Showing 309001 words to 312000 words out of 413917 words

Chapter 104 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4569

arne mara addini? Ko kuwa jahili dabaisan komai ba? Ko matsafi mai goyon bayan matsafa wurin aikata zalunci"!

Kiris Ya rage Ya yanke jiki ya fadi saboda wutar bacin rai data ziyarci zuciyar sa

Maganganunta sun ta6a zuciyarshi ba ?adan ba, Yaji zafin su sosai, ita kanta ta tsorata da ganin yadda gumi ke tsastsafo ma shi, duk da tana jin tsoron kada Evil's heart dinsa ta motsa, amma dayake idanunta sun rufe burinta kawai ya amsa bukatarta.

Da wata irin karyayyar murya mai cike da 6acin rai ya furta"Angel, mafarki nake ko gaske? Da kanki kike jifana da waWannan munanan kalaman? ni Angel? Your Shield"? numfashi ya Wan ja kamar bazai iya karasa maganar ba yace"meyasa zaki min haka? Lafin me nayi maki da cancani cin mutunci daga gareki? Angel kema Kina min kallon jahili? Mara asali? Kuma kika kira ni da matsafi"?

Waga mashi gira tai"Hell fucking yeah, ko nayi ?arya ne"? Kasa magana yayi,

"abu Waya ne zakayi wanda zai wanke ka daga gareni, shine Ka cire tsoro, Ka basu haWin kai akai farmaki gidan kurkukun kaddara, ta hakanne kaWai zan yarda dakai in kuma har ka bijire min kaki bin Umarnina, wlh na rantse da wanda raina yake a hannunsa muddin baka bada goyon baya ba, na kwammace in mutu da ciwon sonka, akan in aure ka"! Da sauti mai karfi tayi maganar tare dakai hannu ta daki handrail..

duk abunda ke faru tsakanin su babu wanda ya sani

"In kuwa har ka bari Chief yayi nasarar ruguza kurkukun ?addara batare da taimakonka ba, zan mallaka mashi kaina..." bata kare maganar ba sakamakon zazzafan marin daya kwasa mata wanda shi kanshi bada sanin shi ba, a karo na farko data fara jin tafin hannunsa akan fuskarta da sunan mari, wa'iyazubillah wani azababben radadi taji ya ratsa sassan jikin ta kamar an watsa mata wuta jirine Ya kwashe ta, ta tafi zata kife ?asa cikin zafin nama Ya taro ta da hannunshi ya dawo da ita kan kirjin shi, yayi hanzarin daukarta kan kafadarshi Ya nufi bedroom dinshi da ita gudun kada wani ya riskesu a halin da suke a ciki.

Yana shiga Wakin Ya kwantar da kan gadon shi, kamar matatta, da alama suma tayi saboda azabar da taji.

Hankalin shi idan yai dubu toh ya tashi, Jikinshi sai kerma yake kamar wanda sanyi Ya kama, zafin Kishi Yaja mishi bala'e..

Duk da sanyin A.c din dakin hakan bai hana gumi tsastsafo mashi kan fuskarshi ba, zukunnawa yayi daga bakin gadon yana kallon gefen fuskarta, shi kanshi Ya tsorata da ganin yadda fatar gurin tayi ja sosai, shatun fingers in shi ya fito ruWu ruWu.

Yatsun hannayen shi Ya zuba ma Idanun shi Yana kallon su cike da danasanin marin da yayi mata, ya san yadda marin Evil giant yake da zafi, zata Iya kai Sati da radadin dafin marin a jikin ta.

cike da takaici ya dinga bugun kanshi da hannayen shi kamar zai zauce saboda zafin abun da ya yi mata

Tuni hawayen da suka taru cikin idanunshi suka fara Yar tseral kan kuncin shi, abu biyu ya haWe mashi ga zafin munanan kalaman data jefe shi da su ga takaicin marin da yayi mata.

Cikin karyayyar murya ya furta"ba laifina bane, ke ce kika bata min rai, gashi kinja na mareki bada son raina ba" ya faWa tare da daura tafin hannunsa saitin inda Ya mare ta, dabara ce ta fado mashi da sauri ya saita fuskar shi saitin tata, sihiri gaskiyar mai shi, ruwan hawayensa dake WiWWiga kan fuskarta sune suka goge tabon marin da ya yi mata cikin kankanin lokaci fatar ta dawo fara sol kamar ta jinjira, numfashi Yaja tare da sauke ajiyar zuciya a hankali launin idanunsa suka dawo yadda suke.

kallonta da yake yi ahaka yafi masa kwanciyar hankali akan Ya farfaWo da ita saboda fargaban masifarta.

Daga gefenta Ya raba jikin shi, Ya kwanta tare da lumshe idanun shi, bai ta6a fuskantar tashin hankali irin na yau ba, tayaya zai iya shawo kan Unaisah ta fahimci abunda yake nufi"?

Kwatsam yana a cikin mawuyacin halin nan ba zato ba tsammani ya tsinkayi Muryar Khala a cikin kunnanshi..

"Uhum Garkuwa Namu"

A rude Ya mike zaune yana bin dakin da kallo, cikin sauri Ya share hawayen fuskarsa, jikinshi har 6ari yake garin zumudin ya sauko daga kan gadon, Hasken Wakin shi ne Ya dauke Wuff Duhu Ya mamaye ko'ina, bai nufi ko'ina ba sai gaban mirror Ya yaye madubin idanunshi su ka yi mashi tozali da tsohuwa Khala zaune kan armchair, Cikin shigarta ta gado fuskarta a yamutse ba annuri.

Zama yayi kan Mirror chair din with respect ya gaishe da ita, da fara'a ta amsa mashi

Kafin Ya nutsu Yana jiran jin me zata ce ma shi

"Ina fata kun fara shirye shiryen kawo farmaki"? shiru ya yi baice mata uffan ba.

Yanayin dake a kan fuskarshi ta nazarta nan take ta fahimci baida matsaya

Yar dariya tayi"jikana, faWamin ba, me ake Ciki ne"? dakyar Ya labarta mata abinda ke faruwa bai boye mata komai ba

Girgiza kai tay"yaro man kaza, Har yanzu Jinin Elders ne a jikin ka, amma Alhamdulillah naji dadi da Allah Ya bani ikon ganawa dakai a karo na biyu, saboda na fahimci ka na bukatar in wayar maka dakai, in kuma yi maka karatun ta nutsu ta yadda zaka fahimci su wanene Elders da kuma dalilin dayasa suka raine ka..." aruWe Yake kallon fuskarta...

"Kasan wacece ni, ka kuma san matsayina agidan kurkukun kaddara, nafi ka sanin komai Danish, duk wani abu da suke aikatawa a tafin hannuna yake" ta faWa tana nuna mashi tafin hannun ta.

"Abu na farko da baka sani ba, Elders Mayaudara ne, Maha'inta, maciya amana, bansan ko ka san da labarin nan ba, amma inaso ka sani tun kana jinjirinka cikin tsummanka suka sace ka daga wurin iyayenka, suka rabaka da su batare da saninka ba, sannan suka sadaukar da kai zuwa gidan kurkukun ?addara, Ni nasan su wanene Iyayen ka, wallahi basu san kana araye ba, an yaudare su ne da sunan ka mutu...." dafe kanshi yayi da hannu Waya zuciyarshi cike fal da ruWanin maganarta, bazai ce tayi karya ba sai dai kokwanton da zuciyarshi keyi bazai bari ya aminta da ita ta cikin sau?i.


"Bani da isasshen lokacin da zan yi maka bayani, amma atakaice ka zauna kayi nazari Danish, kai ganau ne ba jiyau ba, kasan komai, har yau zubda jinin mutane suke yi kamar kwari, Laifin me suka yi masu? Ahaka zaka rufa masu asiri uhyum? Ita kanta yarinyar da kake gudun rabuwa da ita ba zasu kyale ta ba, wallahi in har baka bada goyon baya an kawo karshen su ba, da kai da ita sai kun salwanta, saboda suna nan suna shirin yadda zasu kashe ku.."

waro idanun shi waje yayi jin abinda tace.

Murmushin gefen fuska ta saki tare da jinjina mashi kai"hmm wai kana tunanin Suna kaunarka? To wallahi ko Waya basu ta6a kaunarka ba, sun raineka ne don biyan bukatar kansu, idan kai me hankali ne ga misali nan, Yanzu da suke ganin sunci moriyarka amfaninka ya kare kana neman tona masu asiri ba ga shi har sun Wauke mukamin da suka baka na garkuwarsu ba, sun ba Jeremiah, kai kuma nema suke su salwantar da rayuwarka saboda kai kadaine kasan sirrinsu dakai kadai za'a iya farmakarsu...."

wani irin gumin tashin hankaline Ya wanke fuskarshi, Maganar tsohuwa khala tayi matu?ar yin tasiri a zuciyar shi.

Kusan sau uku Tana ambaton sunan shi bai amsa mata ba, saboda zuciyarshi ta lula duniyar tunani

Har saida tayi mashi gyaran murya kafin ya dawo hayyacin sa

"Ina Gabriel? Ya rayu ko ya mutu"? ya Wanyi mamakin jin ta tambayi gabriel ko a ina ta san shi"?

"Yana adakinsa, bacci yakeyi"

"Masha Allah, Naji dadin jin hakan, sai dai, Yar Uwarsa daya bari agidan kurkuku tana acikin mawuyacin hali..."

"Who's she? ya tambaya don sam ya manta da cewa Gabriel Yana da sister.

"His twin sister Gabriella...." a takaice ta labarta mashi rashin imanin da tsohuwa inno tasa giant yayi mata, tsabar 6acin rai jikinshi har tsuma yakeyi

"ta rokeni akan Tana son ganin Wan uwanta, nayi mata alkawarin ko zan rasa raina ne in dai muna da tsawaicin kwana zan haWa ta da Wan uwanta" cikin rauni na murya tayi maganr tare da mikewa daga kan kujerar da take, ta haske mashi Gadon da Gabriella take akwance kamar babu rai a jikinta, sai jan numfashi take dakyar dakyar

"Nayi zaton ta samu lafiya, amma wani abu ya faru jiya wanda Ya Waga hankalina, tana daga zu?unna tayi aman Jini, ta dafe ciki tana faWin Yan hanjinta suna konewa, Inaji araina Inno ce tayi mata asiri, nadai yi kokarin yi mata yan dabaruna ahaka Jikin da sau?i amma tana bukatar taimakon gaggawa daga gare ku idan ba haka ba da wuya ta rayu.."

Jikin shi yayi sanyi saboda tsantsanin tausayin yarinyar daya kama shi, yanzu ya tuna ranar farko da aka kawo su har tsohuwa Zafreen tasa aka raba su.

"Danish Ahaka zaka rufa masu asiri? Shikenan babu wani wanda zai kawoma bayin Allah dauki! Haka zamu barsu su cigaba da azabtar da rayuka? Ba zamu Wauki mataki ba"? Sam ya kasa magana saboda raunin da zuciyar shi tayi

*Da wata irin kakkausar murya ta firta"YA RAGE NAKA GARKUWA, DOLE ?AYA CIKIN BIYUN NAN YA FARU! KO DAI KA BADA GOYAN BAYA AKAWO MASU FARMAKI, KO KUMA SU SU KAWO MAKU FARMAKI SU GA BAYAN KU..."*

Sau Uku ta maimaita Hakan, kafin ta cigaba da ?arfafa mashi gwiwa daga bisani bayan ta ?ara jaddada mashi kwanan watan da zasu yi black night, ta bashi wasu muhimman bayanan da zasu amfane su, daga nan ta 6ace ma ganin shi, kifa kanshi yayi gaban mirror Win Zuciyar shi cike fal da damuwa, anan wani wahalallan bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi.

Lokacin da Batool ta farka daga bacci taga babu Unaisah adakin, bata damu ba, bayan tayi sallar asuba, taji shiru bata dawo ba, hakan yasa ta mi?e ta fito daga dakin tafara neman ta, sai da tabi Wakunan Yan uwansu duka ta duba taga babu Unaisah, Hankalinta ba karamin tashi yayi ba,.

Da sauri ta nufi Wakin Aunty Ummunsu, tayi knocking almost 3 times, kafin ta samu Ummi ta buWe kofar, tana mi?a hadi da yin hamma ko kayan baccin jikinta bata kaiga cire wa.

"Babe, Har kin tashi"? Daga mata tayi"Aunty Ummi sister tazo nan? Na farka banganta ba"

Girgiza kai Ummi tayi"Bata zo ba, kin duba ko'ina"?

"Eh," ta fada da damuwa

"Kada ki damu, nasan duk inda taje tana acikin gidan nan" ta faWa tare da ruko hannunta"mu shiga daga ciki, Ki jira ni in shirya sai mu fito tare" amsa mata tayi da toh.

Bayan shigar su Wakin, Ummi ta kunna mata kallo a laplop Winta, kafin ta shiga bathroom don tay wanka.

Nutsuwa tayi kan gadon tana kallon drama, ta shagala da kallon wayar Ummi ta fara ruri.

?auko wayar tayi daga kan pillow, ta duba screen Win bata gane me aka rubuta ba saboda bata iya karatu ba..

Da karan banin ta tayi picking call Win kamar yadda taga Unaisah nayi, ashe video call ne, yanayin yadda ta ruke wayar yatsan hannunta yayi hiding front camera, wanda Ya kira bazai Iya ganin ta ba, kura idanu tayi aka fuskar mutumin dake kwance cikin bathtub, ruwan kumfa ya rufe Jikin shi fuskar shi kaWai take Iya gani yayi shiru yaki magana itama tayi shiru ta?i furta kalma zuciyarta cike fal da tunanin wanene Wannan ?aton.

"Ummi meyasa kike boye fuskarki? jira kike saina maki magana"? Muryar shi ce ta katse shirun ta..

Jin motsin buWe kofar toilet, yasa ta danna end Call, da sauri ta mayar da wayar kan pillow ta aje.

Ta yi hakanne saboda Ummi ta ta6a gargaWinta, akan in ankira wayarta bata akusa kada tayi picking dama bata ta6a kuskuren daukar mata waya ba saboda ta fahimci bataso.

Koda Ummi ta fito bata faWa mata an kira wayar ba, bayan ta kammala shiryawa atare suka fito daga dakin.

Har wuraren ?arfe tara, basu ga Unaisah ba, gashi Har time Win Yin breakfast dinsu ya yi gaba Waya yan uwansu sun hallara a dining ita kaWai su ke jira sun yi neman har sun gaji kuma babu wanda yai tunanin tana adakin Danish.

Can cikin kunnuwanshi suka soma jiyo mashi sautin tarin ta, firgigit Ya farka da kasala Ya mi?e zaune Yana kallon ta da idanunsa waWanda suka kumbura.

A hankali ta mi?e zaune tana Hamma Wata Irin Yunwa take ji, kwata kwata bata iya tuna abun da ya faru ba, fitsari ne Ya matse, saukowa tayi daga kan gadon da sassarfa ta shige toilet Winshi sai da ta gama tana kokarin fitowa idanunta suka sauka akan shi, Ya zafga Uban tagumi da tafukansa kamar wanda Ya rasa gata a duniya.

Nan take komai daya faru tsakanin su Ya dawo mata acikin tunaninta, gefen fuskarta daya mara ta shafa da tafin hannun ta, harara ta watsa mashi taja tsoki, kafin ta juya zata bar Wakin.

takun tafiyarne Ya fargar da shi, da sauri Ya mi?e ya shagabanta kiris Ya rage kirjinta Ya bangaji na shi

"Bani bukatar Jin komai daga gare ka, bani hanya na wuce"! tana huci ta faWa tana neman rabawa ta gefen shi don ta wuce

Cikin sauri ya ru?o Arm Win ta, hakan yasa ta dakata da tafiyar

"I want to ask you one question."

shirun da tayi ne yasa shi fahimtar jiran shi takeyi

"baki tsoron ki rasa ni"?

"Danish, ko da Ina jin tsoron In rasa ka, Ka tuna ranka Waya ne tak! da shi kadai zaka Iya taimakon dubban rayuka, ka kuma yi silar tarwatsa gang din azzalumai"

"Angel, baki damu dana mutu ba? Ina kaunar da kike mini? Kin za6i da naje na bada raina"? jinjina mashi kai ta yi"nafi maka kwaWayin ka mutu a filin ya?i, kwara mu hakura da duk wani buri da muke da shi, mu bada rayukanmu donmu taimaki bayin Allah, in sha Allah ko bamu ji dadi anan ba, zamuji acan, in ba haka ba mutanan nan bazasu ?yalemu muyi rayuwar farin ciki ba, saboda mun san sirrin su kuma mune na farko da muka gudu daga gidan kurkukun ?addara, mun tona asirin su, zasu nemi hanyar kashe mu ne, ka fada min taya zamuji dadin rayuwa da fargaba a zukatan mu? Kaima fa har yanzu suna atare kai, Ka tuna abunda kayi min rannan, wata rana har kashe ni zaka iya yi ba acikin hayyacin ka ba, dan Allah ka fahimce ni, rayuwa bazata yiwu ahaka ba, kana bukatar ka zama cikakken mutun"W'

duk yadda taso ta jure saida idanunta suka cika tab da kwalla kwata kwata bataso Yaga rauninta, tafi son yasan da gaske take don ta samu ya amince.

Batai aune ba, Taji Ya zube kan gwiwowinsa, A hankali ya jinginar da kanshi jikin laps dinta, ya zagayo hannayen shi kan waist Winta ya ru?e ta gam, da wani irin hucin zafi numfashin shi ke fita ya riga daya sada?as Angel had already won him over, dole Ya mika wuya, abu Waya da bazai ta6a mantawa ba, munanan kalaman da ta furta mashi, tabbas Yana son wata rana ya bata mamakin da zaisa tayi danasanin abunda tayi masa.

Cikin karyayyar murya tamkar ta majinyaci Ya furta"Na amince, zan basu haWin kai, all because of you, Whatever happens to me, blame yourself .." kasa ?arasa maganar yayi saboda raunin da zuciyar shi tayi..

Angel dake tsaye kamar gunki tana kallon sumar kanshi, ruwan hawayen ta dake gangarowa kaitsaye suka WiWWiga saman sumar kan shi, baiwar Allah duk sai taji ba daWi, Zuciyarta ta karaya da kalaman shi,.

Ta rasa farin ciki zatay da amincewarshi ko bakin ciki? ita dai tasan Ita da kwanciyar Hankali sunyi bankwana.

Yatsun Hannunta na kerma Ta shafa sumar kan shi, dakyar ta banbare hannayenshi daya ruke waist Winta da su, ta fuce daga Wakin, akan flooe Ya kwanta tamkar babu jini ajikin shi.

maganganun mutun biyu ne sukayi tasiri akanshi, Tsohuwa Khala and his Destiny, yaci alwashin duk runtsi duk wuya sai yaga bayan Elders sannan Yana son yaje kurkukun kodan Ya haWu da tsohuwa khala saboda yana son ta faWa mashi su wanene iyayen shi saboda ya fahimci su kadai ne zasu iya bashi abun da akeyi mashi gori akaiS'

___________________________________________
'?


Idan muka koma Gidan baba Obie, tun da Owais Ya faWa ma Pravin zancen tafiyar da yake so suyi tare da baba Obie, Hankalin Shi ya tashi hai?am, gaba daya ya rasa nutsuwar shi saboda bakin ciki Ya tafi batare da ya ?arasa aiwatar da mummunar kudirinsa ba, wunin ranar a daki yayi saboda damuwa har hajiya saratu saida ta lura da yanayin shi har tambayar shi tayi meke damun shi yace mata bai da lafiya zazza6i ke damun shi ga owais ya nemi alfarmar ya raka baba Obie lagos, baisan ya zaiyi ba yana jin nauyin yace bazai je ba
Hajiya saratu tace bazaima yiwuwa ba, zatayi ma baban magana anemi wanda zai bi sa suje tunda shi ba koshin lafiya gare shi ba.

kafin hajiya saratu tayi ma baba Obie magana Pravin yaji labari awurin hajjaty, a jiya daya shiga Wakinta ya iske ta zaune tsakiyar gado tana ta kuka ya tambayeta meke damunta, nan take labarta masa baba obie ya kira ta adakinsa ya sanar da ita gobe kafin ya tafi zaisa jami'ai su maida marwa garin su gurin iyayenta, zata fi samun kulawa agurin su su kuma zasu cigaba da bata tallafi.

Da jin wannan maganar, pravin ya washe baki, bai ma tsaya ya karasa jin karashen zancen ba, Ya fuce daga dakin Ya koma dakin hajiya saratu ya tambayeta shin dagaske ne za'a maida marwa garin su tace mashi eh, ay itace ma tayi ma baba obie magana amayar da ita saboda su twins tana son su dawo gidan da zama.

farin cikine ya lullu6e parvin harya manta da karyar ciwon da yakeyi yace mata ay yama ji saukin zazza6in zaibi baba obie suje lagos din, tace mashi a'a gaskiya tafi son ya wartsake in yaso daga baya sai ya bishi, yasa naci akan shi dai zaije tace meyasa zai takura kansa bayan ba koshin lafiya gare shi ba, ya marairaice mata fuska da dadin baki ya shawo kanta harta amince bazata fada ma baba Obie ba.

Washe gari da sassafe, jami'an da za su tafi da marwa, suka doko sallama,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0