Showing 255001 words to 258000 words out of 413917 words

Chapter 86 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4529

har cikin ranta bata jin dadin haka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?n

Kokarin kwantar mata da hankali tayi"pls kada hakan Ya dameki, sai kace bakisan halin shi ba tun a prison, dama can shi ba mai san shiga mutane bane, kinfi kowa sanin halin danish, baya son hayaniya, shi indai zai samu gado ya kwanta yayi bacci toh bashi da wata damuwa, ki daina tunanin ko kunyi masa laifi ne, wlh babu abunda kukayi masa abun a jininsa yake, kuma bawai ya daina damuwa daku bane, kuna aran shi" ajiyar zuciya Batool ta sauke, kalaman unaisah sun kwantar mata da hankalin ta.


Bayan ta gama gyara ma Batool gashin, ta zauna itama ta gyara mata nata daga bisani Unaisah tayi masu make up, powder suka shafa da lip gloss mai kyalli launin pink.

Bayan sun gama suka koma gaban closet Win su, inners suka fara sanyawa, Unaisah ta Wauko mata sabuwar bra ta mi?a mata don ta sanya ta kar6a tafara kiciniyar sakata kamar zatai dambe saboda bata saba ba, batasan ya zata sakata ba, dariya unaisah tayi"bari na taimaka maki" ta faWa tare da ru?o hannun bra Win ta sa?ala mata shi, ajiyar zuciya ta sauke da sauri ta koma gaban mirror tana kallon kirjinta, Yau ne karo na farko data fara sanya bra, tayi mata cuf cuf yadda kasan wadanda suka Wauko bras din sun san size din ta.

Unaisah dake kallonta ji tayi dama ita, yamutsa fuska tayi"idan kin kammala kallon madubin ga kayan da zaki saka nan na zabo maki" ta faWa tare da daura mata su kan gado.

Batare da bata lokaci ba, kowan nan su ya sanya kayan shi, tsayawa sukayi agaban mirror suna kallon tsantsar kyan sukayi
gaba Wayansu Long sleeved gown ce a jikinsu launin Ice blue sai kyalli take da Waukar ido, ga wata hadaddiyar Silver necklace da suka saka a wuyan su, yayin da wrists din hannunsu ke asanye da Beaded Bracelets, sun saki curly hair dinsu ya lullu6e gadon bayan su, yadda kasan wadanda zasu halacci gasar miss word su kansu sun jinjina ma haWuwarsu, sun tasa madubi gaba sai jujjuya jikinsu sukeyi.

Saida suka gama kallace kansu kafin unaisah ta dauko masu fragrance set suka fara barin ruwan turare ajikinsu saida kamshin ya gauraye dakin su tukunna su ka dakata da shafa shi.

"Wlh munyi kyau, Allah Ya zuba mana ruwan kyau sister" batool ce ta fada tana yarfa hannayen ta,
murmushi unaisah tayi tana kallon kanta ta cikin mirror
"Sai yau na kara ganin kamanninmu Allah, dukanmu tubarkalla dogaye ga dogon hanci, Wan bakin mu heart shaped, gaskiya mungode ma Allah..." proudly ta faWa
"Bari na dauke mu hoto" da sauri ta dauko wayarta dake ajiye kan pillow, ta dawo kusa da batool suka hada kai ta fara daukar su pics har kusan kala ashirin..


"Bari inje in nuna ma aunty ummi wankan dana dauka nasan zata ruWe da kyawuna" da gudu ta fuce daga Wakin hannayenta ruke da bazar rigarta kamar wata amarya, har ta fuce daga dakin unaisah bata daina kallonta ba har saida phone dinta ta fara ringing kafin ta kau da idonta, screen din wayar ta duba ganin sunan My man yasa ta Wan yi murmushin gefen fuska kamar yasan jiran kiran shi takeyi girman kai ne ya hana ta fara neman shi, zama tayi daga gefen gadon ta Waga kiran tare da kara wayar a kunnanta


Tayi shiru bata ce komai ba, tana jiran jin me zaice mata.

"My Angel..." bai ?are maganar ba ta katse shi da cewa"Wazu na tura maka message, nace ka sauko down muyi breakfast why didn't you come?"

Ta faWa tana haWe fuska kamar tana agaban shi.


Softly ya furta"Naga sakon da kika tura min, amma ban fahimci me kika rubuta ba, shiyasa ban zo ba" jikinta ne yayi sanyi lakwas duk sai taji ba dadi

"Meyasa baka kira ka tambayeni me na rubuta maka ba? Shiru yayi bai bai tanka mata ba.

"I have no answer,"? Still baice mata komai ba.

"Okey, kayi breakfast dinka"?

Sai lokaci taji ya Wan sauke ajiyar zuciya"nayi, Haris ne ya kawo min adaki"

Lumshe idanunta tay, wani irin yanayi take jin kanta, Sautin muryarshi ba karamin rikita ta ya ke yi ba, A hankali ta kwantar da bayanta jikin pillow, dadin muryar shi take ji, idan suna yin waya har bata son suyi sallama da juna


______________________________
'?

Lokacin da motar dr shureim Ta biyo kan titin Obie Estate tun kafin su karasa Benazir take bin ganin da kallo yau ne karo na farko da ta fara zuwa, ta ruWu da ganin haWuwar katafaren entrance gate din dake abuWe ga wasu fusatattun sojoji dake tsaron ?ofar cikin taku na majiya karfi suke kai komo abakin gate din sun kasa sun tsare babu mahalukin daya isa ya ?etare kofar batare da an basu izni ba.

Hatta dr shureim bai ta6a zuwa ba, ya dai san estate din amma bai ta6a shiga ciki ba.

rage gudun motar yayi slowly yayi parking dinta gefe guda, don yasan ba lallai su barsu su shiga ciki ba.

."Anila kina ganin zasu barmu mu shiga"? Benazir ce tay mata maganar tare da dubanta

"Eh, amma dole saida iznin wani daga cikin mutanan gidan," ta fada tare da daukar wayarta daga cikin handbag, A hankali ta kwantar da baby junaid kan seat ta dubi dr shureim"bari na kira daddyn azeezaty din" amsa mata yai da toh, ta bude murfin motar ta fito daga waje ta danna ma shi kira, bayan ya Waga ta kara wayar a kunne.

"Taj, munzo yanzu haka muna a bakin entrance gate na estate din"

On the other hand taj yace"tare da wa kike zo"? Lokaci daya taji gabanta Ya fadi, tunawa da gargadin da sukayi mata sam ta manta.

Dakyar tay karfin halin ce mashi"tare da Benazir, sai yayanta dr shureim shine ya kawo mu..." bata kare maganar ba taj ya furta"why Anila? Why? Kin manta kashedin da chief yayi maki? Akan me zaki zo da su gidan nan? Ke kadai fa nace kizo saboda Angel tana son ganin junaid"

Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba duk tabi ta rude, ta fahimci ranshi ya 6aci

"Kina atare da su ne"?

"A'a na fito daga cikin motar ni kadai ce, Zanyi maka bayani, nasan zaka fahimce ni"!

Shiru yayi yana sauraron ta

cikin sanyin murya tace"ka yi hakuri idan na bata maka rai, nasan ban kyauta ba, amma ba yadda zanyi ne, bazan iya jure ganin Benazir cikin mawuyacin hali ba, wlh baka ga yadda ta koma ba, saboda rashin Unaisah bata da kwanciyar hankali, ko abincin kirki bata iya ci duk ta rame, Kai kace min da zarar ta dawo hayyacin ta, in sanar da ita cewa yarta ce, yanzu tasan komai..." bata kare maganar ba, Taj yace"kina nufin kin fada mata har abunda ya faru da mu"? Yamutsa fuska tay tamkar zata saka mashi kuka tace"na faWa mata, amma na gargadeta akan kada ta bari kowa yasan kuna araye, sannan nace mata kada ta bari unaisah ta gane itace mamanta kamar dai yadda kukayi mana bayani haka itama na sanar da ita, kuma tayi min alkawarin ba zata sanar da kowa ba"

"yayanta fa kin fada mashi? Shiru tayi gabanta na faduwa
Har saida ya sake maimaita tambayar da yayi mata kafin tace"A'a bai sani ba, mun dai fada mashi zamu zo gurin Azeezaty ne, kuma kasan dr shureim bai son ka ba, bazai iya gane komai ba, balle shi da bai cika shiga sabgar da bata shi ba wlh baida matsala, mutunne mai kamun kai"

saida takai aya kafin yace"Anila na fahimce ki, amma Bana so Benazir ta yi wani abu da zaisa unaisah ta gane cewa mahaifiyarta ce, pls komai ya tafi yadda muka tsara shi, idan kika bari aka samu matsala ke da chief ne"


"In sha Allah baza asamu matsala ba, zamu kiyaye"

Tana jiyo sautin ajiyar zuciyar shi"okay, zanyi magana da chief, ku ?ara hakuri," amsa mashi tay da toh, bayan sunyi sallama ta buWe murfin backseat ta shiga daga ciki ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya, atare dr shureim da anila suka kalle ta

"Ya ake ciki"?

Murmushi ta danyi tare da kallon benazir tace"yace mu jira, za'a bamu iznin shiga" ajiyar zuciya kowan nan su ya sauke.

Dr shureim yace"junaid har yanzu bai farka ba, ko dai kin bashi sleeping pill ne" yar dariya tayi"a'a wlh, nima nayi mamakin baccin shi kamar wanda yasha ?waya, may be ko dan jiya bai samu isasshen bacci bane..." ta faWa tare dakai hannu ta shafa gefen fuskarshi.

Benazir tace"Allah nafara gajiya da jira, Allah yasa kada su shanya mu awaje, nifa na?osa naga babyna" cike da zolaya dr shureim yace"bari maman babyn taji kina kiran sunan ?arta da sunan taki, kotu ce zata rabaku" dariya sukayi gaba dayan su.

Kafin wani daga cikinsu Ya ?ara furta kalma, Suka ji anyi knocking window glass din motar

da sauri dr shureum ya sauke glass din

Wani soja ne tsaye fuskar shi a murtuke ba annuri ya furta"Who is Anila?" Yawu ta hadiya muryar ta na dan rawa tace"I am sir"

"Okay, ku shiga daga ciki, an baku izni" kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, dr shureim ya tada motar ya nufi drive way din da zai sada su da cikin estate Win, Anila ce ta dinga nuna mashi hanyar da zai bi har suka karaso gidan chief, basu sha wahala ba, motarsu na karasowa bakin gate din jami'an dake tsaron shi suka basu iznin shiga ciki bisa umarnin mammallakin gidan hakan na nufin an san da zuwan su, tun da motarsu ta shiga benazir ta ke ta jinjina kai wato sunyi mamakin haduwar katafaren villa din, daga gefen wani stunning fountain dr shureim ya tsayar da motar.

Rungume baby junaid anila tayi akan kirjinta, ta buWe murfin motar ta fito, kafin dr shureim da Benazir suka fito daga ciki, A hankali suke karewa tamfatsetsen ginin kallo, ba su ta6a zaton za'a samun daular data kai ta Alhaji musa haduwa a birnin abuja ba, sai gashi yau Allah ya haWasu da gidan director general Of Isod.

Jikin motar suka jingina bayan su, kowa da abun da yake sakawa aran shi, musamman Benazir ta kosa ta ga taj da Angel dinta murmushi kawai take saki ita kadai tasan dadin da take ji

"Bani junaid din in ruke maki shi" mi?a mata shi anila tayi bayan Benazir ta kar6e shi ta rungume a kirjin ta, Jami'an dake kai komo sai kallon su suke yi.

"Ina zamu nufa"? Benazir ta fada tana kallon Anila, tayi shiru saboda batasan ina zasu dosa ba, har ta yanke shawarar kiran Taj, kwatsam Horn din mota Ya karaWe kunnuwan su, kusan atare suka dubi hadaddiyar motar dake tunkaro kirar black Mercedes


Agaban su motar tayi parking, sun ?ura ido suna jiran ganin wanene mamallakin ta.

Ta ciki aka buWe car door din, gently ya fito daga ciki gaba daya suka bi shi da ido, yana sanye da kayan kakinsu na isod ya rufe fuskan shi da mask, zagayawa yai ta other side Win motar ya buWe murfin, slowly chief ya fito daga cikin, hannun shi ru?e da wayar shi, fuskarshi sanye da face mask, gaba daya dr shureim Ya kasa dauke ido daga kallon su, musamman Benazir gabanta har faduwa yakeyi gani take kamar taj ne sai dai takasa gasgata hasashenta saboda face mask din dake akan fuskar shi yasa ta kokwanton anya shi ne? sai kallonshi take yi shi kuwa ya haWe fuska yama ki yarda su haWa ido da juna don kada ta samu sararin da zata gane shi ne, Hankalin Anila ba karamin kwanciya yayi ba, aranta ta ayyana ashe ma suna atare da chief din tasan already ya fada mashi kwa6ar da tayi masu, fatanta Allah yasa kada ya tuhumeta.

Cikin girmamawa Anila ta gashe da su, chief ya amsa mata, dr shureim Ya mika masu hannu sukayi musaba a mutunce suka gaisa da juna.

Anila ta lura da taj, dama tasan za'a rina, ita ta gane shine kuma tasan saboda Benazir ya sanya face mask, sannan yaki tanka masu don kada taji muryar shi.


"Ya jikin naki" muryar chief ce ta katse mata zancen zucin nata, da sauri ta kalle shi har saida taji gabanta ya fadi, kwata kwata bata kalli fuskar shi ba, sai da yayi mata magana, ta so ta ruWe sai taji kamar muryar Zaki.

jin tay shiru bata amsa ba yasa Aneelerh tayi saurin ce mashi"jikinta da sauki, Alhamdulillah" A hankali ya dubi taj sarai ya fahimci dagangan ya?i magana saboda ex-wife dinsa, ita kuma baiwar Allah ta tsareshi da ido saboda ta gane shi ne.."
"Bismilla..." ya fada tare da nuna masu walkway din da zasu bi

Gaba yai tare da taj su Aneelerh suka bi bayansu, baiwar Allah Benazir ta zama kamar mutun mutumi, jikinta duk yai sanyi la?was cikin muryar raWa tace ma anila"taj ne ko"? Jinjina mata kai anila tayi" shine amma kiyi hakuri dan Allah, kada ki sanya damuwa aranki, har yanzu yana akan dokin zuciya ki bashi lokaci nasan zai kula ki." hawaye ne suka cicciko idanunta, ganin shi da tayi ya fama mata ciwon son shi dake a cikin zuciyarta.


Gaba Waya ya canza mata, ba kamar taj din da ta sani bane ada, Ya zama babban mutun dashi, ga kyawun sura da cikar kamala, har wani ?warjini yayi mata, lallai da da yanzu ba Waya ba, cos ba zata taba manta yadda ta azabtar da shi da soyayyarta ba, ta gasa mashi aya hannu, ta raina shi kamar bawanta haka take sarrafa shi sai abunda taga dama akeyi agidan su, yanzu kuwa taj yafi karfinta, ita kanta ta shaida hakan, dr shureim dake abiye da su kwata kwata bai lura da halin da Benazir take a ciki ba, hankalin shi baya akan su

abakin wata glass door suka dakata da yin tafiyar, Chief ya buWe masu kofar, Sanyin a c ne ya fara busowa ta cikin Wakin mai dadin gaske, atare chief da taj suka shiga, Benazir da Aneelarh suka shiga daga bayansu kafin dr shureim ya shigo, sitting room ne Ya gaji da haduwa, a saman sofas suka zauna, anila da benazir da dr shureim suna akan sofa mai mazaunin mutun uku, yayin da chief da taj suke a zaune kan 2 seater dake fuskantar su.

Mi?ewa taj yai ya nufi benazir, tayi azan zaiyi mata magana ne harta fara dan sakin murmushi bai ko kula ta ba, ya sanya hannu ya kar6i junaid daga hannunta, Ya koma ya zauna tare da kwantar da shi kan kirjin shi.

Da ido Aneelah tayi mata alamar tayi hakuri ta kwantar da hankalin ta, dukar da kanta kasa tay tamkar zata sanya kuka ba dan bata so dr shureim ya gane gaskiya ba ai da tuni ta cakumi rigar taj ta rungune shi.

Takun tafiya ne Yaja hankulan su ga duban mai shigowa, wani jenior agent ne Ya shigo hannun shi ru?e da wooden tray mai Wauke da softdrinks and snacks ya ajiye masu akan table kafin ya juya ya fuce

"Bismillah, zaku iya sha" Taj ne ya fada tare da yi masu nuna da table din, Anila ta Wauki juice ta zuba masu a cups ta mi?a ma dr shureim ya kar6a, koda ta mika ma Benazir girgiza mata kai tay alamar a'a, jiki asanyaye Anila ta fara shan wanda ta zuba mata.

falon yayi tsit baka jin sautin komai sai sanyin a.c din dake ratsa fatar jikin su.

Gaba daya hankalin benazir na akan taj, Ta kasa janye idanunta daga kallon fuskar shi, so take ya Wago su hada ido ya?i yarda, sai ma Ya maida hankalin shi akan junaid dake rungume a kirjin shi, a hankali yake shafa sumar kan shi da hannun shi, son yaron yake kamar yadda yake son Angel dinsa.


"Dan Allah kuyi min bayani wanene daddyn Azeezaty a cikin ku? ina son nasan shi" dr shureim ne ya katse masu shirun nasu.

Da hannu chief ya nuna mashi taj,
murmushi dr shureim yayi"Allah sarki, dama inaso ne in ?ara yi maku godiya, wallahi munji dadin taimakon da kukayi mana, Allah ya saka maku da alkhairi..." atare suka amsa mashi da ameen.

"Daddyn Azeezaty, Ina tayaka murna, ka ?ara gode ma Allah daya baka yarinya mai hankali irin na manya, ga kaifin basira gata da saurin shiga rai" murmushi taj yai har cikin ranshi yaji dadin yabon da shureim yayi ma angel dinsa"thank you so much," ya faWa yana mai nuna jin dadin shi.

"You should call her" chief ne ya faWa tare da mikewa Ya nufi hanyar fita daga dakin.

Curo waya yai daga aljihun kakinsa Ya kira layin Unaisah

Bayan ta Waga yace"daughter kina ina ne"?

On the other hand tace"ina adakin mu" Wagowa yai tare da kallon su anila, gaba daya hankalinsu na akanshi.

Kwantar da baby junaid yai kan sofa, yai ma anila nuna da hannu da sauri ta mike taje ta dauki baby junaid ta rungume a jikinta.

Mi?ewa taj yayi ya nufi bakin kofar dakin ya tsaya saboda baison su ji abun da zasu tattauna, muryar shi kasa kasa ya ci gaba da yi mata magana

"Auntynki tazo tana son ganinki" yana juyo sautin ihun farin cikin data saki
"Daddy, atare da baby junaid tazo"?
"Eh, harma da aunty Benazir dinki,"

"Wayyo Allahna, gani nan zuwa daddy" da sauri yace"ban gama magana ba" nutsuwa tayi tana sauraron shi

"Ina yan uwanki suke"?

"Suna a falo"

"Okay, bana son kizo da kowa, ke kaWai zaki zo..."

"Amma daddy suna son ganin baby junaid, na riga na fada masu mun hadu da aunty anila kuma sun kwallafa rai da son ganin ta"

"Look, kija baki kiyi shiru, kada ki fada masu game da zuwanta, kin riga da kinsan komai ba sai nayi maki bayani ba, idan har yaran nan suka zo zasu iya furta wata kalma da zaisa agane wani abu game daku, kuma hakan ya sa6ama dokar aikin mu, shiyasa nace kizo ke kadai, ke ma din dakyar na samu chief ya amince su ganki, Ina fata kin fahimce ni"? Shiru tayi da alama bata ji dadi ba


Fahimtar yanayin ta yasa shi sassauta muryar shi"Idan ki ka kwantar da hankalin ki, next time zasu sake dawowa ne in yaso sai su hadu da su"

ajiyar zuciya ta sauke"toh daddy, na fahimce ka, amma ya zanyi da batool? Ta riga da taji komai, namanta tana adakin, dan Allah daddy kabari in zo da ita"

shiru yayi baice mata komai ba


"Daddy, naji kayi shiru, pls ita kadai, batool ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0