Showing 300001 words to 303000 words out of 413917 words

Chapter 101 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

2713

da toh sannan ya faWa masa date din daya kamata su je, kamar yadda tsohuwa Khala ta shawarce shi da su kai farmaki adaren ranar, amma bai sanar da shi daren menene ba.

Da tsantsar farin ciki Chief Ya ru?o hannayen Danish a cikin nashi ya ruke su gam.

"Bansan taya zanyi maka godiya ba, kalmomi sunyi kadan Danish, Ka faWamin duk wani buri da kake son cimmawa, Ni kuma na maka al?awarin In har baifi karfina ba zan cika maka shi"

ya faWa da Wan murmushi kan fuskarshi, Danish bai furta komai ba, sai faman lumshe idanun shi yakeyi kamar gyangyaWin bacci ya ke yi.

Lura da hakan yasa Chief ya ru?o hannayen shi Ya taimaka mashi Ya kwanta kan gadon, wani irin bacci ne mai nauyin gaske yayi awon gaba da shi.

(Lallai Gadon Chief Yayi albarka, Unaisah ta kwanta, Ga Danish ma Yayi bacci akan shi=?? saura ni ma zan Wana)

_________________________________
'?

Da yammacin Ranar, Chief Ya kira Meeting din gaggawa wanda su kayi A headquarter din su tare da Manyan jami'an Isod dana Sojoji, da kuma U.s army, gaba Wayan su suka hallara a meeting room Winsu, bayan Chief ya kunna masu audio Win daya dauka na tattaunawar shi da Danish, sunyi matu?ar yin mamakin amincewar shi, musamman big guy, sun kuma ji dadin yadda ya basu hadin kai cikin sauki batare da sun sha wahala ba, ba tare da 6ata lokaci ba, kowa Ya fara kawo shawarar shi dangane da yadda zasu kai farmakin, babu wanda bai tofa albarkacin bakin shi ba, basu suka tashi meeting din ba, har saida suka tsayar da kwanan watan da Danish Ya faWa ma chief amatsayin Ranar da zasu kai farmaki.


Tun daga ranar su ka fara shirye shiryen tafiya Ya?i babu kama hannun yaro, basu da wani hutu, gagarimin shiri suke na musamman kuma komai nasu cikin sirri suke yin shi saboda tsaro ba don tsoro ba, sun tanadi Miyagun Makamai da zasu yi amfani da su agurun gabzawar.

Tawagar Dakarun sojoji Uku ne zasu je kai farmakin, tawaga ta farko Isod Soldiers ne, bayan su sai Tawagar Sojojin Nigeria, Tawaga ta uku ta U.s Soldiers ce.

a bangaren Unaisah Da Danish tun ranar da ta tursasa mashi akan ya amsa zai basu hadin kai, basu ?ara haWuwa da juna ba, walwalarsu ta ragu, rayuwarsu ta ?untata saboda tsantsar damuwar da suka shiga na fargaban kada su rasa junan su, bayin Allah ta ko'ina ba sau?i, kokari sukeyi su saba ma kansu rayuwa batare da juna ba don su saukaka ma kansu radadin son juna da suke ji a zukatansu, sai dai abun yaci tura, abun sai ya zamana kamar suna kara rura wutar son da suke ma junansu ne.

Ba karamin maraicin shi takeyi ba, saboda shirya shiryen da sukeyi na tafiya ya?i yasa baya zama gidan, atare da chief suke zuwa headquater saboda taimakon da yakeyi masu gurin ?ara wayar masu da kai game da kurkukun ?addara, Saida takaiga idan Chief yaje da shi headquarter din su jami'ansu ji suke da shi suna masa biyayya kamar dai chief din, wani irin farin jini gare shi, abunda yafi burge su da shi karfin da Allah yayi mashi, ga kaifin basira da Allah ya bashi, har jaraba shi sukayi ta hanyar haWa shi da ?arfafan Isod soldiers don suyi wrestling da shi, saboda su tabbatar idan giant basa jin bugu aikuwa sun sha ruwan mamaki, Isod Soldiers din da suka hada shi da su gurin damben su kusan hamsin saida Ya sumar da su, a hakan ma baiyi masu bugun da zasu raunata ba saboda baison yai masu illa shiko ko kwarzane ba su yi ma shi.

Idan suka tafi Basu tashi dawowo gida, sai marece idan ya dawo agajiye daya samu yayi wanka ko abinci bai nema bacci yake yin awon gaba da shi, baya tashi farkawa sai lokacin da dare ya tsala kowa yayi bacci tukunna ya ke tashi yaci Dinner din shi.

dauriya kawai yakeyi amma kewarta na neman tayi mashi illa, haka itama ko abincin kirki bata ci, ta rame tayi haske sosai kamar babu jini a jikinta, kullum a bedroom Winsu take killace kanta bata son kowa ya ra6e ta, tafi son kadaici duk da ba karamin azabtuwa takeyi ba na rashin ganin shi, tun tana 6oye abun da ke damunta idan yan uwansu suka matsa mata musamman auntyn umminsu har takaiga sun gano da kansu saboda kauracewa junan da sukayi ita da Danish, nema take ta zauce kullum ciwo ba koshin lafiya, abinci sai aunty ummi tayi mata dole take cin shi akarshe ma ta amayar da shi a toilet ba tare da sanin su ba, bacci Ya kaurace ma idanunta idan dare yayi haka zatay ta juyi kan gado rungume da pillow a kirjinta, idan abun ya isheta nafilfili take tashi tayi kuma duk akansu takeyin sallar, wani lokacin akan prayer mat baccin ya ke yin Awon gaba da ita. wannan wani irin Azababben So neS'


Gaba daya abunda ke faruwa Taj baisani ba, saboda shima ba zaune ya ke ba, ummi har yunkurin kiranshi tayi don ta fada mashi halin da Unaisah take a ciki na rashin Lafiya amma Unaisah ta dinga rokonta akan kada ta sanar da shi saboda gudun faWan da zaiyi mata, dakyar ta samu Ummi ta fasa kiranshi bayan ta gindaya mata sharadi akan bazata ?ara fashin cin abinci ba, tace mata eh ta amince ahaka ummi ta samu ta Wan shawo kanta.

Kamar yadda boyayyan mutumin nan Ya ba Chief shawarar su sanya manyan Malaman addini suyi masu addu'a, bai yi ?asa a gwiwa ba, ya tuntu6i shiekh Imam malik awaya, Ya nemi alfarmar yana son su haWu anan gidan shi.

Shiekh imam yace mashi in sha Allah zai shigo gidan.

After Magbrib Bayan sun kammala yin dinner din su, ba suje sun kwanta ba, gaba Wayan su suna zaune a falo, sunyi shiru babu mai magana acikinsu, kwata kwata babu annuri akan fuskokin su, gashi dai sun sanya kayan baccin sai dai baccin Ya kauracewa idanunsu saboda damuwar da zuciyoyin su suka shiga, babban tashin hankalinsu jin za'a tafi da Garkuwarsu, babu irin magiyar da basuyi ba akan suma atafi da su amma Salsabeel yace bazai yiwu ba, suyi hakuri su biyu sun isa suyi ma Sojojin jagora.


Unaisah ta ?wallafa rai akan son aje da ita kuma har yanzu tana akan bakanta don bazata bari su tafi da Danish batare da ita ba, abun daya daure masu kai har yau babu wanda ya faWa masu date din da zasu je kai farmakin, duk in suka tambayi Taj ko big guy sai suce masu basu fidda lokaci ba, haka shima Danish yake fada masu, gaba daya sun yarda da maganarsu, Unaisah ce kadai hankalinta bai kwanta da zancen ?in bayyana masu kwanan watan ba, ta fahimci sun haWa baki ne, ranta yana bata tafiyar bazata zasuyi batare da sanin su ba shiyasa suka shirya hakan, tun da ta fahimci hakan kusan kullum sai ta addabi daddynta da Salsabeel akan su faWa mata date Win amma suka ?iya, tayi magiyar tayi rigimar duk abanza, harta hakura tadaina tambayar su, ta dai zuba ma sarautar Allah ido.

Fitowa Ummi tayi daga Bedroom dinta, jikinta sanye da doguwar rigar bacci, ta zuba hannayenta cikin aljihun rigar,

Daga inda take ta hango su zazzaune kan sofas na falo, sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki.

Girgiza kai tayi tare da zaro waya daga aljihu ta kira Layin Boss.

Bayan yayi picking suka gaisa cikin girmamawa kafin tace"yalla6ai akwai matsala fa, Yaran nan sun?i zuwa su kwanta ga su can zaune falo sun zabga uban tagumi kamar masu zaman makoki, Ni nasan bai wuci zancen tafiyarku bane Ya Waga hankalin su..." ta fada fuskarta ayamutse.

Muryarshi da damuwa ya furta"Ya sallam, Ummi pls ki yi ko?arin kwantar masu da hankalin su"

"Wallahi ba irin lallashin da banyi masu ba, amma duk abanza"

"Ummi, ki zauna dasu, yanzu zamu shigo gidan In sha Allah"

"Okay, Allah ya dawo daku lafiya"

"Ameen" da ga haka Su ka yi sallama.

Saukowa down tayi, har ta shigo falon ba su ankara ba.

Sau uku tanayi masu sallama babu wanda Ya amsa mata saboda Hankalinsu baya atare da su.

Binsu da kallo ta yi, daga wanda ya Wage kai sama, Sai wanda Ya langwa6ar da kan shi jikin Sofa, kowa dai da alkibilarsa da ya kalla

Bakowane Yafi bata tausayi ba, face Unaisah, baiwar Allah ita kadai ce kwance Kan rug, yadda kasan tsumma, ta nannaWe guri guda kamar kifin gwangwani ko motsi batasan yi.


Kware murya tayi da karfi ta furta"wai bakwa ji nane"? A firgice suka zabura kowannan su Ya gyara zaman shi, kusan atare suka dube ta, In ka cire Unaisah wanda ko gizau batay ba, tana nan yadda take a kwance..

"Aunty ummi har kin bamu tsoro," hanna ce tay maganar.

Haris Yace"wai har yanzu basu dawo ba"?

"Aunty ummi, ko zaki kira mana su? Mun yi ma Unaisah magana tace wai batasan inda ta jefa wayar ta ba, kuma mun duba bamu ganta ba" acewar Batool..

Naufal yace"pls Aunty Ummi, nasan ba zaki rasa sanin ranar da zasu tafi ba, dan Allah ki faWa mana wlh munyi maki alkawarin ba zamu faWa masu mun sani ba"

Bata tanka masu ba, wuri ta samu kan Sofa ta zauna, batare data kauda ido daga kallon su ba.

Calmly tace"yanzu nayi waya da boss, Yace min suna akan hanyar su ta dawowa gida.."

"Aunty ummi duk ba wannan ba, kawai ki fada mana ranar da zasu tafi, in ba haka ba hankalin mu bazai kwanta ba" acewar Naufal.

"ku yarda dani, wlh nima bansan date din da zasu tafi ba, har tambayar boss nayi yace min basu fidda rana ba, kunsan yanayin aikinsu na jami'in sirri, kuskure kadai zai iya lalalata shirin su, yakamata mu fahimce su ko"

ta fada cikin kulawa tana kallon su.

Sarah tace"amma ay ba laifi bane in mun sani, zamu tayasu da addu'a ne kawai,"

Murmushi ummi ta Wanyi"in zaku tayasu da addu'a ay ba dole sai kun san ranar da zasu tafi ba, wannan baya daga cikin sharuddan yin addu'a"

"Look aunty ummi, kin san komai, kawai kina boye mana ne" fuska a daure Sajeed Ya faWa.

Yar dariya tayi"dama nasan zaiyi wuya ku yarda dani, in ma baku yarda ba toh kada Allah yasa ku yarda" ta fada tare da yi masu dakuwa da hannunta, tuntsirewa su Ka yi da dariya itama dariyar tayi

"Kun fiye taurin kai Allah, haba mana, kusan karfe tara, Yakamata kuje ku kwanta, ga little sisters dinku nan sai gyangyadin bacci sukeyi nasan saboda ku yasa suka ki zuwa su kwanta bacci" ta fada tana nuna Azeeza da jemimah da hannunta sun manne ma juna sai gyangyadi su ke yi..

"Hmm aunty ummi kenan, Salon muje mu kwanta bacci, lokacin da zamu farka ace mana sun tafi ko? Da fa wayon mu" dariya tayi sosai maganar javed ta sanyata nishadi.

Mikewa tayi ta nufi sofa din da su jemimah suke a zaune, ta dauki jemimah ta goya abayanta, kafin ta tada Azeeza tana layi ta mike kamar wadda tasha kwaya..

Ruko hannunta tayi, ta nufo bedroom dinsu dasu, sai da ta tabbatar sun kwanta bacci ta kashe masu switch din dakin tana kokarin fitowa unexpectedly Jiniyar motocin dake shigowa gidan ta karaWe kunnuwan su.

Kusan atare suka mimmi?e tsaye suna jiran shugowar su, Unaisah ce kaWai bata motsa ba tana nan inda take akwance..

Cikin takun sauri suka fara shigowa falon, Chief ne agaba hannun shi ru?e dana Danish daga bayan su Shiekah Imam Malik ne, Yayin da Boss da big guy hada ma Salsabeel su ke abiye dasu, mutun biyune babu kaki a jikin su, Danish da Salsabeel, black jean da wh???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ite shirts ne a jikin su kala Waya.

Tun da Ummi taji Sallamar shiekh Imam malik, ta kasa fitowa daga dakin su Jemimah..

Kusan atare suka ci burki suna kallon su, sun yi mamakin ganin su a tsaitsaye curko curko suna ganin Danish jikinsu har 6ari yake garin saurin su karasa gare shi, daya bayan daya saida yayi huggin din su duk da agajiye yake har wani jiri jiri yake gani acikin idanun shi..

Atare suka hada baki gurin yi masu sannu da dawowa, kafin suka gaishe da shikeh imam malik cikin girmamawa..

"Sheikh, mun jima bamu ganka ba, kamanta damu" sajeed ne yai magana

Tattausan murmushi shiekh imam Ya sakar masu"masha Allah na ji dadin ganinku cikin koshin lafiya, Yan jikokina, ban manta daku ba, kuna araina, duk in zanyi addu'a saina sanyaku a ciki" murmushin farin ciki suka saki..

Gaba daya hankalin Taj baya akansu, Yar shi Yake nema Yaga babu ita a cikin su, baisan awani hali take ciki ba, ya yi kewarta ba kadan ba..

"Bismillah, mu shiga ciki" big guy ne ya fada tare da nuna masu hanya

Kafin su karaso, da sauri Unaisah ta mike cike da rashin kwarin jiki ta zauna.

Bayan sun karaso cikin falon Prisoners gaba daya suka zauna kan rug, su Chief suka zauna kan sofas din.

Kwata kwata basu lura da ita ba, ganin daddynta ya mi?e yana kokarin nufar dakinsu yasa tay karfin halin furta"sannu ku da dawowa, ya gajiyar aiki" atare suka dago suna kallon ta, haduwar idanunsu Cikin na jina yasa Danish yin saurin kawar da fuskarshi gefe daya saboda kallonta da yakeyi ba karamin karya mashi zuciya yakeyi ba, hakan da yayi ya sanyata jin wani iri a azuciyarta, gani take kamar fushi yake da ita..

"Unaisah Lafiyarki kuwa? Meke damunki"? Taj ne ya tambaya yana kallon ta..

Murmushi ta kakaro kan fuskarta"bakomai daddy, idan ma akwai abinda ke damuna, bai wuci zullumi da fargaban tafiyar ku bane"

Jiki asanyaye Taj ya zauna gefenta, tare da ruko hannayenta acikin nashi.

Hankalin Chief gaba daya yana akansu, shi kanshi Ta bashi tausayi ya lura da ramawar da tayi.

"Pls ku bamu aron hankalin ku nan" big guy ne yai maganar, gaba daga suka dube shi, a lokacin Unaisah ta kwantar da kanta saman kafadar daddynta..

"Ina Auntyn naku take"?

"Taje ta kwantarsu da su jemimah dakin su, har yanzu bata fito ba"

"Okay, wani ya kira mana ita"

Har mubeen Ya mi?e zaije kiranta, sai gata ta fito komawa yai ya zauna..

Tana karasowa, cikin sanyin murya tayi masu bangajiyar aiki, kafin ta dubi sheikah Imam malik kallon juna sukayi ido cikin ido daga gani sunyi kewar ganin junansu
Muryarta na dan rawa ta furta"ina wuni sheikh ya fama da jama'a.." tamkar bazai amsa mata ba, ya furta Lafiya..daga haka Ya kau da idanun shi gefe Waya.

"Bismillah, Ki zauna" big guy ne ya fada tare da nuna mata sofa, bayan ta zauna falon yayi tsit baka jin motsin komai kamar mutuwa ta gifta.

Gyaran murya sheikh Imam Yayi tare da duban Chief yace"Owais, meke faru ne? naga kamar wani abu na damunku, daga ku har yaran babu mai walwala, ince dai ko lafiya"? Jinjina mashi kai chief yayi"kada ka damu, babu wani abu." ya fada tare da kallon Omar batare daya furta mashi komai ba, da ido ya fahimci me chief yake nu fi..

A tsanake ya fara labarta ma Sheikh Imam, dangane da shirye shiryen da suke yi nakai farmaki, sai dai ba komai ya faWa masa ba, ya dai ce mashi miyagun yan'ta'addane kuma matsafa ne masu hadarin gaske zasu je kaima farmakin a kurmin daji..

Sheikh Imam Malik Ya jinjina lamarin, tun da big guy ya fara zayyana mashi, Yake ta dan jinjina kan shi alamar ya girgiza da jin zancen.

Chief Owais Ya daura da cewa"baba, alfarmar da muke nema agurinku, munaso ku haWa kai da manyan malamanmu na addini don ku yi mana addu'o'i, sannan zamu bada abun sadaka abawa mabukata da marayu suma su taya mu da addu'a."

Numfasawa sheikh Imam yayi fuskar shi dauke da matsananciyar damuwa yace"Owais, Kunyi tunani mai kyau, tabbas tunkarar miyagun matsafa ba abune mai sauki ba, mutanene masu haWarin gaske, amma ta inda kuka fi su ku kun dogarane ga Allah ne, kuma kun yi imanin shi ne zai baku nasara akan su..." ya fada yana Wan jinjina kanshi

"In sha Allah Owais, tun da har kuka nemi mu taya ku da addu'a zamuyi aiki tukuru, bi'iznillahi ba zasu ta6a cin galaba akan ku ba, saboda kyakkyawar niyar da kuke da ita na ganin kun kawar da masu aikata fasadi adoron kasa.." gaba daya sunji dadin furucin sheikh Imam malik

"Zan iya sanin yaushe ne zakuyi tafiyar"? prisoners duk sun baza kunne suna jiran jin amsar da chief zai ba shi.

"bamu fidda rana ba, amma a kowani lokaci zamu iya tafiya"

"Okay, in sha Allah zuwa gobe da safe zan sanarwa yan uwana malamai yan team dinmu wadanda nayi imanin in har muka hada kai da su gurin yi maku addu'a babu wani mahalukin daya Isa Ya ci galaba akan ku, Sihirinsu bazai ta6a tasihiri a kanku ba, in ba wani iko na Allah ba....."

Gaba Waya sunji dadi maganar shiekh Malik,

"Amma, malam, Danish har yanzu bai musulunta ba" gaba daya suka maida hankali akanta, sunnar da kanta kasa tay, ganin irin kallon da daddynta yayi mata.

A hankali suka maida duban su ga Danish, wanda ya dafe goshinsa da tafin hannun shi

Salsabeel Yace"kamar kin shiga zuciyata Unaisah, wlh tun dazu nake ta zucci zuccin inyi mashi maganar shi, gaba daya mun damu da rashin addininsa"

Chief yace"nima abun na damuna, ataimaka mana sheikh, a karkato mana da hankalin shi Ya kar6i shahada, kafin lokacin da zamu tafi"

Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, babu wanda baiyi magana ba, akan damuwar su na rashin addinin Danish In ka cire Big guy ko kadan bai sanya baki a maganar ba.

"Danish, Har yanzu baka da ra'ayin kar6ar addinin musulunci"? Shiekh imam ne ya tambaya yana kallon shi..

Gaba daya sun kagara da su ji me zai ce

Sai da ya mula ya sha iska kafin ya firta"bani da ra'ayi,"

"Meyasa"? Shiru yayi bai tanka ma shi ba.

Hakan ba karamin karya zuciyoyin su yayi ba..

"Inason Yin magana dakai, a Wakin ka" bai yi mashi musu ba, Ya mike sheikh Imam Yabi bayan shi suka nufi second floor har dakin danish bayan sun shiga Shiekh Imam Ya kulle Kofar.

Gaba daya sun kagara da su fito, fatan su Allah yasa Ya kar6i musulunci.

Kasa kasa da murya Taj yace ma Unaisah"kun ci abincin daren ku"?

"Eh daddy,"

"Pls ki daina sanya damuwa aranki, banason ganin ki a rame haka babu walwala, in har saboda tafiyar da zamuyi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login