Showing 117001 words to 120000 words out of 159454 words

Chapter 40 - Tsintacciya Book Complete Naima Nimcey Sarauta

dana gani,
Cikin sauri na fito daga cikin mota ta, na nufi inda take lokacin tana ?o?arin shiga motar ta, ga kuma garin Abuja yay shiru gaba Waya tsaron yana ga airport saboda dawowar ?ar gidan shugaban ?asa, dutse na Wauka tare da kwaWa mata a tsakiyar kanta, nan take ta faWi a wajan bata numfashi, bai wani tsaya duba fuskarta na Wauke ta zuwa cikin mota,
Kai tsaye kuma gidan gona ta na nufa da ita, a nan cikin gonata nai mata fyaWe bayan na gama komai na Wauki jinin kamar yadda boka ya faWa,
Na mi?e da niyyar barin wajan amma fuskar wacce na gani ya gigita ni, ya Sanya ni shiga cikin tashin hankali da kuma ruWu haWi da Zallar dana sani a rayuwata, nai ladamar ganin fuskar wacce na gani wacce take kwance cikin jini na aikata rashin kirki da kuma tuzarci a gareta.."
Shiru yay hawaye na zuba a fuskarsa sosai,
Ajmal kasa magana yay, Abbu kuma ya Waga kai suka haWa ido da Papi, Karim yay shiru.
Akeem da har yanzu idanunsa yana kan Akeela wacce kawo yazo ya zameta a hankali tare da kwantar da ita a kan cinyarsa yana shafa kanta, yana tofa mata addu'a a hankali tare da goge mata zufar da yake yanko mata.
Jadda wacce take da ?arfin hali a cikinsu tace.
"Fuskar wace ka gani?"
Runtse idanunsa Yay sosai yana jin ciwon abun sosai a ransa,
Cikin dauriya yace.
"Fuskar Maryam Meema Ahmad Adil itace fuskar dana gani a matsayin wacce nayiwa fyaWe, itace kuma wacce ake jiran dawowarta bayan shekarun data Wauka bata ?asar 9ja baki Waya"
Yin maganarsa yay dai-dai da shigowar wasu Manyan motoci cikin Asibitin, mitoci ne guda wajan biyar ta farko Mom ce zaune sai kuma wata bafulatanar nata, ?yakkyawa da ita amma shekaru sunja saboda yawan jinya, tana sanye cikin Al?yabba mai taushi.
Mota ta biyu kuma Arif ne da Azzam sai kuma Aaliyah dage gaban mota, mota ta uku Jini Waya ne kuma tsatso Waya a ciki, wato President Ahmad Adil da kuma Mai martaba Aalam Adil Jahid, wanda yake zaune yana ri?e da casbawa yana ja,
Yana sanye da farar Jallabiya mai laushi da taushi ga wani ?yakkyawan hirami daya zagaye fuskarsa dashi, sai Meema dage gaban mota ta ?an?ame Jikinta waje guda tana jin zcuiyarta na bugawa da ?arfi.
Mota guda biyu da sukai saura kuma ta escorts ce, a hankali sukai parking gaba Waya suka fito escorts suka zagaye su Aalam jikinsu har rawa yake, lokacin da sukai arba da Sarkin Makka.
Kai tsaye ward Win da aka kwantar da Akeela, suna ?o?arin shiga cikin room Win Meema taja ta tsaya hakan yasa Mom faWin.
"Yadai Meema"
Girgiza kai tayi ganin yadda tai shiru yasa Laylerh buWe baki a taushashe tace.
"Ma'aa sa baki?" Hawaye na fitowa daga cikin idanun Meema tace.
"Mom, Laylerh ku shiga kawai zuciyata bugawa take zan jira a nan"
Sanin halin Meema yasa Mom tayi gaba sai Laylerh a bayanta, sai kuma Dad da Aalam kana su Arif suka rufa musu baya.
Nan kallo gaba Waya ya koma kansu Laylerh, cikin tsananin al'ajabi da Zallar mamaki kowa ya shiga kallon Aalam da kuma Akeem wanda kansa ya sunkuye a fuskar Akeela,
Duk bayan da ake yana ji kuma yana fahimta amma gaba Waya hankalinsa yana ga Akeela.
Shigowar su Aalam yasa ya sauke wata wahalalliyar ajjiyar zuciya yana mai fesar da iska daga cikin bakinsa.
Kujera aka bawa Aalam da Dad suka zauna, Laylerh ma aka bata ta zauna,Mom ma kaka.
Shiru wajan ya Wauka kowa da abinda yake sa?awa a cikin zuciyarsa,
Banda Aalam daya Wura idanunsa akan Akeem baya ko ?iftawa, a ransa banda hamdala ga Ubangiji babu abinda yake,
Ganin Akeem a haka ba ?aramin sanya masa nutsuwa yay a cikin zuciyarsa ba, har yana jin a yanzu bashi da wata sauran damuwa.
Akeem ne ya Wan girgiza Akeela a tsorace tare da faWin "Kee! Meye haka? Open your eyes ina nan I'm with you noting will happen to you again, Abbu suma take"
Ya faWa a gigice yama mance matsayinsa na likita, domin komai nasa a kunce baya gane komai sai ita daya sanya a gaba.
Abbu ne ya numfasa tare da kallon Dr yace "Dr ka sanya mata jinin nasan rashinsa ke sanyata yin suman"
Idanun Akeem daya gama rinewa da jaa ya Waga ya kalli Abbu ganin yadda fuskar Abbu take a Waure yasa ya kasa magana, saukar ajjiyar zuciyar da yaji a bayansa yasa ya fara Wan ?o?arin juyawa,
Amma ya kasa saboda tsoran ganin abinda zai iya ?ara sanyasa cikin damuwa, a gaggauce Dr ya Waurawa Akeela jinin tare dayi mata allurar suma, da ?yar take iya numfashi za'a sanya mata oxygen Akeem ya hana, ya amshi ice da showel ya shiga danna mata a goshinta zuwa ?irjinta ganin jikinta na rawa saboda soma shigar jinin.
Jadda wacce tashin hankali ya gama ratsa ta bata taSa tunanin haka halin mijin nata yake ba, da sauran ?arfinta tace "Muna jinka, bayan kayiwa ?ar gidan shugaban ?asa fyaWe sai mai ya faru?" Da sauri Mom ta kalli Jadda shi kuma Dad Papi kawai ya kalla yana son yaji tabbacin abinda yake faruwa.
Idanuna ya rufe Saboda tsakani jin kunyar ganin Dad a wajan kafin a hankali yace.
"Na shiga tashin hankali sosai ganin Meema bata motsi, cikin sauri ya Wauke ta zuwa wani prvt hospital a sirrince aka bata kulawa, tunani na shigayi Meema taga fuskata ina da tabbacin zata faWawa mahaifinta abinda ya faru da ita, nasan kuma ?arshe zan dauma ne a gidan yari, hakan yasa na koma wajan boka yace hanya mafi sau?i shine, a haukatar da ita ta mance kowa da komai kuma tayi nisa da garin da take, nan take na amince a kaiwa Meema aiki aka haukatar da ita, kafin na dawo hospital Win na nemeta na rasa, kuma boka ya tabbatar idan ba wani ya ?ara kusantar Meema ba babu yadda za'ai ta dawo hayyacinta, maganar fyaWe kuma ba zata taSa tunawa ba, da wannan na dogara amma kullum tunanin Meema yana zuciyata dashi nake kwana nake tashi ina yawan yin mafarkin ta, haka dai na jure har kawo lokacin da naji labarin Meema ta dawo gidan mahaifinta,
Naji tsoro babu shiri na nemi appointment na ganin President amma har naje na dawo gida bai min mganar yarinyarsa ba, har kuma kawo lokacin da naga Meema wajan taron masu sikila ta duniya, ban san yaya akai tabar hospital ba,ban san kuma Rayuwar da tayi bayan tabar hospital Win ba, haka kuma ban san lokacin data dawo gidan iyayenta ba kawo lokacin da hankalinta ya dawo jikinta, nine mahaifin Akeela haka kuma Meema itace mahaifiyar Akeela ina da Wannan tabbacin"
Wani irin raunataccen kuka Mom ta saka ita da Jadda, mazan wajan kowa shiru kawai sukai.
Meema dake waje kasa nutsuwa tayi ta mi?e tsaye sai kaiwa da dawowa take da Zuciyarta ta kasa jura sai kawai ta fashe da kuka.
Numfashi Dad yaja ya kalli Asheer yace.
"Kira min Meema"
Fita Asheer yay yana fita ya samu Meema tsaye ta ?an?ame Jikinta waje guda, a hankali ya tsaya a bayanta tare da Wan taSa ta, juyawa tayi a tsorace saboda gaba Waya a firgice take, tana ganin Asheer ta faWa jikinsa tare sanya masa kuka, kallonta yay sosai tare da faWin.
"What happened to you dear?" Cikin kuka tace "I'm scared mu bar nan please" tausayinta ya kama shi kenan Wannan dalilin shine yasa yaji Meema ba'a cikakkiyar mace ba?

_(Wai namijin da bai san budurcin mace ba, bai taSa mu'amala da mace ba tayaya yake gane ita ba cikakkiyar budurwa bace?)_
Rarrashinta yay cikin lallami yace "it's okay dear jikin Akeela zaki gani sai mu tafi"
Girgiza masa kayi tace.
"Are you sure?" Gira ya Waga mata yace.
"Of course habibty shall we?"
Kai ta Waga masa ya kama hannunta suka nufi cikin room Win, suna shiga Abbu ya wani ware idanunsa waje ba dai wannan ake magana akanta ba? Ashe zai ?ara ganinta? Daman Ubangiji na sane da addu'ar sa kenan?.
Meema kuwa girgiza kai ta fara lokacin da idanunta ya sauka akan Papi da kuma kan Abbu jikinta yana rawa ta fasa wata gigitacciyyar ?arar daya sanya Akeela ra zana ta ?an?ame hannun Akeem tana sauke ajjiyar zuciya.
Da sauri Mom da Dad suka nufi kanta Domin duk duniya basu da wani abu da suke so kamar Meema, ruwa aka yayyafa mata "Mom! Dad na shiga uku zai kashe ni dan Allah ka barni kada ka cutar dani" Wannan sune kalaman da Meema ta shiga faWa,
Rungome ta Mom tayi tare da sanya kuka,
Laylerh bata saba jin hayaniya haka ba, hakan yasa kanta ya shiga sarawa hawan jininta na neman tashi, a taushashe Aalam ya buWe baki cikin nutsuwa da kamala haWi da irinta Akeem ya kalli Azzam yace.
"Bani maganin Laylerh Azzam" fita Azzam yay babu jimawa ya dawo hannunsa Wauke da maganin, Aaliyah ce ta amsa ta bawa Laylerh tare da shafa hannunta.
Saukar Muryar Aalam cikin kunnuwan Akeem ba ?aramar haifar masa da kasala yay ba,
Gefe guda kuma yana jin sanyi na saukar masa.
A hankali Abbu ya kalli Meema yace.
"Ashe daman zan ?ara ganinki? Mene yasa kika tafi? Mene yasa kika barmu da ri?o har haka?"
Dad ne ya kalli Abbu domin yasan waye shi yace.
"Kai ma kasan Meema?"
Jinjina kai yay yace "Na santa sosai, lokacin ina neman takarar kujerar Wan majalista _(Members federal house of Representatives)_
Ina da wani Malami wanda yake yimin addu'a da saukar Alkur'ani, ya bu?aci kuma na taimaki mace wacce take halin rayuwa da mutuwa, na dawo daka wani meeting ina kan hanya lokacin ana tsaka da ruwan sama ina sauri na isa gida, nazo kan titin Sabon gari dai-dai gefen wata Bola idanuna ya sauka akan wata mahaukaciya wacce take tsirara babu komai jikinta, na jima ina kallonta ina jin inama na shige sai kuma na tuna da maganar Malamina, hakan yasa na sauka daga cikin motar zuwa wajanta, kanta a sunkuye yake ta ?an?ame Jikinta ruwa na dukanta amma hakan bai hanata ambaton sunan Allah ba,
Wajanta na nufa amma tsarin Halittar jikinta ya Wauki hankali na, yasa na shiga surutan da banma san ina yinsu ba, da ?yar na iya janyeta a wajan ina jin idan na taimake ta Tabbas bu?ata na zai biya, wani gida na shiga da ita a wannan lokacin na nemu mata biyu sukai mata hauka suka sanya mata kaya, bata duka bata magana sai dai ambaton Allah, akai akai taci abinci ta?i sai da akai mata allura Sannan bacci ya Wauke ta, kana likita yasa mata drip wanda zai taimaka wajan samun ?arfin jikinta, ni kuma ina fita na bawa wani babban Malami ya fara mata saukar Alkur'ani, daga nan kullum sai nazo wajanta da kaina nake bata abinci sai dai kawai tai ta kallo na bata magana, wani lokaci kuma kuka take na rasa kanta sai na rarrasheta da ?yar take yin shiru, kwanci tashi ta fara zazzaSi kwajin farko likita ya tabbatar tana Wauke da ciki, na razana sosai amma na dake naci gaba da kula da ita, har cikin ya isa haihuwa lokacin bana gari a ranar data haihu na dawo,
Ko gida banje ba na nufi wajanta amma babu ita babu labarin ta, sai yarinyar data haifa kwace cikin jini abin mamaki kuma an yanke cibiyar Yarinyar, neman duniya na nemeta na rasa,
Ina Waukanta kuma na nufi Wudil wajan Baffa na gaya masa komai hatta matarsa bata san zuwa na ba, ya amshi Akeela wace na bata suna iri na Akeem, Wannan shine"
Nan ma shiru akai har lokacin Mom kuka take hakama Meema.
Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke kafin Yace.
"Tunda yau ya zama ranar bayyana gaskiya nima zanyi amfani wajan faWawa Akeem gsky game da rayuwarsa"
Da sauri Akeem ya kalli Abbu cike da mamaki p.a kuwa Murmushi kawai yay.
Kallo ya koma kan Abbu inda yake faWin.
"Kamar yadda kayi tunanin cewa nine mahaifinka ba Gsky bane, baffa shine ya haifeka kawai ya bani kai saboda so da kuma ?aunar da nake maka"
Yana yin shiru p.a yace
"Baffa bai gaya maka gsky ba, amma gaskiyar magana tana cikin wannan ducoment Win"
Amsar ducoment Win Abbu yay, Aalam kuwa tuni jikinsa ya gama bashi Baffa baya raye tunda har yabar wasiyyar komai game da rayuwar Akeem.
A Wan razane Abbu ya Waga kai ya kalli Aalam kana ya kalli Akeem a fili kuma yace.
"Ikon Allah ga zahiri kuwa a bayyane, gaskiyar maganar sarauta da tace TSAMMACI ABINDA BAKAI TSAMMANI BA"
da rashin fahimta Arif yace.
"Mene a jikin ducoment Win?"
Ajjiyar zuciya Abbu ya sauke ya fara karatu abinda yake jikin ducoment Win kamar haka.

_AMIR AALAM ADIL_ shine gaskiyar sunan Akeem, Wane kuma ga Sarkin Makka wato Mai martaba Aalam Adil Jahid, bani na haifi Akeem ba ban taSa samun Wa ba, Ubangiji yayo ni Waya daga cikin wanda basu da rabon samun Wa a wannan duniyar, Wata rana munje aikin hajji nida matata Rabi bayan mun gama aikin hajji ciki ya bayyana a jikinta nan murna sosai, kai tsaye kuma na kira Wan uwana Bukari na faWa masa, a wannan lokacin kuma na samu ganawa da Sarkin Makka akan wani aiki Mutum mai karamci sosai wanda a lokacin sarkin Makkah ba kowa bane face Adil Jahid, lokacin kuma Aalam Wa ne wajan Sarkin Makka amma yana da mata wacce take Wauke da ciki itama amma nata ya samu kafin na Matata, kwanci tashi matarsa Laylerh ta haihu aka samu kyakkyawan yaro wanda babu na biyunsa a kyau, shine AMIR AALAM ADIL wato Akeem.
Bayan wata biyu da haihuwar Matata Rabi ta haihu yarinyar tazo babu rai, sosai nai ba?in ciki kuma nai addu'ar samun alkairi, Rabi kuma ta shiga duguwar suma bata san cewa yarinyar data haifa ta rasu ba.
A daran wannan ranar ina kwance a inda muka sauka naji ana buga ?ofar gidan da nake kamar za'a Salla ta, da sauri na fita ina zuwa naga Aalam cikin mawuyacin hali, jaririn hannunsa ya bani yace, jeka dashi na bar maka shi duniya da lahira inda address naka da komai, idan hali yayi zan sameka,
Cikin mamaki nace "Ranka ya daWe tayay zan iya kula da wannan jiririn? Bayan shi Win tsantson sarauta ne" cikin kuka Aalam yace
"Kai naji kana addu'ar samun zuri'a ta gari, ka Wauka Amir kai ne ka haifesa na tanadi keSantaccen jirgi yanzu zai Wauke ku yanzu zuwa Nigeria, ban baka ko sisi ba domin kula da rayuwar Amir ina so ka rainesa da halaliyarka ka Wauke sa matsayin Wan daka haifa, amsar Amir nayi aka samu mota aka sanya rabi ciki wacce har lokacin bata tashi daga duguwar suma ba, muna zuwa airport zamu shiga jirgi na Wauki photona wanda muke tare da Bukari na bawa AALAM, saboda koda babu raina ya shaida fuskar Aalam, akan idanunsa jirgin mu ya tashi, ashe wai a can gidan sarautar Mai martaba Adil ne yay murabus ya Wura Aalam akai, shine wani yabi dare ya kashe Mai martaba ya kuma nemi kashe jaririn, dalilin daya Sanya kenan aka bani ri?on Amir wanda na sauya masa suna zuwa Abdul-hakeem ina kiransa da suna Maudo domin na lura mahaifiyarsa bafulatana ce, duk wannan lokaci sau Waya muka samu ganawa da Mai martaba Aalam wanda ya sauka 9ja muka haWu dashi a keSantaccen waje lokacin shekarun Akeem 10 ciff a duniya a lokacin na faWa masa na sauya masa suna kuma ina Kiransa da Maudo,
Dai-dai lokacin muka shiga fari gonaki suka bushe saboda wani lalataccen taki da ake bamu, albarkatun noma suka lalace, wannan dalilin yasa nace Bukari ya sanya Akeem bangaren Agriculture, ban taSa nunawa cewa ba Bukari bane ya haifi Akeem domin tun yaye na barshi gidan Bukari lokacin matarsa ta haifa Wa mai suna Adnan,
Har yanzu dana rubuta Wannan wasi?ar Rabi bata san abinda data haifa ba shine Akeem ba.

Wata ajjiyar zuciya Laylerh ta sauke, yayinda Aalam kuma ya zame a hankali tare da kallon gabas yay wa Ubangiji godiya, ta hanyar yin sujudil shukri,
Akeem kasa motsi yay, wato bayan zallar so da kuma ?aunar da ya kewa Akeela harda so irin na haWuwar jini,
Yana jintae a dukkan wata ?ofa ta cikin zuciyarsa, Wannan dalilin yasa Amani ke kama da Akeela, Akeela kuma ke kama dashi ga kuma kamar da Meema take da Akeele, Al-hakkamu kenan bowayi gagara Misali, wanda bai ji tsoron Allah ba ya shiga uku,
Mulki ya sanya kayiwa Wan uwa musulmi illa, yasa ka kashe mutum ka haukata mutum, haka kuma kyakyatatawa mutum zato yafi ka muzan tashi, ka kalli mutum kawai ne amma kasan baiwar dake jikinsa ba,
Haka kuma haifar yara irin su Akeela baya nufin zina akai aka haife su, zina shi ne yin sex ta hanyar amincewar ko wanne jinsi,
Amma ita Akeela fyaWe akaiwa mahaifiyarta kuma aka haukata ta Wannan dalilin yasa akai mata kallon TSINTACCIYA.
Gama Labarin yay dai-dai da ?arewar jinin da aka sanyawa Akeela lokacin kuma yaja domin har anyi sallar Asr,
Ganin jinin ya ?are yasa Akeem zare mata jinin bai kula kowa na Wajan ba ya sanya hannunsa duk biyun ya Wauki Akeela zuwa ?irjinsa ya rungometa sosai, yana shirin fita Papi yace.
"Ina zaka jemin da yarinyar?" Wani mugun kallo Akeem ya watsawa Papi yace "kai ba kaji kunyar faWin abinda ka faWa ba?"
Papi yace "koma mene i made a mistake, amma ka sani Akeela ?arta ce ina da ikon zartar da komai a kanta dan haka ka ajjiye min ita nan mu huce gida taga gidan ubanta"
Banza Akeem yay masa ya nufi ?ofa da sauri Papi yasha gabansa yace "wlh ka fitar min da yarinya sai na kaika Court" Aalam gyara zama yay ba tare da yace komai ba, Tabbas Papi yana da iko akan Akeele domin jini yafi ruwa ?auri, blood is thinker than water amma shima Akeem akwai jinin Akeela dake gudana a nasa jinin,
Rai a Sace yace "kafin ka kaini Court ni na jima da makaka a Court lokacin kawai nake jira kuma yanzo" ganin abin na neman zama faWa yasa Abbu faWin.
"Dr bashi ?arsa"
Kamar Akeem zai kuka yace "Abbu why?" Cikin Waga Murya yace "nace ka bashi ?arsa ko? Ai ya fika iko da ita dan haka ka bashi ita ka huce muje"
Sai a lokacin P.a ya Wan shafa kai kana yace.
"Meyasa zai bashi ita Abbu? Bayan cewa ita Akeelar matar Akeem ce...


TSINTACCIYA is not free contact to subscribe
08119237616
Dan Allah dan girman Allah kuji tausayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login