Showing 390001 words to 393000 words out of 413917 words

Chapter 131 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4483

ta saka Wani guntun veil a kafadarta, baiwar Allah duk sai taji ba dadi ganin yadda abaya din ta Wame jikinta, dirinta nan nata mai jan hankali ya bayyana muraran musamman ta gurin mazaunanta sun fito rudu rudu..

ahaka Banezir taja hannunta suka tafi gidansu, shigarsu keda wuya ta gate din adai dai Lokacin Alhaji musa Yana atsaye gaban dankareriyar motarsa ya dauki wankan shadda hannunsa ruke da waya, kallo daya da Aisha tayi mashi saida gabanta ya fadi saboda ?warjinin dake gare shi, wata irin kirar jiki gare shi irin ta yan dambe.

Benazir ce ta gabatar mata da Uncle dinta, duk irin izzar Alhaji musa da yayi tozali da Aisha saida Ya rasa nutsuwarsa saboda shi irin mazan nan ne masu kwadayin mace mai kyawun sura, sanin da yayi mata tuntana karamarta yanzu kuma ta girma, wani irin kallo yadinga binta da shi harya kasa amsa gaisuwar da ta ke yi mashi, A lokacin rudewa Aisha tayi saboda bai kwanta mata arai ba, musamman da ta ga hakoransa ya sanya masu Gold-plated teeth..

ita kanta Benazir ta lura da yanayin da ya shiga. Hakan yasa taja hannun Aysha suka nufi cikin gidan, Uncle musa yabi bayanta ta da kallo yanayin yadda take tafiya jikinta na girgiza ba karamin tayar masa da maitar sha'awarsa tayi ba, kuma tun daga lokacin ya kudiri aniyar saiya mallake ta.

Bayan sun shiga babban falon gidan, anan suka iske Hajiya layla tare da Alhaji ubaid suna zantawa tsakaninsu, bayan sun gaishe dasu hajiya layla tace su shiga ciki su gaida shureim..

Tun da Allah Ya Halicci Aishatu Bintu Imam bata ta6a ganin mutumin daya kwanta mata aranta ba, da kallo Waya ta fada tarkon son shi sai akan dr shureim yanayin da suka same shi adakin shi yana zaune kan darduma Ya buWe al'kurni yana karatu cikin nutsastsiyar Muryarsa ba karamin jan hankalin ta yayi ba, tayi mamakin girman daya ?ara tsawon shekaru a lokacin rabon shi da Nigeria.

Sai da yakai aya, cikin sanyin murya yace masu su shigo yaga sun yi tsaye bakin kofar dakinsa, Jan hannunta Benazir tayi suka zukunna agaban dardumarsa ta gabatar masa da aminiyarta yar makwabtansu diyar sheikh Imam, ganin kamar bai gane ba don tun suna kanana Yabar Nigeria, Aisha ta gaishe da shi tare da yi mashi bangajiyar tafiya, da murmushi akan fuskarshi ya amsa mata, abunda bata sani ba Dr shureim yasan da zamanta, Yana yawan sauraron kira'arta da take yawanyi a taron musabaka, wanda mutane ke yaWa videon a social media amma saboda miskilancinshi sai ya nuna kamar bai gane ta ba.

sun Wan jima Yana jan su da fira, lokacin da ta tashi tafiya dr shureim ne ya yi mata rakiya tare da Benazir har kofar gidansu, saida suka ga shigarta kafin suka koma gidan su.

a daren ranar Alhaji musa Ya kira Benazir ya soma tambayarta dangane da Aisha, ko tana da tsayayyan da zata aura"? Benazir tayi mamakin tambayoyinsa saboda tasan Uncle din nata mugun miskiline bai cika shiga sabgar da bata shi ba, In fact mata basa agaban shi bata kawo komai aranta ba ta fada masa komai dangane da Aisha, Hankalinsa ba karamin kwanciya yayi ba jin cewa bata kula samari, fargabansa daya Sheikh Imam malik saboda basa ga maciji.

A bangaren Aisha tun bayan data koma gida tunanin dr shureim Ya hana zuciyarta sukuni, Kwana take da shi aranta, haka zalika in tana koyama dalibanta karatu wasu lokuttan shagala take da tunaninsa har sai daliban su ankarar da ita.

ta bayan fage Uncle musa ya fara ba Banezir makudan kudi masu auki don suje yin siyayya da Aisha, kuma yace mata baya son Aishar ta sani, Benazir bata ta6a fada mata Uncle musa ne ke bata kudi ba, Sai ma in ta tambayeta ina take samun kudi sai tace dr shureim ne ya bata, hakan ya sa ta saki jiki duk da bata da kwadayin abun duniya tayi azan yaya shureim yana son ta ne shiyasa yake ba Benazir kudi don suyi siyayya.


kusan kullum sai Aunty laura tayi masu hanyar fita daga gidan batare da sanin Shiekh Imam ba, don suje Mall suyi siyayya harma da yawon buWe ido koda Aisha ta nuna bata son fita Aunty laurace ka tursasa mata in ta turje sai ta fashe mata da kuka tana fadin bata mata biyayya saboda ba ta Wauketa uwa, don taga ita bata haihuwa, in ta fadi hakan jiki na rawa Aisha take bin Umarninta.

Tun bata sake ma Uncle musa in suka haWu harta fara sabawa da shi, tana matukar girmama shi tanayi mashi kallon Uncle dinta.

Haka zalika shakuwa mai karfi ta shiga tsakaninta da dr shureim, Benazir tayi mamaki saboda sanin da tayi ma Aisha bata Kula maza sai gashi dr shureim ya ciri tuta, sun saba da juna, Benazir ta sanya masu ido sosai, Ta fahimci dukansu suna son juna, ita Aisha Kunya ce ta hana ta furta mashi Kalmar so, yayin da shi kuma miskilanci ne Ya hana shi bayyana mata, bayan haka Yana jin nauyin yayi soyayya da Aisha saboda yanayi mata kallon Kanwarsa.


A duk lokacin da Benazir taso Ta bugi cikin shureim don ya fada mata In yana son Aisha sai yace mata shi babu soyayya atsakaninsu kallon kanwa ya ke yi mata, haka In ta bugi cikin Aisha don taji in tana son ya shureim sai tace mata ita fa ba son shi ta ke yi ba, kawai tana yi mashi kallon yayanta ne saboda zumuncin dake a tsakaninsu, In Benazir zata shekara tana tambayarsu amsa daya suke bata.

Bayan da suka kammala Secondry School, Alhaji Ubaid ya sama masu admission a wata Jami'a dake a birnin hagen na kasar Jamus batare da sanin sheikh Imam Malik ba sai daga bisani ya same shi har gida ya sanar da shi.


shiekah Imam bai nuna amincewarshi ba, Yace shi bazai bari yarsa ta tafi uwa duniya karatu ba, duk Universities din dake a Kasar har sai an fita waje neman ilmi? Alhaji ubaid ya ce yayi hakuri da bai nemi shawarar shi ba ya tashi ya yanke hukunci dama yaga Benazir ta kwallafa rai ne akan son zuwa can tayi karatu kuma ta nuna tana son suje tare da Aisha shi kuma yayi la'akari da shakuwar dake a tsakaninsu In aka rabasu ba zasu ji dadi ba shiyasa ma har ya nemi Benazir data kar6o ma shi Academic record din Aishah.

A ranar da su ka yi maganar, bayan Alhaji ubaid yayi mashi sallama ya tafi, ranshi a bace Ya kira Aisha ya fara mata fada akan takardun karatunta data kai ma Alhaji ubaid don ya sama mata admission, tace mashi wallahi ba ita ta bashi takardun ba, hasalima ita batasan da maganar ba, ko da jin hakan nan take ranshi ya bashi da sa hannun Aunty Laura, Har daki Yaje ya same ta da maganar, maimakon ta kar6i laifin ta saima ta dinga masifa tana fadin taje ta bada kuma wallahi bai isa Ya hana Aisha taje karatu kasar waje ba, shi ko dan zumuncin dake a tsakanin shi da Alhaji Ubaid bazaisa Ya amince be? Idan Ma yana jin tsoron wani abu ya same ta acan din Ba Allah ke tsare bawansa ba, bayan haka tun da Ba ita kadai zataje ba hada Benazir ya bar ta mana, shiekh imam yace mata ya gama magana bata isa tasa shi canza ra'ayin shi ba.


Ganin da gaske Shiekh Imam zaiyi mata bukulun kudin da take samu agurin Alhaji musa yasa ta kwashi kafa taje gidan kakarsu ta bangaren Uba da ta rage masu mai Suna Hajjo, ta tsara mata karya da gaskiya akan kullan da Sheikh imam ya ke yi ma yarsa, ta ce ita bakin cikinta gorin da ya ke yi mata akan Aisha sai kace ba diyar yayarta ba, In da kara aisha ai yar ta ce tana da ikon juyata son ranta, bayan haka ta fada mata Alhaji Ubaid Ya sama ma Aisha gurbin karatu a kasar germany ita da Benazir amma Ya hana bai dubi zumuncin dake a tsakanin su ba, Hajjo da ranta ya 6aci ta sa Aunty laura ta kira mata imam a waya tace yazo tana son ganin shi, koda yazo ta balbaleshi da fada kamar zata rufe shi da bugu kasancewar shi mai biyayya yadinga bata hakuri kamar zai durkusa mata kasa tace mashi in har yana son farin cikin ta yabar Aisha ta tafi karatu kasar germany, Shiekah imam yayi kokarin ankarar da ita illar dake akwai na tura Wa karatu kasar waje balle ita da take mace amma Hajjo ta rufe ido tace itafa ta gama magana, kawai yabi abunda tace mashi, ta ko'ina ta matsa mashi lamba ba dan yaso ba ya amince zai barta, don yasan halin Hajjo rikicin tsufa ne ke damunta.

bayan komawarsu gida baibi takan Aunty Laura ba Ya kira Aisha ya tambayeta da son ranta zataje kasar waje karatu? Aisha tace aa bata so saboda batason tayi nesa da shi, amma benazir ta nuna tana so suje suyi karatun atare acan tun da ba wasu shekaru ne masu yawa ba" a maganarta shiekh ya fahimci bada son ranta ba amma tana son ta bi aminiyarta ba yadda ya iya hakanan ya amince.

Bayan Alhaji Ubaid Ya kammala yi masu travel arrangement, ana i gobe zasu tafiya sheikh imam bai iya runtsawa ba, saboda zazza6in tafiyar da Aisha za ta yi, wannan ne karo na farko da zatayi nesa da shi, bawan Allah akan dardumarsa Ya raba dare yana yin nightprayers duk akanta, washe garin ranar aunty laura ta shirya ta tsaf, a motar sheikh imam suka tafi, acan airport suka hadu da Benazir tare da family dinta da su ka yi mata rakiya, Aisha tasha kuka na rabuwa da Baba imam, har nasiha yayi mata akan ta ji tsoron Allah, kada ta canza a yadda yasan ta, sannan ta kare mutuncin kanta, karatu yakaita daga shi bai amince tayi wani abu da zai sa6awa mahaliccinta ba.

Baba imam bai ?yale Aisha hakanan ba saida Ya hadasu da Benazir ya karayi masu nasiha mai tsuma zuciya sannan ya dam?a ma Benazir amanar Aisha yace ya yarda da ita bai ta6a barin Aisha ta kula wata kawa in ba ita ba don haka ya bata amanar yar shi, ta kula mashi da ita.

Benazir jikin ta ba karamin sanyi yayi ba, har kuka saida tayi saboda tausayin baba Imam, Alhaji ubaid ma yayi masu nasiha, bayan ya gama dr shureim Ya kirasu agaban shi Yayi masu addu'o'i tare da yar nasiha A lokacin Aisha ta dinga kallon shi, tayi fatan Ya furta yana sonta kafin su tafi amma sai baiyi ba saboda shi kallon kanwa ya ke yi mata, bawai don baya sonta ba sai don kasancewarsa miskili da zurfin ciki ko kallonta bai cika yi ba, bayan Aunty laura da hajiya layla sun sanya masu albarka tare da fatan alkhairi a karatun su, daga nan suka yi masu bankwana.


Silar hawan su jirgi Allah Ya ?addara haduwarsu Da Aneelerh Muhammad falgore itama a lokacin za ta je yin karatu kasar germany, ta zauna a seat daya da Benazir taga ta burgeta ta Wan fara janta da fira har Benazir ta dan saki jiki da ita, A lokacin Aneelerh batasan da zaman Aisha a cikin jirgin ba tana a seat din bayansu ta rufe fuskarta da mayafinta zuciyarta cike fal da tunanin mahaifinta data bari da kuma muradin ranta.

Bayan jirginsu yayi Landing a airport na birnin hagen, Alhaji Musa Ya turo wani escord Winsa Yazo daukarsu a hadaddiyar mota, sukayi sallama da Aneelerh suka shiga mota, a zaton su kaitsaye escord din zai wuce da su Jami'ar da zasuyi karatu acan, amma sai suka ga akasin hakan, a wani katafaren gida da Alhaji musa Ya kama masu haya a kusa da Jami'ar, Anan Escord din yakai su a matsayin gidan da zasu zauna, Aisha tayi mamakin haduwar katafaren Gidan, tayi azan a hostel zasu zauna amma sai taga akasin hakan, tsabar gatanci hada masu aiki Ya aje masu agidan, kamar ba karatu suka je yi ba Aisha ta Wanji shakkun ta zauna agidan saboda gudun kada ta shagala ta kasa ta6uka abunda ya kawota amma saboda Benazir yasa ta amince ta zauna, rana ta farko da suka fara shiga jami'ar, ba zato ba tsammani sukayi arba da Aneelerh ashe itama a nan zatayi karatu, Sunyi farin ciki da ganinta duk da ba'a department Waya suke da ita ba, rayuwarsu a jami'ar gwanin ban sha'awa shiga class kadai ke rabasu amma da zarar sunfito zasu hadu da Aneelerh a karshe ma da kawancensu yayi karfi da Aneelerh sai suka yi mata tayin ta baro hostel ta dawo gidansu da zama, Aneelerh bata musa ba ta amince masu toh ita kanta data ga inda suke rayuwa saida ta girgiza da mamaki saboda haduwar Gidan.

Uncle musa ba karamin gatanci yayi masu ba, shi ke daukar dawainiyar komai nasu, tun daga cinsu shansu suturarsu masu kyau da tsada har account ya sanya yaronsa ya bude masu na kasar germany, baya gajiya da tura masu dollars kamar baison zafin neman su ba, lamarin shi ya fara daurewa Aneelerh da Aisha kai ganin yadda ya ke ji dasu yana tarairayarsu, wani abun daure kai Duk weekend sai yazo kasar germany daga America, kuma agidansu Yake sauka anan zai kwana su yi breakfast lunch dinner duk tare da shi, har yawon buWe ido Yake zagayawa dasu a motar shi, da abun ya fara damun aisha ta dai gaza hakuri ta fada ma Benazir itafa zata koma hostel da zama saboda tana jin tsoron baba Imam Yaji labarin ba a jam'ar take zaune ba zai iya yi mata fada bayan haka bata son yadda Alhaji musa ke kashe masu kudi abun yayi yawa, sannan meyasa yake zarya duk week end sai yazo ya kwana agidansu? A ganinta hakan bai dace ba, a matsayinsu na musulmai kuma mata su dinga barin Namiji yana kwana a gidan su, Benazir ta nuna kin amincewarta da komawar Aisha Hostel, ta dinga lallashinta akan tayi hakuri ta zauna, na dan wani lokaci ne, kada ta damu da Alhaji musa halinsa ne shi mutum ne mai son yin alheri yana da wayewa don haka kada ta dauka da wata manufa ya ke zuwa kawo masu ziyara, sannan kuma kada ta damu sheikh Imam bazai ta6a sani ba.

dakyar Benazir ta shawo kanta har ta hakura da komawa hostel Win, kusan kullum ne saita kira babanta a waya hakan ba karamin kwantar masa da hankalinsa ya ke yi ba, kuma duk in ya kira sai yayi mata nasihar daya saba yi mata, haka aunty laura ma suna yawan yin waya da ita, wasu lokuttan da dama tana son ta kira Yaya shureim amma idan ta tuna bai ta6a nemanta ba sai ta fasa saboda bata son ta zubda ajinta


Sai dai taji labarinsa awurin Benazir idan tayi waya da shi wani lokacin Benazir tana bata wayar don ta gaisa da shi hakan ba karamin dadi yakeyi mata, haka itama Aneelerh silar Benazir ta san Yaya shureim har suka saba da shi, itama Aneelerh duk in zatayi waya da mami da Abie sai ta hadasu da aminnanta donsu gaisa ta haka suka ?arfafa zumuncin su.

har whatsapp group suka buWe na sada zumunci da family dinsu harta baba Imam saida Aisha ta sanya shi aciki, Aneelerh ta saka abie da mami, itama Benazir ta sanya Alhaji ubaid da hajiya layla tare da dr shureim Wani irin zumunci mai karfi ne ya shiga tsakanin family din su duk time da suka hadu online fira suke sha ba kadan ba, har hotunansu suke tuttura masu.

Duk idan suka samu hutun School Nigeria suke dawowa tun a airport family dinsu zasu harhadu domin tarbarsu har party Uncle musa Yake hada masu, idan hutu ya kare zasu koma germany har kuka sukeyi saboda basu son rabuwa da family din su.

Akwana a tashi ba wuya gurin Allah, Cikin sa'a suka kammala degree dinsu, duk da Benazir da Ummi sun riga Aneelerh kammalawa saboda ita nata course din almost 6 years ne medicine and surgery su kuma Business Administration ne shekaru uku ne, Amma saboda shakuwar da tayi da su yasa ta matsa lamba akan zata ajiye karatun saboda bata jin zata iya cigaba da zama a germany batare da su ba, tasan in suka gama tafiya zasuyi su barta, suma sun damu da hakan, a wani zuwa da Uncle musa yayi gidansu, Benazir ta same shi da maganar Aneeleerh, Sai cewa ya yi karsu damu, zai sa arage mata shekarun karatun ta ya koma daidai da nasu, sunyi matukar yin mamakin hakan, aikuwa sai gashi Ya yi mata hanyar da zasu kammala a shekara daya da ita, Amma duk da haka In ta dawo Nigeria sai ta kara karatu akan wanda tayi.

Uncle musa yayi masu halaccin da bazasu taba mantawa da shi ba, Kyautatawarshi agare su bata misaltuwa, da Ayshah tana kokwanton dukiyar shi ganin yadda yake masu barin kudi kamar baisan wahalar nemansu ba, Benazir ce tayi brainwashing dinta, ta fayyace mata cewa kudinsa na Halal ne, babban Dan kasuwane kamar dai mahaifinta Alhaji Ubaid.


ranar da zasu yi graduation celebration (bikin yaye dalibar) wanda shuwagabannin jami'ar ne suke daukar nauyin yin shi a cikin makarantar, gaba daya family din kowan nan su saida Ya hallara hatta sheikh Imam saida Yaje masu aiko Aisha tayi murnar ganin baba Imam, Ranar sunyi farin cikin da basu ta6a yin makamancinsa ba saboda Yadda yan uwa da abokan arziki suka dinga basu kyaututtuka da yi masu fatan Alkhairi arayuwa, aranar ne sukayi hotuna sosai, abunda yafi basu sha'awa Yadda Family dinsu suka hada kai kamar yan uwan juna, musamman Aisha tayi murna da ganin yadda ya yadda Shikeh Imam ya yarda da Abie din Aneelerh sun zama abokai, haka iyayen su mata sun hada kai sai zumunci suke sadawa a tsakanin su.

(Bayan dawowarsu Nigeria, da sati biyu kacal)



A yammacin wata rana Sheikh Imam Yana zaune akan Sofa dake a cikin katafaren Sitting room din gidansa, yana tsaka da karanta Jarida, daya daga Cikin security Officer na gidansa yayi masa sallama bayan ya amsa Ya isar da sakon Ana sallama da shi, bai motsa daga Inda yake ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0