Showing 120001 words to 123000 words out of 413917 words

Chapter 41 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4468

duba benazir din ba, ran Alhaji musa yai mugun 6aci yace tun da ta hana adubata bazai ?ara sanya hannu a zancen lafiyarta ba....ran kowa saida Ya 6aci da abun da layla tayi Alhaji ubaid har Ya gaji da yi mata faWa, hajiya sarah ce ta basu shawarar su yi gaggawar kaita asibiti don abinciki laifiyarta, ba su tsaya bata lokaci ba, dr shureim Ya dauko benazir da hannu biyu ya tallabota, suka fito daga falon, A mazaunin baya na motarsa ya shigar da benazir, hajiya layla ta shiga ta rungume ta a jikinta, Alhaji ubaid Ya zauna a front seat tare da shureim, yayin da hajiya sarah ta shiga motarta tare da zeenatu kusan atare motocin suka nufi Gate din gidan, WaWannan gabza gabzan security officers din suka tari gabansu har sai da suka kira Alhaji musa Ya basu iznin su barsu su fita kafin suka basu hanya
Direct suka nufi Obie International Hospital.
__________________ANEELERH

Wuraren ?arfe tara, Aneelerh ta kammala shiryawa cikin abaya tayi rolling, gaba Waya ta ?agara su karasa estate din kamar tayi fiffike haka take ji, fitowa tayi daga bedroom dinta ta nufi dakin mami, bayan tayi sallama mami ta amsa mata ta shiga daga ciki ta gaishe da ita
Kallo Waya mami tayi mata ta fahimci kamar bata jin dadi
"Aneelerh baki da lafiyane naga idanunki sunyi ja?
Kokarin danne damuwarta tayi"mami lafiyata lou, ban samu isasshen bacci jiya ba..."
"Meyasa? Kar dai ace damuwar abun da Ya faru jiya ne"? Girgiza kai tay"a'a mami na tashi yin nafila ne shiyasa banyi bacci da wuri ba..."
"Kunyi waya da su benazir din? Inataso inji ko sun isa gida lafiya"?
"Tun jiya bayan sun tafi nake ta trying layinta baya shiga, har da safen nan saida na kira ba'a Waga ba

"To Allah yasa dai Lafiya, Yanzu ina zakije ne naga kin shirya ko hakanan kikai gayu"?
"Mami wani abun al'ajabi na gani jiya awayar zahra, wanda ya daure min kai shiyasa ma na shigo don in faWa maki"
"To fa, menene ?
Zaro waya aneelerh tayi daga handbag dinta, ta lalubo layin zahra ta danna mata kira,
Bugu Waya tay picking"zahra Kin gama shiryawa?
"Eh yanzu zan fito"
"Okey Ki same ni adakin mami dan Allah kada ki bata lokaci"

Bayan ta katse wayar ta dubi mami"gata nan zuwa, abun da zan nuna maki yana awayarta" amsa mata mami tayi da toh cike da zullumin abun da zata gani

Jim kaWan zahra ta shigo dakin da sallama, Itama ta shiya cikin abaya maroon colour, ta yi rolling, hannun ta ru?e da wayarta, a bakin gadon mami ta zukunna"ina kwana mami? Kun tashi lafiya"?
"Lafiyalou zahrana, Ina abun da za'a nuna min"?
danna wayar zahra tayi bayan ta buWo hoton, ta mi?a ma mami wayar tasa hannu ta ?arba.
kura ma fuskar unaisah ido tayi kamar ta Wan ruWe can dai ta mi?e daga kishigiWan da take ta Wan kalli fuskar zahra da aneelerh kafin tace"wannan ay hoton Angel ne ko? Yaushe akai wannan hoton? Amma ya akai naga kamar ta ?ara girma anan..." at same time zahra da aneelerh suka saki murmushi saboda sunji dadin yadda mami itama ta gasgata abunda idanunta suka gane mata tunkafin ma su fada mata wa suke hasashen itace

"Mami wannan yarinyar da kike gani sunanta Unaisah, a wurin dinner din prime minister zahra ta dauko hotonta a dakin taron..." da tsantsar mamaki Mami tace"oh wai da ba Angel din bace? Me kama da itace kenan"!
"Mami itace, abunda muke hasashe kenan, zahra ki bata labarin abun da Ya faru a wurin dinner din...." gyara zama zahra tayi gaba daya ta kwashe abun da Ya faru ta sanar da mami
Lamarin yayi mugun daurewa mami kai
Aneelerh ta ?ara da cewa"yanzu haka can estate din zamuje, don mu tabbatar da abun da muke hasashe akan Yarinyar..." jinjina kai mami tayi ita kanta ta goyi bayan suje saboda kamannin Yarinyar dana Angel sun 6aci, bugu da ?ari da taji cewa Yaran tsintattune watakil su dace

"Aneelerh zaiyi wuya ace yarinyar nan ba ita bace, amma dai kuje kawai, Allah Yasa adace"

"Ameen mami, ki tayamu da addu'a Allah Yasa mu samu ganin ta cikin sau?i, saboda estate din nasu ba karamin tsarone da shi ba, In har ba wani daga cikin Ahlin su Ya gayyace ka ba to basu bari bakuwar fuska ya shiga....."
"Ita zahra ba suna mutunci da mutanan gidan ba"? Acewar mami
Zahra tace"hajiya saratu ce, nasan indai na tuntu6eta zata taimaka mana, duk da nasan mawuyacin abune tun da yaran a hannun chief owais suke da zama, Ba lallai su bari mu gan su ba.....
Shiru mami tayi kafin tace"to me zai hana ku kira Wan jaridan nan shima badaga family dinsu Yake ba kuma ay yasan da zancen 6acewar yarinyar tun da har bayanan an tura masa....."
"Har kiran layinsa nayi kwata kwata baya shiga, watakil ko Ya shiga wurin aiki ne..."
Mami ta gyaWa kai"shikenan Kuje kawai sai ku kira hajiya saratun, sannan dan Allah idan ba abaku damar shiga ba kada ku takura kanku ku dawo gida kawai inyaso sai ayiwa Wan iya magana tun da shi ya saba hulda da yan siyasa watakil ku samu hanyar shiga ta wurinsa.....
Amsa mata sukai da toh,
Kafin su mi?e mami tay hanzarin dakatar da su"ku jira mahboob Ya shigo gidan, kwara kuje da namiji"
Zama sukai har saida Mahboob Ya dawo Mami ta sanar da shi komai, ay tun da yaji zancen Unaisah ya gaza samun nutsuwarsa dama yajima da burin su gano yarinyar ba dan komai ba sai don jarin da Yake tunanin zai samu da ita shi uban son banza....

Lokacin da Motarsu ta shararo kan titin obie estate Aneelerh ta jinjinama haduwar wurin kasancewar yau ne na farko da suka fara zuwa, bata gama shan mamakin daular ba sai da Mahboob Yayi parking a gaban tankameman gate din estate din, hankalin su ba karamin tashi yai ba ganin Jami'an dake tsaron shi, sojoji da Jami'an Isod

Babu wanda Yayi gigin fitowa daga cikin motar, Mahboob Yace"mun kawo kanmu, zahra ni fa tsoron tunkararsu nake Yi Allah, Sai dai wani daga cikin ku Ya ?arasa driving din...

Yar dariya zahra tayi"bansan Iya shege mahboob dalla ka ?arasa mana sai kace ba namiji ba"?

"Indai saina tunkari wadannan masu fuskar shanun zan zama namiji to wlh na kwammace ku kirani da sunan hajara...." dariya suka sanya gaba Wayansu....

Mahboob Fa Ya dage akan bazai karasa da su ba...."

Kwatsam biyu daga cikin sojojin suka tunkaro motarsu hannayensu ruke da bindigogi tuni zufa ta fara wanke fuskar mahboob ganin Yana kokarin tada motar Yasa zahra yin saurin cafke hannunsa"haba mahboob meye haka? Wai dama haka kake da shegen tsoro? Harara Ya galla mata"nifa ba tsoronsu nake ji ba, tashin hankali ne ke banso ..." da?yar Ya ?are maganar ganin har sojojin sun ?araso gare su

Kwankwasa window glass din motar, Waya daga cikin su Yayi da kakkausar murya Ya furta"Put down the glass!" Aneelerh ce tayi karfin halin sauke glass din windown Ya zukunno da kansa Yana binsu da kallo idanunsa jawur
"Su wanene ku kuma daga Ina?
Murya na rawa zahra tace"wurin Hajiya saratu muka zo...."
"Okey, Ku kirata awaya don ba'a sanar damu zuwanku ba"
jiki na kerma ta amsa mashi da toh, da sauri zahra ta kira Layin hajiya saratu, kusan sau takwas baya shiga, Hankalinsu ba karamin tashi Yayi ba
"Bari na ?ara kiran ziyad watakil shi Ya Waga" aneeelrh ta fada yatsun hannunta na kerma ta curo waya ta kira layin ziyad tana ringin baya picking, hankalinsu duk Ya tashi
?asa ?asa da murya Aneelerh tace"mun shiga uku zahra shima bai Waga ba yanzu ya zamuyi"?
Mahboob da ya gama tsorata Yace"mu koma gida kawai shine mafita in ba haka ba wlh wannan mai fuskar shanun tsaf zai Iya bombing motar mu... cikin muryar raWa yai magana
Zahra tace"wait bari na kira zayn duk da nasan mayucin abune yayi picking..." koda Ta kira layin zayn sau uku baiyi picking ba, A kira na huWu ne Ya Waga muryarsa kamar ta mashayin giya ya furta
"Waye"? Ko sallamarta bai amsa ba
Cike da jin shakkarsa ta furta"zahra ce"
"Wace zahra"? Sarai fa Ya gane muryarta har saving layinta Yana da shi awaya
"Am..zahra wadda mommynka ta haWa ka da ita, a wurin dinner din prime minister
"Okey nagane, lafiya kika kira"?
"Munzo estate dinkune an hana mu shiga, sojojin sunce dole sai an basu izni kafin su bari mu shiga
Kafin ta kare maganar Zayn yace"kina hauka ne? Ki rasa wa zaki kira saini? Oh tun yanzu raini Ya fara shiga tsakanina dake! Uban me ma Ya kawo ku estate din?
Hatta su Aneelerh sai da sukajiyo masifar da yake zazzaga mata
"Dan Allah ka taimaka mana, bamu da wata mafita ne shiyasa na kira ka, wani abu ne mai mahimmanci Ya kawo mu...." kamar zata sanya kuka
"Look, Ku koma inda ku ka fito tun da baku da wani ala?a damu" Yana ?are maganar Ya katse kiran, Tashin sense gasu dai agaban estate an hana su shigaa
"Yanzu menene mafita? acewar Aneelerh
"Aunty aneelerh mu hakura kawai tun da kowa yaki Waga kiranmu Inyaso ko zuwa gobe sai mu dawo in ba haka ba wahala zamu sha.."
Gurgiza kai aneerlerh tayi"bana jin zan iya komawa gida, sai dai ku tafi kubarni, Ni kawai zanje na roke su su barmu mu shiga ta fada tare da bude car door din Ta fuce da sauri zahra da mahboob suka bi bayanta

Babu irin magiyar da aneelerh batay masu ba, amma suka dage akan dole sai an basu izni, a karshe ma wani fusatacce daga cikin su Ya tsawatar masu akan su koma inda suka fito

Rai a6ace Aneelerh ta dawo jikin motar ta tsaya fuskarta har ta fara zubda gumi, mahboob da zahra sai rokonta suke akan su hakura su tafi gida, amma ta kafe akan ba inda zataje, su kansu sunyi mamakin taurin kan aneelerh abun da bata ta6a yi ba......

Har mami zahra ta kira tayi mata bayanin halin da suke a ciki, tace su ba aneelerh waya su yi magana bayan ta kar6a mami tace tay hakuri su dawo gida kawai inyaso sai ayi ma uncle dan iya magana.." ta amsa mata da toh bayan sunyi sallama da mami, su zahra har sun fara sauke ajiyar zuciya a tunanin su zata koma akarshe sai cewa tayi"ita fa kawai ta amsa ma mami ne, amma fa ba inda zataje sai taga abun da ya turewa buzu naWi..." kamar su daura hannu akai suyi ihu haka suka ji, sojojin dake zirga zirga sai kallonsu sukeyi su kansu sunyi mamakin taurin kan matar da basu san wacece ita ba, don ma Taci albarkacin Kyan dake gareta ay da tuni sunyi masu korar kare daga Layin.


babban abun da Yafi damunta dayasa har ta kafe akan sai sun shiga halin Da benazir ta shiga jiya Ya Waga hankalinta da ciwon abun ta kwana jiya tasan mawucin abune in wani abu bai faru da ita ba, wanda yasa har bata neme ta ba kuma in ta kira bata samu

Su zahra har sun gaji da tsayuwa tsawon awanni uku har karfe 1 na rana ta buga, kamar zasu sanya mata kuka fuskokin kowannansu sun Yi jawur

Kiran wayane Ya shigo layin Aneelerh a hanzarce ta duba screen ganin sunan benazir ya bayyana ne Yasa tai gaggawar Waga kiran hadi da kara wayar a kunne
Muryarta har rawa take wurin furta"benazir ina kika shiga inata kira baya shiga...." cak ta tsaya da maganar jin muryar Dr shureim
"Aneelerh ba ita bace Shureim ne Ina fata kun tashi lafiya..." tun daga kan yanayin sautin muryarsa ta fuskanci babu lafiya
Gabanta na faWuwa tace"yaya shurem ina benazir din, tun Jiya bayan kun tafi nake ta jaraba kiran layin ta don inji ko kun isa gida lafiya amma ba'a Waga wa...
"Aneeelerh! Kunyi magana jiya da benazir akan mijinta ..."
Murya na rawa tace"eh.. munyi"
"Meyasa kika faWa mata abun da ya faru da su..."
"Yaya shureim wallahi banyi niyar sanar da ita ba, itace ta matsamin..." gaba daya ta faWa masa maganar da sukai da benazir har rikicewar da tayi
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..." shine abun da taji Ya furta... Su zahra dake kallon fuskar aneelerh Hankulansu duk sun tashi tunkafin ma suji me suke magana akai
"yaya shureim wani abu Ya faru ne..."
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: "Nima tunkafin naji muryarta har naji ta kwanta min araina, idan muka dawo gida ki kira min ita mu gaisa pls" a ?agare tay maganar


"Kamar kinsani, farko da muka fara waya da ita sai da tace min idan ina da ?anwa kamarta in haWata da ita, kinga shikenan sai ku ?ulla ?awance" wani irin daWi ne Ya lullu6e Zeenatu har ta fara imagining haWuwarta da yarinyar tunkafin ma su fara magana a waya abunka ga me son ?awaye,

Gaba Waya firar da suke Yi akan kunnan Dr shureim, wanda Hankalinsa ke akan driving din da Yake yi,

Basu sha wahalar gane gidan ba, ta hanyar amfani da address da Aneelerh ta basu har bakin gate din gidan suka iso, da sauri mai gadin gidan Ya buWe masu gate motar su ta kunna kai ciki,
Tunkafin Dr shureim Yayi parking Aneelerh ta fito da sauri ta nufi motar su tsabar son takai garesu har tuntube takusa yi, kafin ta ?araso Benazir tai saurin fitowa da gudun gaske ta nufi Aneelerh suka rungume juna kamar za su koma mutun Waya,

Fuskar Dr shureim Wauke da murmushi ya fito tare da zagayawa other side Win motar Ya buWe ma Zeenatu, fitowa tay daga ciki ta soma bin ko'ina na gidan da kallo kafin ta sauke idanunta kan su Benazir dake a rungume da juna,

"Yaya Shureim wannan itace ?awar Aunty Benazir Win?"
Waga mata kai yai alamar eh,

Tsawon mintuna kafin suka raba jikin su daga na juna, fuskokin su sharkaf da hawaye saboda kukan da suka sha,

Cikin shesshekar kuka Benazir tace"A.. Aneelerh! Ashe da rabon zamu ?ara ganawa da junan mu?
Itama Aneelern da muryar kuka tace "Benazir kinga yadda kika koma? Nayi maraicin ganinki, nayi kewarki aminiyata sosae, wlh bakiji dadin da nake ji ba..." da?yar suke magana saboda kukan da suke yi har lokacin,

Zeenatu sarkin tausayi har ta fara matsar ?walla, shi kanshi Dr shureim dauriya ce kawai Yake Yi, amma ba ?aramin tausayi suka bashi ba, bazai ta6a manta sha?uwar da ke atsakaninsu ba,

Fitowa Zahra tayi daga gidan karaf idanunta suka sauka akan su Dr shureim da Zeenatu Har saida taji gabanta Ya faWi ganin irin kyawun mutumin da kamalarsa da?yar ta janye idanunta daga kansu ta mayar da dubanta ga su Aneelerh,

Murmushi Zarah ta saki saboda taji daWin ganin aminnan atare,

"Ki daina kuka bana son ganin hawayen ki," Aneelerh ce tai maganar idanunta jawur Benazir tace "Idan kinaso In daina kema ki daina, taya bazanyi kuka ba Aneelerh? Nayi babban rashin da har abada bazan Iya ta6a yafewa kaina ba, laifina ne gani nake kamar nice silar da zumuncinmu ya tarwatse..." da sauri Aneelerh ta sanya hannu ta toshe mata bakinta "ki daina Waurawa kanki laifi, saboda bayin kanki bane tafiyar da kikai, kema bada son ranki aka raba ki da danginki damu kanmu ba...." lallashinta taci gaba da yi Zeenatu har ta fara gajiya da tsayuwa dama ita bata saba da wahala ba,
Tana faman jan ajiyar zuciya ta juya ta dubi su Shureim cikin sanyin murya tace"Aneelerh ga Yaya Shureim da Zeenatu Wiyar Uncle Wina" da sauri Aneelerh ta nufe su fuskarta da fara'a ta gaishe da Yaya shureim "sannunku da zuwa Yaya shureim ku shigo daga ciki" tay maganar tare da hugging Win Zeenatu tace "Yan mata sannunki kuyi ha?uri mun barku atsaye"
Kamar bata son haWa ido da shureim saboda girman shi da take gani, tun fil azal tana matu?ar jin nauyinshi kuma tana girmama shi,

"Yawwa anaeelerh mun same ku lafiya",

"Lafiyalou Yayanmu" tay maganar tare da ru?o hannun Zeenatu suka yi gaba Shureim Yabi bayansu tare da Benazir da sauri Zahra ta koma falo tana jiran su shigo don su gaisa,

Lokacin da suka shigo falon Mami da Ummi suna atsaye suna jiran shigowarsu don su tarbesu, koda Benazir tayi arba da Mami wani irin nauyinta da kunyarta ne suka kamata, Mami kuwa fara'a tasaki da sauri ta janyo Benazir ta rungumeta tana Wan bubbuga bayanta "marhabun lale ?ata, tsawon lokaci munyi kewar rashin ki" lokaci Waya Benazir taji hawaye sun sake wanke mata fuska
Muryarta da shessheka ta furta"Ma..mi " sam takasa ?arasa maganar,
"na fahimce ki basai kinyi min bayani ba, Aneelerh ta sanar dani komai, ki kwantar da hankalinki ba kuka yakamata kiyi ba, godiya yakamata mu yiwa Allah daya dawo mana dake cikin ?oshin lafiya" Mamin ta faWa tare da raba jikinsu ta sa tafin hannunta tana share mata hawaye
Kafin ta Wago ta dubi Dr shureim wanda tun da ya shigo ya sunnar da kanshi ?asa saboda nauyin Mami da yaji gani yake kamar har yanzu tabon da yai ma kansa zaisa su guje shi,

Da?yar ya motsa labbansa zai gaishe da ita Mami tayi saurin katseshi da cewa "Allah sarki Shureim kaine ka koma haka? Gaba Waya kun canzamin, Shureim Ka yada zumunci ?iri ?iri Ka guje mu ka koma Egypt ban ta6a zaton zakai mana haka ba"
Cikin sanyin murya yace"Mami ay min afuwa nima bada son raina ba nayi nesa daku, zaman ?asar ne Ya gagareni saboda abun da Ya faru, amma wallahi ko bayan da na tafi kuna araina..." bai ?are maganar ba Mami ta katse shi da cewa "bakomai Shureim, duk abun da Ya faru mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa Ya guje ma ?addararsa ba, naji dadin ganin ku cikin koshin lafiya sosae..."

"Ku mu zauna" ta faWa tare da nuna masu sofas, Bayan kowa Ya zauna Ummi da Zahra suka yi masu barka da zuwa

"Muyiwa Annabi salati" acewar Mami gaba Waya suka yi atare kafin daga bisani Mami ta dubi Zeenatu dake ta faman zare blue eyes Winta, gaba daya tarasa sukuni saboda bata saba shiga mutane ba kamar tana jin tsoron su,

"Tabarakallahu ahsanul khaliqin, ?ata wacece wannan bakuyi min bayani ba, gata dai masha Allah daga gani ba jinsin ?asar mu bane" murmushi Zeenatu tayi,

Ummi tace"kin riga ni faWa, tun da suka shigo ta tsole min ido, kamar in sace ta" dariya sukai cikin raha,

"Sunanta Zeenatu, Wiyar Uncle Wina ce" waro idanu Mami tayi haWi da jinjina kai,

"Masha Allah, sannu Zeenatu" amsa mata tay da "yawwa"

"Dan Allah ki saki jikinki,?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 ki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0