Showing 366001 words to 369000 words out of 413917 words

Chapter 123 - KURKUKUN KADDARA BOOK 3 4 HAUSA NOVELS BY BOSS BATURE.doc

27 Feb 2026

4580

zuciya Taj ya sauke kafin ya dubi Chief"ya zamuyi da sauran yaran, nasan hankalinsu ba akwance yake ba, in shirun yai yawa zasu sanya damuwa"

Ummi tace"Wazu na kira danejo awaya na ce ta kwantar masu da hankali, tace min basu da wata damuwa kawai dai suna tambayar shiru bamu koma ba"

Chief yace"bana so su sani yanzu, bansan ya zasu dauki abun ba, abun daya kamata ku dinga kiransu awaya kuna kwantar masu da hankali ta yadda bazasu fahimci wani abu ba, kada ku fada masu komai daya shafi abunda ya faru dangane da zuwanmu kai farmaki, karma su san munje just muna acikin shiri ne, har zuwa time da Unaisah zata wartsake" with respect suka amsa mashi da toh

Wayarsa ce ta fara ringing, mikewa yai tare da kallon Unaisah still idanunta na akan fuskar shi"me kike son ci? Zan sa akawo maki" girgiza ma shi kai tay"bana jin yunwa, sai dai ko zuwa anjima" Okay ya faWa tare da yi masu sallama kafin ya juya a hanzarce Ya fuce daga dakin Ya nufi part dinsa zama yai daga gefen gadonsa Ya zaro wayar daga aljihu, missed calls ya taras sunkai dari daga gurin yan uwa da abokan aikin sa.

Wani kiran ne ya kuma shigowa, saboda mahimmancin kiran yai picking tare da kara wayar a kunne Yai shiru yana sauraron shi

"A daren ranar da kuka kai farmakin mutun Waya ne daga cikin family Winka bai kwana agidan shi ba, Mahaifinka adaren ranar Ya yi fitar sirri batare da sanin kowa ba, bayan shi gaba daya sauran Uncles dinka sun kwana agidajen su.

Runtse idanun shi yayi, bakomai yake tariyowa ba, face lokacin da suke tsaka da yin FaWa Akan idonshi daya daga cikin Elders Ya murda wuyan evil giant din daya kusa tura kanshi cikin kaskon wuta, Bayan haka Ya jefa shi cikin daki Ya kulle duk da baya acikin hayyacinsa Allah ya nuna masa yaga komai da idanunsa.

Meyasa zai taimake shi shi kadai a filin yaki? Tabbas yana ji aran shi koma wanene na Jininsa ne, yayi masa hakanne don kada su kashe shi..

"Yalla6ai kayi shiru baka ce komai ba!" muryar agent zarah ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin daya lula

"Kaka na fa"?

"Agent din da muka tura donya bi diddiginsa Ya tabbar mana adaren ranar Kakanka baije ko'ina ba, yana atare da amininsa..

"Praveen Shima Yana tare da su"?
"Eh, shima a masaukinsa Ya kwana"

ajiyar zuciya ya sauke har cikin ranshi yaji dadi da baba obie bai fita adaren ranar ba dakuwa ya shiga cikin wadanda Yake zargi.

"sannu da kokari agent, Aikinka Yana kyau, ka cigaba da sanya ido akansu..." sallama sukayi da junan su, kurawa screen din wayar ido yayi, bakomai idanunsa ke hasko mashi ba face fuskar Mahaifinsa Yana jin wata irin karaya da faduwar gaba da ya ke ji.

Shiru yayi jimm na Wan wani lokaci yana nazarin maganar sa, kafin ya danna ma baba obie video cos yaga missed calls dinsa.

Kafin yai picking ya dauko hanky ya rufe bandage din dake akan goshin shi don kada yaga raunin dayaji gudun kada ya tayar masa da Hankali.

Bayan yayi picking, ya nutsu Yana kallonsa ta cikin screen din wayar, Yana daga kwance kan wani hadadden royal bed da ke a wani hamsha?in bedroom wanda ya gaji da haduwar kayan alatu, jikinsa sanye da jallabiya.


"Meya hana ka yin bacci"? Ya fada tare da kallon clock din dakinsa Karfe tara na dare.

Yana dariya yace"mutumina mana, kasan shi da surutu kamar aku, gayanan ya tsare ni da fira.." ya faWa tare da kara mashi wayar saitin fuskar Jan kunne fuskarsa dauke da murmushi cikin harshen turanci yace

"owais bani na hana shi bacci ba, kai shaidane ban cika surutu ba, ya isheni da firar yan mata, tsofe tsofe da shi ko kunya bayaji, yakamata ka aurar da kakan nan naka, yana bukatar mace" girgiza kai chief owais yayi, lamarin su na bashi nishadi in suka fara zolayar juna kamar matasan samari.

"Jikalle, wlh karya yake yi maka, kai kasan mace bata agabana, so yake ya ?ala min sharri, shi ne yake bukatar auren, In ka tashi aurar dani ka hada da shi ka auran da mu mu duka"

6a66akewa sukayi da dariya kamar zasu fasa mashi kunnanshi.

Murmushi chief Owais ya saki yana kallon su kamar ya samu tv, ba karamin nishadi suka sanya shi ba.

"Kaima ka shirya, da zarar na dawo gobe In Allah yakaimu, zamu fara shirye shiryen auranka don nagaji da kiwon tazurai a estate Wina" ya fada da zolaya, yar dariya chief yai tare da sunnar da kan shi ?asa

Jan kunne Yace"Owais Ya fara kula mata ne"? Ya tambaya yana kallon baba obie

"Tun yaushe? Kai kake mashi kallon Ustaz, Yaron fa Ya girma aure yake so, Mata har biyu" baki asake jan kunne yace"Serious"?


"Kwarai kuwa, nan bada jimawa ba za'a shafa fitihar auransu, first wife din shi will be Nazli and his second wife umm..I forgot her name..."

su6ul da baka yayi wurin furta Unaisah, gaba Waya suka sa dariya, Jan kunne yace"ah lallai he really wants to, yaro ya gaji da tazuranci, amma owais mata har biyu a lokaci Waya kamar wani hariji ko dai kakanka da mace Waya ya fara..."

Wata irin Kunya ce ta lullu6e Chief Owais, ji yai kamar ya kashe wayar.

"Meye naka aciki? Kai dai baka ?i yin auran ba? Ka zauna nan, babu kai ba samun ni'imar da ake samu a aure, duk wata garabasa ta lada ta wuce ka..." bai kare maganar ba, Jan kunne Ya rarumi pillow Ya buga mashi akai, kokayi suka kamayi kamar wasu kananun Yara sam sun manta da Owais yana kallon su, yayi shiru tamkar ya samu tv, can yaji Wuff kiran ya katse..

Badan Ya gaji da kallonsu ba.

*>?@?ANEELERH>?@?*

Around ?arfe shabiyu na dare, Aneelerh tana tsaka da yin bacci sambatun da baby junaid ya ke yi cikin magagin bacci ne yayi silar farkawar ta sautin muryarshi da shesshekar kuka haWi da razana Yake fadin"mom...mmy dodo...dodon daya kashe Ana, zai cinyeni, mommy mu gudu!! mu gudu!! mu ma zai kashe mu!!...wayyo mommy...Cikin duhu ta kai hannu ta kunna bedside Lamp Haske Ya kawo fuskarta a yamutse ta dubi junaid, gumi ta gani yana tsastsafo mashi akan fuskarshi, jikin shi kerma yake kamar wanda sanyi ya kama, kanga kunnanta tayi saitin la66ansa ta kasa kunne tana sauraron sambatun nashi.

Lamarin ya fara damunta, kwanakin nan junaid baya iya bacci batare dayayi mafarki ba, kuma mafarkin nasa duk akan dodon daya kashe Ana ne, duk da bata dauki maganar tashi serious ba, amma ta fara kokwanto anya abunda ya gani ba gaske ba ne? in har karya yayi mata meyasa zai dinga mafarki yana razanaS'W'

Kirjin shi ta shafa da tafin hannunta cikin disasshiyar murya ta wanda bacci bai ishe shi ba, ta furta"My baby Boy, wake up,..junaid Wina Yaron kirki"

firgigit ya farka arazane ya ware manyan idanunsa, ganin yadda ya tsoratane yasa tace"junaid, Nice fa" wurga eye balls dinsa yayi akanta, Yana ganin mommynsa Ya fada kan kirjinta ya fashe da kuka yana fadin"mommy nidai tsolo nake ji Allah, dodon daya kashe Ana Yana acikin gidan nan, Nima Zai kashe ni, Kema zai kashe ki sannan ya kashe kowa ba.."

lallashin shi ta shiga yi"in sha Allah junaid, Bazai ta6a cutar dakai ba, saboda Allah Yana atare dakai..."

bata kare maganar ba, cikin shesshekar kuka yace"Ni mommy tsolo nake ji, Mu gudu mu bar gidan.."


"A'a junaid, ba inda zamuje, zan cigaba dayi maka addu'a Allah zai kare mu, in banda abunka yanzu idan muka gudu Ina zamu dosa junaid"?

"Gidansu Angel mana.." ya faWa yana cigaba da sharar kwalla...

"Shikenan, kabari gobe zan kira daddyn Angel din Yazo ya dauke ka, hakan yayi maka" amsa mata yayi Eh, ta fada masa hakanne donta kwantar masa da hankalinsa ko ta samu ya runtsa.

"Mu koma mu kwanta"

Make mata kafada yai "Ni Tea zan sha" ya fada yana faman zumbura baki.

"Okay, ka jira ni inje in hada maka" ma?e mata kafada yayi"Allah sai dai muje atare kitchen din"

"Pls junaid, bana son fita dakai, da tsakar dare, Ka jira ni kawai"

Kamar zai fashe mata da kuka yace"toy ai in kika tafi dodon zaizo ya cinye ni" murmushi tadan saki, kiri kiri Ya saka mata rigima Ya?i bari ta bar shi.

Dabarace ta fado mata, waya ta dauko ta kunna masa kallo ta mika mashi, tun da ya kar6i wayar ya shagala Yana ta yan kallace kallacen shi, har ta fuce daga dakin bai ma sani ba..

Lokacin data fito babu kowa, kasancewar dare ne duk sunyi bacci, cikin nutsuwa take tafiya yayin da a zuciyarta take ta tunanin Taj da Unaisah ta damu da rashin samun su awaya, fatanta Allah yasa lafiya.

harta kusa shiga kitchen sai kuma taWan dakata idanunta akan hanyar dakin ANA bakomai take tariyo ba face irin zaman amanar da su ka yi da juna, cikin sanyin murya ta furta"Nayi babban rashi Ana, meyasa kika tafi kika barni? Idan laifi nayi maki meyasa baki fadamin ba? In wani abu ke damunki meyasa bazaki sanar dani ba? Kin tafi kin barni da tunanin meya faru dake, nidai nasan ban ta6a cutar dake ba, Allah shine shaida ta Ana, ni yanzu inama zan samu yar aiki mai rukon amana Irin ki"?

ita kadai tsaye tana ta yan tunane tunanenta, zuciyarta ce ta raya mata me zai hana ta je dakinta ta Wan ?ara bincikawa watakail ko ta ajiye mata wasiya kamar yadda mafi akasari in irin haka ya faru zaga mutun ya aje wasiya mai dauke da abunda ya same shi.

sam ta manta da baby junaid, ta wuce ta nufi Wakin Ana, murWa key Win ?ofar tayi ta tura ta, tasakai ta shiga ciki duhu ne ya mamaye idanunta da lalube ta gano switch ta kunna kwan Wakin haske Ya gauraye ko'ina, bin dakin tayi da kallo since last da abun ya faru su zahra suka gyara shi wani bai ?ara shiga Wakin ba.

bincike ta fara yi adakin ta bubbuWe drawer chest, tarkacen dake aciki ta dudduba bata samu abunda take nema ba, maida drawer chest din tayi, ta koma gaban closet Win Ana, gaba daya ta zazzago da kayan ciki ta dinga bincika aljihunan rigunanta da wandunanta, Ba karamar wahala ta ci ba, kafin kace me tuni ta hada gumi akan fuskarta, babu abunda bata duba ba amma bata samu komai ba, a gajiye ta nufi kofar dakin zata fuce kwatsam brain dinta ta fara tariyo mata wata magana da junaid ya ta6a fada mata.

A wata rana da ta tambaye shi waya koya mashi boye abu acikin pillow case saboda ita tasan ba dabi'arta bace yin hakan, Yace mata Ai a gurin Ana ya gani in ta samu ?an kuWin ta nan take sa?e su har tayi dariya tace Allah ya shiryaka junaid bansan a ina ka koyi sanyawa mutun ido ba nidai halina bane.

tuna wannan maganar yasa tay wani irin kakkwaran juya ta nufi gadon Ana, ta janyo pillows ta zuge zip Winsu ta dudduba bata ga komai ba, dafe kai tay da hannu Waya fuskarta dauke da matsananciyar damuwa take kallon soson pillows din data zazzago kan mattress din Unexpectedly idanunta suka hango mata kamar wani abu baki a cikin Soson Pillow Waya.

janyo shi tayi tasa hannu ta farke sosan kwatsam Tayi arba da wayar Ana abun mamaki abun al'ajabi yatsun hannunta har kerma sukeyi gurin daukar wayar arude take kallonta, daga gani Cusa wayar akayi ta karfi cikin sosan, ashe duk neman da sukeyi ma wayar tana a gidan, Kenan Ina Ana take? Wanene Ya saka wayar acikin rigar pillow.

power button Win wayar ta danna bata kawo ba, hakan yasa tayi tunanin ko babu chargy ne.

saukowa tayi daga kan gadon ta tura wayar cikin aljihun wandon baccin ta, kafin ta kashe switch din dakin, saida ta fito ta tuna da tea din da zata hada ma Junaid, cikin sauri ta shiga kitchen zuciyarta cike fal da tunanin Ana, cikin yan mintuna ta kammala hada masa tea din ta fito ta nufi Bedroom dinta.

tana shiga ta iske junaid kwance ga wayarta a gefe daya, da alama yana tsaka da kallon baccin yaci karfin shi.

akan table ta ajiye cup din, ta sanya wayar Ana a chargy, Mikewa tayi ta dinga safa da marya atsakar dakin Allah Allah take wayar ta hau koda percent goma ne saboda tayi matukar kagara da taga menene acikin wayar..

jefi jefi take wurga eye balls dinta akan wall clock din dakin kusan karfe biyu na dare, ga bacci dake nema yaci karfinta amma ahaka ta tirje don tana ji aranta akwai wani abu atattare da wayar Ana..."



*DAGA AL?ALAMIN BOSS BATURE=?%?=?%?=?%?
'?*


*Ga me bukatar karanta littafin kurkukun kaddara, 500 ne za'a tura Via Opay, 8103884440 Hafsat Bature Muhammad, shaidar biya za'a tura ta whatsapp, 08169856268 ko 08103884440*
[10/1, 18:58] +234 903 893 6460: ______________________________=?%?=???



Wani irin burki suka ci, ganin babu khala adakin ta, abun daya jefa su arudani gaba Waya dakin nata a hargitse yake, harta gadonta Ya jirkice, tukwanan furannin dake a dakin duk an faffasasu, Ga jinin dayake malale kasa.. YA ILAHIW'W'


Alkalamina bazai Iya misalta tashin hankalin da suka shiga ba.

Sun rasa gane meya faru da tsohuwa khala? Jinin wanene suka gani a kasa? babban abun da suke ma zullumi Fursinonin da suka turo akawo gurin ta, basu san awani hali suke ciki ba, fargabansu kada ace jinin fursinonin ne!

badan zuciyar Imani ba da tuni Chief Ya hadiyi zuciya ya mutu saboda bakin cikin da Elders suka kunsa masu.

La66ansa na kerma ya furta"La'haula walaqu wata Illah Billa, Inna lillahi wa'inna ilaihirraji'un....." wani irin zafi jikinshi ya dauka rau...

Cike da ruWu Commender James Ya furta"ni fa bangane ba, meke faruwa ne? Ina prisoners din da muka kubutar? Ina tsohuwar take? Jinin menene wannan"? ya faWa yana nuna jinin dake malale kasa...

Yawu mai Waci thompson Ya hadiya ga radadi daya addabe shi, cikin sanyin murya yace"bana fata abunda nake hasashe ya zamana gaskiya, Zai iya yiwuwa Matsafan ne suka kawo mata farmaki watakil sun gano hada sa hannunta gurin kawo masu farmaki..."

bai ?are maganar ba, Chief yai hanzarin katse shi ta hanyar girgiza kai yana fitar da numfashi mai Wumi ya furta"in kuwa hakane Elders sun kashe ni, sun gama dani..."

kamar zautacce ya dinga nanatawa


Kanshine ya fara juya mashi wata irin juwace ta fara kokarin daukar shi da sauri Ya dafe bangon dake abayan shi, Yana huci hadi da jan numfashi kamar mayunwacin zaki..

"Ba zamu bar Nigeria ba, har sainaga bayan Elders, dole su fuskanci mummunan hukunci mai tsanani"

rai a6ace commender James ya fada...


"Me yakamata muyi yanzu? Bana bukatar mu 6ata lokaci gurin nemo su"! Commender haroon ne ya fada...

Captain lewis Yace"Where should we begin searching for them? Do you think they're still in this prison?"


Dukansu fa arauna ce suke, gabban jikinsu duk sun raunata ga yunwa da bacci dole su jigata tun dare ake gabzawa har gari ya waye batare da sanin su ba, amma saboda karfin hali irin na soja, burinsu su karasa aikin da suka dauko bata kansu suke ba, dare guda ba bacci sai zallar tashin hankali...."

"I don't think they're here, We should return to Nigeria and devise a new plan, we've lost our soldiers, and we're too weak to fight them now. We need to know what's happening with the soldiers we left outside"

(bana tunani suna nan, ni dai shawarar da zan bamu shine mu koma Nigeria, In yaso saimu sake sabon shiri, tunda yanzu duk mun rasa sojojin mu, Mu kanmu a raunace muke bamu da karfin da zamu iya yin faWa da su a halin yanzu" acewar lieutanant Jackson)

Numfasawa Chief yayi"in sha Allah, karshensu ne yazo tun da har mu ka yi nasarar shugowa kurkukun nan, kuma mun yi masu barnar da ba zasu iya gyarata ba, nasan sun tsoratane shiyasa suka gudu, hakan ma wata nasarace...."

ya faWa yana jan numfashi kafin Ya Waura da cewa"Zaku Iya tafiya amma ni bazan Iya barin kurkukun nan ba, saboda Wan uwana Danish, zan jira har zuwa lokacin da Allah zai fiddo dashi daga cikin rijiyar zamu dawo tare da shi..."

ya faWa idanun shi cike tab da kwalla, tsananin tausayin shi ne Ya kamasu, commender james Ya dafa kafadarshi Cikin kwantar da murya yace"ka yi hakuri Chief, bana tunanin zai rayu acikin rijiyar nan, ka daure kayi hakuri ka lallashi zuciyar ka, Mu tafi kawai..."


Zafafan hawayene suka wanke fuskar sa, wlh kallonsu kawai yakeyi yasan bazasu ta6a jin irin kunar da zuciyarshi keyi mashi ba.

cikin karyayyar murya ya furta"Bazan Iya tafiya ba, tayama zan tafi in bar Danish acikin rijiya tare da wannan Shaidanin? What if he kills him?"


Girgiza kai yai"Idan Nayi haka banyi mashi adalci ba, saboda mu rayu ya jefa kanshi cikin haWari, sai kuma mu tafi mu barshi?

Dakyar ya kare maganar, daurewa kawai yakeyi, cike da tausayinshi su ke kallon shi, su kansu hawayen ne cike tab da idanunsu.

"Abun da nakeso ka fahimta, Danish Ya sadaukar da kan shine don mu rayu! Idan har muka bari muka rasa ranmu hakan na nufin burin shi bai cika ba, pls ka jure ka rungumi kaddara" acewar Commender Haroon.

Girgiza kai yai"ba zaku fahimce ni ba! But Danish deserves to live, wai shi mema Ya mora a rayuwarsa ta duniyar nan? Ya zo awahalce yanzu kuma kuna nufin in barshi Ya mutu? Shikenan fa ya mutu baisan iyayen shi ba, Bai ta6a jin dumin mahaifiyarshi ba, Baisan menene dadin iyaye ba, idan Uncle hateem Ya kirani ya tambayi ina yaronsa wata amsa zan bashi? kai Ina, wlh bazai yiwu ba dole naje na ceto rayuwar sa koda zan rasa rainane..."

da alama chief owais Ya fara zaucewa sai sambatu yakeyi masu marasa kan gado, kafin su gama yanke shawara da zuciyarsu chief yai hanzari juyawa da gudu Ya fuce daga dakin da niyar ya koma gurin rijiyar, da gudun gaske suka bi bayan shi cike da tashin hankali suke ?wala mashi kira haWi dayi mashi magiya akan ya tsaya kada yaje amma ko waiwayen su baiyi ba, saboda Idanun shi sun makance Danish kawai ya ke son gani, bawan Allah kusan sau hudu yanayin tuntu6e Ya fadi kasa ahaka zai mike Ya cigaba da gudu, Yana kokarin shan wata kwana kwatsam ba zato ba

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login
google.com, pub-9213700357025247, DIRECT, f08c47fec0942fa0