu dake bin jikinta kamar tsutsa ba komai ya haddasa
hakan ba sai ganinta da tayi manne a faffaɗan ƙirjin Aryan bakinsa a dai² kan lips ɗinta. *~a yau
comments ɗinku shi zai tabbatarmin da kuna ƙaunar littafin kuma shine zai bani ƙarfin gwiwa
wajan yi maku postin kullum,amma akasin hakan shizai nuna baku sona kuma baku ƙaunar
littafin rashin comments zaisa na hakura da typing wannan littafin nayi kwanciya insha bacci
abuna�a ko ina kike a duk inda kike indai kinsan kina karanta wannan littafi wlh ina buƙatar
ganin comments ɗinki kuma mai ma'ana tnx u guys i luv u all�😘~*

~Comment
Share
Vote~

_Sarauta👑_
08119237616
[12/9, 5:40 PM] +227 99 46 01 51: ```💞HEARTBEAT💞```
*JIDDAH*

```MALLAKIN😘
ANTY NI'EEMERH
Nimcyluv```

CHAPTER 3
```THE LIBRARY```

```Wattpad@nimcyluv```

ةمكح* :مويلا

برض الله الثم ةيرق تناك ةنمآ ةنئمطم اهيتأي اهقزر ادغر نم لك ناكم ترفكف معنأب الله اهقاذأف الله سابل عوجلا فوخلاو

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0