Showing 99001 words to 102000 words out of 159454 words

Chapter 34 - Tsintacciya Book Complete Naima Nimcey Sarauta

Meema matarsa ce? Abubuwan da suke masa yawo a zuciya kenan, wanda kuma suka sanya masa damuwa a cikin zuciyarsa kenan, Mi?ewa yay ya nufi part Win sa, yana zuwa ya kwanta yana al'ajabin abun a kansa tare da matsawa kansa son tunana abinda ya shige.
Da daddare Asheer ya dawo daga sallar Issh jikinsa sanye da jallabiya kai tsaye kuma bedroom Winsa ya shige tare da zama yana danna Wayarsa yana jin yadda kansa ke masa ciwo sosai, Mom dake Parlo suna dinner tace "Meema ki kai masa dinner part Winsa" shiru tayi kanta a ?asa sai dai Mom da gaji tace "Maryam dake nake" Mi?ewa tayi tsaye cike da kunya amma ta kasa cewa komai tray Win ta Wauka lokacin tana sanye da jallabiya ta Waura ?aramin hijab a kanta, a hankali take Knocking ?ofar daga can ciki yace "come in" kamar ba zata shiga ba sai kuma ta shiga yana zaune lokacin ya zame jallabiyar jikinsa babu riga sai 3gauter a jikinsa, da Sauri ta Wauke kanta tare da ajjiye tray Win zata juya yace "taimakamin da bottle of water Anuty Meema" wata kunya ce ta kamata har lokacin kuma bata kallesa ba, ta nufi wajan fridge ta Wauko masa mai sanyi guda Waya, bashi tayi ya amsa yana tashi zaune tare da ?are mata kallo komai nata ya sauya kamar ba ita ba, she's younger than her age, tana bashi ta juya yace "ina zaki?" Tsayawa tayi kanta a ?asa Mi?ewa yay tsaye tare da nufar inda take yana zuwa yasa hannuna ya juyo da ita suna farcing juna yace "Uhm" juya masa tayi ita abin kunya ke mata wai ?aninta shine zai zama mijinta murya a kasalance yace "Muna faWa ne?"
Girgiza masa kai tayi yace "to meye ake juya min baya haka" shiru tayi sai kuma tace "eat your dinner" girgiza kai yay yace "a'a" tace "why" kai tsaye yace "bana jin daWi" da sauri ta Waga Idanunta tare da juya ta kallesa tace "what happened to you Meke maka ciwo" ganin yay shiru yasa ta mi?a hannunta zata Wura a wuyanta ba zato taji ya Waga ta cak bai tsaya ko'ina ba sai kan bed da sauri ta runtse idanunta Zuciyarta na halbawa lokacin da taji bakinsa akan nata..16Idanunta ta runtse tana sauraran abinda Asheer yake mata, gaba Waya kunya ya gama kamata duk Yadda tasu yana shi abinda yake ?o?arin yi amma abin ya girmama tana kallo yay abinda ya keso kana ya Wauke ta zuwa bathroom, bayan sun gyara jikinsu ta sanya Jallabiyar sa ne suka fito yana tsokanarta tura baki gaba tayi tace.
"Allah bana so"
Dariya yay mata yana zama tare da kama hannunta ya zaunar da ita a gefensa yace.
"Ni kuma ina so"
Rufe fuskarta tayi a hankali kuma cikin serious tone yace.
"Maryama"
Yadda ya kira sunanta a nutse yasa ta Wago kanta tare Kallon cikin idanunsa a hankali tace.
"Uhm" gyara zama yay ya ri?e hannunta sosai kafin yace.
"Tell me something"
Idanunta ta juya tace "what?" Yace "do you love me? I mean kina son Aure na dake?"
Kasa magana tayi domin kwarjinin da yay mata hakan yasa ta sunkuyar da kanta ?asa cikin lallami yace "it's okay, na fahimta zoki kwanta to"
Ya faWi hakan yana Waukan Wayarsa tare da yin dailing number Akeem wacce ya amsa,
Wayar nata ?ara ba'a Waga ba, haka nan ya samu kansa da son yin magana da Akeem Win ba tare da wani dalili ba.
A kira na uku Akeem ya Waga hakan yasa Asheer cewa.
"Hello"
Akeem time Win yana part Winsa tare da p.a suna yin magana akan kiran da Abdul-aziz Bamali yay masa kamar ba zai magana ba sai kuma yace.
"Assalamu alaika" ajjiyar zuciya Asheer ya sauke kafin yace "I'm sorry bro kana lafiya?" ?an jim yay kafin yace.
"Who am i speaking with?" Asheer yace "Asheer Ahmad Adil, na amshi number ka wajan taron da akai 2days back" jinjina kai yay yace "uhm kana lafiya ya iyali" Murmushi Asheer yay tare da kallon Meema wacce take kallonsa yace "Allahamdulillah ya naka iyalin" a hankali Akeem yace "Allahamdulillah" shiru duk sukai Asheer dai ya kasa juriya yace "You look like familiar"
Meema wacce take sauraran su tace "Bro ina yarinyar dana gansa da ita" Asheer yay Murmushi yace "daman na kira ne kawai mu gaisa" Akeem na amsar File Win hannun P.a yace "thank you" Asheer na ?o?arin kashe kiran Meema ta amsa tare da faWin "Uhm kana lafiya" tsayawa cak Akeem yay daga duba file Win, dalilin saukar Muryar Meema da yaji,
Muryar daya yake dai-dai da bugawar zuciyarsa dama Numfashinsa baki Waya, Tabbas yasan mai Muryar,
Amma a yanzu yasan ba ita Win bace kawai ka mancecrniya ce, shirun da yay ya sanya Meema faWin "Hello"
Sai a lokacin yaja idanunsa ya lumshe yana sauke numfashi kasala da kuma kewa ya saukar masa,
Cikin ?asa da Murya yace "Allahamdulillah" jin hakan yasa Meema faWin "ina matar taka?" Ware fararan idanunsa yay yana mamaki sai kuma yace "Mata?" Tace
"Eh, wacce na ganku tare ranar taro" numfashi ya sauke yana girgiza ?afarsa yace "lafiyarta lou" ya faWa cike da girmamawa da kuma zallar ladabin daya samu kansa ciki,
"Is she your wife?" Maganar data samu kanta da furta wa kenan wanda ya sanya Asheer kallonta tare da juya idanu alamar "why do you asking?" Kallonsa tai tana Wauke idanunsa saboda sumbatar goshinta da yay, a hankali Akeem yace.
"In sha Allah" Murmushi tayi tace "I'm happy for you, Allah yay maku albarka" cikin kasalar daya samu kansa yace "Ameen, Ngd" sallama sukai suna gamawa Asheer yace "mene yasa kika karanci likita?" Tace "saboda ina so" yace
"To ba dashi kika dace ba" idanu ta juya tace "why?" Yace "Are You questioning me?" Gira ta Waga masa tace "Of course" yace "uhm da lawyer kika dace wannan tambayar naki is too much" mi?ewa tayi tana faWin.
"Uhm good night" shiru yay mata ya koma ya kwanta abinsa yana danna Wayarsa hankali kwance ganin Hakan yasa tace "Baka da lafiya ne" still Shiru yay mata cikin damuwa ta dawo kusa dashi tare da buWe baki zatai magana kafin ta ?arasa ya jata zuwa bed tare da rufe su da duvet ya kashe light.
Akeem kuwa suna gama wayar ya kalli P.a tare da juya file Win hannunsa yace.
"Zanyi signing Win gobe ok" jinjina kai P.a yay kafin yace.
"Gaba Waya an kammala aikin sabon takin da akai, kuma anyi selecting na duk garin da za'a kai, amma har yanzu akwai wanda suke ?orafi akan takin kwanaki"
Gorar ruwan daya Wauka ya kai bakinsa sai daya sha sosai yace.
"Ka tabbatar da kyan wannan an samu nafdac ta duba" p.a yace
"Yana da kyau sosai, komai anyi sa bisa tsari kamar yadda kake bu?ata, kayan aikin duk daka sanya a nemu an kawo"
A wannan karan hankalinsa gaba Waya yana kan system ba tare da yace wani abu ba, gane shirun nasa yasa p.a faWin.
"An samu matsala sosai a zauran majalisar Winkin Duniya wanda yakai ga rikici sosai aka tashi daga tattaunawar bayan an tabbatar da cewa an sauke ministoci guda 10 cif daga kujerun su, haka kuma an maida sabbin ministoci guda 10 but till now ba'ai mentioning name's Win su,amma jiki na yana tabbatar min cewa Tabbas akwai sunanka"
Yana gama faWin maganar Akeem ya mi?a masa wata gorar ruwan mai sanyi yace "drink"
Ba musu ya amsa ya fara sha kana ya mi?e yace.
"Goodnight" idanun Akeem akan system yace.
"Bil khairan alal khair send my regards to Momcy" yace "I'll" ya faWi hakan yana fita saboda dare yayi.
Yana fita Akeem ya mi?e tare da rufe ?ofar part Winsa bayan ya duba ko'ina na gidan ya tabbatar komai lafiya,
Wanka yay ya sauya kaya zuwa white cotton pajamas,
Ya fesa perfume tare da sanya minti a bakinsa, kwanciya yay yana lumshe idanunsa fuskarta ya fara yi masa yawo hakan yasa ya Wan mirgina kaWan tare da jawo pillow ya rungome, time ya duba yaga 11:03 ya tabbatar yanzu tayi bacci, idanunsa ya ?ara rufewa bakinsa Wauke da addu'ar Allah yasa bacci ya Wauke sa, sai wajan 3 na dare ya samu bacci ya Wauke sa.

ABUJA ASOKORO
Sai wajan Issh jirginsu ya sauka saboda jiran da sukai airport,
Suna sauka wata mota tazu Waukar su, kai tsaye aka nufi dasu Asokoro gida mai number ta 111, gaba Wayansu suna a gajiye ne musamman Akeela da bata saba hawa jirgi ba, sai abin yay mata yawa domin har wani zazzaSi ta keji,
Gashi sam bata da sakewa musamman yanayin yadda taka mutane a cikin gidan,
Duk sai ta zama wata Uncontactable, suna shiga wata tattijuwa suka fara cin karo mai suna Dada, tana zaune cikin shiga ta alfarma ga wasu ?an mata kusa da ita, da alamar jikoki ne,
Sai wata daga can gefe mai suna Fati, daga alama bata son mutane sosai, Murmushi Dada tayi tace.
"Ma sha Allah, lale lale da zuwan kishiyoyi"
Aleema ce tace "Lallai ma tsohuwar nan kina hutawa" Dry Dada tayi tana faWin "Yarinya yanzu ko a kasuwa aka samu nida ke sai an siye ni kina zaune" Afaf tayi saurin faWin "Allah ya sauwa?e waike Dadan nan Meke kika Wauki kanki ne?"
"?an mata" ta bata amsa idanunta na sauka kan Akeela wacce take tsaye kanta a ?asa,
Babu wacce tace mata zauna hatta Mami banza tayi da ita, sai a lokacin Dada tace..
"Ba?uwa mukai ne" juyawa sukai gaba Waya harda Fati suka kalli Akeela, da Wan damuwa Aleema tace.
"Dada ?ar Baffa ce fa"
Juyawa Dada tayi ta kalli Mami tace.
"Khadijah itace wacce kike faWa min ko? Allah sarki" Mami ta buWe baki da ?yar tace "Eh Dada"
Sai a lokacin Akeela ta Waga kanta suka haWa idanu da Dada a hankali kuma ta dur?osa cikin muryarta mai sanyin nan tace "Ina yini Dada"
Ta faWa kamar yadda taji suna kiranta dashi, Murmushi Dada tayi tace.
"Lafiya Allahamdulillah ya ?arin hqri?" Tace "Allahamdulillah" Aleema ce ta Mi?e tace "Dada yunwa na keji" Dada tace
"Ai kuwa duk cocon basa nan, saboda dare yayi" cikin sauri Anup tace
"Akeela ko zaki mana?" Da idanu ta kalli Anup ba tare da tace komai ba tana ?o?arin yin magana Mami tace
"Me zai hana tayi itama za taci ai, ki nuna mata kitchen Afaf kuje kuyi wanka kafin ta gama" Mi?ewa tayi ta nufi part Win da take sauka idan tazo, Anup kuma ta mi?e tana wani irin yin murmushi kafin tace "Follow me na nuna maki kitchen ko" a sanyaye tabi bayan Anup tana jin yadda zafin zazzaSin ke son cin ?arfinta suna isa kitchen ta nuna mata ita kuma ta juya.
Mi?ewa Dada tayi duk suka shige part Winsu, ya rage sai Fati wacce har lokacin babu wanda ta kula sai danna waya take abinta.
A hankali Akeela ta fara duba kayan kitchen Win komai akwai ta rasa mene zatai mai Wan sau?i haka, ganin babu lokacin yasa ta fara Waukan wani kifi guda uku manya ba bushasshe ba, Wanye ta wanke tare da gyarawa ta kunna gas kana ta Wura tukunya ta sanya kifin, albasa ta yanka manya manya dai ta zuba Ginger a ciki, kana ta fara feraye dankalin turawa, tana gamawa tayi blending kayan miya babu tomato's, lokacin kifin ya gama, cikin Wan sauri ta soya kayan miyan tare da Wura sanwa yana tafasa bayan ta sanya maggi ta zuba dankalin tare da dafaffiyar albasar,
tare da kifin ta rufe, pineapple juice ta fara haWawa mai zuSo, tana gamawa ta sanya fridge lokacin gaba Waya gidan yay shiru, tsaye tayi tana duba wayarta yau gaba Waya ba suyi waya da Ajmal ba, 5mnts ta ?ara ta gama girkin ta zuba cikin warmers, tare da fita ta waje, tana fita Mami ma fitowa cikin shigar bacci kallo Waya tayi mata tace.
"Kin gama" kai ta Waga mata tace "kije to kiyi wanka kice masu su fito" ta faWa tana nuna mata,
Part Win da suke, cikin gajiya take tafiya da Wan sauri taja baya ganin wata mace ta fito kana kallon matar kasan ba kirki gareta ba,
Kallon Akeela tayi tace "Ke kuma fa?" Jikinta ta ?an?ame tace 'ina yini" tsaki taja tana yin waje abinta, jikin Akeela na rawa ta shige ciki duk sunyi wanka sunyi sallah Afaf na ganinta tace.
"Kin gama ka ruwa can na haWa maki" Murmushi tayi tace "thank you"
Fita duk sukai ita kuma ta shige bathroom domin yin wanka.
Suna fita suka samu Mami duk ta zuba masu fatan dankalin a plate tare da juice Win, zama sukai suka fara ci sai a lokacin Mami tace.
"Fati waike baki iya gaisuwa bane? Wlh Aunty Yana kin sangarta yarinyar nan"
Matar data haWu da Akeele mai suna Yana tace "Rayuwa ce kowa abinda yay niyya shine yake, Anup meet at my room" ta mi?e tare da barin wajan,
Anup kam sai da taci plate biyu ta mi?e, babu jimawa Akeela ta fito sanye da duguwar riga peach mai kyau Waya daga cikin wacce Akeem ya siya mata, ta Wura wula a kanta, kanta a ?asa ta ?arasu wajan Aleema taja mata kujera, kallo guda Fati tayi mata ta Wauke tana ci gaba da cin Abincin, zama Akeela tayi Afaf tace "Mami ina abincin Akeela?" "Daman ba taci ba?" Kallon Akeela Aleema tace "kinci?" Girgiza kai tayi tace "ina gamawa Mami tace naije na wanka na kiraku" Mi?ewa Mami tayi tace
"Ki dafa wani to domin an cinye" gaba Waya suka kalli Mami Afaf kamar tai kuka tace "Amma Mami ya haka?" HaWe fuska Mami tayi tace.
"The you have any problem Afaf?" Girgiza kai tayi tace "noting"
Mi?ewa Akeela tayi cikinta na wani irin kukan yunwa amma ta daure ganin hakan yasa duk suka mi?e Aleema na faWin.
"Muje na rakaki kiyi ni ban iya ba" girgiza kai tayi tace "No, na ?oshi" "Are You sure kin ?oshi?" Cewar Afaf kai ta Waga tana zuwa ta hau gado ta kwanta, gaba Waya tausayinta ya kama su da sun haka ne da basu ci nasu ba,
Wayarta ce ta shiga ringing a hankali tai answering tana manna wayarta a kunne tare da faWin.
"Hello" ta faWa a sanyaye saboda juyawar da cikinta keyi, Ajmal dake kwance yana fama da nasa ciwon yace "what happened with your voice?" Kamar ba zatai magana ba sai tace "bacci nayi ne" ajjiyar zuciya ya sauke tare da faWin "how are you my beauty? I miss you so much kamar nai hauka" Murmushi tayi tace "How are you" yace "I'm fine kefa ya jikinmu" shiru tayi kafin tace..
"Baka da lafiya ne?" Kamar tana kallonsa ya girgiza kai tare da faWin.
"Lafiya nake, soon Zaki zama Matana dat why nace jikinmu" lumshe idanunta tayi saboda tunawa da maganar Bobbonta da tayi kafin kuma tace.
"Ina Abuja fa" da sauri ya tashi zaune cike da mamaki yace "Are You serious Wify?" ?aga kai ta yi tana jan numfashi sosai ta kejin yunwa amma ko ruwa bata samu damar sha ba,
A sanyaye Ajmal yace.
"Uhm Get ready da safe zan zo" zare ido tayi tace
"A'a please kaga bana gida kuma" yace
"Kuma me? Kada nazo na ganki abinda baki sani ba tuni ankai kuWin na gani ina so kuma an bani ke, na kuma sanya lokacin auren mu wata biyu masu zuwa"
Zare ido tayi tana jin gabanta na faWuwa sosai sai kawai tayi shiru, Ajmal hannunsa akan mararsa yana aikin nasa daya sama, a hankali kuma yake sauke numfashi wanda har cikin kunnanta take jiyo sautin fitar numfashin nasa cike da mamaki tace.
"Are you okay" shiru yay mata saboda wata zufa dake yanko masa a lokacin gab yake da samu salama cikin damuwa tace.
"Baka da lafiya ne?" A hankali yace "uhm" tace "Meke damunka" cikin ?asa da Murya yace "i need you please ina son ai auren mu nan da 2 to 3week mana" shiru tai masa jin abin nasa yana girma tace "bye" yace "wait" shiru tayi yace "Abuja ina?" Tace "naji ance Asokoro" a hankali yace "okey ki kula i love You" kashe wayar yay yana ?ara matse mararsa lokaci guda kuma ya ?an?ame jikinsa waje guda yana fidda numfashi.
Da Subhi kuwa Akeem ne yake sakkowa daga strains Win bene, yana sanye da tattausan Embrodiery Islamic jallabiya cotton ash, yana fitowa ya samu Abbu tsaye yana jiransa a tare suka nufi masjid bayan an idar suka dawo a tare, a Parlo Abbu ya zauna yana shan black tea Akeem kuma ya haura sama, saboda Litinin ce yana azumi kamar yadda ya saba.
Yana shiga cikin bedroom Winsa ya zame jallabiyar jikinsa ya kwanta kan bed tare da lumshe idanunsa yana jin bugun zcyarsa samun kansa yay da son jin muryarta sai kawai ya Wauki Wayarsa tare da kiranta da asalin family number nasa, lokacin Akeela tana kwance sai bacci take looking damn cute, sama sama ta kejin ringing Win waya wanda kuma shine kira na biyu, da ?yar ta buWe idanunta wanda sukai mata nauyi sosai, kafin kuma a hankali ta mayar ta rufe lokacin tana danna answering, manna wayar tayi a kunnanta tana faWin.
"Hellooo" ta faWa cikin sanyin murya da tarin gajiya, Ajjiyar zuciya Akeem ya sauke lokacin da yaji sautin saukar muryarta acikin kunansa, shiru yay har Akeela ta kaji ta ?ara faWin.
"Hello" a wannan karan idanunsa ya runtse tare da dafe saitin zuciyarsa saboda tsananin buga masa da tayi da ?arfi sanadiyyar jin muryarta mai cike da tarin bacci, jin shiru yasa Akeela buWe idanunta tare da duba screen Win wayar ganin number ce babu suna yasa ta mayar da wayar kunanta tana faWin.
"Tashi kiyi sallah" ya faWa cikin sanyin murya kamar ba Dr Abdul-hakeem Bukar Bello ba, cikin sauri ta zare idanunta cike da mamakin jin muryarsa, ?ara ware idanunta tayi gaba Waya mamakin abin take domin tama mance dashi.
"Ki tashi kiyi sallah nace"
A hankali ta rufe idanunta tare da faWin "ina ka samu number ta?" Bai bata amsa ba sai cewa da yay "I Said wake up and pray okey" zata kuma magana yace.
"Nace ki tashi kiyi sallah ko?" Baki ta turo tare da murguWa bakin tace "to"
Yace "ke! Nine kike murguWawa baki?"
Zare ido tayi tare da cire wayar tana mamaki kana kuma ta mayar da wayar tace "Ni kuma?"
A hankali yace "A'a ni"
Shiru tayi ba tace komai ba, ta ?ara Lumshe idanunta saboda baccin da yake cinta yace.
"Tashi" ware ido tayi tace
"Na tashi" yace "tashi zaune" da mamaki take sauraransa kamar a sama taji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login